Showing 87001 words to 90000 words out of 149166 words
daga nesa Seebi ta hango Aneesa hanjin cikinta suka kada, ta mik'e tsaye, ai kuwa Aneesa na zuwa ta kamtse Seebi da Mari lafiyayyu har kala biyu, tare da nuna ta da yatsa "stay away from my Family" Seebi dafe da kuncinta, tana hawaye, Ushee tace "haba baiwarAllah me ta miki ne zaki ci zarafinta?" Aneesa tace "ko zaki rama mata ne?" Usheey tayi shiru don ta fi Seebi tsoro, Aneesa yarinya ce ko shekara 18 bata rufe ba, amma girman jiki ne da ita, girmanta zai sa ayi zaton Babba ce shiyasa ake jin tsoron ta, "kuma Wallahi kije ki cire kayan nan, duk randa na sake ganinki da su sai na wulakanta ki" hankalin mutane ya dawo kansu, sunsan Aneesa Lema da Masifa, wani yace "kema kije kiyi yanda tace mana" da sauri Seebi zata juya ta tafi taji an rik'o hannunta tana dagowa taga Miemee tsaye, tace "Ba inda zaki, in Uban wani yace ta sa irin kayan da kika sa sai taje ta cire tunda tafi k'arfin a ga ta sa irin kayan ki" "Ke kuma wacece yar shiga sharo ba shanu?" inji Meesha, kallon Ke gara Miemee tayi mata, tace "Rama marinki" Seebi ta girgiza kai, Miemee cikin daga murya tace ki rama Marinki Nasiba Muhammad" Aneesa da mamaki ya gama kashe ta tace ke banza ke wacece? Ba zata rama ba ko zaki rama mata ne?" kafin ta sake wani magana taji an kaure da mari kala 2, Miemee ce da k'arfin halin nan, Usheey da Seebi da kowa na gun na mamakin Miemee, Miemee ta nuna ta da yatsa tace "She's my Friend, f**k her up, and i'll f**k u down" Aneesa cikin borinkunya tace "We'll meet again, this is not the end of this, Meesha get my bag" tafita ,Meesha taje ta dauko jakkar ta bi bayan Aneesa.
*********
Usheey tace "Seebi me ya hadaku da ita ne?" Seebi na kuka Miemee ta tashi zata bar gurin, Usheey tace "ahh Miemee ina zaki?" tace "i'm giving you two space, ai naga kamar maganan Sirri zakuyi" Seebi ta dago kai idonta sunyi Jaaa tace "wace irin magana kikeyi wannan? Miemee tace " Seriously? Ai naga sirri kuke tayi tun dazun, kuna magana K'asa k'asa, ba kwa so in ji maganar da kukeyi, to tell you the truth it really hurts me, yanda na dauke ku ba haka kuka dauke ni ba, nice me bakin Reza, da idan abu ya sameni na Sharri ko na Alheri ku nake fara sanarmawa, because i love you two like my sisters, Amma ku kwatakwata ba haka kuka daukeni ba, a ganin ku ni ballagaza ce, da naji zanje fesa ma mutane, i'm not worth sharing your secrets, kuna wareni a cikin ku, ai gwara in fidda kaina" zata wuce Seebi da Usheey sukayi saurin kamota, Usheey tace "haba Miemee is not like that wallahi, ba abun da kike tunani bane, kin tsargu ne kawai, dazun cikin aji nine ma ke bata labarin Usman(Saurayin Usheey) kuma kinsan da labarin, kuma abunda ya sa muke magana a hankali kar Mallam ya fitar da mu yace mun isheshi da surutu, yanzu kuma a CAF ne ta fara bani labarin, tace a bari sai kinzo nice na matsa mata coz i'm eager to hear, nace idan kin dawo sai ta sake baki labarin"
