Showing 75001 words to 78000 words out of 149166 words

Chapter 26 - Ke alkhairi ce COMPLETE HAUSA NOVEL

BIEBIE   

22 Oct 2024

25742

bata, Ummi ta mata fadan meyasa ta amsa, Mami tace don na ba diyyata kudi shine nayi laifi? Ko iko zaki nuna min kanta ki nuna min diyarki ce, tace "laaaah Mamin Ayman be kai nan ba, ai an fi so diyarki taji tausayinki" Mami tace kya dai ji dashi, gabaki daya sukayi daria.

*4:00pm*
*Layout, Katsina*

"Sannun ku da zuwa, kun sha hanya" Ya mutan Kaduna? Duk suna lafia, Nene ta gabatar musu da Danwaken da ta musu, tana basu labarin zaman kadaicin da tayi, Nasiba tace "Oho dai, ke kika jawo, sai da na ce miki ki taho mu tafi kaduna, ki ka k'i" tace "ke ni ban son mita ba gashi kin dawo ba? Ko wani abun ya kamani?" tace"kin daiyi kewa ta" Nene tace ko kadan, ban k'i ki koma ba, ko a habar zane na" Abbi dai na jin su sai dariya yake musu. Suna cikin cin danwake sai ga Maalesh da Rafeeq sunyi Sallama, da Sauri Nasiba ta kalli kofar zaure don jin muryar shi, sanin kanta ne tayi missing din Hamman ta, shima karaf idonshi kanta wani naunauyar Ajiyar Zuciya yayi, "Finally! shes back" Maalesh kuwa Murmushi ya bita dashi, Maalesh ya matso ya ba Abbi hannu, ko be sani ba yasan Baban Nasiba ne, Abbi ya bashi bayan hannu don yana cin danwake da hannun, Maalesh a ladabce ya gaida shi, Nene kuwa cewa takeyi Sannu da Zuwa Malush, Nasiba ta tashi da sauri tayi kamar zata shiga kichin, daidai yanda zaijita tace "He's my Dad, show some Respect" harara ya bi bayanta dashi, yayi dan guntun gajeren tsaki ya da zata ji shi ita kadai, ya dan matsa kusa da Abii da k'yar yace dashi "Barka da Yamma" Abii yace "Muna lafiya?" Ido Cikin Ido suka kalli juna, nan da nan yaga baban Nasiba ya mai kwarjini, haka kurum ya kasa shiru ya amsa da "Lafiya k'alau, anzo lafiya?" Abbi yace "Alhamdulilah" Nene tace "Ahh su Dunkum yau anyi Wayau" Hararar ta yayi ya dauke kai, Abbi na kallon shi, akwai wani Hikima tattare da yaron, akwai wani abun da ya hango game da yaron, daga gani Yaron dan Baiwa ne, yanda yake abubuwan shi, yana kallon yanda Maalesh ke bin Nasiba da ido, amma shi wannan kallo bata ishe shi ba, haka kurum yaji yana son sanin game da Yaron, bude baki yayi yace "Seebin Nene, zubo ma bak'i danwake" Maalesh Yace "Aa Baba mungode bana cin danwake" "Abokin ka fa?" da sauri Nene tace "Ya k'oshi da dai Fara ne, wannan ko ba a bashi ba zai dauka" duk suka bita da ido cikin rashin Fahimta, dauke kai Rafeeq yayi, Abii ya k'ara cewa "a zubo maka Danwaken?"Kamar jira Rafeeq yake yayi saurin hadiye wani miyau, tun da ya shigo gidan ya ke bin Danwaken plate din Abbi da ido, ya sha Mai, da kayan hadi, yana iya cewa Danwake ne best food dinshi, rabon shi da ci tun Mami na nan, kuma gani yake wannan tsohuwar da gayya take abubuwa don ya nuna ya na son ci ta samu damar Wulakanta shi, girgiza kai kawai yayi alamun aa, in har yace baya son cin danwaken nan to yayi k'arya, har ranshi ya biya, kuma besan dalilin da ya sa Nene keyin duk wani abun da yake son ci ba, shi da abinci be damai ba, tsaki kawai yayi, Duk abunda yakeyi a idon Abbii, ya kalli Maalesh yace "ya sunanka?" Maalesh