Showing 120001 words to 123000 words out of 149166 words
ruining, tunda kika shigo Rayuwar mu, abubuwa suka chanza, alot of people suffered because of you Saude, a dalilin ki na fita daga hanya Madaidaiciya, a dalilinki Mami da Daddy suka rabu, You killed Rafee'ah, Kin kashemin Rafee'ah ta" sai ya fashe da kuka da ya tuna Rafee'ah, da irin halin ko in kula da ya dinga nuna mata, yace "kuma na san Ke kika kashe Matar Uncle Zaid? Mom din Ayman?, shiyasa i'll show you no mercy, Jininki ya Halasta, i'm going to kill you right now" ai kuka take majina faceface a hancinta, "Wallahi bani na kasheta ba, why would i ever kill her? DonAllah kar ka kasheni, i have to stay Alive for Aneesa" Rafeeq ya saita yace "Goodbye Saude, May all your Evil die with you along" ya ja kan bindigar, yayi pulling trigger ya tattaro dukka bacin ranshi don ya samu kwarin guiwar Harbinta.
"Rafeeq Dont shoot" Muryar Daddy sukaji daga gefe yana fitowa daga mota shi da Uncle Zaid, Rafeeq ya kallesu ta gefen ido, yayi guntun tsaki ya maida hankalinshi ga Saude, Uncle Zaid ya daga hannuwanshi sama yana fadin "No, no Rafeeq kar ka harbeta, lets settle this right, Police sunzo, let them take it over frome here please son" siren din Police kawai kakeji, Polis ne suka iso bayan su kuma Motar Mami ce, tare take da Nene da Aneesa da Seebin da dawowar ta kenan daga makaranta taga wannan tashin hankali, kallo daya zakai musu kasan cewa a Tsure suke. Mami tace "Rafeeqqqq ka ajiye Bindigar nan" da tsawa yace "She killed Rafeeah, i wont let her getaway with it" wani Police inyamiri yace " shes not getting away with it, i promise you this, just hand over the Gun Rafeeq Lema" Rafeeq ya nuna Police din da bindigar yace "Dont come any closer, stay where You are, dukkan ku kar wanda ya matso kusa dani, she has to pay for what she did to my little sister, duk ku ja baya" yanda Rafeeq yake magana ne ake ganin kamar zautace, idonshi da fuskar shi sunyi Ja, be ganin kowa burinshi ya ga ya kashe Saude.
A hankali a dan tsorace take takawa zuwa gareshi, a gajiye take limis, ta sha wahalar Makaranta yau, a hankali ta furta "Hamma Rafeeq, put the Gun down, you are not a killer, put it down please" a tsawance yace " Shut the Hell up Naseebah, 'Yaruwata ta kashe, zan kashe ta itama, i'll avenge Rafee'ah's Death" da sauri Naseebah tace "No please Hamma na, kar ka kasheta, ka ajiye bindigar, you think Rafee'ah would be happy? She wouldnt want any blood to spill in your hands, She wouldnt be Happy if you kill for her, Rafee'ah ba zata taba jin dadi ace yau ka kashe rai ba, duk munin halaiyar Rai, daraja ne dashi, ba zan so ka kashe Rai ba, i wont let you do that" ta matsa kusa dashi tace "Enough Is Enough Please give me the Gun" sosai ya tsura mata Ido, kamar ba zai Sake ba, ya Sako bindigar a k'asa, wani Jami'in tsaro ya zo ya dauki Bindigar Da Handkercheif, Wasu kuma sukaje suka sa ma Saude Handcuffs, suka Sunkuceta kamar wata diyar roba Nene tace "Ofisa minti daya" suka tsaya, Nene tayi hanzarin karasawa kusa da su, duk suka zuba mata ido, tana zuwa daidai Sauda kuwa ta daga Hannu ta kamtse ta da Mari. Duk suka bude baki cike da Mamaki Nene ta nuna ta da yatsa tace "Ki k'ara sawa a k'ona Gidan wani kiga" duk sukayi daria, haka a ka tura Saude bayan Motar Police, Bayan sun Ja Napep da Achabar nan a Bayan wata Mota, suka wuce da su.
