Showing 93001 words to 96000 words out of 289308 words
"Ji wani iyayi wai in xuba masa abinci kamar wani mijina, ashe xai tsufa bai ci abincin ba" Tsaki ta ja ta jawo wayar Nihal for the 10th time ta sake kiran layin Aliyu amma a kashe, kwantar da kanta tayi saman pillow kamar xata yi kuka don har ta gaji da trying layin nasa, tun xuwan Nihal take abu daya, Nihal na komawa kitchen ta fara xuba masa abincin a plate sannan ta dauka ta fito parlor ta nufesa ta durkusa tace "Ga abinci" Yana kallonta yace "Thank you Nihal" Ta mike ta koma kitchen din ta xuba ma ita da Nihad a tare, kadan Nihad ta ci abinci duk hankalinta a tashe yake bata samu Aliyu ba, Nihal ta ci abinda xata ci ta bar mata ta koma saman gado ta dau wayarta tana dannawa, Daga karshe wajen karfe goma da taga Nihad ba ci xata yi ba ta dau plate din ta fita, Bayan ta kai kitchen ta fito khalil na kallonta yace "Wani level kike a makaranta?" Ta tsaya tace "Level daya muke da Nihad" Yace "But in tambayeki" Ta ?an tsaya sai kuma ta dawo parlon ta xauna tana kallonsa yace "Ke kika ce ma Abba Ahmadu Bello University kike so?" Nihal tayi murmushi tace "Aa, kawai cewa yayi can xan je ni" Yace "Ita kuma er uwarki fa?" Ta sunkuyar da kanta tace "He gave her option" Khalil dake ta kallonta yace "Ohk ke daga baya baki ce masa makaranta daya kike son xuwa da er uwar taki ba?" Nihal tace "Ya Usman da Mumy sun masa magana a lkcn, Mumy tace masa tunda har Nihad ta zaba Maryam Abatcha nima ya biya mun Maryam Abatcha din mu tafi tare ko kuma duk mu tafi ABU, amma sai yace Nihad kawai xata je ni in tafi ABU, he can't afford the fee of Maryam Abatcha for the two of us" Shiru Khalil yayi yana kallonta, can yace "Kuma Ummanku bata ce komai ba?" Nihal ta girgiza kai tace "Kawai ce min tayi inyi hakuri in tafi ABU din" Khalil ya gyada kai yace "Amma secondary daya ku ka yi ko?" Nihal ta girgiza kai tace "Shi ma ba daya muka yi ba, ita Nigerian Turkish tayi, ni kuma Yan dutse nayi" Khalil ya gyada kai yace "Ohk, yan dutsen kamar su Amina da Sudais nan suke xuwa ko?" Nihal tace "Har Aunty Kamila da Ya Usman da ya farooq ma can suka yi, Nihad kadai ce tayi Nigerian turkish" Khalil yace "Amma kamar er uwartaki tafi sabawa da Ummanki akan mamanta ko" Nihal tace "To ai a bangaren Umma take, ni kuma ina side din Mum dinta, though I don't know for her" Shiru Khalil yayi yana kallonta, can yace "Maa sha Allah, hakan yayi.... amma wani saurayinta da ya zo can gida ranan, sun dade tare ne?" Nihal tace "Wai Aliyu? Yea definitely shi, don ita bata kula wani saurayi idan ba shi ba, shekaran da ta shiga Maryam Abatcha suka hadu, shekara uku kenan" Yace "Ohk, kinsan saurayin sosai kenan?" Nihal ta bude ido tace "Nasan shi mana, he is the son of General Jikamshi..." Muryan Nihad dake labe jikin pillar din corridor tum daxu ya katse Nihal, cike da bacin rai Nihad tace "A gidan uwar wa kika san shi? Shi Aliyun kike tunani kinsani? Har da wani gaya masa sunan babansa salon yayi masa mugun abu irin nasu na kauye? To wallahi baki san shi ba kuma baxa ki ta6a saninsa ba, dama don ki zo ki hadu da wannan mutumin ku kafa munafurcina ya sa