Seebi tace " I am sorry Miemee Wallahi ba haka bane, abunda Usheey ta fada gaskia ne, Wallahi i love you both equally, kiyi hakuri please don't think otherwise" Miemee ta kalli bestfriends dinta, ta amince ba k'arya suke mata ba, don ta yarda dasu tayi murmushi tace "Group Hug" suka rungune juna su 3. Nasiba ta sa hannu cikin jakkarta ta ciro wayarta Iphone Ta daga musu sama a tare sukace "Nooo way" tace "Yes wayy" Miemee ta amsa tana Omg, this is real Wallahi Iphone dince" suka ta Daria, Seebi tace " da kayan jikina da wayar nan, Uncle Zaid ya bani su" Miemee tace "Uncle Zaid?" Seebi tayi daria tace "wannan da kika ma lak'abi da Azababbe, shine wannan da kika zauna gaban motarshi randa mukayi lectures 4-6, randa mukayi trekking har bakin gate, wanda kikace ya hadu Sosai, wanda ya fara kaiki gida Kafin ya kaimu namu gidan" Miemee ta katse da murna tace "ya isa Seebi, na ganeshi wallahi ko ba me waya ta AUX ba? Kuma shine ya kawo ki School? Babe whata are you hiding? Ki fada mana Please" tayi daria tace "to kunji kunji......" ta gaya musu komai tsakaninta da Lema Family Amma banda Mafarkanta. Sun tausaya ma Rafeeq matuk'a amma Miemee ta ta6e baki, tace "Poor R-Lema, He's lost, but thats no reason da zai dinga treating mutane asif they are trash or something" Seebi ta Usheey suka hada baki sukace "kina da Damuwaaaaa" daria sukayi duka, Usheey tace "Seebi, gaya min kinason Uncle Zaid ko?" tace "Wallahi i dont know nidai nasan kawai ina ganin girman shi" Miemee tace "Shegs kina so,lemme lecture you on how to keep a boyfriend" Seebi tayi daria ta dauki jikarta tace ku tashi mu tafi gida, kunsa munyi missing lectures ba gaira ba dalili, saura 15mins a gama kun ga kuwa zuwan mu be da amfani" Usheey tace "ba Sallah ba salati, labarin ne kamar kar ya k'are kamar a film, saukin ma dai munci Abinci" Miemee tace mu biya Central Mosque muyi Sallah, in munci Sa'a mu samu bus muna fitowa" haka Miemee ta biya musu Plate dinsu 600duka don cikin su 3, ta fi su hali, suka bar CAF.
********
"Lahh ga motar R-Lema da alamu yana cikin Massalacin nan" Miemee tace sai me? Ga bus nan kuzo mu shiga kafin a ciketa, Seebi tace "Aa, mu jira ya fito, kinsan ko ganin mu yayi anan bazai barmu ba, gwara mu jirashi" Usheey, tace "Ni wallahi nagaji kafin mu isa Bus ta jigata mu" Miemee tace banson raini wallahi, duk me ya mana yau kuka ja mana, Nasiba tayi daria tace naji na yarda, wurin motar suka tsaya, sai ko gashi kamar an jefo shi yana tafiar nan nashi cikin isa, kallo daya ya musu ya dauke kai, a ranshi yace "Wannan ta kile yau ita ne da Veil, tayi kyau" chan kuma yayi tsaki yace "sha its none of my Bussiness" ya bude motarshi ya zauna, shi be tafi ba shi be basu damar shiga ba, Seebi tayi Jihadi tace mu shiga, suka bude suka shiga, tace "Hamma ina wuni" kamar ba zai amsa ba yace "lafiya" Usheey tace Ina wuni yace "Sannu fah" Miemee kuwa ta dauke kai duk abun Miemee bata san Raini da wulakanci, bata fiye hakuri ba(waya ga Diyar Aminene Mamman) Shi be ma lura da ita ba ya ja motarshi ya bar School, duk suka kasa magana sai gudu yake tayi dasu, ya bi ta Ringroad, kamar ya rufe bakin su duk sukayi shiru, sai gasu sun bullo ta Salamah, har ya wuce k'ofar Gidan Nene zai yi kwanar Gidan Lema Nasiba tayi saurin cewa "Hamma zamu sauka a nan" "Oops na manta" ta k'irkiro murmushi tace "bakomai" yayi parking suka fita, Miemee ta cika tayi pam, tace "Wallahi Gayen nan dan rainin hankali ne, abun nashi wallahi harda Iskanci" Usheey tayi daria tace mu ai munzo gida, muje ki samu Napep, Seebi tace "ai tunda tazo nan sai ta shiga ta gaida Nene, kuma taga Daughter na" suka sa Shewa, suka nufa Gidan Nene.
