Showing 45001 words to 48000 words out of 149166 words
asked, u never wanted to talk about her" Idan har kana so ka kara ganin kafana a gidan ka, This woman has to leave, bana so in sake ganinta, kar kuma ki sake daukar min kanwa don kar ta koyi baki da mugun halinta" Zaid ya kaura mai Mari, ya nuna shi da yatsa" I wont let you disrespect your mother" Baby ta fashe da kuka, Rafeeq ya rungumeta, be damu da marin da ya sha ba yace "yi shiru kinji fee'ah, zan samo miki me raino, mace mai mutunci ba kamar wasu matan ba" Zaid yayi saurin kwace diyar shi daga hannun Rafeeq, yace "bata da wata mai raino da ya wuce Mami, ba ta da Uwa da ta wuce Mami, itace Uwarta, duk me zakayi kayi" Rafeeq ya kalli Mami da fuskarta yayi jazir saboda kuka yace "Ba zaka sake gani na a gidan ka ba" ya fita a fusace, Mami ta bishi da gudu tana "Rafeeq, ko kallonta beyi ba" Zaid ka bishi kar ya dauki hanyar Katsina yanzu, kar wani abu ya same shi" haka Zaid ya bishi a hanya, ya dinga lallashi, da yake Rafeeq din be iya fushi da Zaid, nan da nan ya sauko amma dole ya bar Kaduna a ranar ya wuce Katsina a ganin shi zaman shi be da amfani.
Bayan Shekara Daya (A gurguje)
Abubuwa da dama sun faru a shekarar da ta gabata, Kamar yanda Sauda ta sha k'okarin Kashe Rafeeq ta hanya da dama bata samu nasara ba, har ta hakura ta barshi na wani lokaci, kila yayi amfani, Daga abubuwan da suka faru, ciki kuwa har da Spilling din da Rafeeq yayi a Makaranta, an rasa gane dalilin spilling dinshi, don an binciko takardun shi an ga Yayi passing, an rasa ta ina aka samu tangardan(Ni dai nace Boka na kan tudu), Rafeeq kuwa ko a jikin shi, dama da Uncle Zaid ya koma karatu last year, amma yanzu ko sama zata hade da kasa ba me sashi komawa School, Su Maalesh sun fata bautar kasa.Zaid yayi Mamaki matuka, dole kenan sai ya sake dawowa? Matsalar shi daya yanda zaiyi convincing Rafeeq ya sake wasting shekara daya, Sai da Zaid ya hada da kuka kafin Rafeeq ya amince da zai sake dawowa, da sharadin idan ya sake failing ba shi ba boko har abada, Zaid yayi saurin Amincewa da hakan, a ganin shi Wannan karon akwai nasara.
A wannan karon ne Seebin Nene suka Shiga Jamiar Umaru Musa Yaradua.
*Wacece Alheri?*
Ta yaya ta zama Alheri?
*Shin Sauda zata cigaba da Samun Nasara a duk abunda ta sa gaba?*
*Rafeeq na tava dawowa daidai kuwa?*
Da tambayoyi da dama da kuke son amsoshin su, ku biyoni sannu a hankali.
***********
CIGABAN LABARIN.
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg3⃣2⃣
*UMYU Katsina*.
"Nasiba Muhammad, maabociyan sa nikab, yanzu da hukumar Makaranta tayi hani da sa nikab sabo da matsalolin tsaro ya zakiyi?" Miemee ce ke maganar nan, ta na yi tana daria, Ushee tayi saurin shafewa tace "Ahh, k'ila zata daina zuwa Makaranta, yajin aiki zasuyi ita da yanuwanta Ustazai masu sa Nikab" suka sake fashewa da daria. Nasiba ta dan harare su, tace ba abun daria bane "Dollah ku bar dariya, its not like its funny, ni ban ga amfanin hana mu sa Nikabi ba, idan yan Boko Haram din sun tashi shigowa Makaranta Nikabi zasu saka?" Miemee ta sake fashewa da wani dariyan tana cewa "Seebi dangin Shekau" Ushee ta tuntsire da daria, duk suka k'ular da ita, ta san cewa idan ta biye musu zata iya fashewa da kuka, sai ta tashi ta bar musu Ajin, su kuma daria taci k'arfin su, sun kasa bin ta.
