Showing 81001 words to 84000 words out of 289308 words

Chapter 28 - NIHAAD-complete by KHALISAT HAIDAR

04 Jul 2024

63686

seconds ya daga kai ya kalleta yace "Ya jikin Mumy?" Cikin sanyin murya tace "Alhamdulillah Ibrahim, ya gida?" Ya sauke kansa yace "Lafiya lau, Allah Ubangiji ya kara Lafiya" Tace "Ameen Nagode" Bai kuma cewa komai ba, Hajiya Zara ta mike ta fita daga parlon, bayan few minutes Mumy tace "Kayi hakuri Ibrahim, an cuceka an hadaka aure da warce bata cacanceka ba, nasan baka da yanda xaka yi ne kuma baxa ka iya k'in amsan tayinta da mahaifinta yayi maka ba...." Da sauri yace "Aa Mumy, Allah ne ya tsara haka, kuma muna fatan Allahn yasa hakan shine mafi alkhairi" Hawaye na sauka idon Mumy tace "Ni kam bani da abinda xan ce maka sai dai in baka hakuri akan abinda Alhaji ya maka, sannan ni baxan ce kayi hakuri da Nihad ba, idan kaga baxa ka iya ba ko xaka cutu ina me goya maka bayan ka saketa kawai ta dawo gida...." Cike da karfin hali Khalil yace "In sha Allah baxa ayi haka ba Mumy" Mumy ta share idonta bata kuma cewa komai ba, Wani duniyar tunani khalil ya fada gaba daya jikinsa yayi sanyi, he couldn't even think straight, kiran sallahn magrib da ake ne yasa ya dago kai ya kalli Mumy ya ga kallonsa take, a hankali yace "Xan je masallaci Mumy, Allah ya kara lafiya" Tace "Ameen Ibrahim nagode" Tashi yayi a hankali ya fita daga parlon, Umma ya tarar a main parlor ta masa wani kallo sai kuma ta ja tsaki tayi hanyar kitchen, ya bi ta da ido kawai. Bayan an idar da sallan magrib tare suka shigo gidan da Abba har xuwa parlonsa, Khalil ya xauna ya gaida Abba da ladabi, Abba ya amsa yace "Ya gidan?" Yace "Alhamdulillah" Abba yace "Ya kamata xuwa gobe ku shirya ka tafi da ita can garinku ta gaida iyayenka, bayan kwana biyu sai ku dawo" Khalil ya ?an yi jim, sai kuma ya dago ya kalli Abba yace "Toh in sha Allah Alhaji, Allah ya kai mu goben" Abba yace "Ameen, farooq ya zo min da wani batu jiya amma sai kun dawo dai" Khalil yace "Toh Alhaji, nagode" Abba ya ciro dubu dari ya mika masa yace "Ka yi full tank, sannan kayi ma iyayenka tsaraba da sauran" Khalil ya sa hannu biyu ya amsa yace "Toh Allah ya saka da alkhairi Alhaji" Abba yace "Ameen, Allah ya maka albarka" Khalil ya amsa da "Ameen" a tare suka fito main parlor da Abba, Umma ta fito daga kitchen kenan ganinsa da Abba tace "Aa Ibrahim har xa ka tafi, bari to ga abinci ka kai ma Nihad tunda an gama" Ya kalleta yace "Toh" Komawa kitchen tayi da sauri, Abba dai ya zauna parlon har sannan kana ganinsa xaka san yana cikin damuwa, dake xuciyarsa kawai yake yana ma Nihad wasu abubuwan as form of punishment amma shi yasan sonta a jininsa yake, but he can't help it, tayi disappointing dinsa sannan ta xubar masa da mutunci a idon duniya, Umma ta cika warmer da abinci, sannan ga wani warmer din daban na kaza ta fito parlor, sai da ta bubbude warmer din tana kallon khalil cike da damuwa tace "Don Allah idan ka je ka lallabata ta ci abincin nan, duk ta rame ta lalace wallahi, Shekaranjiya da naje ma da ya na samu ta ci abincin, yanxu kam ban san halin da take ciki ba baiwar Allah, wa yasani