Showing 228001 words to 231000 words out of 289308 words

Chapter 77 - NIHAAD-complete by KHALISAT HAIDAR

04 Jul 2024

63615

cin amana.... Dama ashe duk yaudarata kika dinga yi a baya ban sani ba? Ki rasa wanda zaki aura a karshe sai makiyi na? And you are trying to make it look as if baki san hakan ba?" Nihad dake kallonsa zuciyarta na bugawa tace "Kai ban kiraka da munafuki ba sai nice zaka ce ma munafaka? Naga ai ban ta?a amfani da sunan mahaifin wasu a matsayin mahaifina ba, i never lied to you about who my dad is, hasalima har gidanmu na kai....." Bata kai karshe ba ya sauke mata mari, ta dafe kuncinta da mamaki tana kallonsa babu ko kiftawa, yace "Sai kinyi da kin sanin sanina a rayuwarki, kuma duk sai na fanshe bata min lokaci da kika yi ta hanyar da baki ta?a zato ba wallahi, i am promising u this" Dai dai nan aka bude kofar parlon Aunty Hassana ta shigo rike da tray me dauke da kwalin lemo da glass cup, tana kallon Aliyu da sauri ta ajiye tray din hannunta tace "Me ke faruwa Daddy?" Kofa Nihad ta nufa da sauri hawaye na sauka idonta, Aunty Hassana ta gwalo ido ganin haka ta bi ta tana kiranta amma tuni Nihad tayi nisa, Aunty Hassana ta dawo parlon cike da masifa rai bace tace "Kai wani irin shashasha ne mara lissafi Daddy? Kai me yasa baka jin magana ne? Nace maka a sannu za a bi komai amma sai da ka yi mata magana? Toh yanzu ina kake son in bi ta in bata lemon nan fisabilillahi? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, baka kyauta min ba Daddy" Aliyu yace "Ke kika ga haka mum" Daga haka ya fice daga parlon kamar zai tashi sama, Hankali tashe Aunty Hassana ta kira wata long time frnd dinta Maimuna da ta hadu da ita zuwansu kano ta shige daki da sauri. Direct Nihad dakin Mimi ta koma ta zauna gefen gado hawaye na sauka idonta sai kuma ta fashe da kuka sosai, ko minti biyar bata yi da shigowa ba aka bude kofar dakin, Khalil ya shigo, da mamaki yake kallonta ganin kukan da take, sai kuma ya nufeta da sauri yana kallonta yace "What happened?" Hade kai tayi da gwiwa tana kuka sosai, ya zauna gefenta ya dagota hankali tashe yace "Talk to me plss an maki wani abu ne?" Tana shesshekan kuka tace "Aliyu slapped me" Khalil ya dinga kallonta ba ko kiftawa, as if counting his words yace "Aliyu slapped you?" Nihad ta gyada kai cikin rawan murya tace "Mimi ta kai ni mu gaisa da yan gidan shine muka hadu da shi a parlon warce muka je kano tare da ita" Khalil bai jira ya gama sauraronta ba ya mike ya fice daga dakin kamar zai tashi sama, direct dakin Aliyu ya nufa that is almost 5 minutes walk daga dakinsu Mimi, a hanya ya ga wani vase din flower ya dauka yana ci gaba da tafiya kamar zai tashi sama, bai kuma hadu da kowa ba har ya isa part din Aliyu, dai dai nan shi kuma ya fito daga dakin sa babu wata wata khalil ya fasa vase din jikin bango ya caka masa da karfi a kafarsa, Aliyu yayi wani kara ya dafe bango da sauri yana zaro ido, kan kace me sai ga jini kamar an bude pampo, hakan