Showing 33001 words to 36000 words out of 149166 words
miki asiri wallahi" Sauda tayi daria tace "Hafiz kenan, to barin fito maka da real color dina, idan nice me zakayi? Uban me kake iya yi? Kasan dai halina ko? Ka ka shiga gona ta, idan ka min shishigi zakayi kuka da kanka, kar ka manta Rayuwarka a tafin hannuna yake. I own u, so watchit" ta fice ta barshi tsaye.
Bakin gate ya hadu da Maalesh, yace ka kai Motar? "Eh Uncle Zaid" ok ban key dina ni, Maalesh ya nika mishi, yace "Uncle Zaid" Zaid yace ina sane da kai Maalesh, nasan there are millions of questions da kake so kayi, ka jirani ina zuwa, and Rafeeq give him space" Maalesh yace "Sai Ka dawo". Ya shiga ciki Zaid kuma ya fito.
Da Zaid ya koma gida be ga Mami ba, hankalin shi ya tashi, ya sauka kasa ya tambayi baba mai gadi yace ko ya ga wucewar ta? Ya bashi tabbacin ya ga ta fita da kaya, da alamu tafia zatayi, da sauri ya shige mota ya nufa gidan Baba Tijjani.
A sukwane ya shiga Parlorn, Baba Tj na zaune yana Azkhar, yace Zaid "lafia ka shigo a haka?" yace "baba ina Mami?" cikin mamaki yace wace "mamin? "Ina Aunty Aisha mamar Rafeeq?" Zaid ya dan fada a fusace, Baba Tijjani yace tana gidan ta mana, ce maka tayi zata zo nan? Baba dagaske ba ta nan? Yace "dama Ina maka karya?"Zaid yace "aa baba ba haka nake nufi ba, tabar gida ne na zata nan tayo, kuma wayarta a kashe" yace "aa ba mu ganta ba" Zaid be jira ba ya fita ba tare da ya basu labarin abun da ya faru ba, a ganin shi abun kunya ne suji Yayan shi ya sakar musu diya bayan hallacin da Baba Tijjani ya musu.
Mama tace "Alhaji ya ba ka gaya mishi gaskia ba? Yace kinsan halin Zaid, ba zai barta ba, duk inda take sai yaje ya daukota, abar ta ta gama iddan ta, she needs time" tace "Hakane"
Hankalin Zaid a tashe Matuk'a, duk inda yasan zai bincike Mami Aisha yaje be ganta ba, ya kira wayarta yafi a irga a kashe, Zafi biyu, ga rashin sanin inda take, ga matsalar Rafeeq, a bayyane yace "Allah kayi mana Agaji" yayi niyyar zuwa gidansu Maalesh don ganin Rafeeq, sai ya fasa don yasan Rafeeq na bukatar lokaci sai kawai ya wuce gida.
Hafiz ya sake labarta mai abunda ya faru, Zaid yace "wallahi Hafiz Shiri ne, ban yarda ba, akwai wata manakisa, kuma i promise i wont rest har sai na gano who is behind this na sada shi da hukuma" Hafiz ya danyi jim, so yake ya gaya ma Zaid wacce yake zargi, amma sai ya tuna gargadin da ta mishi dazun, inda take cewa "Hafiz, dont try to bring me down, if i go down, i'll drag you down with me" miyau ya hadiye yace "gaskian ka Zaid, its hard to believe, Allah ya baiyanar da Gaskia cikin sauki" Zaid be ce komai ba saboda yanda Zuciyar sa ke tafasa. Wurin Yayan shi ya hau a sama, ya ci saa shi kadai ke Parlorn, ya shiga da Sallama, har yanzu be bar kukan ba, Zaid ya kalli yayan shi cike da Tausayi, yace "Yaya kaima kuka kakeyi?" Habib Yayi murmushin takaici yace Zaid " kaga abun da uwar dakin ka ta yi min ko?" Zaid cikin bacin rai yace "yaya kaima ka yarda? Haba yaya, wai ba ka san wacece Aisha ba? Shekarun ku nawa da ita? Tun kuruciyart bata kawo gardi gida ba sai yanzu da ta fara tsufa har da diyanta? Haba Yaya kai haka kake baka bincike? Haka fa kamin a baya, dai daga baya kazo kana da nasani, you should have give her a time to explain, am sorry but ka dinga amfani da hankali." Habib yayi shiru yana nazari, magananganun Zaid sun shige shi, daga kallo daya zaka san cewa jikin shi yayi sanyi, amma ya kasa cewa komai, Sauda da ke labe a bakin k'ofa ta ja tsaki, tace wannan Zaid din yana neman bata min shiri, amma da sannu zanyi maganin shi"
Tana shiga daki ta kira Boka na kan tudu, ta nemi da ya janye tunanin Aishatu daga kan Habib, Boka yace ba matsala, anyi an gama, tace "yauwa, saura Maganan k'anin nan nashi, Zaid, Boka yace "uhm uhm Sauda, kar ki b'allo ma kanki ruwa, ki rabu da wannan, amma shi kina iya hadawa da kissan ku na mata" tace "to shikenan yanzu dai ka janye min hankalin Alhajin".
