Showing 51001 words to 54000 words out of 149166 words

Chapter 18 - Ke alkhairi ce COMPLETE HAUSA NOVEL

BIEBIE   

22 Oct 2024

25730

ki ka biya ma wa, hakan ya wadatas" Nasiba tace "Zanyi hakan InshaAllah " tace nagode". Nasiba ta muskuta daga baccin da tayi, don ta jima batayi mafarki ba, ta koma bacci.

Washegari
Tunda tayi Sallahn Asuba ta dinga tunanin Mafarkinta na jiya, Neneta lura da ita tace "lafiya Seebi?" Nene nayi mafarki da wata jiya, tana rokona in biya mata bashin lemun da ta siya, ina so in yi yanda tace" Nene tace "Sannu Sharifiya, wa yace miki Mafarki Gaskia ne?" nan Nasiba ta shashantar da maganar.
Tun daga ranar Nasiba ta dinga wasu Mafarkai masu tsoro, sai in dai bata kwanta bacci ba, da ta kwanta sai mafarkai masu ban tsoro, Yau dai ta tsaya tunanin dalilin mafarkanta, zuciyarta tace k'ila wannan mafarki na da nasaba da k'in biya ma wannan matar bashinta, tunda rana daya ta fara wannan mafarke mafarken, dole zata je ta biya mata bashin, ko ta samu kwanciyar hankali ta daina Mafarki.

Yau ta na zuwa Makaranta ta wuce Masanawa Super Market, ta ciro dari biyu ta mik'a ma me shago, yace "me zaa baki?" tace bakomai, wata rana kawata ta zo siyan Lacsera da dubu kace ba chanji, shine ta aiko ni in kawo maka, me shago ya amsa ya mika mata chanji, tazo juyawa taji ta taka kafar wani, a tsorace ta dago, ganin Rafeeq ya sa zuciyanta halbawa, be tsaya bin ta kanta ba ya wuce fridge ya ciro Soy milk, yazo gun biya ya ciro dari 5 ya bashi, be tsaya karban chanjin shi ba ya bar Shagon. Me shago yayi Murmushi yace "R-Lema kenan" Nasiba tace "mallam ka san shi ne?" yace ai ba wanda be san Rafeeq ba" Nasiba ta matso gunshi tace donAllah kasan dalilin da yasa yake haka? Yace "da Rafeeq na kowa ne, da da ya shigo zai dinga ja na da surutu, rana daya ya chanza, ba wanda yasan dalilin chanjin shi, gashi da k'okarin shi, duk Sciences shine over roll, amma Shekarar shi 6 a jamian nan, mates dinshi duk sun gana services dinsu, ba wai be da k'okari bane, aa ba wanda yasan dalilin Spilling din da yake tayi" Nasiba ta jinina kai tace "abun akwai ban mamaki, amma me ya maida shi hakan? Yace "ba wanda ya sani, iyakar abunda na sani kenan". Nasiba a ranta taji tana son sanin me ya maida R-Lema haka.

*MAFARKI*

"Ina Godia da Biyan bashin da kika min, Nagode, don yanzu na samu kwanciyar hankali" Nasiba tace toh "Alhamdulilah, bakomai" Yauwa kinyi abu na farko cikin Uku da na keso ki min, abu na biyu da nake so kimin shine; ina So ki binciki wani Makwabcin ku mai suna Rafeeq Habib Lema, ina so ki san ko shi waye, sannan kuma ina so ki shiga rayuwar shi" a razane Nasiba tace what? Kinsan me kike fada ne? Saboda mene zaki ce inyi haka, baiwar Allah don na taimaka miki dazun ba shi zai saki ki dinga sani abubuwa ba, ba zanyi ba, ba zan yi ba, mutumin da ko kallon arziki ban ishe shiba, toh ba zanyi yanda kike so ba, Musulmi na kwarai shine wanda be shiga hakkin da ba nashi ba" Yarinyar ta kama hannun Nasiba, kamar zatayi kuka, donAllah ki taimakeni, ki yarda dani" Cikin masifa Nasiba tace "Sabida mene zan yarda dake? Bansanki ba, bansan komai game dake ba, kinzo kina sani abubuwa? Toh wannan karon ba zan tainaka miki ba, kizo kiyi abunda kike sani da kanki, duk nisan da kike kizo ki yi aikin ki da kanki, idan kinso daga yau ki di ga zuwa min da mummunar siffa, ki hanani bacci, ba zanyi yanda kike si ba" . Yarinyar tayi dan murmushi, tace "da zan iya da nayi" Nasiba tace" zaki iya mana tunda kina tunanin ni zan iya" tace ke zaki iya don kina nan duniya, ni kuma ba zan iya ba, don bana duniya" cikin firgici Nasiba tace "me kike nufi da hakan?" Yarinyar tace " *My Name was Rafee'ah Habib Lema, na Rasu Shekara daya da Rabi da suka wuce*".