ma ko bata cin komai" Shi dai Abba bai ce komai ba, khalil kuwa banda kallonta babu abinda yake, Abba ya mike yace "Ka jirani Ibrahim" Khalil yace "Toh Abba" Ba a dau lkci ba sai ga shi ya dawo da dubu talatin ya mika ma Khalil yace "Ka siya mata carton din maltina da na madaran gwangwani" Ta gefen ido Umma ke ta kallon Abba, Khalil ya amsa yace "Toh In sha Allah Abba" Abba yace "Sai da safe, Allah ya tsare" Juyawa Umma tayi ta shige kitchen ta tsaya jikin cabinet kamar me nazari. Khalil na isa gida sai da yayi isha a masallacin dake layin sannan ya shiga gida da motar yayi parking, bayan ya kulle gate din ya dawo ya fiddo abincin daga cikin mota ya kai parlor ya sake fitowa ya kai maltina da madara parlon ya ajiye sannan ya kulle gidan, xaunawa yayi saman kujera ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido, da yasan haka abubuwa xa su kasance masa da bai yarda ya fara shigowa garin kano ba, where will he even start this amendment from?? Babu warce ta tsaya masa a rai sai Mahaifiyarsa, this seriously isn't going to be easy, Mikewa yayi daga karshe ya nufi dakinsa yana tafiya a hankali, har ya bude kofar sai kuma ya fasa shiga, ya dawo ya bude dakinta, zaune ya ganta a kasa idonta yayi bulu bulu alamar tayi kukan gaske yau, ya tabe baki ya kulle kofar ya koma parlor kawai yayi xamansa, tashi Nihad tayi ta bi bayansa, ta tsaya bayan kujera tana shesshekar kuka..., ya ?an daga kai ya kalleta kamar bazai ce komai ba sai kuma yace "Da bashi ne?" Wani bakin ciki ya rufeta a fusace tace "Ban sani ba, ka zata kai ka isa ka dinga punishing dina? Waya biyu aka kawo min gidan nan ka salwantar min da su, toh wallahi zaka sha mamakin abinda xai faru idan baka bani wayata ba" Mikewa yayi ya bar mata parlon ya shige dakinsa ya kulle, kuka kawai take kamar ranta xai fita, babban tashin hankalinta shine Aliyu da xai yi ta kiranta ya ji a kashe, yanxu babu ta inda xata yi ta iya kiransa, da ma baya kulle gate ne ko makota ita sai ta shiga don ta kira Aliyu, amma ko daxu da xai fita kulleta yayi ta ciki, ko bin ta kan warmers din abincin dake parlon bata yi ba ta koma daki ta dinga kuka kamar ranta zai fita, har kusan karfe biyun dare Nihad bata yi bacci ba, abun duniya ya taru yayi mata yawa, last week fa warhaka tana baccinta peacefully a saman gadonta, tashi tayi a hankali ta goge idonta ta nufi kofa, a hankali ta bude kofar dakin nata ta fito, taga ya kashe duk wutan gidan, ko ina yayi duhu, tana lalubawa ta tafi hanyar dakinsa ta kai hannu handle din kofar ta murda a hankali ta bude ta shiga dakin, nan ma dai ya kashe fitilar, sai da ta fara tattaba socket din dakin cikin duhun ko xata ga karamar wayarsa a jiki taga babu, cikin sanda ta nufi gadon dakin ta durkusa, hannu ta kai xata laluba kan gadon taji hannunta saman broad haired chest dinsa, zaro ido tayi a mugun tsorace xata mike ta gudu ya fixgota ta fado saman gadon daga gefensa, yayi kneeling dai dai inda take har tana jiyo respiration dinsa, yana kallonta cikin duhun kafin yace komai jikinta na rawa tace "Wayyo na shiga uku, wallahi torchlight nake nema xan je in sha ruwa a kitchen...."