"Rafeeq be kamata ace kana fadan mugun kalamai kan mahaifiyar ka ba" Maalesh ne ke zancen nan cikin bacin rai, Rafeeq ya kalleshi galala yace "Maalesh, ka min shiru, idan kuma so kake ka nuna min nan Gidan ku ne, sai na tafi na bar maka gidanku yanzu, ba wai ce maka akayi na rasa wurin zuwa bane" Maalesh ya buga tsaki tare da fita ya bar mai dakin don idan ya biye ma Rafeeq zasuyi ba dadi cikin daren nan.
Bayan Kwana 3
Gari yayi ma Zaid Zafi, ba inda zai saka ranshi yaji dadi, Gashi ba inda be nemi uwar dakin shi ba labarin ta, Gashi Idan ya ma yayan shi maganar ta sai ya hau masifa don jiya saura kiris Ya mareshi don yace mishi ya kamata ya yi bincike don gano gaskia(Bokan kan tudu yayi aiki kenan) Gashi idan yaje gun Rafeeq don su tautauna kan Mahaifiyar shi sai ya birkice yak'i ko tari, don Zaid ya fara magana har ya gaji Rafeeq ko k'ala ba zai cemar ba haka zai bar Gidansu Maalesh ya koma Gun Yayan shi, nan ma ba wani sauki, sannan kuma ya zagaya duk inda ya san zai ga Mami Aisha amma shiru ba wani dace.
Bayan kwana Uku
Yau Sunday aka kira Zaid a Office, aka ce ya dawo Kaduna saboda akwai aikin da zaa tura shi Lagos, be da wani zabi da ya wuce ya koma Kaduna, kafin ya bar Katsina sai da yaje Gidan Baba Tj, ya roke shi da ya gaya mai gidajen Yanuwan su da ya ke ganin Mami zataje amma fir yak'i gaya mishi, haka ya bar gidan cikin rashin jin dadi, Gidan su Maalesh ya nufa.
Maalesh ya gani tsakar gida yana Basketball, Maalesh ya karaso ya gaida shi, Zaid ya amsa mai cikin sakin fuska ya tambaye shi "Mahmud, ya abokin naka?" Maalesh yace Uncle Zee wlh ba sauki, abun Rafeeq gaba yake kara yi, tun gaisuwan da naji ya maka jiya da Safe, Wallahi har yau ban sake jin yace ko a ba, haka zan gama surutai na ko kallo ban ishe shi ba" Zaid ya jinjina kai, yace Abun Rafeeq sai Addua bari in ganshi".
