Showing 216001 words to 219000 words out of 289308 words
da Nihad din kenan?" Umma na shessheka tace "Ina na sani, tun dazu ni dai ban ji duriyarsu ba kinga ai sun koma kenan, ita kanta Nihad din har yanzu zancen nan da nake maki bata shigo ta dubani ba, Yallabai da ya shigo dazu kafin magariba yake gaya min miliyan daya Jikamshin ya bada a raba ma yan gidan" Turai ta zaro ido tace "Toh baki ga ta kuka ba gaskiya Sumayya, kuka ba naki bane yanzu, amma dai su ba su da labarin videon da yayi leaking a gari ne kwanaki?" Umma tayi shiru, sai kuma tace "Kai bana jin sun sani gaskiya, wa zai so ?an sa ya auri irin wannan yarinyar? Ai da sun gani da tun a Abujan za su sa ya saketa" Turai tace "Toh kawai kudi zaki bada a ba popular bloggers kamar biyar haka su sake dawo da labarin da zafi zafinsa, nan da nan zaki ga ya karade duniya" A hankali Umma tace "Ko??" Turai tace "Kwarai kuwa" Umma na share hawayenta tace "Kamar nawa zan turo yanzu?" Turai tace "Ko dubu dari uku ce a kacalcala masu, kyau a samu bloggers kamar shidda lafiyayyu" A hankali Umma tace "Turai zoben fa saura kwaya daya yanzu, duk mun siyar an kai ma malamai" Turai tace "Amma ai kuma bukata na biyuwa idan ba yanzu da aka samu cikas ba, yanzun ma rufe ido zaki yi ki siyar kawai a biya bukata da shi, Allahn da ya baki shi zai sake baki" Umma ta sauke ajiyar zuciya tace "Toh shikenan Turai, Nagode sosai Allah ya bar zumuncinmu, in sha Allah gobe xan aiko Amina da shi, ni kinga bazan iya fitowa goshi a fashe, ga hannu nayi targade" Turai tace "Ba damuwa goben ma zan shigo ba sai kin aiko Amina ba" Umma tace "Toh nagode sai kin zo" Daga haka Umma ta katse wayar, nan taji hankalinta yayi mugun kwanciya, ai da Nihad ta zama surkar jikamshi gwara ko tsirara ne tayi yawo a duniya, sai tasan yanda tayi ta rabata da Khalil wallahi, mikewa tayi ta nufi kofa ta jawo zata fita taga Abba tsaye bakin kofar bandakin, Sake wayar hannunta tayi cikin daburcewa tace "Yall.. yallabai yaushe ka shigo?? Bayan gida na shiga inyi...." Abba dai kallonta kawai yake, can ya juya ya bar bakin kofar bandakin, walking slowly ya fita daga dakin gaba daya, jikin Umma ya dau rawa ta dinga nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un a zuciyarta, da kyar ta karasa fitowa daga bandakin taga ledan fruits da ya kawo mata ajiye a kasa....
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
*CONGRATULATIONS*????
*For taking this smart move to growing your business....*
I am zainab Suleiman you can save my contact ummu shaheed or kabzee 08033242995
* I will be giving you the opportunity to connect to Over 80 direct suppliers and major dealers of various products in Nigeria, where you will be getting goods at factory prices without Importation and reselling as an wholesaler to make great profit.*????????
*This is for everyone that wants to start getting products at good purchase price/factory prices and become a major wholesalers that other business owners can buy in bulk from*????
*This suppliers contact bundle has solved 70% of the problem of startups, small business owners, distributors, dropshippers etc...which is the inability of getting goods at good affordable prices to resell...*
*But the *GOOD?EWS is I will allow Only 20 people access this contact bundle at a discount rate of N5000 ONLY*
*Ps: this offer is available for just 24 hrs.* ????
*After that price goes back to the usual price of N7,000* ??
