Showing 21001 words to 24000 words out of 149166 words

Chapter 8 - Ke alkhairi ce COMPLETE HAUSA NOVEL

BIEBIE   

22 Oct 2024

25711

makaranta, kullum suna Cafteria shi da Abokin shi Mahmud Maalesh, Maalesh abokin Rafeeq ne tun Secondary School, Abotan Maalesh da Rafeeq ne ya sa Iyayensu ke zumunci, idan ka ga Mami da Mummyn Rafeeq zaka zata yanuwan juna ne, Maalesh is his partner in crime, idan sunyi laifi Uncle Zaid ke hukunta su, don ba sa jin magana, duk wani party sai sunje sun sha rawa, ba sa shaye-shaye, ba sa bin mata, amma yanmatan su sunfi 50, don shi Rafeeq kafin yace yana so to an riga cewa ana sonshi, Irin Matashin nan ne wanda be da wata matsala a rayuwa, kowa na shi ne, kar kuyi zaton Rafeeq be mayar da hankali a karatunshi, to ba haka bane, Duk Department din su na BioChemistry, ba kamar Rafeeq, Lecturers kance, "idan akwai abun da yafi 5point, to tabbas Rafeeq zai buge shi" irin su ne ake cewa "Always ahead of the Lecturers" saboda kokari, Allah ya ba Rafeeq k'wak'walwa, both ilimin Addini da na boko, a shekaran shi na 16 ya sauke AlQurani mai Girma ya kuma shiga Jami'a, Yanzu haka yana da shekaru 20 cifcif kuma bana zai gama Jami'a.

Rafee'ah kuma tana karantar Sociology tana aji 2. Ba su fiye shiri da Rafeeq ba don ita shiru shiru ce, shi ko yayi ta tsokanan ta, Rafee'ah kyakyawa ce, bata fiye son magana ba, amma indai Rafeeq na gida dole sai ya sata magana da yawan surutun shi da tsokanam ta da yake yi, tun bata biye mishi har ta fara biye mishi, da ya mata take ramawa, idan kuma abun yafi karfinta, sai taje tana ma Mami kuka, mami kuma ta ma Rafeeq fada, hakan ba zaisa gobe ya kuma tsokanan ta ba.

Gidan Habib Lema, gida ne da aka ginata cikin So, Aminci da yardan juna, suna matuqar son junan su, ba su da Matsalan komai, Mami(Hajia Aisha) ta tsaya tsayin daka wurin tarbiyantar da yaran ta bisa tafarkin Addinin musulun ci, tun suna yara Uncle Zaid ne Discipline Master, idan sunyi laifi shi ke hukunta su, Shiyasa Suka tashi da son junan su (Wannan Kenan).

Daga sama Mami taji ana "Assalam Alaikum" ta bude idanunta a hankali don a gajiye take tun bayan biki, ta dan bude murya ta amsa sallaman tare da cewa "ku hawo saman please" Suka nufa sama, su biyu ne, kana ganin su kasan uwa ce da diyarta, diyar ba za wuce shekara 17 ba, a bakin kofa suka iske Hajia Aisha, tana ganin ta fadada murmushin ta, "Saude kece anan? Sai da muka gama bikin zakizo?" Saude tace "Ayyah madam, wallahi naje gida ne, shiyasa banzo biki ba" "bakomai ai, wannan diyar ki ce? Kafin kace wani abu yarinyar har ta zube kasa tana kwasar gaisuwa, Mami ta dago ta tana kallon ta, wani irin kama taga yarinyar nayi da Rafee'ah, tace what's ur name? Yarinya tayi murmushi tace "Sunana Aneesa" Wow nice name, sannun ku da zuwa, ku shigo" suka shiga ciki, kafin kace meye wannan Mami ta cika musu gaba da kayen ciye-ciye, suna ci suna fira jefi-jefi, Saude tace "bakowa a gidan sai ke?" tace "eh wallahi, ni kadai ce, duk suna kaduna, tunda aka kai Amarya basu dawo ba, Saude tace "Ayyah Allah basu zaman lafia" tace "Amin"