*Littafin Nihad dari biyar ne, ki fita hakkina kafin ki karanta min littafi hankalinki kwance*

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence via????


07087865788Kunna wutan dakin Khalil yayi ya koma gefen gadon ya zauna fuskarsa daure yace "Ohk, dauki torchlight din ki fita" Har sannan gabanta bai daina faduwa ba, a hankali ta dawo edge din gadon tana satan kallonsa, ba tare da ya kalleta ba yace "Dauki ki fita nace" Ta sauke ?afafuwanta kasa a hankali tana kallon karamar wayarsa da ta hango gefen pillow, Ya jefa mata wani mugun kallo yace "Ko bayan shi da wani abun da kike so ne?" Ta ?an turo baki tace "Ga can torchlight din da xan ara" Ya kalli inda take nuna masa, sai kuma yace "Ohk" dauko wayar tasa yayi ya mika mata yana kallonta, a hankali ta kai hannu xata amsa, da karfi ya buge mata hannu da wayar, da sauri ta janye hannunta ta bude baki tana kallonsa tana yarfe hannun, ya mike ya dau shirt dinsa ya saka sannan ya nufi kofa ya bude mata da kyau, fuska daure yace "Zo ki fita" Ta fashe da kuka tace "Shine har sai ka kwala min waya a hannuna? Sai kace kai baka shigo min daki idan ina bacci" Cikin kakkausar murya yace "Zo ki fita nace" ganin babu alamar wasa tattare da shi ta mike ta nufi kofar hawaye cike idonta, tana fita ta juyo ta kallesa tace "Ban yafe buge min hannu da kayi da shegen wayarka ba, don ma ka samu xa a ari torchlight din shegen wayar" Yi yayi kamar xai bi ta, ta ruga ta shige dakinta ta kulle kofar da sauri tana maida numfashi. Washegari da yamma bayan Khalil ya gama shiryawa yanda xai je ya sanar ma Nihad ta shirya xa su yi tafiya ne babban aiki a wajensa, tun safe ya fice gidan don kawai ya daina ganinta, ko awa daya bai yi da dawowa ba kuma bai ji motsinta ba bai kuma duba dakin nata ba, daga karshe kawai yayi dialing number Nihal tana dagawa ta gaishesa ya amsa yace "Ya makaranta?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Kin dawo ne?" Tace "Aa ya farooq yace min yana hanya" Khalil yace "Toh Allah ya kawo ku lafiya" Tace "Ameen" Shafa kansa yayi yace "Dama so nake ki sanar ma er uwarki ta shirya kayanta kala uku xa mu je can gida, kawai haka xa ki ce mata" A hankali Nihal tace "Baxa ka iya gaya mata ba kai kenan?" A takaice yace "Ehh" Tace "Toh Shkkn, ka bata wayar" yace "Zan kai mata yanzu" Nihal tace "Ohk" mikewa yayi ya tafi dakin Nihad ya bude kofar dakin, tana tsaye jikin window abun duniya ya tarar mata, har ta gaji da kuka, tun da garin Allah ya waye ruwa kawai take ta sha don ta gaji da cin indomie gashi babu kayan miya a gidan, yunwa take ji sosai, jin ya bude mata kofa ta juya a fusace tace "Malam ka daina shigo min daki kanka tsaye kamar wata matarka, idan ma wani abun ne baxa ka kwankwasa ka jira in fito ba?? Balle ma ni bana son kana min magana a gidan nan har abada" Kallonta kawai yake, ta murguda baki ta ci gaba da kallon tsuntsayen da take kallo ta window, khalil ya sa handsfree a wayar hannunsa yana daga inda yake tsaye yace "Gashi ki gaya mata" Nihal tace "Hello Nihad" Nihad ta wani tamke fuska tace "Menene??" Nihal tace "Abba yace ki shirya kayanki xa ku je can gidan" Nihad ta buda ido sosai tace "Don Allah da gaske?" Nihal