Showing 60001 words to 63000 words out of 149166 words

Chapter 21 - Ke alkhairi ce COMPLETE HAUSA NOVEL

BIEBIE   

22 Oct 2024

25722

sentence din da ya fi biyar? Kuma ba da Uncle Zaid ba ko Maalesh? Lallai abun mamaki tsaki yayi yace ma kansa "I wont let this girl affect me, shes not Rafee'ah, stop getting into my head" Jiki a sanyaye ya kunna mota ya bar gurin.

*"Allah sarki ashe Nene bata ji dadi ba? dole kam muje mu dubo ta after School"* Miemee gayu ke maganar nan, Usheey tace "gaskia kam da mun gama lectures sai muje mu tari Bus" hankali Seebi be gunsu, tunanin diramar da sukayi dazun da R-Lema takeyi, lallai ta yi k'ok'ari.

Miemee ta zungure ta, kina jin mu kuwa? Firgigit ta gyada kai, suna mamakin sabon haliayar Seebi, amma dai ba su ce komai ba, haka suka cigaba da lectures har karfe 2.
Da sauri suke tafia amma sun makaro, Buses sun tafi, sai sun jira dawowar su, Usheey, tace da muyi ta Wannan jiran, gwara mu taka bakin gate mu tare su a chan, kafin suzo nan duk mazan nan su shige su bar mu, kunga anyi ba'ayi ba" haka suka dauki hanyar gate suna fira jefijefi, banda Nasiba da ta lula duniyar tunani, kamar daga sama ta ji horn din motar shi, waswasi take anya kuwa shine? Miemee kuwa tuni ta fara gyara zaman rigarta, tana fadin "kunga wata Azababben mota na mana horn?" a tare suka juya ga motar, gaban Nasiba ya fadi ganin motar Rafeeq, bata son su Miemee su san halin da suke ciki, a dabar ce tace "kun ga dai kuzo mu wuce" Miemee tsce wlh idan ba ku shiga ni sai na shiga" Usheey tace "muje Seebi, ba mu san lokacin da za mu bar Makarantar nan ba, muje kawai" Miemee tace daga ganin wannan gayen Ya Azabtu, don ba kowa zaki ga an bar shi ya shigo da Tint makaranta ba, Allah kasa yace ya na sona" Seebi kawai sai taji daria ya zo mata, a ranta tace "Lallai Miemee, indai Rafeeq ne zaice yana sonki to zaki bushe". Usheey tace kun ga dai kuzo mu shige kafin ya chanza raayin shi, Miemee ce tayi gaba suna binta a baya, ta bude k'ofar gaba ta shiga, Seebi tayi murna da hakan fatan ta daya kar ya nuna ya santa, ita da Usheey suka shiga Baya, Waiyo Allah Miemee na ganinshi taji wani irin dadi, tana fari tace "Ina wuni" Usheey ma ta gaida shi, bece komai ba ya kunna motar shi ya bar wurin, suka bar makarantar suna tafia, Miemee ta sake cewa "sannu fa? Ya School?" nan ma ba amsa, daga baya Seebi ta rada ma Usheey a kunne kar ki sake magana, ta dinga zungurar Miemee ta baya don tayi shiru, amma Miemee Zak'al taki yin shiru, wai kai baka magana ne? K'iiii ya taka burkii, ya gangara k'asan titi yayi parking, tsaf Seebi ta gane me yake nufi, yana nufin su fitar mai a mota don Miemee ta dame shi, idan ya bar su a dajin nan ai be kyauta musu ba, Miemee da fi'ili tace "yadai motar ce ta lalace? A hankali yace "Get Out" da mamaki Miemee da Usheey sukace "What?" cikin dan daga murya yace "ku fita nace" a tsorace suka kalle shi, Usheey tace DonAllah BawanAllah kar ka aje mu nan, kaga nan ba inda zamu samu abun hawa, ka taimaka ka kai mu ciki gari, be ce komai ba, be kuma tada motar ba.