Zaid ya Iske Rafeeq Zaune, kallo daya ya mai ya ga rama da Baki'n da Rafeeq yayi, Zaid ya cire baki ya kira sunan shi cike da tausayawa, Be amsa ba ya juyo ya kalleshi, idon nan har wayau jajir, Ya tsura ma Zaid ido, Zaid yace Rafeeq zan tafi Kaduna yanzu, akwai abun daya da nake so kamin please ba don na isa ba" da Sauri Rafeeq ya tashi yayi hanyar toilet, don baya son zancen da Uncle Zaid ke son mishi, da sauri Zaid ya dakatar dashi ta hanyar cewa "Rafeeq ka saurareni, Wallahi ba maganar Mami zan maka ba" Rafeeq ya dan dakata don shi a zaton shi maganar Mahaifiyar shi zaa mishi. Zaid ya umurce shi da ya zauna, kamar ba zai zauna ba ya zauna, Zaid yace "Son, Ina so ka koma Gida, zaman ka a gidan aboki ba zaiyuwu ba, kar ka manta ba zaman kanka kake ba, kana da mafada, na baka lokaci don ka dawo daidai, amma abun naka girmama yake, dole ka koma Gida, kaji ko?" Shiru Rafeeq ya mishi, Zaid yace "Rafeeq Habib Lema, kajih ai?" kamar ba zai tanka ba ya gyada mai kai alamun yaji, Zaid yayi murmushi yace "thank you, Rafeeq, zan koma Kaduna yau, there are somethings i need to attend to" Shiru dai Rafeeq ya mishi be ce komai ba, Zaid ya gaji da zaman shi ya tashi yace "to Rafeeq ni na wuce" nan ma be ce mai komai ba, Har Zaid ya kai bakin kofa a hankali Rafeeq yace "Uncle Zaid" da sauri ya juyo yace "naam Rafeeq, me kake so? You need something?" Rafeeq dai yayi shiru kamar bashi ya yi magana yanzu ba, ya rasa me zai ce mai, Zaid dai yayi tsaye yana jiran me zaice mai, amma yaji shiru, da Rafeeq ya rasa me zai ce ma kawun nashi sai ya taka har gaban sa ya rungume shi, Zaid ko ya rungume shi shima, daidai da saukan hawayen Rafeeq, Zaid ya dinga lallashin shi, a hankali Rafeeq yace da Zaid "Please dont tell Rafee'ah..
_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg2⃣7⃣
Zaid ya dago yace "kar ka damu Rafeeq, Rafee'ah ba za ta sani ba" gyada kai kawai Rafeeq yayi, Zaid yace "akwai wani abun kuma? ya sake girgiza kai Alamun Aa, Zaid yace "toh, na tafi" Rafeeq ya koma kan Gado ya zauna. Zaid ya fice, gun Maalesh ya isa, yace "Mahmud, ni na wuce Kaduna, sai weekends kuma, Nagode sosai, Yau zai koma gida, ka cigaba da kula mun da Rafeeq, zan dinga kiranka ina jin yanda yake" Maalesh yace "Bakomai Uncle Zee, mudai fatan mu Allah ya sa gaskia ta baiyana, Rafeeq ya dawo normal self dinshi, don nafi kowa Affected da yanda Rafeeq yake yanzu" Zaid ya jinjina kai ya chanza zancen yace "In bada na shan Mai?" Maalesh ya sosa kai yana daria, Zaid ya ciro Bandir din dari 200(20000) a Aljihu ya ba Maalesh. Maalesh yayi Godia sosai ya raka Uncle Zaid har mota kafin ya dawo gun Rafeeq.
Rafeeq ya kalle shi zai yi magana sai kuma ya fasa, ya mik'e ya zira takalman shi, ya je gaban Tv inda Maalesh ya ajiye Key din mota ya dauka ya zo ya ba Maalesh, cikin wasa Maalesh yace "kai ni fa ban san iskanci, kurma ka koma ne?" Rafeeq uban Zuciya ya galla mai wata muguwar harara ya wurgar da Key din ya fice daga dakin, Maalesh yace "ikon Allah har yayi fushi? Duk da muke wasa fiye da wannan be ta fushi ba sai yau?" binshi yayi a guje har ya taddo shi, yace haba "R-Lema, wasa ne fa, Gida zakaje ko? Muje" Rafeeq dai be ce komai ba ya zagaya ya shige mota.