tace "Ehh" Wani farin ciki ne ya rufeta, cike da murna tace "Ai kayana a hade suke ban ciro su a akwatin ba" Khalil bai bari Nihal tace komai ba ya katse wayar ya juya ya fita, kan kace me Nihad ta gama rurrufe akwatunanta ta ja su ta kai parlor gaba daya, ji take kamar mafarki wai xata koma gida, she sooo happy, da ido Khalil ya dinga bin ta, haka ta ja akwatunan duk da nauyinsu har gun mota sannan ta koma ta dauko handbag dinta, xata fita khalil dake ta bin ta da kallo yace "Duk wa enan kayan ina xa ki kai su?" Tayi masa wani shegen kallo tace "Ohk da so kayi in bar maka wasu ka dauka kaje ka siyar ka samu na xubawa a aljihu? To baxa a bari ba" tana gama fadin haka ta fice ta tafi jikin mota tana jiransa, bayan few minutes sai ga shi ya fito, cike da gadara tace "Bude min booth Malam" Ba musu ya bude mata booth din, ta daddage ta shigar da akwatunanta booth da duk karfin da Allah ya bata, back seat ta bude ta shiga ta zauna farin ciki fal ranta, ta lumshe ido tare da sauke wani ajiyar xuciya, at last.... Ganin ya ki tada motar ta ki ce masa komai, don ita kam baxata biyesa ba tunda dai ta samu xata koma gida, bayan few minutes ya sauka motar yaje ya bude gate, lumshe ido Nihad tayi bayan ya ja motar sun bar compound din, ya sauka ya kulle gidan sannan ya dawo cikin motar, Ta madubi yake ta kallonta kai kana ganinta kasan she is over happy, tun Nihad na tunanin traffic yake kaucewa ganin hanyar da suke ta bi har dai taga sun dau hanyar da baxae ta6a kai ka gidansu ba, ta dake tace "Malam mance hanyar gidan namu kayi ne ko kuma Shaye shaye ka fara? Ba ga can hanyar da xaka bi ba" Banza yayi mata, a mugun fusace tace "Tunda kai ba kurma bane nasan kana ji na, ka gaya min ta ina hanyar nan da muke bi xai kai mu gida??" Nan ma yaki tanka ta, mamaki ne ya cika Nihad ta dinga bin hanyar da kallo, to ina xai kai ta, bata kuma ce masa komai ba tana ta kallon ikon Allah, bayan tafiyar kusan minti arba'in taga sun shigo wani karamin gari da xa a iya kiransa da kauye, she was more than shock, wanda hakan yasa ta kasa ce masa komai, sae kallonsa take baki bude, a wani gida da aka xagaye da katangar kasa yayi parking bayan sun lula can cikin garin, ya kashe motar, sannan ya bude ya sauka, duk motar tayi butu butu da jan kasa, ga yara da ke ta bin motar tun shigowarsu karamin garin, har Khalil yayi parking, yaran duk suka kewaye motar suna murnan ganin mota, Haka Nihad ta dinga kallon inda suke with shock, khalil ya bude side dinta yana mata kallon cikin ido yace "Sauko" Ta fashe da wani matsanancin kuka tace "In sauko in yi me?? Wallahi baxan sauko ba" Duk da dariyar da ta basa haka ya dake ya hade rai yace "Baxa ki sauko ba??" Cikin kuka tace "Ehh, ina ne nan din da ka kawo ni da kake cewa in sauko?" A takaice yace "Garin mu!!! don ki tabbatar mu ma muna da gida, dolenki kuma ki sauko ki gaida iyayena, sannan adadin kayan da kika kwaso adadin kwanakin da xa mu yi a garin nan kenan" Ta fashe da kuka hankali tashe tace "Na shiga uku na lalace...." Ko sauraronta bai kuma yi ba ya xaga bayan booth ya hau sauke akwatunanta, ta gwale ido ganin yayi hanyar shiga cikin gidan da shi, kuka take kamar ranta xai