Ba tayi niyyar magana ba amma tasan hali nai, ba zai tafi ba har sai sun bar mai motan shi, daidai yanda zai jita tace "kayi hak'uri Hamma" ta mirror ya kalle ta, yayi dan guntun tsaki, ya kalli Miemee yace "kina da hayaniya" da sauri tace "yi hakuri, ba zan sake magana ba" ta bude murfin motar ta fita ta zagaya gun da Seebu ke zaune ta bude, "inshort Seebi koma gaba donAllah ke baki da hayaniya" Daria suka bata su duka, ta bude murfin motar ta fita ta koma gaba, ta na rufe wa kuwa ya ja motar shi ya bar gun, ba wanda ya sake magana har suka shigo cikin gari, a Royal Reataurant yayi parking ya fita, suka tsaya kallon kallo, ko cewa zaiyi su fito, yayi shigewar sa abin shi, Usheey ta tuntsire da daria Seebi ta taya ta, dariar da suke rik'ewa tun Batagarawa, Miemee ta hade girar sama da ta k'asa, sai da sukayi mai isar su, Usheey ta kalli Miemee tace "kina da hayaniya" Seebi ta sa daria, Miemee ta harare su tace its not funny wallahi, Wannan wani irin Guy ne? Kullum cikin k'unci, kun ga fuskar shi murtuk'e?amma fa hakan be hana kyawunshi fitowa fili ba" Seebi ta girgiza kai tace "kina da damuwa" duk suka fashe da daria, suna ganin ta fito duk suka yi shiru kamar sunga wani dodo, dauke yake da ledoji a hannu, ya bude motar ya ajiye wurin kafar Seebi, ya ja mota ya tafi, tafia sukeyi, shi be tambaye su inda zai aje su ba, Miemee ta rada ma Usheey ince mishi ya aje mu nan? Usheey tace baki daddara ba ko? To ba ruwana, duk suka ja baki sukayi shiru, mamaki ya cika Usheey da Miemee da suka gansu a Asibiti, to ko da ma ya san nan zasu zo? To waya gaya mai? Seebi ce ta fara bude motar kafin su Miemee, duk suka mai Godia, be ce komai ba, sauri sauri Seebi ta bar gun suna binta a baya, ya juya ya kalli ledar da ta bar mai a mota ya buga tsaki da k'arfi, ni ta bar ma Abinci?ni me zanyi dashi? Tsaki ya sake bugawa ya kwashi ledojin zai shiga Asibitin kenan ya ga Baba Maigadi, yayi mamaki amma be nuna mamakin sa ba, illa dauke kai da yayi dob be san tambayoyi, da sauri Baba maigadi ya karaso yace "Ahh Rafeeq me kazo yi a Asibiti? Nuna mai ledojin hannun shi kawai yayi, Au abinci ka kawo wa wasu? Ya gyada kai, yace "Nima wata makwabciyar mu nazo duba wa" da sauri Rafeeq yace "Nene?" da mamaki yace "eh ita" ko da yake ba abun mamaki bane tunda Nasiba ta san shi, amma dai Aminene ta ciri tuta tunda har Rafeeq zai zo dubata harda karin ciwo, Rafeeq yace "Baba ka kai musu wannan inji Uncle Zaid" "ya dawo ne?" tsaki Rafeeq yayi yace "baba ka amsa" da sauri ya amsa Rafeeq yace "daki na sha2" don kar ma ya sake sa shi magana ya juya ya tafi, shi ko Baba maigadi ya wuce cikin Asibitin.

