Showing 81001 words to 84000 words out of 149166 words

Chapter 28 - Ke alkhairi ce COMPLETE HAUSA NOVEL

BIEBIE   

22 Oct 2024

25747

wayance da amsar Ayman hannun Rafeeq, Zaid ya durk'usa yace "Barka da Dare Yaya" Daddy yace "Engineer, saukar yaushe?" "Jiya na dawo" sai ga Saude ta shigo tana takun ta, wai ita tazo taryar Miji, aiko ganin Zaid ya sa ta 6are baki "Meema ga Uncle Zee" "inalillahi" zaid ya furta a ranshi, kafin ya ankar sun rugo da gudu ita da Aneesa wai su zasu mai Oyoyo, da azama ya mik'e yayi saurin mik'a musu ledar Tsarabar su don ya san dukkan su ba mai hankali ciki suna iya fado mai, Meema da ta shagala da kallon Zaid, bata taba ganin hallita me kyaun Zaid ba, Zaid ya gama tafiya da ita, wannan karon ko ta halin k'ak'a sai ta samu cikar burin ta, Dole Sai ya aureta, like hell look at him, ya hadu ne, balle ya sha madarar England, duk ya k'ara cika, ya kusa 40 amma dubeshi kamar dan 25, ita kadai take tunaninta. Aneesa da dadi ya gama kasheta, yau Rafeeq ya zo Sama, ta matsa kusa dashi "Yaya Rafeeq, wata sabon ganin" dogon tsaki ya ja ya mik'e tsaye, tunda Shigowar Sauda ya fara ganin duhu, ya kalli Zaid yace "Uncle I'll be downstairs" be jira cewar kowa ba ya fita ya sauka k'asa. Aneesa tace "kagani Uncle Zaid? Yaya Rafeeq ya tsaneni, ba yason ko magana in dinga mishi, duba fa yanzu yana ganina kamar ya ga kashi, shine ya fita" "Ki cigaba da hakuri" kawai yace da ita. Saude tayi k'wafa ta juya taga Alhaji Habib Dauke da wata kyakywan diya tace "Alhaji ina ka samo yarinyar nan? Yayi danyi yak'en takaici yace " 'yar gurin Zaid ce" ai ko Meema tayi saurin cewa "Laaah Ayman ce yau a gidan mu, daddy kawota, Aneesa ma ta yi hanzarin cewa ni za a ba ita, saude ma tace " ku bari in fara daukarta, ai tana nan gidan, ganin su uku sunyo kanta gadangadan, hakan kuwa ya ba Ayman tsoro ta fashe da wani irin kuka, Zaid ya dafe kai ya girgiza kai, Alhaji Habib yace "kunga kun bata tsoro, Karbeta Injiniya" Zaid yace "k'uiya gareta bata yarda da kowa" ya sa hannu ya amsheta. Saude tace "baka taho da nanny dinta ba?" a ranshi Zaid yace "Nanny dai? Dama Ayman na da Nanny?" Meema ce cikin kissa tace "kema Sis banda abunki wace Nanny zai zo da? Bayan ya kawo Ayman wurina ai ba sai yazo da wata ba, i know how to take care of kids more especially my Daughter" Saude da Aneesa suka sa Shewa, wannan gaskia ne, shidai Zaid wani yak'e kawai yakeyi, wanda da shi gwara yayi kuka, har yanzu Ayman ba ta daina Tsala kuka ba.
"Ka san kuwa tana yarda da Nasiba? Duk k'uiwan Ayman bata yi ma Nasiba, don har goyata takeyi taje gidansu da ita idan tayi bacci ta maido min ita, so nasan ba zaa sanu matsala ba ko kwana nawa zatayi gun Nasiba da kakarta" Muryan Mami ya ji a kanshi a lokacin da ya tuna labarin da ta bashi kan shak'uwar Nasiba da Ayman.
da sauri ya sauka k'asa Meema zata bishi Daddy yayi saurin cewa "da kin barshi ya lallasheta, sai ya maido miki ita tunda a gurinki zata kwana". Dadi ya kamata don duk zaton ta, ita aka kawo ma Ayman.