Gidan su Rafeeq kamar ba mutane, shiru kake ji, Rafeeq ya fito daga motar Maalesh ya bi Haraban Gidan da kallo, komai ya dawo mai sabo, yaji ranshi ya kara jagulewa, part dinshi kawai ya nufa ko cikin gidan be kalla ba, Maalesh yace "R motar Daddy na nan, ba zaka je ka gaida shi ba?" ko kallo Maalesh be ishe Rafeeq ba ya bude dakin shi ya shige, Maalesh ne ya shiga cikin gidan, ya iske Daddy da Saude a parlor suna fira, da alamun ba su da damuwar komai, ya karisa da Sallama, Alhaji Habib ya dago yace "Mahmud ne?" "eh daddy nine ina kwana?" ya amsa mai cikin sakin fuska, "Maalesh ya su maman ka?" inji Sauda yace "suna lafia sunce a gaidaku aunty" A. Habib yace "Mahmud ina abokin ka? Maalesh ya fara sosa kai, yace "yana daki be dan jin dadi ne" Zumbur ya mik'e yace "SubhanAllah barin je inga dan Zaid" ya fita Sauda ta rufa mai baya, duk ranta ba dadi ganin yanda mijinta ya rude don yaji ance Rafeeq be lafia.
Sunfi minti uku suna Sallama ba amsa, a zaton su bacvi yakr yi, Maalesh ne ya tura kofar suka shige ciki, ga mamakin su zaune yake idon shi biyu, kallo daya ya musu ya dauke kai, ganin da ya ma Daddyn shi cikin koshin lafia, be da wata damuwa abun ya bashi haushi, wato be damu da abunda matar shi tayi ba kenan? Kwafa yayi a ranshi".
Sauda ta dan matso kusa dashi cike da kissa tace "Rafeeq my boy, are u Alright?" Rafeeq ya kawar da kanshi kamar be san da wata halitta tsaye a gun ba, muryar ta ya tuna lokacin da take cewa "Yanzu yaya kwarto kika kawo cikin dakin auren ki?" haka kurum yaji ya tsane ta, be son ganin su duka har Daddyn shi. Alhaji ya matso yace "Rafeeq ka min magana, wani abu ke maka ciwo?" da kyar bakin shi ya motsa yace "donAllah ku fita" don kwata kwata be son ganin su. Ba Gardama Alhaji Habib yace "muje Sauda he wants to be alone "
Suka fita suka bar mishi dakin har Maalesh. Wayar shi ya jawo har zai danna kiran Uncle Zaid ya fasa, sai ya tura mishi sakon message "I'm home" kadai ya tura mai, lokacin da sak'on ya isa ga Zaid tuk'i yakeyi, ya bude sak'on yayi murmushi yasan Rafeeq ba zai k'i yin abunda yake so ba, sai ya maida mai Reply da "Nagode".
Haka Rayuwar Rafeeq ta kasance cikin k'una da dacin rai, duk ya koma wani iri, ga wata uwar K'asumba ya fara ajiyewa, ba ruwan shi da kowa da komai, har mahaifinshi don ya zame mishi dole ne yake amsa mai magana shima maganar bata wuce "a" ko "aa", Alhaji Habib be jin dadin yanda danshi ke yin dari dari dashi, ya kira kaninshi Zaid ya kaimai kara, Zaid ko saidai ya bada hak'uri yace a tayashi da addua. Hakan ba zai hanashi gobe ya koma dakin Rafeeq din ba, tunda shi ba shiga yakeyi ba, sai a kwana a yini Rafeeq be ce "a" ba, tun Maalesh na damuwa har ya daina damuwa.
Hankalin Maalesh ya tashi da ya tuna Jibi zasu koma Makaranta, 2nd Semester Level 400 final Semester dinsu kenan a Jami'ah, ga project ga defence ga wacece, taya Rafeeq zai wuce idan yana haka? Da sauri ya dialing number Uncle Zaid ringing biyu Zaid ya dauka "Hello Mahmud?" bayan gaisuwa Maalesh yace "Uncle Zaid Jibi fa muke komawa School, ga shi shine final semestern mu a makaranta, Dole sai Rafeeq ya kwantar da hankalin shi yayi focusing kan Semestern nan, shi ke topping din Department dinmu, Uncle Zaid Wallahi duk Sciences bs kamar Rafeew Lema, lecturers naji da shi, idan ya sa wasa zaiyi k'asa sosai don abun nashi k'ara girmama yakeyi wallahi, yanzu da idan nazo tayashi fira ya kan dan kulani, amma yanzu wallahi har inzo in gama surutu na, in gama zama na in tafi in ya tanka ni, kai da ba ka gurin ka tanka, Uncle am afraid for him" hankalin Zaid yayi kololuwa gun tashi, burin da ya jima yana ci kan Rafeeq na son rugujewa, tunda Rafeeq ya shiga nursery yake adduan Allah ya nuna mai randa zai gama Jami'ah, to ga lokacin yazo daidai da k'addarar sa, ya zaiyi? Dole Rafeeq ya maida hankali, dole Rafeeq ya dawo normal self dinshi, Zaid yace "Mahmud kar ka damu, gobe InshaAllah muna nan dawowa da Rafee'ah tunda hutu ya kare, komai zai daidai ta."
