Showing 9001 words to 12000 words out of 149166 words

Chapter 4 - Ke alkhairi ce COMPLETE HAUSA NOVEL

BIEBIE   

22 Oct 2024

25710

tare da ririke mai hannu gam, ba yau ta fara hawan jirgi ba, amma Duk sanda jirgi yazo tashi haka take tsintar kanta cikin tsananin tsoro.

Sai da Jirgi ya daidai ta a sararin samaniyya ta dawo hayyacin ta, da sauri ta kalli Habib baki bude, tace "donAllah kayi hakuri, i'm always like this duk sanda jirgi zai daga" Habib ya kalleta baki bude, yace "dama kinajin hausa" ta harareshi cikin sigar wasa tace "wai ma, ga zahiri ka gani"

Habib dai kasa magana yayi, yana satar kallon ta. Kwata-kwata bata yi kama da bahausa ba, tafi kama da larabawa, a hankali ya karance ta; Fara ce sol, mai siririyar fuska, hancinta kamar fensir, tana da dan tsawo, sanye take da bakar Jallabiya ta nade kanta da bakin gyale, kai duk yadda akayi ta hada iri da Larabawa. Tana sane da irin satar kallon ta da yake yi, murmushi kadai tayi ba tace komai ba, ta ciro wani novel daga cikin handbag dinta.

Habi dai ya kasa hakuri sai da ya tanka ta, yace " Erhm, amma ke ba bahaushiya bace ba ko?" ta dan daga kai sama tarw da murmushi tace "bahausa ce mana, bakaji hausa na radam ba amma meyasa kace haka?" yace "anya kuwa ke hausa ce?" kila zama da hausawa ya sa kika iya hausa, ko kadan bakiyi kama da hausa ba kinfi kama da balarabiya" dariya takeyi sosai, tace toh Baba na bahaushe ne gaba da baya mama tace yar kasar lebanon" Habib ya dan tafa hannayen shi biyu, yace "Ahap, ga magana nan ta fito, kin dai hada jini da Larabawan" dariya tayi, haka suka cigaba da fira har suka iso Aminu Kano Airport.

Bayan sun gama Clearance ne suka fito wajen Airport din, Habibullah yace "nan garin kike?" tace "aa, katsina nake" Habib ya zare ido yace "Lah,ashe yar garin mu ce" yace toh zaa zo daukan ki ne? Tace noo ai bama su san yau zan dawo na, i want to make it a suprise" yace "that's nice, toh muje mu yi shatar motar chan" ya fada y na nuna motar kwamkwasiya da sukayi layi a chan gefe, tace "kar ka damu, i can take myself home" ya harareta ba tare da yace mata komai ba ya ja trollyn ta ya yi gaba, bata da zabin da ya wuce ta bishi a baya tana murmushi.

Kafin ta isa har sun daidaita da da mai motar ya sa akwatin ta a booth, Habib ya bude mata baya yace "Bismillah", ba gardama ta shige baya, shi kuma ya bude kofar gaba ya shiga direba ya ja suka dau hanyar Katsinan Dikko dakin kara.

Karfe 8 suka iso, Yace wani unguwa kikayi tace "GRA Bayan gidan Govenor", ya juyo da sauri yana fuskantar ta, yace ai unguwar mu ce, tace wai dagaske? Ya ce eh, to wani gida kike?" tace gidan Alhaji Tijjani Masanawa ai nan Habib ya hangame baki Yace u must be kidding me, Gidan Baba na kike? Itama da mamaki tace "nifa bana son zolaya" yace dagaske ba wasa ba" shine last person da nayi magana da shi a jirgi, Abokin baba na ne sosai, he's like a 2nd father to me and my siblings" tace "banyi mamaki ba, its a small world afterall, yace "haka ne but ya akayi ni ban sanki ba? Tace "da yake a Cairo nayi College zuwa Masters dina, so ban fiye zama a Nigeria ba, ko na zo banyin 1month nake koma wa" Habib yayi mamaki matuk'a yace wai ko kece Aisha?" Tayi murmushi tace ya akayi kasan sunana? Yace ai na kanji baba na waya dake, na taba tambayan shi wacece suke yawan waya?" Yace "kanwarka ce Aisha, tana Misra tana karatu" a haka suka iso Gidan Alhaji Tijjani, wani tangamemen Gida ne, har ciki direba ya shiga dasu.
Habib ya fito ya bude mata ya ciro kayan ta yace" Shatu, Allah ya huta gajia ko?" sunan da ya kira ta dashi ya bata daria, tace "wato ba zaka shigo ba? Ko daman labari ne kawai ka keyi?" yayi darian shima yace mutum da gidansu sai an gayyace shi ciki?" karki damu inaso naje gida na huta, zuwa da safe zanzo ma gaida Baba " tace to shikenan, ta shige gida, shikuma ya koma mota suka fita daga gidan.