cikin ladabi yace "Sunana Mahmud" Nene tace "laah gaka da suna me dadi amma ka yarda ake ce maka Malush" daria kawai yayi, Abii ya maida hankalin shi kan Rafeeq da kwatakwata ya dauke kai, yace "Kai fa ya Sunan ka?" Rafeeq yayi kamar be ji ba, shi kuma Abii be sake tambayan shi ba, Nasiba kuwa jikin ta ya fara rawa, bata so Rafeeq yayi banza da mahaifinta, bata so mahaifinta ya tsani Rafeeq kan halaiyar shi, da Rafeeq yaji shiru, ba a sake tambayan shi ba, ya dago kai a hankali ya kalli Abii, shima shi din yake kallo, gajeren tsaki yayi a hankali yace "Sunana Rafeeq" Abii ya jishi sarai, yace "Banji ba" kamar ba zai tanka ba, amma Abii ya mai girman da ba zai iya share shi ba, ya dan bude murya yace "Sunana Rafeeq". Abii ya jinjina kai, Rafeeq yayi Zumbur ya mik'e sabida yana jinshi wani iri gaban Abii, ganin haka Maalesh yace "to Nene mun gaida ku, bari mu wuce" tace "Toh Malush mungode, su Dunkum a gaida gida" tuni ya kusa Zaure, Abi ya bude murya yace "Rafeeq" k'yam ya tsaya ya kasa tafia, da k'yar ya juyo, Abii ya kalli Nasiba yace "Je ki zubo mishi Danwaken" a hankali Rafeew yace "Nak'oshi" Abbi yace "Ka tafi dashi anjima sai kaci" dama tuni Nasiba ta cika Umurnin Mahaifinta, ta kawo ma Rafeeq Coolern, dauke kai kawai yayi, ganin haka yasa ta ba Maalesh Coolern, Maalesh ya amsa yayi Godia, ya ja Rafeeq suka bar Gidan. Nene tace "Yau kam me ke damun Dunkum?" Abii ya zauna yace "Seebin Nene, Wanene wannan? Me kika sani game dashi?" Gaban Nasiba ya yanke ya fadi, Nene tace " ai wannan shin d'an Zaidu Bawan Allah da na jima ina baka labari, shi haka yake, wani Dunkum, ba fara'a, ba ilhamar fuska, yanda kasan takashin shanu, haka fuskar shi take murtuk'e kullum" Abbi ya jinjina kai, yace "Seebi, bakin ki akwai Magana, me kikasani game dashi? Ni na hango bak'in duhu tattare dashi" Nene tayi karaf tace "bawani bak'in duhu, Fadin Rai ne kawai ya mai yawa" Seebi tace "aa Nene, akwai wani Labarin da ban sanar dake game da Rafeeq ba, kunji kunji••••••••••. Tsaf ta kwashe labarin Gidan Lema ta basu, kamar yanda Baba Maigadi ya sanar da ita, kamar Yanda ta gaya ma Mami, Ta dai b'oye Mafarkin da take da Rafee'ah. Allahu Akbar inji Nene "Allah Sarki Dunkum, ashe ba yin ka bane, Lallai akwai B'oyayyen Alamari a tattare da Gidan nan, ni gaskia ina zargin matar Baban su" "aa Nene kar kiyi saurin zargi" "tace dole iz zargeta mana Mahamman, ita kadaice zata yi hakan" Abbii yace "kamar yanda shi da kawun shi suka taimaka miki lokacin da baki da lafiya, InshaAllah zan taimaka mishi da wasu Adduoi, kuma kafin in bar Katsina zanje gun Abokina Me *Arriyadh Islamic Medicine* a taimaka mishi da magunguna, har shi mahaifin shi, in ma akwai Kaidin Mace da yardar Ubangiji komai zai warware cikin iko na Allah" Nene cikin jin dadi tace "Yauwa dan Mallam Jikan Mallam, da ba ka shashanatar da kanka kan boko ba, da yanzu ni nasan kai babban Malami ne da ake tak'ama dashi a k'asa baki daya, yanzu ma na san zakayi k'okarin ka" Nasiba kuwa bata san kalar Farincikin da zata yi ba, hak'k'un ta yarda da Mahaifinta, kuma ta na murnan zai taimaka ma Rafeeq, sai dai su Rok'i Allah ya basu nasara.