Miemee da Usheey suka ma Nene Sallama, Seebi ta fito rakasu, a bakin k'ofa suka hadu da Baba Maigadi, ta gaida shi, tace "baba barin raka k'awaye na, yauwa 'yar baba je ki dawo ina nan" sai da ta rakasu bakin gate din Asibitin ta dawo, yana nan inda ta barshi, yace "ya jikin Aminene? tace "da sauk'i" yace "gashi inji mutumin ki Rafeeq, wai inji Zaid" ya mik'a mata ledar, ta bi ledojin da ido, ohh dama na su ne? Lallai Rafeeq a gaishe shi, tace "Yanzu muka rabu, be ce min namu bane" ai na mayi mamakin ganin shi anan, bayan abun da ya faru yau da safe a gida" da sauri tace "Baba Me ya faru yau?" Ya kwashe komai da ya faru tsakanin Rafeeq da Baban shi da su Aneesa, harda abunda Saude tace da martanin da Aneesa ta mayar, Nasiba ta tsorata, tace *"Baba kar suyi mishi wani mugun abu, Dole Rafeeq ya dage da Adduo'i, zan tambayi baba na ya rubuto min adduoin tsari"* Baba Maigadi yayi murmushi yace "lallai Nasiba, baki san waye Rafeeq ba, Yo Allah na tuba Sallah kadai Rafeeq keyi don ya zama dole yayi shi, to tsaya kiji, Rafeeq be Sallah a Massalaci baya jam'i, sai a daki, kuma da ya idar yake tashi, baya addua a ganin shi be da bukatar wani abu da zai rok'a, be da saurin jin dadi, shifa yanzu be k'i ace ya mutu ba, a takaice dai Rafeeq baya Addua" Nasiba ta fashe da wani irin kukan da bata san lokacin da ta fara shi ba, cikin kuka tace *"Waiyazubillahi, wani irin Masifa ce wannan? Wane irin mugun hali yake son jefa kanshi ? In banda abun shi wa ke cire rai daga rahamar Allah? Waye baya da bukkata gun Ubagijin shi?"* cikin Masifa da dacin rai kamar tana gaban shi tace *"R-Lema kana cikin 6ata Wallahi, kuma ko ka k'i ko ka so sai ka dawo hanya"*

_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

This is for you *Maryam AD Bappa(Umm Eeman)* Thanks for Everything ILY❤❤❤
Pg3⃣9⃣

Nasiba ci kukan ta ita kadai, ta share hawayenta, ta kimtsa fuskarta gudun kar nene ta ishe ta da tambayoyi, suka dunguma zuwa dakin tare da Baba mai gadi. Kowa da abun da yake sak'awa a ransa.
Shigar su dakin yayi daidai da fitowar nene daga bandaki, inda ta dauro alwala zatayi sallah, Hajjo kuma na zaune kan darduma tana lazumi.
Nene ta washe baki ganin Baba maigadi suka hau gaisawa, yai mata ya jiki, Seebi kuwa duk yadda taso ta boye damuwarta ta kasa, Nene ta dan gane yar jikallenta na cikin damuwa, ta tambaye ta "ko lafiya?" Seebi tace "Nene ba komai, gajiya ce kawai amma nasan in na dan huta zan ware" Nene ta amsa da to Allah huta gajia.

Bayan tafiyar Baba ne suka zauna suka ci abinci su ukun duka, suna kammalawa Seebi taja gefe ta rusuna tana tunanin ta inda zata fitowa *R-LEMA* don tabbas rayuwarsa na cikin gagarumin hadari.
Kuma He is proving so difficult to deal with.
Haka ta dinga 'yan tunane tunanen ta, ta sak'a wannan ta kunce wancan har bacci ya dauketa ba tare da ta samu mafita ba.

Yau Alhamis kwanan su hudu kenan a Asibiti.
Seebi ta idar da sallar Asubah ta kammala adduoin ta, littafanta ta janyo ta dan dudduba don tana da lectures 9am kuma Malamin ya iya test din bazata.
Bayan ta gama revising ne ta rufe ta maida komai cikin jakarta, ta saka Hijabi kan kayan baccin dake jikinta tare da gyara fuskar ta sama sama don batayi wanka ba,
tayi wa nene da hajjo sallama ta wuce gida don shirin Makaranta saboda sauran kayan da ta da ke Asibitin sun yi Datti.