Nihad ta gama shirin kwanciya a bedroom din Mumy wajen karfe tara da rabi, Aunty jamila da bata yi tafiyar tata ranan ba sai bin ta take da kallo tana ganin ikon Allah, sai da ta bari ta kwanta sannan tace "Ke kam ashe har yanzu baki da saiti ban sani ba Nihad" Nihad ta juya ta kalleta, Aunty jamila tace "Mijinki na gidan nan tun dazu amma common kije ki ga ko ya ci abinci ma baki je, ko yana da bukatar wani abu ke duk ba damuwarki bane, babu ruwanki sai harkan gabanki kike, to kuwa idan kina nuna i don't care attitude din nan naki akan miji kya samu warce kina ji kina gani zata kwace maki miji" Nihad ta mike zaune tana kallon Aunty jamila, a duk maganar da ta mata na karshen ne ya tsaya mata a rai, Aunty jamila tace "Shi namiji in gaya maki riritasa ake, wasu na can a waje suna harinsa ke kuma kina nan kina shashanci, tun daxu da ya shigo gidan nan sai kije ki samesa ki ji ko yana da bukatar wani abu tunda nasan Mumy dole zata basa abinci...." Dai dai nan Mumy ta bude kofar dakin ta shigo, tana kallon Nihad tace "Ke baza kije kiji ko yana da bukatar wani abun ba?" Aunty Jamila tace "Maganar da nake mata kenan yanzu Aunty" Nihad ta sauka daga saman gadon a hankali ta dau hijab dinta ta sa, har ta nufi kofa sai kuma tace "Toh ai ni ban san inda yake ba fa" Mumy tace "Yana dakin Farooq" Bude kofar tayi ta fita, Aunty Jamila ta rike ha?a tace "Aa gaskiya tana bukatar counselling akan auren ma gaba daya, don ban ga alamar tasan komai ba" Mumy tace "Toh idan ba ke ba wa zai mata Jamila" Aunty Jamila tace "Allah ya kai mu gobe" Mumy tace "Ke baza ki ci abincin ba?" Aunty Jamila tace "Aa na sha shayi... Uhmm Aunty bamu samu mun yi magana ba har yanzu" Mumy na kallonta tace "Magana akan me fa?" Aunty Jamila ta rike ha?a tace "Me suma daga ji da ganin abun arxiki, ke kiji hassada kiri kiri, zuciya ta kasa adana hakan har sai da ya fito fili cikin bainar jama'a, duk me hangen nesa a parlon nan yasan shock din al'amarin ne ya sumar da ita ba wani abu ba, and shock in the sense that she wasn't expecting things to turn out that way, wallahi she never expect that kamar yanda mu ma bamu yi expecting ba kawai a bazata abun ya zo mana, wato Sumayya ta gina ramin mugunta without considering zata iya dawowa ta afka ciki ko wani nata ya afka, yau ai ga Kamilar da take takama tana auren mai kudi a gida ba wai farin ciki nake da hakan ba don babu wanda zai yi farin ciki da mutuwar auren wani, amma ishara ta fara gani tun a nan duniya, sai ga Nihad da ta so lalata ma rayuwa tana auren wanda ko a mafarki bamu ta?a kawo hakan a kai ba, na sha gaya maki da akwai wani boyayyen lamari game da Khalil din nan, tun ran da na fara ganinsa a gidan nan..." Mumy dai ta sauke ajiyar zuciya ta ma rasa abinda zata ce ma er uwartata. Nihad na tafiya a hankali ta nufi dakin Ya farooq, ta tsaya bakin kofar tayi sallama hade da Knocking, bude kofar dakin aka yi taga Khalil tsaye, ta shiga cikin dakin tana kallonsa tace "You need anything?" Ya kafeta da ido, sai kuma ya kulle kofar dakin ya jawota, ta zaro ido tace "What are you doing??" murya can kasa yace "I need nothing, but you...." Ta wani turo baki tace "Ni ka sakeni kar Ya Farooq ya shigo, dama su Mumy ne suka ce in zo in tambayeka ko kana da bukatar wani abu shi yasa na zo...." Kallon lips dinta kawai yake tana magana kuma ya ki sakinta, ganin haka tace "Ni don Allah ka sakeni, meye haka...." Bai bari ta rufe baki ba ya hade bakinta da nasa giving her a deep kiss, lokaci daya ta ji tana neman faduwa tsabar yanda ta kasa tsayuwa da kafarta ya jinginar da ita da bango, kissing her romantically, knocking din kofar dakin aka yi ya saketa da sauri zai koma baya amma tuni Farooq ya shigo, yana shigowa kuma yayi kasa da kansa ya juya ya fita daga dakin, Nihad ta marairaice tana kallon Khalil wanda shi ma kunyar Farooq ya cikasa, wani harara ta galla masa ta nufi kofa da sauri, ya bi ta da kallo yana shafa kansa har ta fita daga dakin, sai sunkuyar da kanta take wai ko zata ga farooq a hanya, amma har ta koma bangaren Mumy bata gansa ba, ta sauke ajiyar zuciya ta shiga parlon, ?in karasawa bedroom din Mumy