Zaid ya kalli Nasiba ya sakar mata Murmushi, murmushin kinyi k'okari, itama Murmushin ta maiyar mai, Zaid mamaki yakeyi tun da yazo nan yake ba Rafeeq hakuri kan ya ajiye bindigar nan yayi banza dashi, amma yaji magana daya da Nasiba tayi, meaning he loves her so much da har zai take maganar shi da na Daddynshi dana kuma Maminshi, Zaid ya raya a ranshi cewa "Sai na Aura maka Nasiba InshaAllah Rafeeq".
"Oya ku wuce Gida Shatu, ni da Zaid zamu je Police Station din". Haka duk suka shige mota sukayi Gida, 'yan motar Uncle Zaid kuma suka wuce Police Station..
Bayan Kwana Uku.
Saude na nan a Prison, abun duniya ya isheta, bata lafiya sosai tun da aka kawota, Ciwon jiki ne, da Ciwon ido, tun Iskar Napep dinnan ya shige mata Ido, gaba da gabanta Cell mates dinta sun rainata, haka suke lakada mata na jaki, dalilin da ya sa aka maida ta wani kazamin daki dake gefe, warin ma ya ishe bawa, balle kazantar da ke ciki, sai taji Sauk'i zaa makata gaban Kotu don a yanke mata hukunci..
*Bayan wasu 'Yan Sattitika*
A cikin kwanakin nan kuwa, wani sabon Kwanciyar Hankali ya shigo Gidan Alhaji Habib Lema, Basu da wata Damuwa, Suna zaune da junansu cikin Aminci da kwanar juna, Harta Aneesa suna janta a jiki don kar ta ga kamar an Wareta, Matsalarta Rafeeq, ita ta hakura da shi don ta san ya mata nisa ya mata fintinkau, amma kallon Azziki baya mata, abun na damunta, Mami ta ritsashi a daki tace kaga " R-Lema, bana son abunda kakeyi? Why are you blaming Aneesa fo what happened? Ai komai ya wuce tunda Saude is behind bars, ba laifinta bane, please ka daina blaming dinta she's your sister ka daina kaji yaro na?" Rafeeq ya dan daure fuska a hankali yake magana "Mami ni bansan irinki ba, for all her Mother did, you still consider her as your daughter, lemme remind incase you've forgotten, Her Mom is a Monster, shes not human, She doesnt Deserve to be Human, She killed your Only daughter" Mami tace "haba Rafeeq Yar Adam ce we all make mistakes, ka daina cewa She's not human" yace "Lord of Mercy, why cant you see what i'm Seeing? Sanyin ki yayi yawa, after all she did to this Family? Mami tell me What can define this? Framing you with Adultery and Fornication. Having baby with the Younger brother then Marrying the Older brother and killing her child's Dad afterwards tell me Mami is this Human? What she did was unforgiveable" tace "Rafeeq na san ta saba mana ta saba ma Allah, ba ta kyauata ba ko kadan ba, amma tunda yanzu tana nan a kurkuku ba shikenan ba, and shes going to pay for all she did, when she recovers zaayi Sentencing dinta, what i'm saying is kar ka bari fushin da kake yi da ita ya shafi Aneesa please" Rafeeq dai ya daijita ne kawai.
Sai da Mami tayi dagaske kafin Rafeeq ya fara amsa gaisuwar Aneesa.