6:50 ta isa gida, sai da ta share gidan ta ta gyara ko ina kafin ta fada toilet tayi wanka ta shirya ta, ta fito Gida 7.55am. Sauri take ta isa bakin titi don ta samu abun hawan da zai kaita National don kar tayi missing Bus.

Kamar kullum, Tuk'in shi yake cikin qasaita, daga nesa ya hangota, kamar ita kamar ba ita ba, kai itace, wannan yarinyar ce, a ransa yace "Wannan kuma me takeyi a nan? (kuji se kace be san nan gidansu yake ba) guntun tsaki yayi yace "Da naje daukan ta a Asibiti da nayi zuwan banza kenan" ya sake wani tsakin kamar yana gabanta. Horn taji da karfi, da sauri ta dode kunnenta tare da juyawa a k'ufule don ganin me neman kashe mata dodon kunne, ita da ba kan hanya take ba, Idonta ya kai ga Motar Rafeeq, haka kurum taji dadin ganin shi duk da ta san ba wai kulata zeyi ba, ko ba komai, ba zatayi latti ba, kuma zata samu daman mishi magana.

Bude motar tayi ta shiga don tasan ba ce mata zaiyi ta shiga motar ba, cikin wata muryar da bata san tana da shi ba tace "Ina Kwana Hamma Rafeeq"
Jan motar shi yayi, ya dau hanyar school yayi kamar be jita ba, har ta cire rai da zai amsata, don sunyi tafiyar kusan 4mins kafin taji yace *"lafiya"* da mamaki ta kalleshi, ta ma manta da ta gaishe shi, a ranta tayi dariya tace *"bakasan waye jikar nene ba sai ka dawo hanya da Yardan Allah"* wani kwarin guiwa taji, ta gyada kao tace "i can do it" Cikin sigar shagwaba tace *"Hamma na please..."* sai kuma tayi shiru tare da duban sa.
Wani uban tsaki ya buga da sai da taji tsoro, ya maida hankalin shi ga tukin sa, don duk yanda ta kirashi da *"Hamma Rafeeq"* sai numfashin sa ya dauke, balle yanzu da ta zak'e wai *"Hamman ta"* "wannan yarinyar ta fara koyon surutu, ta fara zak'ewa"
Kamar ba zai ce komai ba yace " what?" ta ji dadi tare da samun karfin guiwa, tace dama zance ko in munje wancan shagon zaka dan tsaya na sai Ziza Milk, don banci komai ba ina sauri kar nayi latti.

Besan lokacin da murmushi ya subuce masa ba, cikin sakwan da be wuce 2 ba ya daure fuska, a ransa yace "what is funny?" ji yadda take sunne kai kamar mara gaskia, lazy girl she cant even skip breakfast. Be dai ce da ita komai ba

Daidai wani shago ya tsaya, tayi murmushi tace "yawwa Hamma na Nagode" Ta dauki jakarta, tana k'okarin bude kofar taji ya bude tasa kofar ya fita tare da rufowa. Gyada kai tayi cike da tausaya wa, don shi duk abunda yakeyi bata jin haushin, illa ma tausayin da yake bata. Be dauki lokaci ba ya dawo da leda kunshe da soft drink da kuma date bars ya aje mata kan cinya, ta masa godia suka dau hanya.
Ta bude jakarta don saka ledar a sama ta tsinci muryar sa *"EAT NOW"* tace " *to Hamma na*. Ta bude tana ci har suka iso School, har bakin Department dinsu ya kaita, kimtsa bakin ta tayi masa godia ta fice. Shikuma ya ja motarsa ya k'ara gaba.
Yana wucewa ta sauqe wani gauron numfashi tace "Wai Allah nagode maka da ka sa min dauriya, Allah ka kara shige min gaba Ameen"