kika zo gidan nan ashe ban sani ba? To wallahi ni dai ki tashi ki tafi baxa ki kwanan min a gida ba, ai dai mun ga juna, har da wani ce masa ni kadai nayi Nigerian turkish, to wani yace kar kema kice ma Abba can kike so? Naga dai choice dina ne kuma Abba yayi accepting, sannan Maryam Abatcha ma wani yace kar ki sakar ma Abba kuka kice ke baxa ki je ABU ba sai dai Maryam Abatcha? Wallahi kin ban mamaki har xaki zauna da bare kuna cakalkalar namana ko tausayina baki ji ba, to Allah ya isa wannan gulman nawa da kika yi" Nihal dai bata ce mata komai ba, Banda kallon Nihad babu abinda khalil ke yi, tana huci tace "Shi kuma saboda gulma har da wani cewa nafi son Umma, dama ashe maza na gulma ban sani ba? Kuma ai Umma da Mumy duk daya suke a wajena babu wani bambanci, to tunda dai mun ga juna zo ki dau handbag dinki kiyi tafiyarki" Mikewa Nihal tayi ta nufi daki, Nihad ta bi ta da harara, sai ga ta ta fito sanye da hijab tana rike da handbag dinta ganin xata nufi kofa Nihad ta rikota tace "Ina xa ki tafi da daddaren nan" Nihal ta fizge Hijab dinta hawaye cike idonta ta nufi kofa, Nihad ta bi bayanta da sauri tace "Ke ni fa wasa nake maki ina zaki da daddaren nan" Tuni Nihal ta fice daga parlon, Nihad ta marairaice tana kallon Khalil tace "Don Allah kayi mata magana, ni wallahi ba haka nake nufi ba" Ko kallonta Khalil bai yi ba, hakan yasa ta fita da sauri, can ta tarar da Nihal zaune bakin gate dake kulle tana rera kuka, kukan ta ita ma ta fara ta durkusa gabanta tace "Don Allah kiyi hakuri wallahi i didn't mean it, ni ba da ke nake ba, da shi nake"
*Nihad* dari biyar ne, ki fita hakkina ki karanta hankalinki kwance yar uwa
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah ur evidence via????
07087865788
*Assalamu alaikum er uwa, kina neman organic Supplement irin masu gyaran jiki ciki da waje? Ko kuma mai fitar Maki da duk wani infection komai nacinsa? Sannan mai maido Maki martabar fatarki? Ko kina fama da dry HQ? Ko hips ne matsalarki da boobs? To kwantar da hankalinki *GHT Organic supplement care gat ur back*
Domin karin bayani ki tuntubi wannan number ????
+2347057607751???
https://chat.whatsapp.com/G91KmKaihzAL76lSmkXqG9
Ganin Nihal taki tanka ta sai kuka take, Nihad ta mike da sauri ta koma cikin gidan zata kira Khalil, a bakin kofa ta kusa buge sa ya turata tayi baya xata fadi ganin hakan yayi saurin jawota ta fado chest dinsa, ta zaro ido ta daga kai tana kallonsa, ba tare da ya kalleta ba ya turata gefe ya sauka xuwa wajen Nihal, bin sa tayi da kallo, yana isa wajen ya durkusa gabanta a hankali yace "Ki yi hakuri Nihal, don't take all what she said personal" tana goge hawayen da ya ki tsaya mata tace "Ka bude min gate in tafi gida" Yace "Ba amfani hakurin da nake baki kenan?" ta girgiza masa kai kawai, yace "Now, Behave like the good girl u always are, tashi mu koma ciki" Daga haka ya mike, ita ma ta tashi tana ci gaba da goge idonta, yana gaba tana bin sa har xuwa parlon, Nihad ta riga su shiga parlon kafin su karaso, bayan sun shigo tana kallon Nihal a hankali tace "Kiyi hakuri plss, i didn't mean it" Nihal dai bata ce mata komai ba ta yi