_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

*Allah Sarki Yanuwa da Abokan Arzikki, da Masoya❤ duk na ga sak'onnin Ta'aziyoyin da kuka min, nagode Allah shi karb'a, ya biya ku, shikuma mamaci Allah ya ji k'anshi (Baba Hashimu) Allah ya gafarta mishi, Allah kasa ya huta. Da duk Musulman da suka riga mu Gidan Gaskia, mukuma in tamu tazo, Allah ya sa mucika da kyau da Imani Amin, Nagode Nagode Nagode, Allah ya barmu tare.👏🏽👏🏽👏🏽.*

Pg3⃣5⃣

Firgici da tsoro suka ziyarci zuciyar Nasiba, ta fara karkarwa, ta na ja da baya, baki na rawa tace "Fa+ta-talwa" Rafee'ah ta yi saurin cewa "DonAllah kar ki ji tsoro, banda niyyar cutar dake, ke musulma ce, kuma kinyi Imani da hakan, karda ki sa ma ranki ni Fatalwa ce, ni ba Fatalwa bace, da iko da k'uddirar Allah nazo miki a Mafarki, Mafarki kike yi dani, DonAllah ki kwantar da hankalin ki, banda niyyar cutar da ke .(Mu sani Ba Fatalwa a musulunci, Wanda ya mutu ya mutu, ba yanda matacce zaizo cutar da kai, in ka ga Mattace a ido, to gizo yake maka, ko kuma kayi mai mugun abu kafin ya mutu, ka sa ma ranka ne,shine kake ganin kamar zaizo maka, amma Tabbas ana mafarki da Matattu, _to Nasiba dai Mafarki takeyi da Rafee'ah_.)
Nasiba ta sauke numfashi, hankalin ta ya dan kwanta, Sai da Rafee'ah ta ga Nasiba ta samu natsuwa sai tace "Kamar yanda nace, ina so kin dan wanene Rafeeq, ina so ki shiga Rayuwar Rafeeq, ina so ki sauya duk wani abu da ya danganci Rafeeq, ina so ki warware zare da abawan cikin gidan Lema, akwai abubuwa da yawa da zaki fuskanta, akwai hadari a cikin wannan aikin, amma ki sa Allah a gabanki, ba zai barki ke kadai ba, sai kin jure kin daure". "Bazan iya ba, ni ala musuru ce? Da zan miki duk wadannan abubuwan? Saboda mene zaki dinga bibiyata cikin mafarki kina sani abubuwa?" inji Nasiba, Rafee'ah ta nuna ta da yatsa, tace saboda *"KE ALHERI CE"* cikin rashin fahimta Nasiba tace *"NI ALHERI CE?"* Rafee'ah ta gyada kai tace *"Eh, KE ALHERI CE"* ba za ki gane ba yanzu, amma a sannu zaki fahimci dalilina na ce miki haka, ta dan sasautar da murya tace "Nasiba, Rafeeq yaya na ne ina sonshi sosai, Rayuwar shi na cikin 6ata, ki taimake ni ki min wannan aikin, Allah kadai zai biya ki" Nasiba tayi shiru tana tunani, tabbas ita shaida ce kan halin Rafeeq na Shariya, da k'yaliya, itana tana kwadayin jin labarin shi, kuma tasan tabbas yana cikin damuwa, chan tace "Shikenan, Allah ya mana jagora" dadi ya lullube Rafee'ah, tace "Nagode Sosai, but one more thing, you must not tell anyone about your Dreams and your Mission, kar ki gaya ma kowa, komai kusancin ki da mutum, ki min Alkawari kinji?" Nasiba tace "InshaAllah ba wanda zai sani" Nagode sosai, ki fara binciken ki da wuri, ba mu da lokaci" Rafee'ah tace "InshaAllah". Rafee'ah ta mata sallama ta tafi, daidai nan Nasiba ta sauke ajiyar zuciya me nauyi cikin bacci, gyara kwanciyarta tayi.