A k'asa ya ga Rafeeq a dafe kai, duk yanda yake jin kukan Ayman a ranshi, ya fi tsanar ya ga Aneesa da Uwarta shiyasa ya kasa komawa sama da yaji kukan Ayman, Zaid ya kalleshi yace " Start the Car" ba gardama ya fita da sauri ya fada motar shi, ya kunna Zaid na zuwa ya shige, suka fita daga gidan, a hankali Rafeeq yace "Ina Zamu?" a wahalce Zaid yace "Gidan Nene" don har yanzu Ayman bata abr kuka ba, cike da mamaki yace "What? Gidan Nene? Are you kidding me? Sabida me? Why there of all places" Zaid ya kalleshi yace "Sabida chan tazo hutu, akwai matsala ne?" da sauri Rafeew yace "yes big one, matsala babba" "that woman is very noisy, and annoying tana da Hayaniya" Zaid yace "Thank you, but She's living with them for as long as my stay in KT" sai da Rafeeq yayi kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa, ya murtuk'e fuskan nan da ta samu sassauci kwana biyu, sai ya koma dunkum din shi yayi focusing kan tukin shi har k'ofar gidan Nene.

Har Cikin Gidan Baba Maigadi yai mata Iso, da Aneesa ta ci karo, wani kallon da ta watsa mata yasa hanjin cikinta kadawa, "ke wa kike nema?" baki na rawa Nasiba tace "Alhaji na ke nema" "burauba, daddy na kike nema? Uban me zai maki? Shegia karuwa har gida" hayanniyar da Aneesa keyi ne ya sa Hajia Sauda saukowa tace "Anee ke da waye? Ta bi Nasiba da ido, haka kurum taji gaban ta ya fadi, nan ta ji ta tsani Nasiba, ke me kikeyi a gidana karfe 7 din dare? Nasiba tayi shiru, karaf Aneesa tace " Wai Daddy take nema" Meema tace " ke ko turo ki akayi ki kashe shi? Ko ki fadi me kika zoyi ko miyi miki Zindir Wallahi" jikin Nasiba ya fara rawa, da ta sani da ta yarda sunzo da Nene, don sai da ta buk'aci ta rakota saboda dare amma tace "aa ta bari zata iya, ai dare be gama yi ba, kuma yanzu za ta dawo. Nadamar rashin barin Nene ta biyo ta. Sauda tace "kai ku amso min ledar nan, k'ila kayan Asiri ne a ciki, ana so a juye hankalin Mijina" Meema da Aneesa su kayo kan Nasiba, matuk'a ta gama tsorata, Meema ta damk'o ledar, *kar ki bari kowa ya ga magungunan na sai Alhaji, don kiga yan gidan na cikin Zargi, ba mu san waye mugun a ciki ba* maganar Mallam Usman ya fado mata, da sauri ta