An gama Gyaran Gidan Nene ya koma Sabo dal, Mami ta rok'eta da Allah kan suyi zaman su nan a tare da ita, don sun Saba sosai, Nene tace "Ahhh Wallahi aa Gidana zan tafi, kawai sai in ta zama Gidan 'ya'ya? Aa zaman da nayi ya isa haka, nafiso in koma chan ni da Seebi ta, Mami tace " Tabdi, ai Seebi na nan har nan da Wata 1 da Rabi, anna zaayi Aurensu da Zaid, Daddynsu ya Amshe miki ita, amma tunda kince zaki goma Gidanki barin je in gaya ma Daddy kince a Aura miki Maigadin Lema sai ku zauna A tare" Nene ta zaro ido tace " Ke Aishatu ki fita idona, haka na ce miki? Wani aure zakuyi man ana zaune kalau? Auren buta ko me? To walle ki fita idona, tam na gaya miki, ai sai muyi ta zama har ki gaji dani, kuma kin ja ma kanki Habibu zan sake ma Aure" Mami ta fita tana daria sosai.
Busy Rafeeq da Nasiba suke, saboda Exams dinsu da ya k'arato, a lokaci guda Kuma wani Son junar su na shiga cikin jinin jikinsu, Rafeeq yace da ranshi if you kee on seeing her, you'll only Love her More and you wont fulfill your only Dream, which is to Make Uncle Zaid Happy, Dole ya daina haduwa da ita ko don Uncle Zaid, ya kagara ya gama Makaranta, da ya gama zai ware ya bar k'asar, don yasan Uncle Zaid he would stop at nothing har sai ya aura mai Nasiba shi kuwa idan har Uncle Zaid be aureta ba shima ba zai aureta ba, saidai suk su rasa. Alk'awarin da ya daukar ma kanshi kenan, haka a fannin Nasiba, ita dai tasan Tana mugun ganin girman Uncle Zaid, tana jinshi a ranta kamar Babanta, kunyar shi takeji, kwarjininshi ya mata yawa, Hallarci, So da k'aunar da ya musu ita Da Nenenta zai sa ba zata ta6a butulce mai ba, duk da ba wani Son Soyayyar da take mishi amma ganin girmanshi zai sa ta Aureshi ta kula mishi da tillon diyarshi, ko tana so ko bata so, dole Ta Auri Uncle Zaid, Dole ta yakice Rafeeq Lema a ranta, bata taba zaton tana ma kanta irin Son da take ma R-lema ba, tana me tausaya ma kanta, ta kasance me Son maso wani koshin wahala. Dole ta nisantar da kanta daga R-Lema, don yawan ganin da take mishi ne ya ke k'ara mata sonshi.
***********
Rayuwa Kenan, Gaskiar Hausawa da sukace Ramin K'arya K'urarre ne, In zaka gina ramin mugunta ka ginashi dan k'arami, kuma komai nisan Jifa kasa zai dawo, Kuma duk wani abu da ba a ginashi ta hanyar Allah ba, to ba a ganin daidai, K'aryar Saude ta k'are, ba ta da saurin gata, Cikin lokacin kalilan Saude ta koma watta halitta, abubuwa sun mata yawa.
Skin Disease har uku, K'azuwa, sankarau da kezbi, hakan ya sa ta koma kamar bushahshen kwado.
Sai Idonta daya ya tsiyaye, mai lafiyan kuma ya kamu da ciwon polio mai kwantsa da Yana.
Ga kuma ciwon ga6obi a guri uku; bayanta, wuyanta da kwankwasonta.
Sai kuma basir mai tsiro gaba da baya.
Shi ya sa ta tsani kanta, duk ta koma wata hallita daban, jinya take tayi, da wannan wuri ya warke sai wani ciwo ya baiyana har Allah Allah take Alk'ali ya yanke mata hukunci, don a halin yanzu tafi son mutuwarta fiye da komai.
Kotu
Kotu ta cika Makil, Iyalan Habib Lema zaune a kujerar gaba don jin hukuncin da zaa yanke ma Saude, a ka fito da ita, da kyar Mami ta shaida ta, duk ta jeme ta kanjame, wasu kuraraji a jikinta ba kyan gani, ga ido daya a makance. Hat tanta ta tausaya mata, Aneesa ma kukan takeyi, Nene ko sai tabe baki.