Tafiya takeyi tana mita, R-Classes ta nufa, hanyan da tasan ba kowa ta bi, tana ta tafiyar ta ta na tunanin yanda zata cigaba da zuwa Makaranta ba Nikab taji kamar K'andagare ya hau ta, wani irin tsalle ta daka sai ta ji ta buge wani abu, a firgice ta dago, tsoro ya kamata da ta ga R-Lema, yana lulaya goshin shi don anan ta kaimai karo, ta tattaro nutsuwar ta tace "donAllah kayi hakuri, K'andagaru suka biyo ni, ban ganka a gabana ba, sannu kaji? rabawa yayi ta gefenta ya wuce ba tare da yace mata uffan ba, Mamaki ya turnike Nasiba, a baiyane tace "shi kuma wannan wane iri ne?".
*Malali, Kaduna*.
"Ayman, ga Daddyn ki" dugul dugul ta tako tana ta washe baki, Zaid ya daga ta ya wulla ta sama ya chafe, ya rungume ta yana juyi da ita, ita ko sai dariya take tayi. Mami da ke kallon su tace "ka ga, kar ka sake min d'iya ta fadi" Zaid yayi daria, yace wane ni in kada diyar Mami?dariar tayi tace "ashe kana tafe? Ya hanya? Ya yan katsina? Yace "Alhamdulilah suna ta gaishe ku" tayi dai murmushi don ta san in banda iyayenta ba wanda zaice a gaida ta, tace "barin dora ma ka abinci, nasan ka gaji" yace "Wallahi kuwa Mami, Yunwa nikeji banyi breakfast ba na taho" me kake so kaci? Yace "tuwo miyan kuka" tace "ahh ba yunwar kakeji ba, tuwo ai zai dauki lokaci" yace "Wallahi ina jin yunwa, amma ina iya tsayawa har ayi tuwon" tace "sai dai daddawata ta k'are" ya mike tsaye yace "kar ki damu na miki tsarabar daddawa da kuka, duk sun bide min mota da wari, Wallahi kiris ya rage na wurgar dasu, ashe zasu min rana" be jira ta cewarta ba ya fita, Ayman a hannun shi, har ya bude mota ya dauko ledar k'ullin ya dawo, ya mik'a mata, ta bubbude tace "Zaid wadannan kayan daga ina? Yace " Wallahi wata tsohuwa ta bani" Tsohuwa kuma a ina? Yace "a Katsina" tace Zaid ka santa ne ka amshi wadannan abubuwan? What if shes upto something, number 1 lesson, u cant trust people?" Yace "Relax, i trust this one, i trust Nene, yanzu dai ki sa daddawan da yawa, miya ya fi dadi" Mami ta kwashi ledar ta na mita, tace "yanda na ga dama haka zanyi, in kayi fushi kayi aure and stop ordering me around" Daria yayi sosai yace "yi hakuri Mamin mu".
Haka Mami ta gama tuwo miyan Kuka da ya ji busasshen kifi, Zaid ya ci sosai, yaji dadin Miyar nan, ita ma Mami taji dadin Kukar, daga jinta sabuwar kuka ce, sai santi suke tayi, Mami ta kwashe kwanukan ta kai Kitchen shi kuna Zaid yac cigaba da ma Ayman wasa, Yarinya kyakyawa sosai, yar shekara 1 da yan watanni, idan ka ganta za kayi zaton tayi 3years din nan, sabida yanda take yar b'ulb'ul da ita, kuma ba wai Nono ta sha ba, bayan Rasuwar Safiyya Madara ta ke ta sha, NAN kuma aka ci saa ya karbeta, Dangin Mahaifiyar ta sunso su amshe ta amma Zaid ya hana, yace shima Mamar shi(Mami) zata riketa, haka suka hakura, Little Rafeeah na zaune tare da Mami a unguwar Malali, kullum Zaid sai yazo ya duba lafiyar su kafin ya tafi Gidan shi, yana tausayin Ayman, amma idan ya tuna tana tare da Mami sai hankalin shi ya kwanta don ya san Ayman ba za tayi maraicin Uwa ba.