bai sa Khalil ya fasa shakesa ba yana huci yace "Stay away from my wife, idan kuwa ba haka ba, ni ne doom dinka, i promise you" Yana gama gaya masa haka ya turasa da karfi ya juya ya bar wajen kamar wani soja.... Mimi ta fita da trolly din Aunty Maryam zuwa mota ta dawo kenan ta hadu da khalil tace "Yayanmu Aunty Maryam tana ta nemanka fa" Bai ce mata komai ba ya fice daga parlon, Mimi ta tafi ta gaya ma Aunty Maryam yana parking space yana jiranta..... Khalil na kai Aunty Maryam Airport ya dawo sai bai shiga gidan ba, yayi parking kofar gida yayi dialing number Mimi, Mimi na dagawa yace "Are you with me?" Tace "Yeah ina ji" Yace "I want you to come out now with Nihad but kar ki gaya ma Mami, zata siya abu ne a Supermarket" Mimi tace "Alright" Daga haka ta katse wayar, ba a dau lokaci ba sai ga ta ta fito da Nihad, tun daga nesa yake kallonsu har suka karaso, yana kallon Mimi yace "Thank you" cike da damuwa Mimi tace "Yayanmu they just rushed Aliyu to the hospital now, i think ko kwalba ne ya fadi a kafarsa i don't just understand, he is bleeding seriously" Khalil yace "Ohh really" Bai jira me zata ce ba ya bude gefensa yana kallon Nihad yace "Shiga mu je ki siyo abun" Nihad ta shiga motar, ya kalli Mimi yace "Za mu dawo yanzu but don't say anything to Mami" Tace "Ohk" Yace "Noor fa?" Mimi tace "Noor na gidansu Nadeeyah" Yace "Ohk" Daga haka ta kulle motar ta koma cikin gida shi kuma ya bar layin, sai a sannan Nihad ta kallesa da damuwa tace "Me yasa zaka yi injure dinsa haka?" Yace "Saboda ya ta?a Nihad" Tayi shiru tana kallonsa, can ya girgiza kai yace "Dama i have been targeting him for so long, so this is just an opportunity that comes but once" Nihad da hankalinta ya tashi tace "Mimi said he is bleeding heavily" Khalil yace "Serves him right" ta daga kai da sauri ta kallesa ganin gidansa ya kawota, deep down her she felt happy saboda bata jin dadin zaman gidan nan nasu, bata son gidan har cikin ranta, ya sauka ya bude gate din ya shiga da motar ciki sannan yayi parking, da kansa ya sauka ya bude mata side din da take, ta sauke idonta sannan ta sauka daga motar, yana rike da hannunta suka shiga cikin gidan, sama ya tafi da ita, yana kallonta yace "Which room will u prefer amongst the room?" Nihad dai sai kallon dakunan take bata ce komai ba, yayi hugging dinta a hankali ta baya yace "Ko in zabar maki?" Still dai tayi shiru feeling him at her back, a hankali ta fara kokarin janye jikinta ya ki saketa dragging her closer to him, murya can kasa yace "Na zabar maki this one" Ta kalli dakin da yake nuna mata wanda yake kusa kusa da bangarensa na master Bedroom, rubbing her flat tummy yace "Kina so?" Kai kawai ta gyada masa, wasu abubuwa ya dinga yi mata ita dai bata hanasa ba sai kafafuwan ta ne kawai suka kasa ci gaba da daukanta, he could feel how fast her heart is beating, he noticed jikinta ba shi da wuyar reacting to stimulation, bata ankara ba sai ganinsu a bedroom dinsa tayi....