Bayan Saude da Mak'ale sun Ansa laifin su, Alk'ali ya yanke ma Mak'ale hukunci Kisa ta hany,ar rataya bayan kuma ya tona asirin Abokanshi da suka kashe Hafiz Lema tare, Saude kuwa hukuncin Daurin rai da rai da kuma horo mai tsanani, wato Life Imprisonment with hard labour, Ihu d kururuwa ta dinga yi, tana fadin "Alk'ali, dama ka sa a kasheni, donAllah kunkasheni da me zanji? Da cututukar da ke damuna ko da Wannan hukuncin? Na tuba, ni ko Kisa ta hanyar rataya ne ku min, ko harbi na zakuyi kuyi, donAllah kar ku barni da Rai, ku kasheni, Please end my Suffering, li want to die" haka Saude ta dinga Ihu tana sambatu, da yawa ta ba tausayi a kotun nan, ko da Nene taji wasu mata Na cewa ta basu tausayi tace "don ba ku san abubuwan da tayi ba, haka ta dan basu labari a takaice, matan nan suka tabr baki tace, ya mata daidai, Ai duniya Makaranta, abunda ta shuka ne take girba. Ba na tunanin zata k'ara Sati biyu a raye don Wannan kurarrajin jikinta ba na warkewa bane" Nene tayi daria tace "yauwa yan gari" Mami kuka Seebi kuka Aneesa Kuka, Rafeeq na ganin haka ya tattara su ya maida gida don ko kadan bata bashi tausayi ba, yana ganin hakan ne daidai ita, baya so ta mutu don yasan mutuwa hutu ne a gareta, gwara ta tsaya da ranta bakin ciki ya cinyeta.
Biki Saura Sati Biyu
*Mafarki*
(Afuwan. Abunda ya samu kenan.
Zan cigaba, ina Makaranta☹☹☹
Masu min mgn ta prvt da ban samu nayi replying dinsu ba ba Afuwan.abubuwan da yawa)
👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
This page is for all Members of JUST NOVELS, Baby nice and above all Sadeeqah Ummu Sudais, ILY'lls Oceans and Galaxies❤
Pg5⃣9⃣
Biki Saura Sati Biyu
*Mafarki*
Daria sosai sukeyi, Rafee'ah tace "Kakar ki na da abun daria, Allah dai ya ja kwana" Seebi tace "Ai zama da Nene sai hak'uri, wanda zai zauna da ita sai ya kai zuciya nesa, don haka zata dinga dasa miki kayan haushi, idan Nene ta k'unsa miki wani abun to sai kinyi kuka" Aiko Rafee'ah ta tuntsire da daria, sai da tayi me isarta kafin ta tsagaita, ta kamo hannun Seebi, ta murza a hankali ta na me Kallonta cike da So da k'auna, chan kuna ta rungume ta sosai ta na shafa mata baya tace "KE ALHERI CE Nasiba Muhammad, kin cika min buri na, Everything is now in place, now i can rest in peace, kin gama min komai, Allah kadai ne zai biyaki da daukacin Zuriar ki, kun kasance Haske a cikin Zuriar Lema, kun kasance abun kwatance a Alumma, kinyi Jihadi, kin sadaukar da Rayuwarki akan mutanen da baki san ko su waye ba, dalilin ki abubuwa da dama Sun faru, Ina Alfahari dake, Ina kuma miki Fatan ALHERI, Allah ya hadaki dauwamamiyar farin ciki, Allah ya tsare ki da Yayana" Seebi tace "Allah sarki Sis Rafee'ah, zaki sani kuka, Amin ya Allah, ke kika bani hope a Lokacin da nake zaton hakan ba me yiwuwa bane, Wannan shine kallan tawa Jarabawar, ba dabara ta ba wayau na" ba zan gaji da gaya miki *KE ALHERI CE* ba" Seebi na daria ta rungumeta tace "Kema Alheri ce Sister Rafee'ah, without you, none of these would have Happened" itama Rungumeta tayi ta na shafa