fizge ledar daga hannun Meema, Meema kuwa ta kamtse Nasiba da Mari, marin da bata taba gani anyi ma wani ko da a film ba, wani ihu ta saka, ihun da ya fargar da Alhaji Habib da ke sama, yana jin hayaniya k'asak'asa, ya sauko da sauri ganin yarinyar nan me kama da Rafee'ah durkushe rungume da wani abu Aneesa da Meema suna ta jibgarta kamar Allah ya aikosu, ya sa shi karasawa gurin ta da gudu, ya dagota, Saude ta sake "Salati, shikenan Karuwar sa ce, dube yanda ya dagota, Alhaji wannan 'yar cikin ka ka ke bi?" ya dago jajjayen idonshi ya kalleta, amma sai ya kasa magana, yace "Nasiba, tashi mu tafi" tana kuka ta mik'e, Sauda tace "Alhaji kar ka fita" chak ya tsaya, amma ga mamakinta sai yace "Kiyi hakuri yanzu zan dawo" ya ja Nasiba har gun Motarshi, ya mata umurni sa ta shiga, Saude kuwa kamar wacce aka dasa a gurin idonta ya koma bula(lols i cant even imagine) "wata sabuwa inji yan chacha" yau Alhaji ne da mata gardama? "Meema tace Lahhh sis ya fita, ya fara miki gardama" Sauda ta yi wani ihun takaici ta bar gurin kamar zata tashi sama.
********
Sai da ya fita bakin Gate ya danyi parking, yace "Diyata, ban san ta inda zan fara baki hakuri ba, ni na ja miki, kiyi hakuri donAllah, ta tsagaita kukan tace bakomai Daddy, ta ciro ledar da mik'a mai tace " gashi inji Mallam, yace zaka dinga sha Safe, Rana Dare, kuma ka dage da Addua, ka dinga tsayuwar Dare, InshaAllah zaka fita daga sharrin me sharri" yanda take mai bayani sai yaji ta burgeshi, ya ji ya na sonta, irin son da yake ma Rafee'ah, yake ji dama diyar shi, ya nisa yace "Nagode kinji? Allah ya miki Albarka", ya sa hannu ya ciro kudi masu yawa ya bata, ta girgiza kai tace " Aa ba zan amsa ba, DonAllah nayi" yace "nasani ni na baki ki karba" ta ki tace "zan je Gida" yace "barin fara kaiki Asibiti a duba ki" tace "haba ba komai" yace "Kinga fuskar ki ya kumbura, dole a duba ki" tace "Allah bakomai zanje gida kafin Nene ta shiga damuwa" yace "dama zan biki in ba su hakuri kan abun da ya faru a sanadiyata" tace "daddy thats not necessary please" ya nuna ta da yatsa yace "bana son musu, ki nuna min hanyar Gidan ku" tace "to a sanyaye" ta shiga nuna mai hanayar Gidan