*KATSINA*
"Me ya samu Nasiban Nene na ga ranta a bace haka? ko shi lapturo(lecturer) din ku ne ya bata miki rai gobe in mishi asubanci inji dalili?" ba ta san lokacin da ta fashe da daria ba, tace "Nene, Wallahi Hukumar Makaranta ce wai mu daina sa Nikabi saboda k'asa ba lafia, ana iya yin Basaja a shiga Makaranta ayi barna" Nene tace "kai sun kyauta, ba ki san yanda na k'ijinin in ganki da nikabi ba, kamar wacce tayi k'arya, ke da ba tsiraicin kika fiddo ba, amma duk ki rufe fuskar ki ruf" Nasiba ta shagwabe fuska tace "Kai Nene, so kike ranar Makaranta ta kodar dani? Kuma mutane suyi ta kallo na?" Nene tace "ke tafi chan, yo ai sai ki shafe fuskar ki da hoda, kuma in ta kallo ne ai kin kai a kalleki, yar jikalle ta jikan Yan Sudan, donAllah ki dinga gyara fuskar ki kamar wannan yar gayun, Meemo take ko wa?" Nasiba ta fashe da dariya, ta tashi ta yi hanyar daki tana cewa "Miemee ake cewa ba Meemo ba" Nene tace "ni rabani da sunan Aljannu, yarinya da sunan ta me dadi Maryam ta koma wata Meemai ko wace tsiya" ita dai Nasiba daga cikin daki take ta daria, Nene ta cigaba da Mitar da idan ta fara bata san tsa tsaya ba, "kema Baban ki ya bata miki suna wai ba a iya kiranki da sunan Yankan ki sai Seebi har ya koya min nima" a hankali tace "Amma fa sunan fa da dadi, na yan gayu, Seebi, Seebin Nene" me Nasiba zatayi in ba daria ba. Nene ma ta sa daria ashe ta na jinta, ta mik'e tana fadin "Uban me ake ma daria cikin k'urya?".
Maalesh ya fito daga Motarshi da ya parka ta a haraban Gidan su Rafeeq, Aneesa na ganin shi ta k'araso da sauri tana yauk'i tana karairaya, Maalesh ya fara mata murmushin da be kai zuciyar sa ba, " Yaya Maalesh, howfa" yace "Anee baby ya kike?" Lafiya fa, dama ina so in kara maka tuni kan Yaya Rafeeq, Wallahi son shi na cinye min yan Hanjina, na rasa me na mishi da ko ganina ba ya son yi, idan na je gurin shi yanda kasan yaga bak'ar Jab'a, kallon arzik'i baya min, gashi zuciya ta ta kasa hakura dashi, ya zanyi?" Maalesh da ya k'osa ta gama maganar ta don warin gashin dokin ta ya cika mai hanci, yace "karki damu zan mai magana" dadi ya rufeta, kafin tace wani abu Maalesh yayi gaba.
"Guy Yane?" Rafeeq ya dago kai ya kalli Maalesh da ya shigo yanzu, da k'yar yace "Normal" Maalesh yace "ba ka kirani nazo nayi picking dinka yau ba?" kamar ba zai ce komai ba yace "Da mota naje" "Ohh, is that so?" nan Maalesh ya shiga bashi labarai, abubuwan da suka faru da friends din su, har zuwa inda Aneesa ta tare shi, Rafeeq dai be ce komai ba ya cigaba da latsa wayan shi, Maalesh be damu da shariyan Rafeeq ba don inda sabo ya saba, wasu lokuttan Maalesh na bashi labarai ne ba don yaji ta bakin Rafeeq ba, kawai don dai Yayi keeping dinshi Company, kasancewar he's alone, Ba wai Rafeeq be gane Labaran da Maalesh ke badawa bane, tsaf ya ke fahintar shi, don wasu lokaci idan Maalesh ya bashi daria ya na dan murmusawa abu kadai ke mai wuya, Magana. Ya na jin k'yuwan Magana, yana ganin Asaran Yin magana.