wucewarta daki, Nihad ta jefa ma Khalil wani kallo tace "Ai dai kaga abinda ka jawo, kawai ka sa yarinya a gaba kana koya mata gulma da munafurci alhalin ba halinta bane" Daga kai yayi ya kalleta, speaking calmly yace "Idan kina ci gaba da min rashin tarbiya, Billah xan tattara ki in mayar da ke kauyen can" Shiru tayi tana kallonsa, sai kuma ta 6ata fuska tace "Toh ni nace wani abu ne?" Bai sake kallonta ba, ta turo baki ta juya ta koma dakinta. Har Nihad ta gama shirin bacci Nihal bata ce mata komai ba, Nihad ta gama saka kayan baccinta wanda shi kadai ta tsira da shi a gidan ta dawo gefen Nihal da damuwa tace "Shine ina ta maki magana kin ki cewa komai ko?" Nihal ta daga ido ta kalleta tace "Me kike son in ce maki?" Nihad tace "Wallahi kema kinsan i didn't mean it, you know i love u to the extent that i will never hurt you" Nihal ta ?an yi murmushi tace "Amma duk kwanan nan jaraba kike min a waya ai" Nihad ta marairaice tace "Toh me yasa xaki dinga magana da worst enemy dina a waya? Yanxu da Amina ce ke waya da shi ko wasu can daban ai ni baxan damu ba, amma ke fa kinsan i Cherish u so much, why will u be communicating with my worst enemy?" Nihal tace "Toh shikenan, na maki al?awarin baxan sake waya da shi ba, dama yawanci ina ce masa ya kai maki waya ne...." Nihad tace "No, just block him kawai" Nihal tace "If that will please u" Tana fadin haka ta dauko wayarta tayi blocking number Khalil sanan tayi deleting number daga wayar tana kallon Nihad tace "Done!!" Nihad tayi Murmushi tace "Kin hakura yanxu?" Nihal tace "On one condition" Nihad na kallonta tace "Ina jin ki" Nihal tace "Ki tashi ki tafi dakinsa" da mamaki Nihad ke kallonta, can tace "Amma ina ga baki da hankali, inje dakinsa inyi masa me? So now u are keeping it in mind cewar mijina ne shi da har xa ki ce in je dakinsa? Why will u leave such thought a xuciyarki idan har ke masoyiyata ce?" Nihal bata ce mata komai ba ta ja bargo ta lumshe ido, Nihad ta ja tsaki ta mike ta koma can edge din gadon, ta fi minti sha biyar zaune kafin daga karshe ta mike fuskarta daure tana kallon Nihal tace "If that will please you shikenan" Daga haka ta dau Hijab dinta ta fice daga dakin kamar xata tashi sama, bayan ta saka hijab dinta ta kunna wutan corridor din tana kallon kofar dakinsa, can ta kyabe baki a ranta tace ba gwara taje parlor ta kwanta abunta kawai, kashe wutan tayi ta karasa cikin parlon tana tafiya a hankali sbda duhu, laluban dogon kujeran da xata kwanta ta shiga yi bayan ta shigo tsakiyar parlon, a tsorace ta koma baya rana zaro ido bayan lalubenta ya kai ta har jikinsa, ya mike zaune yana haskata da karamar wayarsa, kunya taji ya kamata ta juya tana sosa kai xata bar wajen, yace "Da wani abun da kike so ne???" Ta juyo duk da bata ganin fuskarsa sbda haskata da yayi ta daure fuska tace "Wani abu kamar me?" Yace "Kin fi ni sani ai tunda kika biyo ni nan kina tattaba ni" Tsayawa tayi tana kallonsa kamar me son fahimtar abinda yake nufi, can tace "Kai kasan abinda kake nufi ni ban sani ba" yace "Aa ki dai fada abinda kike so" a takaice tace "Abinda ke ranka shi nake so" daga haka ta xabga masa