tayi don gani take suna ganinta za su gane abinda Khalil yayi mata, ta kwanta saman 3 seater tayi lamo zuciyarta na bugawa, har sannan tana jin kamar bakinsa na cikin nata, the imagination is making her whole body weak, a hankali ta kai hannu soft lips dinta tana ta?awa. Farooq na bar masu dakin na Usman kawai ya wuce yayi kwanciyarsa a nan, dama daga bangaren Umma yake wanda taki fadin dalilin kukan da take kamar warce ta amshi sakon mutuwa, ba yanda bai yi da ita ba amma taki gaya masa daga karshe tace masa ai hannunta ne ke damunta, babu yanda ya iya ya fito dakin nata kawai. Daren ranan yanda Umma ta ga rana cike da bakin ciki haka ta ga dare cike da fargaba, Kamila bar mata dakin tayi ta koma na Nihad daga karshe tsabar irin kukan da take yi, Umma bata ta?a shiga tashin hankali irin wannan ba, can kuma wata zuciyar ta dinga assuring dinta ai Abba bai ji wayar da take ba fa, ta yaya zai ma ji bayan ta tura kofar bandakin, kawai dai abinda ya ?ata masa rai yanda take magana cikin bandaki, wannan tunanin yayi contributing wajen calming dinta down, amma fa bata runtsa ba har asuba, ga dislocation dinta yayi tsami sai azaba yake mata, goshinta ma sai yanzu yake mata fitinannen ciwo... Da safe Mumy ta shigo duba jikinta, Umma ta ki bari su hada ido tace "Jiki Alhamdulillah" Mumy tace "Toh Allah ya sauwake, ya sa kaffara ne" Tace "Ameen Ameen" Mumy ta ?an zauna a parlon na wani mintuna kafin ta tashi tace mata zata shiga kitchen, Umma na ganin ta fita ta lallaba ta saka Hijab dinta ta fito main parlor don Mumy ce da girki kuma tun dazu take jiran ta ji ta a kitchen kafin ta tafi parlon Abba, bata tadda kowa parlon ba don it is still early, ta nufi bangaren Abba da sauri ta bude kofar parlon ta shiga, bata gansa a parlonsa ba which is very rare, yana dawowa masallaci parlonsa yake zama har zuwa lokacin da zai fita office sannan ya shiga bedroom dinsa ya shirya, hankalin Umma a tashe yake sosai, gabanta sai faduwa yake, tayi karfin halin nufa kofar dakinsa a hankali ta murda, zaune ta gansa saman gadonsa ya jingina da pillow yayi nisa tunanin da yake, ya daga kai ya kalleta, gabanta ya fadi sosai, cike da karfin hali ta karasa cikin ta zauna saman kujeran dake dakin ta dake tace "Ina kwana yallabai" Abba ya kalleta kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Lafiya lau" Umma ta ?an ji hankalinta ya kwanta jin ya amsa, nan ta fara kame kame ta marairaice tace "Yallabai jiya, kawai ina bandaki... Dama kuma kasan...." Dakatar da ita Abba yayi yace "Ni ban tambayeki komai ba Sumayya" Bude kofar dakin aka yi, Mumy tayi turus bakin kofa ganin Umma a dakin, sai kuma tace "Ohh ban san ma kina nan ba ai..." Umma dai tayi wuri wuri ta kasa cewa komai, Mumy zata kullo masu kofar Abba yace "Ya aka yi Maryam?" Mumy tace "Aa tambaya zan yi ko yanzu kake son black tea din" Yace "Aa sai anjima" Tace "Toh" Daga haka ta juya ta kulle masu kofar dakin, Umma ta rasa abun cewa suna ta zaune haka for almost 3 minutes duk jikinta yayi sanyi, yanxu da gaske ya ji wayar nan da take? Abba yayi breaking silent din yace "Sumayya" Gabanta yace rassss, ta daga kai da kyar tana kallonsa amma ta kasa amsawa, Yace "Za ku ba Bloggers 300k don su sake dawo da Video din Nihad ke da kawarki a social media, kin nuna kina ba?in ciki da gidan da Nihad ta samu, kin nuna you can't even withstand seeing her married to her current husband kawai saboda selfish interest dinki, kika ce duk kun siyar da zobenki na gwal kin kun kai ma malamai, baxan tsaya bin diddigin abubuwan da malaman suka maku ba Sumayya, baxan yi hakan ba, kawai dai nayi farin ciki da na gano duk wani abu da kike ma Nihad ba da zuciya daya kike ba, ke kina da wata manufar taki ta daban ne a zuciya, this is so unfortunate Sumayya, idan kuma aka ce min da hadin ba?inki video din 'ya ta yayi yawo a gari, kuma da sa hannunki wajen yin video din ma baxan musa ba, kin gurbata mata rayuwa kin bar mata ta?on da baxai ta?a gogewa a rayuwarta ba, kin cuceta" Umma ta fashe da wani matsanancin kuka tace "Wallahi wallahi wallahi Yallabai ban san ta inda wannan video din ya fita ba kaji har na