Nene na ta dirka ma Ayman Kokon da rage dazun da safe, tana ganin Seebi ta mik'e ta mata Oyoyo, duk sai ta burgesu, Seebi ta daga ta sama Oyoyo my baby" Ahh su Miemee 'yar gayu, da Usheshe, sannun ku, shigo ku zauna, A'ah Nene mu gaisa wucewa ma dai zamuyi, nan suka gaisa, sukayi Ayman tazo gunsu ta mak'e ta lafe gun Seebi, Seebi tace Nene bari in rakasu, sai da suka tsaida ma Miemee Napep, sannan ta raka Usheey gida kafin ta gangaro gida.
****
Daga Nesa Aneesa ta hango Nasiba rungume da baby, tace "Ohh dama nan Unguwar kike? Matsiyaciya aiko zaki ci Ubanki, ta dinga bin bayanta a hankali a motar ta, har taga Nasiba ta shiga wani gida, Aneesa tace a ranta ban minti 10 yanzu zan dawo gareki" kuma in dai idonta be gaya mata k'arya ba, to tabbas diyar Zaid ce a hannun Seebi, tace "Bala'in chan" Nasiba na shiga ta zauna kusa da Nene, ta na tambayarta abunda Ayman taci, Nene tace "Baban ta be dade da maido ta ba, yanzu taga ina shan kwakwo naga ta na kallo na, ko da na bata sha take tayi, mik'ota ta shanye kingin" Kafin Nasiba tace wani abu taji Sallamar shi, da Mamaki ta dago ta kalle shi, tace "Hamma" be kula ta ba ya kalli Nene da ke dirka ma Ayman Koko yayi cukun cukun da fuska, ya danyi tsaki yace "Neh-neh, meye wannan take sha?" ta kalleshi tace "Ahh Neh-neh Naji kace? Wai kai in tambayeka komai sai ka fade shi da turanci ne? Nenen ma sai ka fade Shi da boko? To nidai ba sunana NehNeh ba, in ka koyi kiran sunana Sai kazo in baka Amsa" yayi dan guntun tsaki tace "Tsukakke" ya kalli Nasiba yace "Meye take bata?" tayi murmushi tace "Kokko Ne" "shine ya bata mata baki haka?" ya sake dan guntun tsakin yace "Zanci Indomie and Egg" jiki na rawa tace "Bari in dafa maka" tayi saurin shiga kicin ya zauna kan kujera yana mik'a ma Ayman hannu yana cewa "Come here Angel, hamma is here" Ayman ta mak'e kafada alamun Aa, aiko Nene ta fashe da daria, tana ma R-Lema gwalo, daria ta bashi, gudun kar yayi daria gaban Nene ya sa shi dauke kai.