_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

Assalam Alaikum, ina muku fatan Alheri, ina godia da yanda kuke biye dani a wannan labarin, ina me baku hak'urin rashin ji na da kukeyi kullum, hakan na faruwa ne saboda wasu 'yan dalillai, kuyi min uzuri don zan dinga tsallake kwana daya banyi typing ba, in kuma an samu yanda nikeso, zaku dinga jina kullum kullum, Nagode Allah bar zumunci.

Pg4⃣5⃣

Abbii da Nasiba gaban Mallamin *Arriyadh Islamic Medicine* bayan Abbii ya karanto ma Mallam Matsalolin Gidan Lema. Mallam Usman ya jinjina kai, yace "Alhamdulilah, wannan labari da kuka bani akwai 'kulalliya, ko ba sihiri zamu taimaka da adduoi, balle wannan ma daga ji an san akwai Sihiri, ta iya yiwuwa Shi Alhajin an sa shi ya mance Uwargidansa, tunda kunce be sake waiwayarta ba, sai kuma shi Rafeeq baa so ya gama Makaranta tunda ance shekarar sa ta biyu kenan yana maimaita aji, kuma ba wai don ba ya ganewa ba, kuma ba ya k'aunar uwarsa, alhalin duk yanda Uwarka take to akwai wannan So da K'auna dake tsakanin su, toh tabbas akwai Mak'arkashiya a ciki kuma InshaAllah zaa warware komai da yardan Ubangiji. Abu na farko;
Ina so su sa a ransu cewa duk abunda ya samu bawa to da yarda da ikon Allah ya same shi. Su kasance masu Adduoi da Tauhid, Zaa musu magani duka, Shi Alhaji zaa bashi maganin da zai taimake shi ya tuno abubuwan da suka faru a baya, shi kuma Rafeeq zaa bashi Maganin da zai sa mai dangana a ranshi, yanda zai yafe ma Mahaifiyar shi, wani Jarka Mallan ya dauko, yace "Wannan Ruwan Karatun Kurani mai girma da Addu'oin Shifa, Lallai Rafeeq da Habib su maida shi ruwan Sha din su, in so samu ne ko abinci a dinga dafa musu da shi, shi zai tsare su daga Sharrin mai Sharri" ya ciro wani robar swan, yace wannan kuma Man itattuwa ne, Man Habbatussauda, Man Ridi, Man Hulba, Man Zaitun, Man tafarnuwa, Garin Luban, da Adduoi kama daga AmanarRasulu, Ayatul kursiyu, da zikirin Safe da Maraice, Wannan na Rafeeq ne, shi ne zai saka mishi Salama da dangana a rai har yaji cewa yana son sanin abun da ya faru a wannan bak'in rana. Sai Kuma Saukar Alkurani da zaa musu sai ayi tawassali da Karatun sai a rok'i Allah ya baiyanar da Gaskia. Amma dole sai sun yarda da hakan, maana sai sunyi Imani da Allah shi zai firda su daga Abun da ya shige musu duhu".
Abbii yayi Godia Sosai, yace "InshaAllah zaayi yanda kace Mallam Usman, Nasiba kina ji ko?" Nasiba da zufa ya gama keto mata, tana tunanin yanda zaa sa Rafeeq shan wadannan Magungunan. Da sauri ta gyada kai, tace "Eh Abii, zaayi yanda yace" yace to Madallah. Magungunan Dubu Sha biyar ne, amma saboda Sanayyar da ke tsakanin Mallam da Abii yace su bada dubu 10, kafin Abii yace wani abu Nasiba ta zaro kudin da Mami ta bata ta mika ma Mallam, Abii ya bita da ido, ta shaida mishi "ai kudin da Mamian Ayman ta bata ne" haka suka dawo gida cikin Keke Napep.