fita tana cewa ta shiga uku ta lalace, tun da aka haifeta ita kam sai dai taga irin wajajen nan a Tv, dama da gaske akwai irin garin nan a reality?? Ba a dau lokaci ba sai gashi ya fito da wata dattijuwa tana washe baki ta taho ba ko takalmi a kafarta tana cewa "Lale lale" Sake baki Nihad tayi tana kallonta a tsorace, matar ta karaso kusa da mota tace "Sannu da xuwa, lale lale" Nihad ta hadiye wani abu da kyar tace "Ina yini?" Khalil dake tsaye gefen matan yace "Sauko" Da kyar tayi karfin halin saukowa daga motar, kana ganinta kasan a tsorace take, matar tace "Bismillah mu shiga ciki, lale" Tana jan kafa ta bi matar xuwa cikin gidan, Khalil ya bi ta da kallo yana wani side smile, sai da Nihad ta duka kafin ta iya shiga cikin gidan, nan taga hut a jere kusan hudu a karamin tsakar gidan, lkci daya tsikar jikinta ya dinga tashi taji ta fara jin sanyi kamar xaxxabi xae rufeta, Matar ta shiga wani hut din tace "Bismillah shigo ciki...." Nan ma sai da Nihad ta duka sosai kafin ta iya shiga hut din, banda karnin nono babu abinda hut din yake, sae da ta kara gwalo ido don ta tabbatar kasa ne kwance a dakin kamar waje, sai gadon kara an shimfida wani yamutsatsen zanin gado a kai, daga can gefe kuma kwarya ne sun kusa goma an jera, Matar ta dinga nuna ma Nihad gefen gadon karan wai ta xauna, cike da karfin hali Nihad ta xauna tana kokarin ganin bata fashe da kukan dake cin ta ba, dattijuwar ta fita daga dakin tana cewa "Bari a kawo maki ruwa" Wani hawaye ya xubo idon Nihad a hankali tace "Na shiga uku na lalace" da sauri ta goge idonta ganin wasu mata sanye da kaya irin na fulani sun tsaya bakin kofa suna gaisheta da fara'a, Da kyar tayi karfin halin gyada tana kirkiran murmushi tace "Nagode" Ai kuwa da wannan set din matan sun tafi sai wasu set din sun taho duk ana zuwa yi mata lale, sai ga dattijuwar da kwanon sha dauke da ruwa ta ajiye ma Nihad a kasa, Nihad ta dinga kallon ruwan ganin particles na ta swimming a ruwan, tun da aka haifeta bata ta6a ganin irin kwanon shan da aka xubo mata ruwan ba a ciki gashi duk yayi tsatsa, wata mata ce ta shigo rike da kwarya da nono a ciki, ta ajiye mata da wani karamin kwaryar me dauke da fura, tace "Sai ki dama hurar iya yanda kike so, idan kuma kina son suga sai a amso maki" Nihad dai ba bakin magana sai gyada kai, suka fita suka barta ita kadai da kudaje dake ta zaryarsu a dakin, a hankali ta fashe da kuka tana bin bukkar da kallo, who have she offend to deserve this in her life? Why is all this happening to her?? Khalil ya shigo ciki yana kallonta kasa kasa, cikin kuka tace "Don girman Allah kayi hakuri ka rufa min asiri ka maida ni gida, wallahi baxan sake maka duk abinda nake yi ba...." Ko rufe baki bata yi ba sai ga akwatunanta ana shigo mata da su dakin, da sauri ta share idonta tana bin yaran da suka shigo da akwatunan da kallo kamar idanuwanta xa su fito, Khalil ya jira har suka gama shigowa da su yace "Yauwa sannunku" Tana kallonsa ya tafi ya hau jera mata akwatunan step by step, ta rushe da matsanancin kuka tace "Na shiga uku na lalace, me nayi maka kake min haka don Allah???" Ko tanka ta bai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login