A hankali Khalil yayi kissing din goshinta yace "Wake up, it's almost Magrib...." Nihad ta bude Idonta, ya dagota zaune yana kallonta, yana son sanar mata maganar da Aunty Maryam tace ya gaya mata amma ya kasa don bai ma san ta inda zai fara ba, Yayi kasa da murya yace "Za mu tafi can gida yanzu" Sosai gabanta ya fadi jin abinda yace mata, ta kasa ce masa komai. Har suka sauka downstairs Nihad ji take kamar ta fashe da kuka, ya dau wayarsa da ya ajiye a parlon, nan ya ga missed calls din Janar har uku, sai na Mami kusan goma, shi gaba daya ya ma mance da wani abu da ya aikata sai yanzu da yaga kiransu, ya mayar da wayar aljihunsa yana rike da hannun Nihad suka fita daga gidan. Sai da suka isa gida Khalil yayi parking a layin yana kallon Nihad, kamo hannunta yayi a hankali, gathering all courage yace "Kin san kafin Abbanki ya hadani aure da ke ina da budurwata warce har da akwai maganar aure tsakanina da ita right?" Nihad ta daga kai tana kallonsa kamar bata fahimce abinda yake nufi ba, Ya lumshe ido ya bude amma ganin irin kallon da take masa kawai ya fasa ci gaba ya ja motar yana driving din a hankali, ana bude masa gate yayi parking a parking space, Nihad bata sake second daya a motar ba bayan ya bude lock din ta sauka, ya bi ta da kallo har ta shiga cikin gidan, ya sauke ajiyar zuciya ya jinginar da kansa jikin kujeran motar. Sai da Khalil yayi sallah sannan ya shiga gidan yana ciro wayarsa dake ring a aljihu ganin Abbansa ne ya daga, Janar na gama maganar da zai masa ya katse wayar, Khalil ya nufi bangaren Aunty Hassana kamar yanda Janar din ya umarcesa yana bude kofar parlon ya ga Janar a tsaye, ga Aliyu zaune a kasa an nannade masa kafa da uban bandage wanda har yayi stain da jini, sai zufan azaba yake, Aunty Hassana na zaune parlon sai kallon kafar Aliyu take ta kankance ido zuciyarta na tafarfasa, Ga Mami a tsaye duk jikinta yayi sanyi, ko magana bata yi, Hajiya Amina ma na dakin sai girgiza kai take cike da alhini, Janar ya juya yana kallon Khalil cikin daga murya yace "I need an explanation to this Ibrahim" Khalil yayi shiru bai ce komai ba, Janar yayi masa tsawa yace "Magana nake maka" Khalil ya gyara tsayuwarsa jikin kofar yace "Tsautsayi ne, amma ba da gangan bane" Janar na masa wani kallo yace "Tsautsayi?? Shaye shaye ka fara da zaka kira hakan da tsautsayi? Where u out of ur mind" Khalil dai yayi shiru, can a hankali yace "Kayi hakuri" Janar ya hau zaga parlon fuskarsa a murtuke, Can ya juya ya kalli Khalil yace "Sai ka shirya gobe ka tafi Germany ka hadu da business partners dina na can" Aunty Hassana ta daga kai da sauri tana kallon Janar baki bude, shi kansa Aliyu kallonsa yayi da sauri, Khalil yace "Ohk" Daga haka ya juya ya fita daga parlon, Mami ta kasa dago kai don bata yi expecting jin abinda Janar ya fada ba, Aunty Hassana ta kasa daurewa cikin ?acin rai tace "Yaya kasan kuwa illar da yayi ma kafarsa? Har fa ?ashinsa sai da ya tsage ya dagargaje" Janar ya kalleta yace "Sai a fita da shi waje a sake duba kafar...." Aunty Hassana na huci tace "Iya abinda zaka gaya ma ?an ka kenan bayan illata min ?a na da yayi?? Amma yaya ka bani mamaki, wallahi ka ban mamaki, iya matakin da zaka dauka kenan a kan wannan mugun raunin da Khalil ya ji masa??" Janar ya tsaya kallonta bai dai ce komai ba, tana girgiza kai tace "Toh wallahi baxan yarda ba, idan na yarda shegiya uwata da ubana suka haifeni, kafin in dau mataki dama sai na fara kiran duk family sun san abinda