_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

Pg1⃣1⃣

Washegari
Habib yayi sallama parlon Alhaji Tijjani da Asuba, duk'a wa yayi har kada yace "Baba Barka da Safiya" Alhaji ya dago kai yace "lafiya lao Habibullah, ya gajiyar jiya? Habib yace "gajia ta bi jiki baba" Alhaji ya tambaye shi game da ayyukan da yajeyi a Cairo ya shaida masa komai na tafiya daidai.

Yace "Jiya sai ku ka ga bak'uwa", Alhaji yace " Aisha ko? Sai da tace min tare kuke na gardama mata, amma daga baya na yarda da na tu a kaima fa jiya ka dawo, amma ya akayi ka shaida kanwar ka, don na san ba ku san juna ba?" Habib ya kwashe komai ya gaya mai, Alhaji ya jinjina kai yace "haka Allah ke abunshi".

A kwana a tashi Habib da Aisha sun yi wata irin shak'uwa da junan su, har so ya shiga tsakanin su, soyayyah mai tsafta sukeyi, Alh. Na sane da su amma yayi shiru, a zahiri kuma yana farin cikin wannan abu don Habib mutumin kirki ne, irin shi yake so aura ma Tilon yarsa, amma tunda sun hada kansu tun wuri toh falillahil hamd.

Wata rana Habib ya shigo gidan don zuwa kiran Baba tijjani, ya aika a kirashi, Bayan gaisuwa Alhj ya muskuta yace " Habib dalilin kiran ka shine in shaida maka yau za muje mu kai kayan sa bikin Aisha, tunda kai kadai ne yayan ta, ina so ka hallara wurin zuwa, idon Habib ya rufe, be san sanda yace "baba, wace Aishar? Ban gane ba? Yace " Aisha kanwarka ko? Aishan Misra" Habib ya zabura yace "what?, Baba kar ka min haka, wallahi nike son Aisha, kuma tana sona baba kar ka rabu mu don darajan Allah, cikin fushi yace kuma ai a aladance zuwa ake gidansu yarinya a daidaita tsakani, ba wai da ga gidansu yarinya zaaje gurin Namijin ba, hala dan sarki ne" ya fada a fusace.

Sosai Alhaji Tijjani yayi daria, sai da ya tsagaita yace " Habib in banda abinka, ya zaayi dangi mata suje kai kayan biki? Ai ko a masarauta ba a haka, kwantar da hankalin ka d'a na, Kayan Biki zamu kwasa ni da kai muje chan gidan k'anena kuma waliyyin Aisha, in nema maka aurenta gun shi. Kunyar duniya ta lullube Habib, a take ya bar parlorn don kunyan baban da yakeji yana murmushi.

Aisha tsallen murna takeyi da Habib ya gaya mata abunda ya faru tsakanin shi da baba dazun, tayi daria sosai tace "wato kai loverboy ko?, ka mance baba kana ta sakin layi" yayi daria shima yace "sanki ne ya jawo hakan" tace ni ba "ruwana".