harara xata bar wajen ya fixgota ta fado gefensa, a tsorace tace "Don Allah kayi hakuri wallahi kwanciya na zo in yi, ni ba wajen ka na zo ba" Cikin husky voice dinsa yace "Duk dakinki babu wajen kwanciya sai kin fito parlor?" Ta boye fuskarta a huge muscles dinsa tace "Nihal ce tace idan ina son ta hakura sai na je dakinka, to ni kuma ina son ta hakura" kallonta kawai yake yana kara tabbatar da ainahin childishness dinta, Wani sanyayyen kamshi ke tashi a jikinta har gashin kanta, lkci daya kuma ya hade rai ya saketa, ta dago kai a hankali tana kallonsa, matsawa yayi daga kusa da ita ya koma daya side din kujeran, With full audacity tace "Xan shiga dakinka in kwanta kuma kar ka sake ka shigo har sai na fito" Bai tanka ta ba, ita ma bata jira yace komai ba ta mike ta nufi dakinsa, murda kofar dakin tayi ta shiga tana bin ko ina da kallo, wani kamshi ke tashi a dakin, ta kalli jakarsa dake dakin ta juya ta kalli kofa, tana ta tsaye tana kallon kofar sai kuma ta nufi jakar ta tsugunna ta bude zip din, Chargern Iphone ta fara cin karo da, ta dinga kallon chargern tana jujjuyawa, wannan kuma na waye? Ko dai na Nihal ne? Tabe baki tayi ta ajiye, ta maida idonta kan Diary Milk chocolate masu uban yawa a jakar, kai....a ina ya samu kudin siyan wannan uban chocolate din, ko da yake kudin babanta ne, wato saboda samun waje har da su siyan chocolate, wani hoto ta gani ta dauka tana kallon matar da ke jikin hoton warce baxata wuce shekaru 54 ba, kana ganinta kaga halfcast, keenly Nihad ke kallon hoton tana ji a jikinta kamar ta ta6a ganin wannan matar, amma a ina?? Duk yanda ta so tunawa ta kasa, as in, she k6s sure ta ta6a ganin hotonta but where?? Bude kofar dakin aka yi ta mike a rikice, da sauri ya nufota ya warce hoton daga hannunta ya hadeta da bango yana mata wani mugun kallo lkci daya kamanninsa suka sauya, Sosai ta tsorata jikinta na rawa tace "A bude fa naga jakar xan...." Turata yayi har sai da ta fadi kasa rigijib, ya dau jakar gaba daya ya fice daga dakin. Da safe karfe tara saura khalil na zaune parlor Nihal ta fito, ta tsaya jikin kujera ta gaishesa ya amsa yace "How was ur night?" Tace "Alhamdulillah, Nihad bata tashi ba har yanxu?" Duk da tun jiya da daddare rabonsa da dakin bayan ya fita amma haka yace "Probably" Tace "Ohk, ni xan tafi" Yace "Ina za ki tafi?" Ta sunkuyar da kanta tace "Umma ta aikeni gidan wata frnd dinta in amsar mata sako, so karfe tara matar ke fita aiki, shine tace in je kafin tara" Khalil yace "But baki yi breakfast ba ai" Tace "Na tashi da azumi yau" Shiru yayi yana kallonta tace "Idan ta tashi kace mata naje amsar ma Umma sako" Yace "Toh mu je in ajiye ki" Da sauri tace "Aa ba fa nisa, kuma in sha Allah xan dawo anjima" Yace "Are you sure?" Tace "Sure" Yace "Toh Allah ya tsare" Tace "Ameen" Daga haka ta nufi kofa ta fita. Goma saura Khalil ya tashi ya shiga dakinsa don wanka yake son yi kuma yaga bata da niyyar fitowa, kwance ya sameta a kasa, ya tsaya bakin kofa yana kallonta, ta mike xaune cikin rawar tace "Ba shkkn ba hankalinka ya kwanta kafana na min ciwo yanzu" Kallon kafar yayi, kafin ya karasa kusa da ita ya durkusa