ake ciki, duk sai na bi na tura masu video din kafar Aliyu, Khalil ya nakasa min ?a amma kai ta business dinka ma kake a Germany ko?? To wllh bazan yarda ba samm, sai inda karfina ya kare a wannan abinda Khalil yayi ma ?a na" Janar yace "Ni kike gaya ma maganganun nan Hassana?" A fusace tace "Na fada, ai ?a bai fi ?a ba, shekaru kusan ashirin baya haka nan yayi masa rauni a baya har yau ta?on na nan a bayansa, a wancan lokacin ma babu wani mataki da ka dauka banda asibiti da ka kai Aliyu, kawai ka dauki son duniya son jaraba ka daura ma yaro yana ta abinda ya ga dama ya zama terror har da su sace sace a lamarinsa, ohk don ba ubanmu daya ba shine zaka dinga fifita ?an ka a kan ?a na?" Janar ya gyada kai yace "Ki sameni parlona Hassana" Daga haka ya fice daga parlon nata, Aunty Hassana ta dinga bambami tana zage zage, babu abinda ta mance bata gaya ma Mami da tayi shiru tana kallonta, daga karshe ta fice daga parlon nata ta bi bayan Janar tana huci, dama ta saba fesa masu rashin kirkinta kuma ta zauna lafiya a gidan, babu yanda har shi Janar din ya iya da ita, ita abinda ya kona mata rai Germany da Aliyun bazai je ba sai Khalil, shine babban ba?in cikinta a yanzu, tana isa parlon Janar ta ki zama tace "Ina jin ka" Bai ce mata komai ba banda zaga parlon nasa da yake, bayan few seconds ya daga kai ya kalleta yace "Ki tattara komai naki ki bar min gidana yau ba sai gobe ba Hassana" Buda baki tayi tana kallonsa da mamaki babu ko kiftawa, can tace "In bar maka gidanka kace?" Yace "Ehh ba sai gobe ba, dama da na duba wasu mugayen halayyenki a baya da yanda kika hadani da mahaifiyata har ta koma ga Allah, to da ko anguwan da nake bazan bari ki karaso ba balle ki shigo gidana har ki zauna zaman shekara talatin...." Aunty Hassana ta dinga kallonsa ko kiftawa babu, yace "Ba hauka Ibrahim yake ba da zai raunata Aliyu haka nan kawai, they must definitely be something, they must be a reason...." Aunty Hassana na huci tace "Toh ai naga akwai cctv a gidan a duba mana a ga dalilin tunda goyon bayan ?an ka kake Abubakar" Janar yace "Cctv din da ku ke kashewa ko wanne kike nufi a ciki? Hassana yau ba sai gobe ba ki bar min gidana kada in sa sojoji su fitar min dake, wallahi karfin zumunci kawai nake dubawa nake zaune dake banda haka a irin makircin da kika hada min a baya ko kusa da inda nake bazan bari ki zo ba" Wani murmushin takaici tayi tace "Ohk" Daga haka ta juya ta fice daga parlonsa, direct bangaren Hajiya Amina ta nufa, Hajiya Amina ta taso tace "Ya ake ciki yanzu?" Hassana tace "Ragowar kudin nan na wajenki zaki turo min yanzu" Hajiya Amina tace "Kudi kuma? Aa ni babu ko sisi a wajena, ai kudin sun kare" Wani axababben kallo Aunty Hassana ta jefa mata tace "Me din suka kare?? Miliyan 15 din nan da yayi saura fa nake nufi" Hajiya Amina tace "Aa, ni fa nace maki babu ko sisi a tare da ni" Aunty Hassana tayi mici mici da ido tace "Kan uban can, to kuwa zan maki rashin mutunci, ni zaki ce ma babu ko sisi?" Hajiya Amina tace "Yau ga ikon Allah, kudin haihuwa suke ne, kwanaki kin san sa na tura ma sadiya miliyan 3, to dama ai shikenan ya rage a kudin ko bakya lissafi ne??"





Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788






Assalamu alaikum
Barkanmu da war haka masoya Khaleesat da Nihad??. Nasan kowaccenku na cike da son sanin turarukan da wadannan taurari namu guda biyu ke amfani dashi dake tafiyar da xuciyar maxajensu ya rikita musu lissafi ya kuma goge masu hada??.