_7:50am_

"Nene yi zaman ki, barin je in siyo k'osan", aa Seebi budurwa dake sai a ga kin tsaya bakin titi siyan k'osai? Yo meye? Wa ke bina bashi?" ni zanje, ba me bina bashi" Nene tace "kawai sai a ga yar budurwa kamar ki na bin layin k'osai?" Nasiba tace "ni kuma gani mara tausayi, kina fama da Masassara don kar ace gani budurwa, sai in barki kije siyan k'osai, to ba dani ba, kinga tafiya ta" Nenen tace "ai sai kiyi, tun yaushe zazzabin ya sauka?" Nasiba ba ta tsaya tanka ta ba ta fita daga dakin, Nene kuwa ta dan kishingida, ko minti daya baayi ba wayar Nasiba ta hau ruri, Nene ta buga tsoki " wani dan anacen ne ke kiran waya da fara saffiyan nan? Sun maida waya Kamar wata Ramadana, haka ta dinga mita har wayar ta tsinke, chan ta hau ruri, Nene ta mik'e ta zaro wayar k'ark'ashin pillown Nasiba ta latsa tare da cewa "Hello" "Assalam Alaikum Seebin mu ni da Nene" Nene tace "Laaah, Zaidu bawan Allah, Kai ne?" yayi murmushi kamar yana gavanta, yace "Eh Nene, nine, kamar kinsan kiran nan naki ne" tace "Allah ko? In ka ji kira Samu ne" yayi daria, yace "Addua nake buk'ata, an tura ni Ingila wani Aiki, kuma zanyi sati 3zuwa wata 1 a chan, shine muke barar addua" tace ai addua kullum cikin yinta muke, Allah ya kareka daga masu jan Kunne" yace "su waye masu jan kunne?" "Tabdijam! Turawa mana" Dariya Zaid yayi sosai, tace "Af! Daria na baka ko? Ai turawa muggai ne, sai an hadasu da *Li'ilafi kuraysh*" Sosai Zaid ke dariya, yasan idsn ya biye ma Nene, haka zata dinga sa shi daria har yayi missing flight dinshi, yace "nikam ina Seebin mu?" Taje siyo K'osai da burodi" Zaid tayi dan jim, Nene ta fuskanci shirun Xaid, Ehtace "kai ma kagani ai, gardama tsiya gareta sai da nace mata ta bari in siyo, tace wai aa, wai ban lafiya ita zata ta siyo" Zaid yace "baki Lafiya Nene? "Zazzabi ne ya lullube ni jiya da daddare, amma yanzu ta sauka, na ji sauki" "Nene ko zakije asibiti? "Kai ni rabani, komi Asibiti, to naji sauki" yace "to shikenan Nene, ni zan tafi, kice da Seebi zan kirata idan na sauka" Nenen tayi Murmushi tace "to Zaidun Seebi, Allah ya tsare ya kare ya bada saa" kiris ya rage dadi ya kashe Zaid, yaji dadin wannan kalami na Nene, yace "Amin Nenen mu".