ya daga kafar, ta sakar masa kuka ta janye, hade rai yayi yana kallonta sai kuma ya sake jawo kafar, ihu ta kwala tace "Wallahi ciwo yake min" Targade ya ga tayi a kafar, ya mike ya fita daga dakin ta bi sa da kallo, da kyar ta iya daurewa ta shiga bandaki da asuba ta wanke bakinta da mouth wash ta dauro alwala ta fito tayi sallah, kamar kar ta ?an motsa xuwa bandakin shine kafar yayi mata tsami kafin gari ya waye, dawowa dakin yayi ta daga kai tana kallonsa, ya karaso gabanta ya durkusa ya bude man zafin hannunsa, ita dai kallonsa kawai take, bayan ya debi man zafin ya kamo kafarta, zaro ido tayi tana kokarin janye hannunsa a kafarta ya daure fuska yace "Kar ki sake ta6a ni Malama" yana gama fadin haka ya fara ja mata kafar yana kokarin gyara mata targaden, ai bata san sanda ta yunkuro ta rirrikesa ba tana kukan azaba tace "Nashiga uku Abba" Bai sarara mata ba har sai da ya tabbatar kafar ta dawo dai dai, kuka kawai take ta kankamesa duk ta hada zufar wahala, bayan ya sakar mata kafa shi ma ta sakesa tana komawa baya, kallonta kawai yake, ta turo baki tana share idonta, yace "Sallan asuban ma yafe maki aka yi sbda kinyi targade ko" Ta hade rai tana kallonsa tace "Ai ni ba kafura bace" Bai ce mata komai ba ya mike ya nufi kofa, da sauri tace "Ka kira min Nihal plss" yace "Warce kika kora ko wacce?" daga haka ya fita dakin, a hankali ta lallaba ta mike ta hau saman gadon ta kwanta tayi lamo a saman pillow, wato tafiya Nihal tayi upon all her pleas. Kafin azahar Nihad taji tana iya taka kafar, a hankali take dingishin ta fito daga dakin, ta shiga nata dakin, kallon katon ledan dake saman gado ta dinga yi, kafin ta karasa ta bude ledan, abaya ta gani masu ?an karan tsada sun kusa kala goma, da mamaki ta dinga kallonsu tana warwaresu, sannan ga undies da cream din shafawa da turarurruka duk a cikin katon ledan, da sauri ta fito parlor tana kallonsa tace "A ina ka samu kudi ka siya min abayan nan?" Ya kalleta a takaice yace "Kudin babanki mana" Nihad tace "To amma wa ya zabo abayan?" Yace "Ni ?an aike ne, kasuwa kawai aka aike ni naje na amso" Ta kyabe baki tace "I thought as much" Daga haka ta juya ya bi ta da kallo har ta shiga daki, wani Murmushi yayi ya maida idonsa kan tv da yake kallo. Bayan ta yi wanka ta shirya cikin daya daga abayan, sosai yayi mata kyau ya amshi fatarta, ba laifi haskenta ya fara dawowa amma ramar na nan, ta fito parlor, kallo daya yayi mata ya dauke idonsa, ta wuce kitchen sauran abincin da Nihal ta dafa daren jiya ta kara dumamawa ta xuba ta koma daki ta ci, har kusan la'asar Nihad na ta xuba ido taga ko Umma xata zo yau din ko sai gobe, amma bata zo ba, wajen karfe biyar ya bude kofar dakinta yace "Ki sameni a mota" Da ido ta bi sa har ya bar wajen, sai kuma ta mike ta dau mayafinta ta bi bayansa, duk da yana cikin motar ta ki shiga, she can't take that risk anymore, tana kallonsa da kyau tace "Ina za mu je?" Yace "Gidanku" Ta ?an yi jim, sai kuma dai ta shiga bayan motar ta kulle, suna barin gida taga sun dau hanyar gida, ta ma rasa ko farin ciki xata yi ko akasin hka, the only good thing of going to that house is that xata