Yau bakin Habib har kunne don ko Baba Auwal kanin Baba Tijjanj yace wata daya kawai ya sa bikin 'yarsa. Baba Tijjani yace " ni da dana muna godia da wannan abu, Allah shi kaimu lokacin, na maka Alawarin dana zai kula da diyarka yanda ya kamata" duk sukayi daria.

Baba Auwal yace "Yaya, ya maganar aikin Aisha a Wannan Oil and Gas Company din da Gwamnan Kaduna ya bata? Yace duk sanda taso yin aiki ta kai offer din nan, unlimited time ya bata, don yace ko ba shi ke mulki ba, ya riga yayi signing kuma dole a amince da offer" Alh ya tabe baki, yace " Kaduna fa? Toh gashi kuma kace aurar da diyar ka zakayi nan da wata, kaga ko aiki wani gari ma be tashi ba, in ma zatayi aiki, to wannan hakkin mijinta ne ya barta ko ya hanata, kuma dole sai inda zasu zauna"
Habib ina kake so ku zauna? "Habib yace Baba nan gidan Marigayi da nake Gyara ginin nake so mu zauna, amma muna iya komawa Kadunan, sai na dinga zuwa katsina duk weekends, "sam ba zaayi a hakan ba, inda kayi niyyar zama nan zaka zauna, wato nan Katsina, sai ka zaba mata cikin ministries din nan, kaga wanne ya kamata tayi aiki a ciki, sai na kaima SSG CV dinta ya bata offer" sosai Habib yayi godia, yaji dadin adalcin Baba Tijjani, dama shi be da burin zama a gidan da aka haifesu, balle shi da ya ci gadon Gidan Ubansa.
Yace Baba Nagode, Allah saka da Alheri, ina ga kuma tunda Public Admin ta karanta, zata iya aiki almost ko ina, ko za a duba BOA (Bank of Agriculture)? Baba Tj, yace "duk yadda kagani, ga baban ta nan kuyi shawara, ni idan ma zai yarda da kun barta da aikin nan, don na tabbata ba zata rasa komai ba da yardan Allah, kar taje ta wahalar da kanta gurin wani aiki" da sauri baba Auwal ya katse shi da harara yace"haba yaya, bari mana, diya ta fa Masters ne da ita, abar ta ta amfana da karatun ta mana" Baba Tijjani yayi daria, yace "daga bada shawara, yau Auwal harda harara na? Allah baka hakuri nima da karambani na na shiga maganar diyarka" ya kalli Habib yace "tashi muje kaji d'ana kafin a sake mana karnuka " Habib yayi dariya.

"Oh boy! wai ya maganar Gadon ku ne? Tunda tsohon ku ya rasu shiru nakeji, kasan zaka ja kaya, ga ka da Gadon Uba ga ka daUwa, Oboi u rich oo" Abokin Hafiz ke wannan maganar, sun dawo hutun aji biyar, da sun koma zasu shiga SS3.

Hafiz yayi murmushi, yace wai shi Anas meye damuwan ka da Gadon nan ne? Ince dai baka da gadon baba na? Wannan naci haka, tunda na dawo kake tambaya na, to ba a raba ba, ba ma bukkatar Gado yanzu, burin mu Allah ya gaffarta musu duka.
Anas ya shek'e da daria yace "kai ni zaka ma bariki? Ni zaka ce ma ba ka da bukkatar Gadon ka? To bari kaji ina sane da an raba Gadonku, ka tashi da Miliyan 50 da Gidaje 3 da filaye. Hafiz yayi daria yace " Ohh, Anas, to ka sani me yasa kake tambaya na? Kai ni fa ba abunda zanyi da kudi" Anas ya sake shekewa da daria yace karya kake, kai ke ko da abunda zakayi da kudi, kai fa nan Millionaire ne, ga ka da kyau da kwarjin, zakayi abunda kaga dama ba me ce maka don me?, ka sa kallar kayan da kake so, ka hau motar da kake so, mata ma sai wacce ka zaba, kai kasan if you have money u have everything"