******
Ta dibar ma Ayman a dan bowl ta zuba ma Rafeeq a plate ta tsiyayo mai Ruwanshi ta kawo mai, "Thanks" yace yace "Nene in zubo miki? nene tace ni rabani da Indonie dinnan, zan shi waina na nan anjima, Nasiba ta zauna tana ci tana ba Ayman A baki,
Bam Sukaji an bugo k'ofa da k'arfi, Nene tace "oh Allah, Iska ne haka? Allah na tuba nidai kar k'ofata ta 6alle Kafin wani ya sake magana sai ga Saude ta shigo gidan tana ma gidan kallon wulakanci, ta chakare dankwali gaban goshi, hannunta kan k'ugu, Meema da Aneesa na bin bayanta, ashe Aneesa taje ta gaya musu k'arya da gaskia, Nene tayi saurin mik'ewa shi ko Rafeeq tunda ya musu kallo daya ya dauke kai ya cigaba da cin Abincin shi, Nasiba tuni ta fara kyarma, Aneesa tace "Ya Rafeeq me kakeyi a nan?" kallo bata ishe shi ba, Saude ta kalli Nene galala tace ke tsohuwa, nazo in ja ma wannan kilakin kunne, amma tunda gaki to gwara in miki sai ki ja mata kunnen da kyau, Wannan karamar kilakin na bibiyar Mijina, tana bibiyar k'anin mijina, Kuma tana bibiyar dan mijina don ga zahiri nan, ta nuna Rafeeq, har ta isa ta daga hannu ta mari diyata? Ta sa k'awayenta su mata duka? Wannan 'yar iskar har ta isa? Meema ta chafe "ni ai kamar na so in gane wannan tsohuwar, Anee ba ita bace ta taba tsaida mu a hanya ta bamu waya ko mu kira mata Uban wa? Matsiyaciya, Asiri suke ma mutane dube Rafeeq da be ko kallon pampon gida ya zage ya bude ciki yana cin Abinci, dubi kayan jikin ta komi irin na Anee, Asiri suka ma UncleZee ya siyo mata irin shi, banzaye matsafa kawai. Har yanzu jikin Seebi be bar rawa ba, Nene ko sai dai ta bi wannan da kallo ta bi wannan da ido, sai da ta gama karance su tsaf. "Ke Aneesa dauko Ayman mu ta fi gida, idan na k'ara minti 1 anan zan iya sik'ewa don nan ko gidan Karena Albarka" Aneesa ta dauki Ayman, Ayman ta 6are baki, sai a sannan Rafeeq ya dago, da rinannun Idanunshi yace "Let her Go" be san meyasa ya kasa tanka su Saude da suke cin Zarafin su Nene ba, "Saboda mene Rafeeq?, mune fa dolen ku, baku da kowa, mune yanuwanku ba su ba, You are not related by any chance" cikin tsawa yace "I said let her go" da sauri Aneesa ta direta, ta tattaka ta nufa Nasiba ita kuwa ta kasa daukarta, don gudun abunda zai dawo, Rafeeq yace "duk abunda zakuyi ko zakuce kuce, but dont you dare touch this Soul" Saude ta kalle su ta watsar tace "ku taho mu tafi, tsayuwan mu nan is useless, ke dai Na gaya miki ki jama jikar ki ne ko diyarki kunne, in ko ba haka ba to sai zaman Katsina ya gagareki"
Nene tayi murmushi tace "nidai tambaya daya zan muku, donAllah kune kuka taran ma Nasiba jiya da daddare?" Aneesa cike da Rashin kunya tace "Eh mune, yanzu ma ba ita ba har ke sai mu taran mawa" Nene tayi daria tace "Alhamdulilah MashaAllah dama amsar da nike son ji kenan" ta kwance dankwalin kanta ta daura a kai, ta kalli Nasiba tace ke dauki Aymana ku shige daki kar ki sake ki fito, Nasiba ta san Nene ba Alkhairi zatyi ba tace "Nene DonAllah--" Nene tayi saurin katse ta da cewa "dan Ubanki ku shige daki nace ko, zaki dauketa ko sai na fara da ke? Jiki na rawa ta dauki Ayman ta shige daki, Meema tace " What is she trying to do" Aneesa tace 3 against 1" sukayi daria duka.Nene ta k'ulu ga turanci sun yi, sun k'ara da6awa ta kalli Saude tace " Uwarki ce Ogan kilakai, cikin dakin kwarto ta mutu, ke kuma randa na baki waya nace ki kira min, ai baki tsaya kinji wanda nace ki kiramin ba, Ubanki nake so ki kiramin a lokacin, cikin ku wa ya fara taba fatar Seebi? Saude da ta gama harzuk'a da zagin da tsohuwar nan ke musu tace "Nice nan" bata ankara ba taji Nene ta