Zaune take gefen nene tana waya da Uncle Zaid, inda take sanar dashi cewa Nene ta warke, likita yace zuwa magriba zai Sallamesu. Uncle zaid yace "Alhamdulillah, Nene ta ji sauk'i, idan anyi sallamar ki sanar dani" tace "toh"
Ta masa godiya suka yi sallama. Ta miqe ta shirya tace "Nene zan shiga makaranta bani da lecture, amma ina da Assignment din da zanyi submitting kafin lokacin sallahr Juma'a, da an gama sallahr Jumaa'h zan dawo wuraren k'arfe biyu, sai a hada kayan kafin likitan ya zo ya bamu Sallama".
Murna gun Nene kamar me, tace "wlh dama na gaji da Asibitin nan, Mutum da lafiyarsa amma an kawo Asibiti an ajiye, amma fa zanyi kewar 'yar gasasshen Kazar da dunkum ke kawowa" (Dunkum ne sunan da Nene ta sa ma Rafeeq) ba Seebi ba harta Hajjo dake gefe sai da ta dara tace" Kai k'awalliya, jika na ne Dunkum?" Nene tace "yo ehmana, ayi mutum shi he daria, be murmushi be magana? Hajjo tace "lamarin Rafeeq sai du'ai, haka yake" Nene tace "Shiyasa na rik'e furfurata, ba ruwana dashi, don in na mai magana ya share ni, ina iya kulle shi daki karfe ukun dare inci Ubanshi, dan uban mutum" me Hajjo da Nasiba zasuyi in ba daria ba, Nasiba har da kwallah, Hajjo tace "Lallai Nene Lafiya ta samu" Nene tace "dama garas nike, uwayen fiili suka daura man zaman dole a Asibiti, wato Seebi da Zaidu bawanAllah" Nasiba dai ba ta tanka ba.
Dan zaman da sukayi na kwanaki biyar Hajjo da Nene suka Saba don Nene akwai surutu da saurin shiga rai, hajjo kuwa akwai barkwanci..

Ku daga daga k'afa mu isa on time kunga yau Friday, Buses cika zasuyi da wuri. Seebi ce mai maganar nan, Usheey tace "in ba haka ba sai mun ci uwar trekking kafin mu samu naAllahn da zai bamu Lift.

Kamar Baki, ga Buses har uku amma duk a cike mak'il har bakin K'ofa, Seebi ji take kamar tayi kuka don haushi.
Tasan Nene na chan na zuba idon ganin ta, ita da ce mata 2 zata dawo, gashi har uku.
Miemee ta bada shawarar su fara takawa Ko Allah zaisa su samu lift ko kuma rage hanya kan Buses su jiyo atleast yafi tsayuwar.
Usheey tace "Miemee don Allah in za a bamu lift yau kar ki yi over sabi please" Seebi na gimtse daria tana fuska, Miemee ta daure fuska tace "Munafuka, say your mind" Seebi tace "Kina da Hayaniya" Miemee tace "Kuna da damuwaaa" ai kuwa duk suka fashe da daria, Miemee tace Wallahi gayen nan ya mugun raina ni" sukayi daria suka fara tafia.

Tafia suke tayi, sun danyi nisa sai ganin motar R-lema sukayi a gaban su, basu tsaya wata wata ba suka nufe motar, Seebi zata bude kofar baya ta shiga Usheey ta buge hannun tace "donAllah shiga gaba kar ya chanza raayin shi" Miemee ta harare su tace dama ce muku akayi zan shiga gaba? Seebi ta shiga gaba duk suka koma baya, a tare suka gaida shi, kai kawai ya daga musu, ya ja motar shi ya tafi, ko da suka iso cikin gari ya kalli Ushee ta mirror kamar zai yi magana sai fasa, tsaf Seebi ta dago shi, so yake yace dasu Usheey ina zai sauke su amma ya kasa, Seebi tace "DonAllah ta wurin Asibitin Dr Dara kayi?ni nan zan sauka" Shiru yayi kamar be ji ba, ganin be da niyyar tsaiyawa ya sa tace "Kana iya ajiye mu anan" kamar jira yake kiiii yaci burki, yayi parking, Usheey da Miemee suka mai godia ko uffan be ce musu ba, suka bude suka fita, Seebi zata bude k'ofar kenan ta fita ya sa lock, su Miemee na kullewa ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login