*Kaskon Mai K'osai*

Lubbatu mai k'osai (Sorry Lubie😂) ta shahara gun soyen k'osai, ga dadi, ga tsafta, gaban kaskonta mutane ne sosai suna jira a soya a basu, Nasiba na daga cikin masu jira, tayi tagumi daga gefe tana tunanin Mafarkin ta na daren jiya, tana tunannin yanda zata bullo wa lamarin, taya zata shiga Rayuwan R-Lema ba tare da taimakon kowa ba? Ta ya zata san ko shi waye ba tare da ta tambayi Zaid ba? Allah ka kaow min Mafita" sama-sama ta ji firan Lubbatu mai K'osai, da wani dan datijjo, da alamun Customern ta ne inda datijjon ke cewa "Ni banga k'awar fada ta yau ba, da ta na nan ba zan gaji da jiran layin nan ba" lubbatu tayi daria, tace " nima bangan ta ba yau, da ta na nan da ta dinga mitar har yanzu ba a soya min nau ba?, ko kuma tace ta rigaka zuwa nan" daria yayi yace "aiko idan zan wuce gida zan biya gidan ta inji ko lafiya yau ba ta fito siyen k'osai ba" lubbatu mai k'osai tace "anya Maigadin Gidan Lema ba da Aminene za'ayi ba?" ya fashe da darian jin dadi yace "ai na fi k'arfinta" Nasiba da ta yi k'ask'e tana jin su, a ranta ta maimaita "Maigadin Gidan Lema? Isit possible gidan su R-Lema yake Gadi?" Don tana da tabbacin wuraren nan gidan su R-Lema yake, kuma tabbas maganar Nenen ta suke yi, Allah sa haka ma, Don ta fara aiwatar da aikinta tun wuri.
Ba jimawa a aka sa ma Baba Maigadi Gidan Lema k'osan shi, cikin saa a ka zuba ma Nasiba nata, Baba Maigadi yayi Gaba Nasiba tabi bayan shi, tace "ina kwana baba?" da faraa yace "lafiya lao Jikata" haka suka cigaba da tafia har Nasiba tazo gida, zata shige kenan yace "Jikata dan tsaya?" cikin gidan nan zaki shiga?" tayi murmushi tace "eh, Baba" yace "ko Aminene na ciki? Na jita shiru yau bata zo siyan k'osai ba" tace "eh ta na nan, bata ji dadi bane jiya da daddare " yace "Assha! DonAllah kice da ita, Maigadin Lema na Sallama" bawai don tana da tabbas ba tace "Baba kai Maigadin su Rafeeq ne?" ya washe baki yace " Yo eh, ai nine Maigadin su, tun lokacin Iro Kakan Rafeeq kenan" Murmushin Nasara Nasiba tayi, tace "Baba, barin maka Sallama da Nenen" ta shige gida.

"Nene ana Sallama da ke?" Nene tace Sallama kuma? Wanene? Seebi cikin sigar zolaya tace "bazawarin ki" ke zan saba miki, badai Zaidu bane don yanzu ya kira yace an turashi Ingila aiki zaiyi wata Guda" Haka kurum Nasiba taji ba dadi, zata yi kewan Zaid, tace "wani Maigadin gidan Lema" murmushi Nene tayi tace "Danrainin wayau, nasan zuwa yayi jaje na yau be ganin ba a gurin siyan K'osai" Nasiba tace "Toufa, har kun saba da Shi, ko dai ko dai?" harara Nene ta jefeta da shi, tace barin je mu gaisa" Nasiba tayi saurin cewa aa, barin dai ce ya shigo sai ma in shek'a mana koko, Nene ba ta ce komai ba Nasiba taje ta shigo da Baba Maigadi.

Bayan sun gama kalaci ya musu Sallama, Nasiba tace "barin raka ka baba" yace to Jikata, ya kalli Nene yace to "Aminene, Allah ya kara sauk'i, sai na sake zagayowa" cikin wasa tace " Idan zaa dawo a dawo da karin ciwo, bawai azo a isheni da dimin surutu ba" Gabaki daya suka sa daria..