Hafiz yace "na san da haka, amma yanzu karatu mukeyi, idan mun mallaki hankalin mu Yaya Habib zai bamu hakkin mu nida Zaid, for now mun amince ya dinga juya mana kudin" Anas yace "Ban taba sanin kai solobiyo mara tunani bane sai yau, dan Uba zaka sake ma ragamar dukiyar ka kace ya juya maka? Lallai a ruwa kake tsundum wallahi"
Baki bude Hafiz ke kallon shi, ya daure yace "kai Anas, ka iya bakin ka, Yaya Habib matsayin Uba yake a gurina, kuma ba Gado na kadai ke hannun shi ba, harda na Zaid, kuma nasan zai rike Amana" Anad yace kai ni rabani da maganar nan, zaka yi nadamar barin Gadon ka wurin dan Kishiya, Aure zaiyi, Gida ya kera ma matarshi, daga Kasar Dubai ma ake Ginin, zai hada kayan aure, duk a dukiyar wa? Kana zaton a na shi? To kai wawa ne indai kayi tunanin haka, a cikin dukiyar ka zai yi duk wata hidima ta shi, da na ma kanin shi wanda suke Uwa daya, Saboda me? Sabida kai dan kishiya ne, kuma ba za su taba sonka ba"

Idona hafiz yayi jaa sosai, da alamun zanttukan Anas sun shige shi matuka, Zuciyar sa ta fara zafi, shaidan na dada ingiza shi, yace Anas yanzu meye abun yi? Anas yayi dariya ganin ya samu nasara, yace "abu daya zakayi shine Ka karbi Hakkin ka".

_Bibilicious Biebee_👧

🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

Pg1⃣2⃣

Anas ya cigaba da cewa "Ka same su kace su baka hakkin ka kana da bukatar su, duk yanda zasu so shawo kanka ka fandare musu ka bada ma idon ka toka, duk inda suka bullo maka to ka bulle musu" Hafiz ya jinina kai, yace "toh, bari zan gwada bayan bikin Yayan sai na bijiro musu da bukata ta" Anas yace "bayan biki ai ya gama bushashar sa, yanzu ya kamata kaje ka sake sa" Haifz ya mike yace "bari inje" Anas yace Allah bada sa'a kar ka manta, sai ka nada ma idanuwan ka toka".

"Yadai Hafiz?" naga kamar bakinka akwai magana? Ya akayi ne?" Habib ne ke tambayan Hafiz da tunda ya shigo dakin yake ta kame-kame. Hafiz yayi ta maza yace "Yaya, Gado na nake so a bani in rike a hannuna, a bani hakki na" Habib cike da mamaki yace "Lafiyar ka Hafiz? Bakaji me baba Tijjani yace ba? Sai kun gama Jamia za'a baku, Hafiz ya fandare ido yace "shidai a bashi yana da buk'ata"
Habi yace "to shikenan Hafiz zan yi shawara da Baba Tijhani".
Hafiz ya dan yi ysaki yace "Yaya, Gado na ne ko? To nace abani kayana ban son ajiyar, ina da hankalin da zan rike abu na, banga dalilin yin shawara ba, tunda dai shi da kanshi ya kira a ka raba Gadon nan, toh ni dai nace a bani kaso na"

Yanda hafiz yake magana ya ba Habib Mamaki, zuciya taci Habib ya mike yace biyoni, ko kunya Hafiz be ji ba ya bishi, a waje suka ga Zaid, da sauri ya taro su yace "lafiya? Yana ga fuskar ku ba walwala? Habib yace "kaima biyo mu" ya fada motar sa ya bar gidan hanyar Bank yayi. Zaid da Hafiz mota daya suka shiga, a hanya ne Zaid ke tambayan Hafiz" Bros, wai ya naga yaya haka? Me ya faru? Hafiz ya dan tabe baki yace" ba fa abin da ya faru, kawai don nace yaban Gadona a hannuna ba sai ya ajiye min ba, ni zan aje abu na da kaina shine ka ganshi haka"