"Ahhh muryar wa nikeji kamar muryar Zaidu bawan Allah?" Murmushi yayi yace "nine dai Nenen mu ni da Seebi" tace wacece wannan take ta tsala kuka haka? Ya mik'a mata yace "Jikar ki ce" ta amsheta ta tillata sama ta chafe, ta fara yi mata tawai har sai da tayi shiru, kafin ta shiga daki ta goyeta tsaf da zani, kafin ta fito, ta kalli Rafeeq da ya sha mur tun bayan Sallamar da yayi lokacin da suka shigo be sake magana ba da murmushi tace "Ah ah, gaye ya akayi ne? Naga fuskar ka yau kamar lokacin da kake Dun... Sai kuma tayi shiru tare da sa hannunta kan baki tana daria" guntun tsaki ya ja ya kawar da kai gefe, gyatsine tayi irin i dont care dinnan, tace kaji dashi "dunkum dangi tsaka" ya kalleta da sauri, tace "kaji ai cewa nayi dunkum, ko ba tsaki yayi ba? Magani sai ya fara aiki, sai abu ya rikice, to yau obados (over dose) zan baka.Tsakin ya kuma yi, shi dai Zaid daria yake tayi, yace " Nenen mu mun same ku lafiya?" ta janyo kujera ta zauna tace "Lafiya lao mutan Ingila, haka ka koma? Kaga yanda kayi kyau kuwa? Kamar da Amurka(America) daria kawai yayi, Daria kawai yayi, tace "Wannan fa?" ta nuna bayanta, yayi murmushi yace " 'yar guna ce" tace "Ahh wannan ba jika bace, wannan diyata ce, ni diya zanyi da ita, ina Mamar ta ta? Tsaki Rafeeq yayi yace " she asks to many questions, tana da damuwa gata da hayaniya" shifa a ranshi yayi maganar be san maganar ta fito fili ba, Nene ta mik'e ta shiga daki sai gata ta dawo da igiyar chargy na radio ko fitila, cikin daga murya tace "Zaidu bawanAllah, yau ko ni ko Dunkum, ta hau k'okarin kwance Ayman da ke bayanta, wai zata ma Rafeeq dukkan tsiya, Zaid yayi saurin tashi, don shi a zaton shi wasa takeyi, amma yanda ya ga ta dage ya sa shi bata hakuri, shi kuwa Rafeew yana nan ko gezau beyi ba tace " Haba Zaidu Bawan Allah, na dade ina hakuri da Dunkum, sai yayi ta gaya min Maganganu yana min turanci, rannan har bangaje ni yayi ya bi ta kaina ya wuce, Nagaji, yau ko ni ko shi" Zaid ya shiga bata hakuri, yana ma Rafeeq ido da ya bata hakuri, shi kam ya dauke kai kamar be san ta nayi ba, ana Cikin haka ne Nasiba tayi Sallama. Daga muryarta Nene a san cewa ba lafiya, duk suka zuba ma Soro ido, Nene tayi saurin karasawa gunta tace " Seebin Nene, me ya samu fuskar ki?" Nasiba tace "bakomai" tayi gaba ta tsaya kusa da Uncle Zaid tace "Ina wuni? An dawo Lafiya" ba ta jira amsarshi ba tayi gaba zuwa daki, don idan ta tsaya dogon magana ta na iya fashewa da kuka. Zaid duk ya bi ya damu yana so ya ji matsalar ta, "Ke Seebi" inji Nene, chak Nasiba ta tsaya da ta ji yanda Nene tayi kiranta in a serious tone, Nene ta matso kusa da ita tace " ni nasan ke baki da abokan fada, baki da neman tsokana, kina da gaskia ana iya dukkan ki ki kasa magana, ki gaya man, wani dan abun uban ne ya bugeki har ya kumburan maki da fuska? Kamar jira takeyi ta fashe da kuka, Nene ta sake hawa sama tace "a gidansu Dunkum din ne a ka bugeki? Eyi? Ki gaya min" ita dai bata fasa kukan ba, Rafeeq yayi guntun tsaki ya matso kusa da ita yace "kinje gidan mu ne?" yo eh daga gidanku take "Me kika je yi a gidanmu? Eh?" Nene cikin fada tace "kai dallah dakata min, go gefe, zaka tasata a gaba kana mata fada, sak'o takai ma babanka, shine aka samu watsatssu da suka mata hakan? To wallahi ba zan yarda ba ko uban waye ya taba man 'yar jikata sai ya yaba aya zak'inta"
Sai yanzu Zaid yayi magana duk da be gane me suke nufi ba duka ya kalli Rafeeq yace "Calm down Feeq, Nene fada ba zai maganace komai ba, bari ayi abun a tsanake, Seebi, su waye suka buge ki?" cikin sheshekar kuka tace "wasu mata ne su biyu, don sunce in basu ledar hannuna nak'iya shine mamansu ta sa su suka dinga duka na, sai da babansu yazo ya k'wace ni tare muke yana waje" a hankali Rafeeq yace "Aneesa da Meema" Nene tace "Babbar Balaeen chan, wallahi da Aneesar, da uwarta da wace tsiya sun tsokalo tsuliyar dodo, ba su san da su ta6a Seebi gwara sun kamu da farar masassara, yau sai na gwada musu wacece Aminene Mamman" ta figi hijabinta da ke kan igiya, ai ko duk suka yo kanta, Zaid yayi saurin rik'e mata Hijab, ai ko ta daddage ta buge hannun Zaid, daidai Soro ta ci karo da wani Mutum ta kalleshi galala tace "kai kuma fa?"