"Tabdijam, ai yanda ka bashi Magungunan nan haka zai dire maka su don ba sha zaiyi ba Wallahi" cewar Nene bayyan sun bata labarin abunda ya faru a Islamic center, Nasiba tace "Abii ka kirashi ka mai Magana k'ilan idan yaji daga bakinka, ya dinga sha" Abbii ya jinjina kai, yace "Kira min shi a waya" da sauri Nasiba ta amsa wayar Abii ta sa mai Number Rafeeq tayi dialing, Wayar ta dade tana ringing, har ta gaji da ringing ta mutu, kallon Abbi tayi tace "be dauka ba" Nene tace "ina zai dauka yasan zaku sa shi magana, Abii yace "sake kiran Shi" Nasiba ta sake kira, sai da ya kusan tsinkewa ya daga, dama yana ganin kiran farkon, ganin be san number ba yaki dagawa sai yanzu, Karawa kawai yayi a kunne ba tare da yace komai ba "Assalam Alaikum" muryan Abbi ya ratsa mai kunni, zumbur yayi ya mik'e, sai dai ya kasa amsa Sallamar, Abii yace "Rafeeq, in ka samu lokaci, kazo gidan Nene yau ina jiranka" Abbii be jira amsar Rafeeq ba ya kashe wayar, Rafeeq ya tsura wa Wayan Ido kamar zai ga Abii a hankali yace "Why is he Bossing around?" guntun tsaki ya koma ya kwanta.

Da kyar ya iya cewa "Assalam Alaikum" Abbii ya amsa tare da umurtan shi ya shigo, ya shiga ya zauna kan tabarma, Nene da Nasiba na ciki, basu san shigowar shi ba, Abbii ya tsura ma Rafeeq ido, guntun tsaki yayi yace "Barka da Yamma" Abbii yace "lafia lao Rafeeq, ka ci Abinci?" samun kanshi yayi da girgiza kai alamun "aa" Abbi ya ciri baki ya kira Nasiba "Seebin Nene, zubo ma Rafeeq Abinci" Nene ta kalleta tace "Dunkum yazo ne?" Seebi tace "ya zaayi in sani ni da muke nan zaune dake" Nene ta kai mata duka tace "Tambayar ki nayi ba ce miki nayi ki gayan magana ba". Rafeeq ya kalli Abii, yana so yace mishi kar a zubo mai abinci amma ji yayi bakin shi yayi nauyi, ya kasa Magana, shi besan dalilin da yasa yake jin shi wani iri gaban Baban Yarinyan nan. In ma dai girma ne Daddyn shi ya girme Abbii Nesa ba kusa ba, guntun tsakin mts yayi, Nene ta zubo mai Shinkafa da Miya, da lettuce a gefe, tazo ta ajiye mai, karaf idon shi ya kai ga Zoben yatsan ta, kafin ya samu damar sake ma Zoben kallo ta tashi, tace "Hamma Ina wuni" bata sa ran ya amsa ta ba ta koma cikin daki, Abbii yace "Bismillah" ba musu ya ja plate din gaban shi ya fara ci a hankali, be ci da wani yawa ba ya ture, Abbi bece komai ba yace "Rafeeq" Kasa amsawa yayi ya dago kai ya kalleshi, Abbii Wani makaranta kake? A k'agauce yace "Umyu" wani Course? "BioChem" Abbii yace shekarar ka nawa a School din? Da sauri Rafeeq ya kalleshi, Abbi ya mishi alamun ina sauraren ka, guntun tsaki yayi yace "6years" Abbii yace "Spilling kake tayi?" "Uhm" kawai yace don baban Nasiba ya fara k'ureshi, "Let me help you" a dan tsawace yace "I dont need your help" Shiru Abbii yayi ya kawar da kai gefe, ganin be kyautu a ce ya daga ma Babban Mutum murya haka ba yasa shi cewa "Look i'm sorry, but i dont need your help". Ya mik'e zai tafi, Abbii beyi yunkurin hanashi ba don yasan dole Rafeeq zaiyi wuyan Sha'ani, amma zai lallaba shi har ya yarda.