Toh turaruka neh na oil masu kamshi sosai da rike jiki daga scentmania. Wadannan turaruka sunfi kala goma. Dan mace ba'a Santa da xama da kamshi iri daya kullum ba. Dole adinga jin kamshi ma banbanta ajikinta kullum. Ana hada wadannan turaruka biyu xuwa sama asaka alokaci guda dansu bada sihirtaccen kamshin dake tafiyar da hankalin duk wanda ya shaka.
Dan haka muka hada package na wadannan turaruka muna kiranshi da 'Nihad pack' ?? ??
Akwai Nihad silver pack: ya kunshi turaruka kala biyar. 6mls guda biyu da 3mls guda uku N5000.
Akwai Nihad gold pack: ya kunshi turaruka kala bakwai. 6mls guda uku da 3mls guda hudu
Sannan akwai Nihad diamond pack: ya kunshi turaruka kala 8. 10mls guda daya 6mls guda hudu 3mls guda uku.
Ga sunayen turarukan nan kamar haka
1. Love letter (na musamman akowani pack akwaishi)
2. Baccarat Rouge
3. Jadore
4. La vie est belle
5. Pink shiffon
6. Pure seduction redplum
7. Versace Eros woman
8. Black Opium
9. Kim Kardashian
10. Love spell
Note that turarukan package a discounted price aka bada, kuma ana hada scents din da sukayi complimenting juna neh yadda xaifi tashin kai in anyi amfani dashi. Amman in kinason kiyi maki choice dinki shima ana badawa standard price dinmu 3mls N800, 6mls N1500 10mls N3000
Akwai 20mls N5000, 30mls N7000 and 50mls N10000. Turaruka araha ina mai tabbatar maki kikayi amfani dasu sai kin dawo. Mudae burinmu kowa tayi kamshi na musamman????

Ga number da za a tuntuba kamar haka. +2347065525409
Mami ta koma ?angarenta tana hada sauran ankon da zata tura Drivernta ya kai ma kawayenta da bata tura ma ba Noor ta shigo parlon, hankali tashe tace "Mami Aunty Hassana da Mumy suna ta fada fa tun daxu" Mami ta mike tsaye tana kallonta da mamaki tace "Fada kuma?" Noor tace "Wallahi har da dambe" Mami ta zaro ido tace "Damben lafiya" Noor tace "They are fighting seriously fa a part din Mumy" Mami ta nufi kofa ta fita da sauri, Noor ta bi bayanta, tun daga Babban parlon gidan take jin muryoyinsu suna kunduma ma juna zagi kafin ma ta karasa bangaren Hajiya Amina, tsaye ta ga Janar bakin kofa yana kallonsu, bai kuma yi attempting dakatar da su ba, Suhaila da mai aiki na ta rirrike Aunty Hassana warce ke kokarin kara finciko Hajiya Amina su fara wani sabon damben ga Attachment dinta yashe a kasa Hajiya Amina ta tuge, Hajiya Amina na huci tace "Ku saketa don Allah ta zo, Banza kawai er wahala, kafura...." Aunty Hassana na tura su Suhaila da karfi take cewa "Ku bar ni in illata yar iskar, ni kike kira da er wahala? Ni? Toh wallahi zaki san ni kika ce ma er wahala" Hajiya Amina na tafe hannu tace "An fada, er wahala, dama ba wahalalliyar bace?" Cikin daga murya Aunty Hassana tace "Yanda nayi sanadin aka aureki haka duk abinda zan yi sai nayi an sakeki Amina, wallahi karshenki ya zo a gidan nan, ke banda na shiga na fita ko a er aikin gidan nan kin isa ki shigo balle matar gidan? Waye bai san karuwancin da kika yi ba a baya ba?? Waye bai san har madigo kin yi ba, ke da har London ana booking dinki ki ayi iskanci dake? Banda ni din ina za ki san Janar ki auresa???" Hajiya Amina tayi wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login