buggan mata Baki, bata ankara ba taji Alamun gishiri gishiri a baki Aneesa tace "Laaaah Jini? Kika fidar ma Mom dina Jini? Tayo kan Nene gadan gadan, nene ta kwashe ta da Mari, Marin da ta ga Stars na walkiya, tace "ga Marin Da kika ma Nasiba,Yo ni Allah na tuba Ai Ba Uban da ya isa ya sa Zaman Katsina ta gagareni, naci uwarki in baki hana zaman katsina gagarata ba" Rafeeq yayi murmushi yace "Interesting! Thats what i'm talking about" ya kwashe plate da cup dinshi ya kai kitchen, ya fito yana daria yace dasu "You all can leave while you still can, this the only opportunity you have, is now or never" Saude ta dago ta kalleshi cikin masifa tace "I never back down from a fight, this woman will regret doing this to us" Rafeeq yayi murmushin mugunta yace "in that case, i'll sit back and Watch" Nene tace "Uban me kake ce musu? Yayi Daria yace "ce musu nayi su fita shine tace wai ba zasu fita ba sai sun koya miki hankali, wani abu ma da tace ba zan iya fada miki ba saboda yayi nauyi da yawa" Nene tace "kayi wa Allah ka gaya min? Girgiza kai yayi, Nasiba daga ciki take cewa "Hamma stop, its not funny" Nene kuwa cewa tayi ''in kika fito sai kinci ubanki Nasiba" ta damk'o wuyan Saude ta chusa ta a hammata, ta matse, Meema tayo kanta,Nene ta wurga Saude kamar kayan wanki Saude ta buge da bango, Nene ta ci nasarar damk'o gashin dokin Meema ta dinga ja, Meema sai ihu takeyi, Nene ba ta bar Meema ba sai da tsinka kitso daya, kan Meema sai jini itama ta yadata k'asa, ta cicibo Aneesa da har yanzu bata gama kukan marin da ta sha ba, Nene ta buge bakinta tace ke me bakin rashin kunya ko? Ni kikeyi wa turanci? ta waiga ta hangotayizar da ta dauko jiya don dukkan Rafeeq, ta waiga taga Rafeeq na darian mugunta harda rik'e ciki, tace "kai dunkum mik'on Chazar chan" da sauri ya dauko ya mik'o mata, ta dinga shauda ma Aneesa, Aneesa na ta ihu, Saude ta taso don cetar diyarta ita ma bata tsira ba, Nene ta hau shauda mata itama, Meema kuwa lafe wa tayi chan baya, dafe da kanta, Saude Ihu, Aneesa Ihu, Rafeeq Daria harda Hawaye, jin Alamun zaa shigo yasa tace "kai dunkum maza kaje ka rufo gidan nan" Rafeeq harda tuntube gun fita don tsabar dariya, nan suka ci Karo da Zaid, cikin tashin hankali yace "Feeq ihun me nakeji haka?" Rafeeq daria ya hana shi magana sai nuna baya yake tayi, Zaid ya shiga da sauri, ganin Nene na laftar Saude, Aneesa da Meema kamar Allah ya aikota ya sa shi cewa "SubhanAllah, Nene me zan gani haka?" ba ta fasa laftar su ba tace "Wallahi Zaidu bawan Allah ka matso gurin nan sai na Lafta maka kaima".
(Toufa Readers, shin Hankalin Nene Daya?)
_Bibilicious Biebee,_
👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
Pg5⃣0⃣
Zaid ya daga hannun shi alamun ban hak'uri, yace "Nenen mu DonAllah kiyi hak'uri" Inaaa sam Nene Hankalin ta yayi nisa ta ba ta jin abun da Zaid ke cewa, haka ta cigaba da kilar su, Zaid yayi saurin cewa "Nene kin ta6a cewa idan ina son wani abu a gunki, kar inya shakkan sanar dake, ko menene zakiyi min shi, in har befi karfin ki ba, Nene wannan ne abu na farko da na fara tambayanki Nene DonAllah, ki bar su haka, kiyi hakuri, sun ladabtu, na tabbatar ko me suka miki sun gane kurensu" Kallon Zaid tayi tana nazarin shi, chan kuma sai ta yada Chazar tace "Wallahi, sunci darajar ka, kai kadai ka isa ka hanani wlh, don ko Mamman ya dawo duniya yanzu sai mun kai ruwa rana kafin zan hakura wallahi" Zaid yayi murmushi yace "Nagode Sosai" Saude ta tashi tana kakkabe jikinta, Aneesa da Meema ba su bar gurnanin kuka ba Saude ta tuna cewa ba abunda Tsofin mutane ke tsoro kamar Yan sanda,