bayanta a hankali, chan tace "Nasiba, This the last time you'll see me, Its been a priviledge to know you though i didnt get to spend more time with you, i wish we met while i was still Alive, but Nevertheless I Thank Allah for making these all possible, Cikin ikon shi, Izzar shi da Zatin shi ya sa kike mafarki dani, Ba abunda zance sai Alhamdulilah" Nasiba kuka takeyi sosai, tace DonAllah ki tafi, you've become part of me, dont leave me please" "Ohh Nasiba, dont cry Habibty, ina ma laifi we met for the 4th time? You'll miss me but abun zai zo miki da Sauk'i, tunda gaki ga Hamman mu, in kina tare dashi, zaki dinga ji kamar kina tare dani ne, you'll see him in me" Seebi ta wurga idonta ta sama tana cewa "That your Arrogant pompous Brother, he makes me sick" Daria Rafee'ah tayi sosai tace "Alright enough, i have to go now, but ina da Sak'o ga kowa" ki gaya ma Daddy nace " Ya gina Massalatai da Islamiyoyi da Rijiyoyi, ya kuma dinga Sadaka da bada Zakkah, ya kuma dinga Ciyar da Marayu " Nasiba tayi Murmushi ta maimaita abunda Rafee'ah tace, kamar a kunne Daddy zan gaya mai" tace yauwa Mami kuma kice nace ta cigaba da Hak'urin da na santa dashi, ta kula da Mijinta, ta zama Mace ta gari, kar rudun duniya ya sa ta shagala, kar Kawayen Banza su sata bin bokaye don Mallakar miji ko wani abun daban, ta Tsare Ibadunta, ta rik'e Adduoin InshaAllah zata ci ribar Rayuwa" kamar dazun Nasiba ta sake Maimaita abun da Rafee'ah tace, Fee'ah ta cigaba da cewa "Uncle Zaid the Noble Gentleman,wanda zai kuntata ma kanshi don ya faranta ma wani, kice mishi Allah kadai ya san yanda zai biya shi, Allah ya Saka mishi da Alherin sa, Ya raya mishi Takwara ta, ya bashi mata ta gari wacce zata kula dashi kamar yanda ya dade yana kula da mutanen da ke kewaye dashi, Allah ya biyashi da gidan Aljannah" haka Nasiba ta sake maimaita abunda Fee'ah tace, Rafee'ah tayi daria tace My Next message is for Nene, kice mata nace "Ba kamarta, Allah ya hada mu a gidan Aljannah Firdausi" Seebi tayi daria ta maimaita, Lastly Hamma na, kice mai nace "Stop getting angry Easily, Dont get Mad at anything, dont be Sad anymore, Live your Life, and Be happy, I love you so much Hammana" haka Nasiba ta maimaita sak'on Rafeeq, "And you, i dont know if i'm supposed to ask you this, because you've done alot for me and My Family, but i really want you to do this, I want you to take very good care of Hamma Rafeeq, i want you to love him for the rest of your life, Please" Sister Rafee'ah me kike cewa ne haka? Wannan hakkin matar da zai aura ne, how am i supposed to take care of him for the rest of my life? I'm getting married In 2weeks time, i cannot promise you this, i'm sorry i cannot do this, i shall take care of my Husband" Murmushi me kayartar da Fuska Rafee'ah tayi, ta lumshe ido a Hankali tace "Goodbye Nasiba, Be Happy" "Wait Sister Rafee'ah, kar ki tafi donAllah"
************
Cikin Barcinta taji ana shafar k'afarta, bata son tashi daga mafarkin don tana sa ran sake ganin Rafee'ah, amma sai dai kash tasan Rafee'ah