Cike da mamaki da takaici Zaid ke kallon shi yace "Hafiz kasan me kake cewa kuwa? Me zaka yi da Gadon ka haka? Idan wani bukata ne dakai ka sanar dashi, shi me iya baka ne ba tare da ka taba Gadon ka ba, Haba danuwa na" da sauri Hafiz ya katse Zaid ta hanyar daga mai hannu yace "in kai yaro ne, ni ba yaro bane, ina da damar da zance a bani hakki na, idan kao ba za ka amsa naka ba, to ni zan amsa nawa, so please spare me the lecture"

Kasa magana Zaid yayi har suka zo Safe din babansu, inda ya ke ajiye kadarrorin sa, Tuni Habib ya haye sama, suka bi bayanshi, Cikin Lokaci kalilan ya tattara duka Gadon su, da ma a kashe suke, ya kalle su yace "tunda, baba ya rasu ban taba daukar ko sisi ba nayi amfani dashi, duk kudin da kuka ga na taba to kudi na ne, hakkin gurin Aikina ba na Gado ba, to yanzu Hafiz ka bukaci Hakkin ka, ni Musulmi ne na san hukuncin wanda ya danne ma wani hakki, nikuma bana daga cikin masu dannewa mutane hakkinsu" ya tura mai wani dan safe box yace "Wannan Miliyan hamsin da hudu(54) ne, a ciki akwai filaye 3 da location dinsu, da gidaje 2 a garin Katsina" ya juya ya kalli Zaid yace kai kuma ga naka hakkin Miliyan hamsin da--" da sauri Zaid ya katse shi ta hanyar cewa "Haba Yaya? Me zanyi da kudin nan? Ni bank'i a sadakar da su Allah ya Jikkan su Baba, ba abunda zanyi da su, shi da ya ga zai iya ai Shikenan ka bashi hakkin sa" a fusace Zaid ya tilla ma Hafiz key din mota ya juya ya bar gurin rai a bace.

Hafiz ya duka ya dauka key din motar da murmushi a fuskar sa yace "Nagode Yaya, hakika kai uba ne a gurin mu,tunda har ka san Hakkin dan Adam baka tauye ni ba, Nagode Allah ya bar Girma" mamaki ya hana Habib Magana. Hafiz ya dauke Safe din ya fita.

Sai da ya kai Safe din Bankin da Baban su ya bude musu kafin ya kira Anas a waya, tunda suka hadu da Anas, Anas ke faman kuran ta shi" The multiple Millionaire, yanzu za a dama da kai, ina dukiyar? Hafiz ya dan bata rai yace ba ruwanka da inda suke" Anas yayi daria yace to shin kai filayen nan d gidaje me za kai dasu? Ai kawai kasa su a Kasuwa ka ci kudin su, in yaso in Ka tashi mallakar Gida sai ka gina Uban uban su".

Da wannan huduba na Anas Hafiz ya sa gidajen shi da filayenshi kasuwa, a ka siyesu a wulakance ba tare da sanin kowa ba, Hafiz ya zama wani tauraro cikin abokan shi, yayi ta musu bushashar kudi.

Baba Tijjani yayi fada sosai da yaji abunda Hafiz yayi, amma ya fi ba Habib laifi akan biye mishi da yayi, Habib yace "Baba ya zanyi dashi?, tutiya yakeyi Hakkin shi ne, ba wanda zai danne mishi, baba naga nima wannan nauyi ne ka sa mun, shiyasa na sauke nauyin, shi Zaid da na mika mai naahi kin amsa yayi yace ba abunda zai yi dasu, ina ga kar ka daga hankalin ka, kowa yayi da kyau zai gani. Baba ya jinjina kansa yace "Allah shi kyauta" Zaid "yace Amin".

Bayan Sati daya
Aka sha bikin Habib Iro Lema da Amaryar sa Aishatu Tijjani Masanawa bisa sadakin Naira Dubu Dari. Biki ne wanda ya amsa sunan biki, ba a tsawalla ba, ba ayi karya ba, ko lefe akwati 6 yayi a cewar Baba Tijjani Albarkar aure akeso.
Ran da akayi dinner Hafiz ya taka rawar gani,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login