Sun Iso Katsina Lafia, tunda suka shigo Haraban Gidan taji Gabanta ya fadi, ta kalli Uncle Zaid tace "Uncle Zaid gaba na ke faduwa, kamar wani abu na shirin faruwa" Zaid yace "kin fara superstitious beliefs din nan naki ko, ba abunda zai faru kinji Rafee'ah?" tace "Allah ya sa, i cant wait to see my Mami and my troublesome Hamma Rafeeq" Damm gabanshi ya fadi, ana wata ga wata sai yanzu ya tuna Rafee'ah bata san wainar da ake toyawa ba, ba ta san me ya wakana ba tun bayan Zuwan ta kaduna, ko da ta ishe shi Kan tana kiran wayan Mamin ta a kashe sai yace taje India Medical Checkup, kuma Dr ya bata rest so ko waya bata amfani da shi, ta yarda dashi don ta san be mata karya, kafin yace wani abu tuni ta fita daga motar, ta na kiran "Hamma Rafeeq i'm home" da karfi ta ke maganan, Gaban Rafeeq ya fadi jin muryar Rafee'ah, be san lokacin da ya shige toilet ba ya wanke fuskar sa don kar ta ga damuwa itama ta tada nata hankalin.
Cikin gida ta shige ta na fadin wai ya na ji Gidan shiru ne? Ba kowa ne? Alhaji Habib ya fito yana Oyoyo Baby, hajia Sauda tana biye dashi a baya, da sauri Rafee'ah taje ta rungume Daddyn ta tana "Daddyna i've missed u" daga ta yayi sama yana juyi da ita kamar wata baby ita ko tana ta daria. Ya direta yana "i missed u more my angel" taje ta rungume Sauda, Sauda na ta murmushin munafurci tana "haba ai gwara da Zaid ya dawo da ke, tunda ya dauke mana ke gidan ba dadi" ita ko Rafee'ah sai k'yalk'yala daria take yi, tace ina Aneesa? Sauda tace tana chan BUK wurin kanwata, zuwa k'arshen wata zasu dawo" Daddy yace ya Safiyya(Matar Zaid)? Rafee'ah tace "Daddy ta na nan lafia, ta kusa haihuwa ma" Allah ya raba lafia. "Daddy wai ina Uncle Hafiz da Hamma Rafeeq?" Daddy yace Uncle dinki na Yobe na aike shi, Rafeeq kuma na Dakin shi. Tace "Ohh yana jina yayi shiru ya kyale ni ko? Barin je in iske shi" ta sauka k'asa tayi hanyar dakin Rafeeq.
Tunda daga waje take kiran "Bigbro Rafeeq, wai ba zaka fito ka ganni ba? ta kutsa kai cikin dakin, turus ta tsaya ganin Rafeeq zaune kan kujera sanye da Bak'in Gilashi, mamaki ya baiyana fuskarta, da sauri ta je ta rungume shi, ganin yanda ya mata ne yasa ta dagowa da sauri, "Hamma na, baka ganni ba? A hankali yace "naganki, Rafee'ah" baka yi murnan gani na bane? Shiru ya mata, ta dinga mishi tambayoyi be bata amsa ba, Ga mamakin ta sai ganin hawaye tayi ya gangaro kan kumatun sa, cikin rudewa tayi saurin zare Gilashin idonshi, tace "mai ke faruwa ne? Baka da Lafia ne?" Daidai nan Zaid ya fito daga toilet din dakin yace "Rafee'ah, ki rabu dashi, be da lafia ne, kuka ta fashe da tace be da lafia? Wani irin rashin lafia ne wannan?