"Sis nikam Nagaji, ya zanyi wai da son Zaid?" Sauda ta kalli kanwar tace "Meema, dont give up so easily, kafin ki samu abun da kikeso dole ki wahala, kar ki manta wahalar da na sha kafin na samu kaina a Gidan nan, kar ki damu, ke dai kawai ki cigaba da jawo hankalin shi" wani Jawo hankali? So nawa kuma? Ai ni ina ganin idan har na yi Zindir gaban Zaid ba zai ji na burge shi ba" Sauda tace kar ki damu in ya san wata, be san wata ba".
_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
3⃣3⃣
Wannan Pagen Naki ne *Aunty Sady Yar Mutanen Jegal*, Nagode Da Kaunar da kike nuna min, Allah ya bar Zumunci Amin😘😘.
*UMYU Katsina*
Kallon wurin da ta ci karo da R-Lema take tayi da suka zo wucewa ita da su Miemee, kamar ance ta waiga ta ganshi Zaune kan dakali, ba Waya, ba littafi ba komai da ke taya shi hira, shi kadai tal, Miemee tace "Lahh, ku kalli Azababben gayen nan na rannan, Usheey ta kallo shi, Seebi dama shi take kallon, Miemee tace " Wallahi sai naje mun gaisa" Nasiba tace "Uhm uhm Miemee ina jiye miki Wulak'anci" Miemee tace "haba Seebi ba kalar mu bane a ke Wulakanta wa, just watch me" ta gyara zaman rigar ta tana karairaya ta nufi R-Lema. Kusa dashi ta zauna tana cewa "Sannu fah" kallo daya ya mata ya dauke kai, Miemee bata damu ba tace na ga kai kadai ke zaune, its seems you are lonely, shiyasa nace barin zo in taya ka fira. Rafeeq ya tashi tsaye ya bar mata gurin a ranshi kuwa cewa yayi "wannan ta cika hayaniya" Me Nasiba da Usheey zasuyi? In banda Daria. Miemee ta k'ulle iyakar k'ullewa, tace to meye abun daria, cewa yayi yana da lecturers, Nasiba tace "kaii Miemee, muna fa kallonku, ko A be ce miki ba" Usheey ta kara tuntsirewa da daria, Miemee da haushi ya kamata ta harare su tace "to sai me?" tayi gaba, suna daria suna binta a baya don abun ya basu laugh.
*Malali Kaduna*
"Waalaikum Salam" Ummi ta amsa Sallamar da taji daga waje tare da fitowa, "Ahhh Mamin Ayman ce da Ayman? Sannun ku da zuwa" da sauri ta koma ciki ta ciro tabarma. Mami dake dauke da Ayman a hannu kuwa tana ta murmushi, Ummi ta fito ta Shimfida tabarma tare da umurtan Mami ta zauna, suka gaisa. Mami tace "wato Ummin Anan, na ganeki, bakya son shiga gurina ko? Gashi Allah ya riga da ya hadamu, ko Anan ba kya turomin yazo tayamu fira, ko ba ki san Hak'k'in Mak'otaka bane? Ummi tayi Murmushi tace " Wallahi ba haka bane, abubuwan ne sai a hankali, kiyi hakuri zamu dinga shigowa" kafin su k'ara magana Wayar Ummi dake kan window tayi ringing, Ummi ta mik'e ta dauko wayar, Seebin Nene ta gani a jikin Screen din, ta dauka da Sallama, daga chan aka amsa, Ummi ina wuni? Ya gida da kowa da kowa? Lafiya Alhamdulilah, ya karatun ki? Muna tayi Alhamdulilah, toh Allah ya bada sa'a, ina Anan?yaje Islamia, ina Nenen? gata nan, Nene ta amsa wayar da cewa "Halo, Dije, ince dai kuna lafiya? "Lafiya lau Nene" Ina Mahammadu? tace "ya fita" Nene tace "to kice mai jiya kiris ya rage muyi gobara, wannan abun chanza layi yayi ta k'auri, ni kadai cikin Gida kamar Mayya, lokacin Nasiba na Makaranta, ina ta bacci kawai naji abu na k'auri, da kunji sak'on mutuwa ta, ko da ka fito wajei neman taimako sai da na share kusan minti 30 waje banga ko akuya yazo wucewa ba, sai ga Zaidu bawan Allah har da mai gyara ya kawon, Na dade ina gaya ma Mahamadu bani son unguwar nan, ba mutane, wai sai yace "Haka Unguwan yan gayu suke" yo ni ina ruwana da wata Unguwan Gayu? Yanzu da ba dan Zaidu bawan Allah ba, da gidan nan ya kone kurmus" Ummi tace "SubhanAllah, Allah shi kyauta gaba ya kuma kare" Nene ta cigaba da mitar ta "daidai da burodi idan zaka saya sai ka taka har bakin titi, k'osai kuwa sai kin ci uwar tafia zaki ga mai k'osai, ni na saba Unguwar mu ta da, duk lungu da sako akwai mai k'osai, ko tari nayi zaa jini a Mak'ota, nidai gaskia ba zan iya ba, a maidani cikin Mutane, ba na son Unguwar nan na masu k'arya". Ummi ta karai da murya tace Nene kiyi hak'uri zan sanar dashi InshaAllah, za'a samu Mafita". Nene cikin tsegumi tace "Ai gwara a samu Mafitan, kuma kice--" Nasiba tayi saurin kwace wayar tace "Laahh, Katin sun K'are" tayi hakan ne don ta san Nenen ta da mita, idan ta kama zance bata san ta tsaya ba, ko bari batayi sun gaisa da Umminta ba da kyau, aiko zata sake kiranta da ta k'ebe.
Ummi ta kalli Mami tace " hakuri Mamin Ayman, ina magana da surukuwa tace, Mami da ta gama jin Zancen Ummi na waya, kasancewar Wayar China Phone ce. Mami tace " Bakomai, najita akwai barkwanci, wani gari take ne? Ummi tace tana Katsina, diyata na chan tare da ita, tana karatu a Jamiar Garin. Mami taji faduwar Gaba don duk yanda taji an ambaci Katsina sai ta jita wani iri, balle wannan da taji wani bak'on almari na ziyarta tace "Allahu, Ayman zo mu tafi Gida" Ayman da ke ta wasa ta gunguro gun Maminta Ummi ta musu Rakiya har bakin kofa.
Bayan Wau 'yan kwanaki.
*Katsina*
Zaid ya shigo Unguwar su Alhaji Habib Lema da misalin k'arfe 3:30pm, yana tuk'in shi cikin kwanciyar hankali Daidai Gidan Nene ya tsaya ya parka Motar shi, bari ya shiga ya gaida Nene, ya fita ya shiga Soron Gidan da Sallama a bakin sa, "Assalam Alaikum" Wata siririyar murya yaji ta amsa mai Sallamar shi, Hijabi ta jawo kan igiyar shanya, tana me mamakin yau waye a gidan su? Lek'awa tayi ganin Zaid tayi tsaye ya, shima kallon ta yakeyi, ji takeyi kamar ta sanshi wani gurin, shikuma kallo daya ya mata ya gane ta, itace ya taba lift ita da kawayenta kwanaki, Sansayar Murmushi ya mata yace Seebi? Da sauri tace Ina wuni? Ya amsa mata, cikin wasa yace "Me kikeyi a gidan Kakata?" ta zaro ido cikin sanyinta tace "Nenen ce Kakar ka?" Dariya yayi yace "ehmana" daga ciki Nene ta fito, Nasiba ke da waye ke ta dumi a waje? Cikin murna tace "Lahhh, ga Zaidu bawan Allah" da