"Dunkum Yazo daki ya gaida ni, k'afana na ciwo" chak Rafeeq ya tsaya shi beyi gaba ba shi beyi baya ba. Me wannan tsohuwar ke nufi da shi ne, kamar yayi gaba kuma sai ya tuna She's Uncle Zaid's Favourite, in har ta kirashi ta gaya mai bata da Lafiya, to tabbas zai maido shi yace yazo ya dubata ko kuma ya kaita Asibiti, kuma dole ya buge mata warning, ta daina ce mai Dunkum" Dogon tsaki yayi ya dawo ya wuce Abbi, ya cire Takalma gaban daki ya shiga ko Sallama, Nasiba na ganinshi ta mik'e tsaye, bata yi tsammanin zai dawo ba, ko kallo bata ishe shi ba, ya kalli Nene cikin b'acin rai yace" ki daina ce min Dunkum, ba sunana kenan ba" Nene tayi daria tace "Au haba? Ashe ba sunanka kenan ba, ai ni bansani ba, duk zato na sunan ka Dunkum, ya sunanka? Cikin daga murya yace *"I am Rafeeq Freaking Lema* "get that into your Oldie Skull" Nasiba cikin rudu tace "Heyy, Watch It" ya juyo ga Nasiba a fusace yace "Warn your GrandMother She should Stay the Hell away from me, you all should" ya bar Wurin a fusace be ma lura da Abbii baya nan ba ya fice, Nene ta bude Murya, "Sunanka Kenan Dunkum dangin tsaka, har sai randa ka koyi Magana kuma ka bar tsaki, rannan zaka koma sunan yanka ka, amma yanzu dai muje a Dunkum din" yana jinta amma be tsaya tankata ba, don ya san ya sake bude baki yana iya fashewa da kuka.

"Nene meyasa kike ce mai Dunkum? Ki bari donAllah, kinsa shi ya tunzura har yana gaya miki magana, Gudumuwar da zaki bada wurin ganin Ya warke kenan?" cewar Nasiba, "Ke dallah rufen baki, kinzo kina min fada kamar Inna Ladingo(Maman Nene) ni ko zan bada Gudummuwa babba wurin saito Rayuwar Dunkum, Gundunmuwata daya shine zan taimaka in dinga sa shi yana magana ko ya k'i ko ya so, tun beyi har yazo ya saba ya dinga magana, kuma wannan shegiyar tsakin, dole sai ya bari, in yayi tsaki har k'walkwata wallahi, amma dai yanzu ya daina ban haushi tunda na fahimci cewa ba yin kanshi bane, be 6atan rai, tun asali ma be 6atan rai, shirun shi da miskilancin shi ne bana so, kuma dole sai ya koyi magana" Seebi ta kalli Nene ta girgiza kai "to wa ya ce miki ana so ya dinga magana, miye matsalarki da rashin magana?" "ke tafi chan, ke me kika sani? Sai ya koyi surutu ko yana so ko be so, wata rana kuma sai ya gode mun dana bada guddumuwa gun sa shi magana" Daria kawai Nasiba tayi tace " ta ina bayan kin korashi, bana tunanin ko gidan nan zai sake zuwa" Nenen tace "Lallai yarinya baki sanni ba, ai ni ba wanda ya isa ya shareni, ko ka shareni kan ka ka mawa, shiyasa lokacin ina kamar ki banjin komai don saurayi yace ya fasa, don ba a kwana zai dawo, kar ki damu da sannu Dunkum zai kawo kanshi" daria Nasiba tayi tace "yo ai ko halinki ya isa ya kori saurayi, nasan lokacin ki an sha gwagwarmaya da ke" Nene tayi shewa tace "Kamar kinsani, duk samarina sun sha masifata, Kakan ki kadai ne ya kasa ya tsare yace sai Aminene" ta girgiza kai tace "Allah ya ji k'anka Mallam, ka cika masoyi na hak'ik'a" Nasiba tayi daria, Nene ta cigaba da bata Labarin kalan Soyayyar da sukayi da Kakan Nasiba.

Ashe yana binshi a baya har ya isa gida, yana jin duk abunda ya faru tsakanin Rafeeq da Nene, yanda ya fito daga gidan rai a bace ya sa shi binshi a baya har ya banka gate din gidan su ya shiga a fusace, Baba maigadi ya mik'e yana cewa Rafeeq Lafiya? Banza yayi da shi yayi hanyar dakin shi, Sallama Abbii ya ma Baba Maigadi, suka gaisa a mutunce, yace "gun Rafeeq nazo" Baba Maigadi ya kalleshi yace "Anya zaka so gannin Rafeeq a halin da yakr yanzu? Yanzu ya shigo gida rai a bace" Abbii yace "ba damuwa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login