Saude Secretary din Hajia Aisha Lema ne a Office, watan ta 6 kenan da fara aiki a office din Matar Habib Lema, tana da kwazo wurin aiki, shiyasa Hajia Aisha ke ji da ita. Six months back ne ta kawo CV dinta da qualification dinta na NCE, office din Madam Lema.
Wurin interview ne suka bata tabbacin ba sa daukar masu NCE sai masu Degree, ta dinga kuka wai a taimake ta, mijin ta ya rasu, ya barta da diya daya, ba halin ciyar da ita suna cikin hali na kuncin rayuwa, yanda take kuka taba interviewer din tausayi, yaje ya sanar da madam din su, madam ta nemi ganawa da Saude, ta bata bayani, itama taji tausayin ta, tace "Madam ki taimake ni, kamar yanda Allah ya taimake ki, you are a mother, kinsan irin son da uwa ke ma diyarta, Miji na ya rasu ya barni da diya daya, dangin shi sun kwashe Gadon, ta tsaya a Secondary, ki taimake ni ki bani aiki da zan kula da diyata" Hajia Aisha ta ja numfashi, sosai Saude ta bata tausayi, tace "can you be my Secretary?" ai ko nan Saude ta zube ta na godia, tace tana so ta gode Sosai harda kukan murnan ta" washegari ta fara aiki as Madam's Secretary, Saude akwai kokarin aiki, da zasu tafi Hajia Aisha ta shiga Dakin Rafee'ah ta tsinto ma Aneesa kwancen kayan Rafee'ah, ta cika su da abun arziki.

Bayan Wata Daya

Gaba ki daya suke zaune a Babban parlorn Habib Lema, Uncle Zaid na fira da Uwar dakin shi Mami, Rafee'ah na kusa da Baban ta tana karanta mishi newspaper, daga gefe kuwa Rafeeq ne ke ba ma Aunty Seema(Matar Zaid Safiyya, sunzo ne) labarin yanmatan shi na makaranta da na Unguwa, tana ta daria, da kagan su kasan Happy Family ne wanda basu da damuwan komai da kowa. Wayan Alhaji Habib Lema yayi ringing, Rafee'ah ta tashi ta dauko mai kan sidestool, ta amsa ta sa ma babanta a kunne, "*Hello* *Yaya*? Dam gaban Alhaji Habib ya buga, ya mik'e tsaye cikin kidima, a hankali yace "Hafiz, kaine? Zaid da Mami suka mik'e tsaye suka nufo Alhaji da jikin shi ke rawa, ya kasa cewa komai, Zaid ya amsa wayan ya sa handsfree yace "Hello?" daga dayan bangaren aka ce "Hello Brother" Zaid yace "Hafeeez, is this you brother, where are you?" karbe wayan akayi daga hannun Hafiz akace "Hello This is Secret Service Agency Lagos, Hafiz Lema's been Jailed 10years ago, he's completed his Sentence, and is fined 500usd, come to the Agency for more details". Dif ya kashe wayan.

_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

Pg2⃣0⃣

"Inalillahi wa ina ilaihir rajiun" duk suke fada, Alhaji Habib ya zauna ragajab kan kujera ya dafe kanshi da hannuwan shi, tunani yake me Hafiz yayi haka da aka kulle shi for 10years ba? Zaid yace yaya "meye abunyi?" Habib ya hadiye miyau yace "Zaid, a siyo ticket mu wuce Lagos din kawai, Zaid,yace "Yaya ka bari ni zanje Lagos din gobe da safe" Habib yace shi sam be San wannan ba, tare zasu tafi, nan da nan Zaid yayi waya Chanchangi Airlines ya siya tickets biyu.

Shiru sukayi kamar anyi mutuwa, Rafee'ah ta yanke shirun tace "Abba wanene Hafiz?" Abba ya kasa magana sai Uncle Zaid yace "Yaya na ne, you were too little when he left, i dont think ko Feeq zai ganeshi" Rafeeq yace "na tunashi but i can't remember anything about him" Uncle Zaid yace yeah u were all young then" duk sukayi shiru, kowa da abun da yake sakawa a zuciyar sa, tunanin su daya, me hafix yayi a ka kulle shi har tsawon shekara 10?.