rantse, believe me wallhi i know nothing about the video, idan kuwa karya nake Allah ya dauki raina a nan" Kuka take sosai tana kallonsa, Abba yace "Ba komai Sumayya, koma dai menene bana jin bayan abubuwan da naji kuna fada a waya dake da kawarki kuma a hakan ma ba daga farko na tsinci wayar naku ba, bana jin zan iya ci gaba da zama da ke, all what u are saying on phone ya nuna baki son Nihad, baki ta?a sonta ba, fuska biyu kika dinga mata Sumayya, idan har tun ba yanzu kika fara cutarta ba kuma kece sillar duk abubuwan da suka sameta Allah Ubangiji ya saka mata cikin gaggawa, kuma kije na sake ki amma zaki iya ci gaba da zama gidan nan, don da girmanki bazan ce ki bar min gidana ba, zaki ci albarkacin zuri'an dake tsakaninmu, zaki ci gaba da zaman yaranki, ki ci gaba da duk harkarki a gidan nan amma babu aure tsakaninmu, and this should be just between i and you, sai Maryam wanda ita ma dole ta sani ne for some reasons, amma ko yaranki ni ban baki goyon bayan ki sanar masu komai ba balle wani a waje, ki ci gaba da duk yanda kike a gidan nan, aure ne dai babu tsakanin ni da ke" Bitterly Abba ke maganar, Tsabar shock Umma ta kasa cewa komai ta dinga kallon Abba babu ko kiftawa, Abba yace "Ki je na sake ki Sumayya" Wani kukan tashin hankali Umma ta fashe da tace "Ka sakeni fa kace Yallabai, wallahi yallabai sharrin shaidan ne amma kasan ba halina bane, ban ta?a nufin Nihad da sharri ba dai dai da rana daya, wallahi rudin shaidan ne, don girman Allah ka rufa min asiri ka janye batun sakin nan, tsofe tsofe da ni kace ka sakeni, ko albarkacin yara baxan ci ba Yallabai" Abba yace "Albarkacin nasu yasa nace kiyi zamanki gidan nan kiyi harkarki yanda kika saba, sannan ko Mahaifiyata ni baxan je ince mata na sakeki ba, i am leaving it to my self, sai in kece kika je kika fadi a gari...." Kuka Umma take kamar ranta zai fita tana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, saki da tsufana Yallabai, saki fa kace" Abba yace "Kin ga ki tashi ki je kar ki ja mana attention a nan, you can leave pls Sumayya" Tashi tayi tana kuka sosai ta nufi kofa ta fita daga dakin nasa..... Umma na komawa dakinta ta dinga kuka ba ji ba gani, Kamila dake ta kallonta tace "Toh wai baki kira Hajiya Turan bane" Umma tayi banza da ita tana rusa kuka uwa yar yarinya.
Aunty Maryam ta girgiza kai tana kallon Mami tace "Mami i am not supporting Khalil in anyway, ki fahimce ni Mami, yanzu ko Janar ne yace bai yarda da auren nan ba ba sai inda karfinki ya kare ba Mami? Ki daure ki dinga duba halacci irin na iyayen yarinyar wllh sai kiga kin samu rest of mind kin rungumi auren nasu hannu bibbiyu, uban yarinyar fa cewa yayi saboda kyawawan halin Khalil ya aura masa 'yar sa, ki ga fa kauye yaje yayi hiring mutane a matsayin iyayensa ya kai ma uban yarinyar, amma hakan bai sa uban ya kyamacesa ba ya basa er sa, mun dai je gidan kinga babu alamar tsiya tare da su, kuma da ganinsu kasan yan babban gida ne, Mami in dai Nadeeyah ce damuwarki to ki kwantar da hankalinki babu wanda yace Khalil bazai aureta ba, ai Janar bazai ma yarda ya mayar da shi karamin mutum ba dole ce masa zai yi ya hadasu gaba daya, kai idan ma tsoronki idan Khalil ya dawo zai iya cewa ya fasa to ko ni kadai na ishesa wallahi, balle kar ki manta Mami muna nan duk bamu san da aure tsakaninsa da Nihad ba amma kuma ai bai fasa shirye shiryen aurensa da Nadeeyah ba, ya yarda har aka kai kudi aka sa masu lokaci, da bai da niyyar auren nata ai kakkaucewa kawai zai dinga yi...." Mami ta dakatar da ita tace "Bana son ki dinga kawo min maganar shirme Maryam, ko min rashin sona da auren nasa ba sai dai in zuba ido inyi shiru ba tunda aikin gama ya riga ya gama, kina ganin zance ya saki yarinyar ne? Ni takaicin dake damuna yanda har ni ya iya boye ma auren, Maryam babu ranan duniyar da bana kiran Khalil fa, a rana nakan kirasa sau uku sau hudu, ko kece ?anki ya maki haka baza ki ji dadi ba Maryam, yasan dai ko da za a juya masa baya akan batun auren nan ni bazan juya masa idan ma zan yi fushi na ?an lokaci ne, amma yayi min haka saboda bai daukeni a bakin komai ba wai har ni ya boye ma, kinga kuwa