_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

Pg3⃣6⃣

A hanya, Nasiba ta dinga jan shi da fira, da yake Baba Mai gadi saurin sabo ne dashi, nan da nan yake bata amsar tambayoyin da ta ke mai, Nasiba a ranta tace "Hanya Mafi saukake da zan san ko kai waye Rafeeq" Baba mai gadi yace "ke Nasiba, kinga har kin rakoni Gida, na jaki da yawa" tace "lahh har mun iso? Ya nuna gidan da yatsa, yace "ga gidan nan" gabanta ya yanke ya fadi, wani irin Tamfatsetsen gida ta gani, gidan ya hadu, a ranta tace "So this is where you live R-Lema" Baba yace to ki koma gida Nasiba, sai nazo gobe, ta dan marairaice fuska tace "Baba nasan Nene ta koma bacci, idan ba damuwa in zauna nan in tayaka fira" bench ya dauko ya ajiye gaban Gidan, ta Zauna, yayi daria yace wani irin fira zamuyi? tace "labari zaka ban" "wani iri kenan" a ranta tace "Astagfurullah Zanyi karya" ta sausauta murya tace "Baba labarin Rafeeq zaka bani, Makarantar mu daya, da ni budurwar shi ce, yana sona sosai, amma rana daya ya sauya min, ina son shi kamar me, amma sai naga ya daina kulani, yanzu ko gani na yayi kallo ban ishe shi ba, shine nake tunanin ko yaudarata dama chan yakeyi?" da sauri ya girgiza kai yace " kar kice haka, Rana daya Rafeeq ya sauya ma kowa, Rana daya K'addara ta gifta ma Rafeeq" Nasiba tace Baba ka ban labari *Wanene Rafeeq* Ajiyar Zuciya yayi, yace Rafeeq D'a ne kamar kowa, mai fara'a da son Jama'a, kinji kinji................ Tsaf Baba maigadi ya kwashe ya bata labarin duk abunda ya sani game da Gidan Habib Lema har zuwa zaman da sukayi yau. Sosai Nasiba ke kuka har da Majina, lokaci daya tausayin Rafeeq ya lullube ta, Sam bata ga laifin Rafeeq ba, lallai Rafeeq abun tausayi ne, Lallai Rafeeq na buk'atar taimako.

Baba Maigadi yace "Nasiba mun dade zaune a nan, ki tashi ki tafi Gida" ajiyar zuciya ta sauke tace "Baba, Labarin Rafeeq na cike da Abubuwan ban Alajabi da Mamaki, da tausayi, baba yanda kasan a fim" Baba maigadi yace a takaice ma kenan, "zato zunubi amma ina Zargin Matar Ubanshi Saude ga duk wani abun da ke faruwa cikin gidan nan, ban taba dai ce ma kowa komai ba" da sauri tace "Saboda me kace haka Baba?" "Saboda randa aka ce an kama Mahaifiyar Rafeeq da kwarto cikin daki, Saude ta fito ta aikeni siyan Gayen lataz, kafin na dawo har an saketa, tun daga rannan komai ya sauya, Alhaji be kara maganar da kowa ba, kinga kuwa beyiwu haka, ko yaya ne sai an maida magana, amma ko maganar ka mishi zai nuna be ma san wacece Aisha ba, kinga ko anan akwai ayar tambaya, sai maganar Karatun Rafeeq, makarantan ku daya, ke kinsan irin kokari da fasahar da Allah ya bashi, amma har yau ya kasa gamawa, abokin shi Maalesh har ya gama bautar k'asa, nan ma akwai ayar tambaya, sai maganan Rasuwar Rafee'ah, mutuwa dole ce ta na kan kowa, Ana gobe Rafee'ah zata rasu, ta fito da Cooler abinci ta fito nan tana zolaya ta, tace dani "Baba, yau da Hammana zan ci abinci" nace kice sanwa kika ma yayanki tace "Aa, antu saude ta dafa mana" ta shiga ciki, chan sai ta fito, nace har kun cinye? Tace "be ci ba ya riga da ya siyo nashi, ni kadai naci, ko na juye maka sauran a plate? Nace "aa Rafee'ah nagode" washe gari Rafee'ah tace ga garinku nan. Tunda Aisha ta bar Gidan nan, ban kara cin komai na Gidan ba, don ba bani ake ba, ruwa Saude bata taba miko min ba, Alhaji be taba cewa don me baa bani abinci ba, shi da ke ganin girma na da darajata, Zaid kadai ke min ihsani, da idan kinga yanda muke wasa da daria da Rafeeq, abun ba aa magana, amma yanzu komai ya jagule, ni Wallahi ina Zargin Saude, hanalina be kwanta da ita ba". Nasiba ta nutsu ta na jin Zancen baba Maigadi tace "Allah shi saka ma wanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login