_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

_Nagode da Adduoin ku, masu kirana da masu min message a Whatsapp da Sms Ina godia, ina muku Albishir da naji Sauk'i sosai, kuma zaa cigaba da yanda akeyi InshaAllah. Allah ya bar Zumunci.

Pg4⃣8⃣

Duk suka bi bayan Nene, Rafeeq na gannin baban shi a ranshi yace "Interesting! Daddy a gidan Nene" shi kuwa Zaid cewa "yayi Yaya me kakeyi anan?" nan Nene ta gano bakin Zaren tace "touu Alhaji Habib Lema ne, gaya min, da saninka ne Matarka da 'yayanta suka ma jika ta mugun bugu?" Alhaji Habibi duk ya daburce, be taba ganin tsohuwa me masifa haka ba, yace "kiyi hakuri Wallahi ba da sani na bane, ni ne na kar6eta" Nene tace yo abun azziki kayi? Dalilin wa aka bugeta? Nace dalilin wa? A hankali yace "kiyi hakuri a dalilina ne, hakan bazai sake faruwa ba" tace "k'warai kuwa, hakan ba zai taba sake faruwa don yau watna cin ubansu ya tashi, har matarka" tayi hanyar fita da sauri Seebi ta rik'ota, duk suka shiga bata hak'uri tana cicijewa banda Rafeeq da ya koma gefe yana Murmushi, ya tabbatar Nene yar daru ce, da k'yar suka shawo kanta don tana ganin kimar Zaidu dan Albarka, ta dawo ta zauna kan kujera, Nasiba tace ma Daddy kayi hak'uri, shez always like this" murmushi ya mata yace "karki damu" ya zauna kusa da Zaid dake kan tabarma, cikin gunguni Rafeeq yace "ai da kun kyaleta taya zata je gidan mutane ta buge su?" ashe ta ji shi cikin fada tace "Ai da kun bari naje sai ka ga ta yaya naje har na musu dukkan tsiya, sai ka tantance, kaima bawai k'yaleka nayi ba" Uncle Zaid yace "Feeq quiet!".

Zaid yace "Yaya wai ne ya faru? Wani Sak'o Nasiba ta kai maka? Ajiyar Zuciya Alhaji Habib yayi, ya fayyace musu komai tun haduwar su a Gun mallam, har zuwa yanzu da ta kawo mai magani, Zaid ya jinjina kai yace "Ashe ba nikadai nake ganin Nasiba kamar marigayiya Rafee'ah ba" Nene tace "kama sukeyi ne wai?" Alhaji Habib ya bata amsa "basa kama anma yanayinsu iri daya komai" Rafeeq dai be je komai ba, sai kallont yakeyi, ita kuma hankalinta baya nan yana gun Aymana da ke rik'e a hannunta, hayaniyar Nene ya hanata bacci, Zaid yace "Yaya to maganin dai ka sha su yanda ya kamata, don ka daina jin Yanda kakeji Allah ya sa a dace" yace "Amin" Zaid yace "Feeq ka je gida ka kwaso kayan Ayman, dare na k'ara yi" a zucciye yace "Seriously shes sleeping here? Cikin daga murya Zaid " Yes Rafeeq, shes sleeping here" kamar zaiyi magana ya fasa ya wuce fuuu kamar zai tashi sama, Nasiba ta bishi ido a ranta tace"why? Yana da matsala ne don zata kwana nan?" ta ta6e baki.
"Engr. nace baza ka kai Rafeeq gun Malamin nan me magani ba, yana maganin Sihiri ko asiri, ko aljannu, da masu taurin kai, abunda ya sa na yarda Mallamin, ba dan tsubbu bane, kuma be aiki da Aljannu, da kalmar Allah da Adduoi da suek a cikin Kurani da Hadisi ya ake amfani, ba a san inda zaa dace ba, wannan zucciya ta Rafeeq na bani tsoro" Zaid yace "Duk da akwai Chanji a halaiyar Rafeeq zan kai shi a duba shi, Nasiba kin san wurin ai? Idan kim dawo school gobe sai ki rakamu, Nasiba tayi gyaran murya tace "da akwai abunda baku sani ba Uncle, Rafeeq Yana na magani already, ko yau da Daddy ya ganni a gun Mallam Ruwan maganin shi na koma an so mai don wanda aka bashi da farko ya k'are, Ruwan Adduoi ne, ya maida shi ruwan sha, in kuma a gidannan zai ci Abinci, to da ruwan maganin ake mishi dahuwar, sai kuma Wani maganin hadin magunguna, shigen naka ne Daddy, shi maganin zai sa mai hakuri da dangana a zuciyar shi, to Alhamdulilah an fara samun Nasara".

"Allahu Akbar" inji Daddy, "Engr. Ka lura da wani abu game da Rafeeq bayan dawowan ka?" Zaid yayi murmushi idonshi kan Seebi, duk ta gama tafiya da imanin shi tsaf, maganarta yanayinta, komanta y bureshi, yace "eh Yaya, Rafeeq is somehow changed, naga chanji wallahi, ashe akwai silar chanjin shi" Nene tayi magana, tace "ai da Mahammadu yazo ne ya mishi wuriwuri har ya amso mai magani ya kuma tilasta mai sai ya sha, yanzu ms zai dawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login