Lagos
Karfe 9 na safe Uncle Zaid da Alhaji Habib na Secret Service Agency (SSA), bayan long process aka sa da su da wani Oga, tambayoyi ya musu na Alakar su da Hafiz, Habib ya bashi amsa da "mu yanuwan sa ne, ni yayan shi, wannan kuma kanin shi" Ogan ya dauki wasu files guda biyu ya mika ma Alhaji Habib, ya amsa hannu biyu ya bude, hotuna ne na Hafiz da wasu 6, Zaid ya gane daya daga cikin su, abokin Hafiz nr wato Anas, a cikin hoton aka ga Boma-bomai,Bindigogi da wuk'ak'e, cikin su ya juya, Habib ya bude dayan file din, paper ce doguwa, ya shiga karantawa, Hafiz was an accomplice to Armed Robbers. Hankalin Habib ya tashi, ya fara hawaye, Zaid ya amsa ya karanta shima, kanshi ya girgiza cike da takaici. Oga yace "toh sati 2 da suka wuce ne ya cika Shekarun da aka diba mishi, an ki sakin shi ne sai ya bada 500usd, mun ta tamabyan shi wa zaizo bailing dinshi, yak'i magana, da ya ga bamu da niyyar sakin shi ne shine ya bada numbern ku, Zaid yace "yanzu 500usd za a baku sai ku sake shi?" Oga yace "eh" Zaid ya danyi guntun tsaki ya sa hannu cikin aljihun shi, ya ciro rafar dubu 3 ya dora ma Oga kan table, mutumin yayi murmushi yace "Sir we dont do it this way, u go to the bank and draft it to our Account" Zaid ya dan daga murya yace "you should have said that at first, u think we have time for this? Habib ya kalli Zaid yace "Calm down Engr" Mutumin yace "unless you'll pay here the change will be mine, you know 500usd is approximately to N250,000, and this is 300k" Zaid ya mai tsawa yace "shut the fuckup, take d goddam money and get us our Brother" Mutumin yayi daria ya mike tare da kallon Alhaji Habib, yace "i see your bro has guts, i'll get ur brother now" ya fita.

Alhaji Habib yace "Zaid, kayi hakuri, muke nema gurin su, dole mu kwantar da kan mu" Zaid cikin fushi yace "yaya rabu dasu, iskanci ne, ji fa yanda yake magana, matsiyaci, kudi ne matsalan shi" Habib yace "ayi dai hakuri" duk sukayi shiru.

Turo kofa akayi, Habib da Zaid suka mik'e tsaye, idon su kan kofar shigowa, Ogan ne ya fara shigowa Hafiz a bayan shi, Hafiz yayi bak'ih duk kyaun nan ya disashe, ga wata uwar k'asumba ya ajiye, duk yayi ba kyan gani, Rige rigen zuwa gunshi Zaid da yayan shi sukayi, Hafiz ya fashe da kuka, suko ba su damu da yananyin da yake ba suka rungume shi suna hawayen suma. Da kyar hafiz yace "ku gafarce ni yanuwa na, na san ban kyauta muku ba" Alhaji Habib yace "shhh, Hafiz not now, lets get outta here"

Suka nufa hanyar fita, Zaid ya watsa ma Oga harara, shi ko dariya ya bashi don yaga Zaid ya dauki abun da Zafi, yace ga Kayan shi da aka amsa kafin a kulle shi, Zaid yace "ka jika ka sha an bar maka" sosai Officern yayi daria, yace "till we meet again ko" Zaid yace "ganinka ba Alheri ba, ba Amin ba" ya fita shima.

Drivern Office din Lema textile Company Zaid ya kira, within some minutes ya hallara Agency din, ba jira suka shiga, Golden Hotels suka nufa, Hafiz ya shiga dakin shi, yafi 1hour yana wanka, yana fitowa ya ga Wasu riga da Wando da Zaid ya siyi mishi, ya dauka ya saka yaci abinci yayi Sallah. Bayan sun huta Driver ya sake zuwa ya dauke su, yayi Airport dasu, don yau suke son wuce wa. Bayan mintuna kalilan jirgin su ya tashi, Cikin Awa daya suka iso Kano ta dabo. Kafin suje masauki sai da suka biya Barbers Corner don a ma Hafiz Aski, Tsaf hafiz ya fito da kyau, don yini dayan da yayi ya fara kyau. Washegari driver ya dauke su sai Katsina ta dikko dakin kara.

Tana tsaye tsakar Gida tana jiran isowar su, don tun da suka shigo KT Alhaji ya kirata yace sun iso, ga su nan karasowa. Rafeeq da Rafee'ah na school, Mota na shigowa Haraban Gidan gaban Hafiz ya bada Hinqim, komai ya dawo mai sabo, a ranshi yace "it all started here" Sannu da zuwa Aisha take ta faman yi ma Hafiz, harda hawayenta, Hafiz duk ya koma wani sukuku, be sakin jikin shi, ta gabatar musu da abinci, kadan Hafiz yaci, yanda kuka san bak'o sai rab'e rab'e yake tayi. Alhaji Habib ya lura dashi yace "ka sake jikinka Hafiz dis is your home" Hafiz yayi murmushin takaici, yace "Yaya, nasan duk kuna da miliyoyin tambayoyin da kuke so ku min, kuna so kuji yanda na tsinci kaina a kurkuku" Habib ya katseshi yace " Aa Hafiz, abunda ya wuce ya riga ya wuce, kar a maida hannun Agogo baya, muyi addua Allah ya tsayar nan kawai" Hafix ya girgiza kai yace "Aa yaya, dole ku san me ya faru, dole kusan irin rayuwan da nayi bayan bari na Gida" Zaid yace "Gaskia ne, muna sauraronka" Hafiz ya fara labarinshi kamar haka:

Shekaru Goma da suka gaba ta(Last 10years)

Muna barin Katsina, Straight dauki hanyar Porthacourt, ni da Abokaina 2, Anas da Eskaley, mun kwana mun yini a hanya, har muka isa wani gida, Gidan Thug Gang (Sunfi kama da kauraye )din su Anas ne Amstrong da Willy, Kwanan mu 2 a PH Anas suka nuna min wuraren bude idanuwa, kamar Night Club, Gambling Center, Da Gidajen giya, duk na kware a harkokin nan.

Ba mu rufe Sati 2 ba naji Armstrong na gaya ma Anas su shirya akwai Operation yau da daddare gidan Commisioner, yace "okay we'll prepare" nace da Anas wani irin operation ne wannan? Anas yayi daria yace "my guy, ba zaka gane bane, share kawai" Nace "haba Anas, kar ka mun haka, ka fada min mana" yace "kagane, Amstrong ce min kawai yayi zamuje iperation, amma be gaya min takamaimin me zamuyi ba" Nace "then i will go with u" Anas yayi dariya yace "no u cant, yi shiru kar ma Armstrong ya jika" ashe Armstrng na jin mu, yace "he's right you cannot come with us boy" boy ne sunan da Armstrong ke cemin kenan tun zuwan su PH, a ganinshi ni karamin dan iska ne, cikin fusata nace "i am not a boy" Armstrong yayi murmushi yace "show me, today get ready and be prepared" Anas yace "Oga i dont think this is a good idea" Armstrong yace "its time we train him".

3:00am
Gidan Commisioner of Youths suka kai ma farmaki, duk suka hade kan mutanen gidan cikin babban parlor harda shi Commisioner din. Hafiz aka bari a Cikin mota, da bindigar Katako, bayan Armstrong ya buge mai warning, kar ya bar bakin mota, no matter what, don zasu iya fitowa at anytime, Anas, Eskaley, da armstrong suka shiga ciki, duk a zaton shi sauran ma bindigar katakon ne, duk a zaton shi kudi kawai zasu amsa suyi gaba, sai labari ya sha bambam da yaji karar bindiga, sosai ya tsorata, Be ankara ba yaji Siren din motocin police, Hafiz ya kidime ya fito daga motan da gudu, charap police suka kamashi da yake Ajebo ne be iya gudu ba.

Su Eskaley kuwa sai fafatawa suke da jamian tsaro, suna harbin junan su, nan take a ka harbe su 3, ko shurawa basuyi ba suka mutu, Iyalan Commisioner kuwa ba wanda ya mutu, sai dan shi da Anas ya harba a kafada, an garzaya dashi Ambulance.

Abun da ya faru shine, Ashe Akwai diyar Commisioner da take wayan dare(NightCall) ta bayan dakin ta taji ana cewa "Idan ya kawo gaddama kawai mu harbesu mu shiga mu nemi golds a dakun nan su, yanzu kawai mu nemi hanyar shiga cikin gidan" da gudu ta diro a kan gado ta fita da gudu, straight dakin babanta tayi ta gaya mai Abun da taji, da sauri ya danna waya ya kira Jami'an tsaro ya sanar da su, suka bashi tabbacin gasu nan zuwa, da sauri ya nufa dakin matar shi da babban danshi don sanar da su, kafin kace meye wannan yaji an dora mai bindiga a kai, Anas ne yace "idan ka motsa sai na tarwatsa kanka" Commisioner ya sandare, Eskaley da Amstrong suka shiga sauran dakuna suka fito da duka mutanen gidan, suna tambayan kud'adde ne Police sukayi surrounding dinsu duka har suka kashe su Anas.

Hafiz ya cigaba da cewa" ko bincike ba a tsayayi ba aka maka ni kotu, kasancewar ni kadai suka kama jikina yayi sanyi, na fada musu gaskia, na amsa laifi na, Kotu me adalci ta ya yanke min hukuncin 10years a Jail+ hardships da 500usd Fine, to kunji abunda ya faru dani bayan bari na Gida. Allah sarki danuwa mai dadi, daga Alhaji Habib da Zaid kuka suke barin ma Aisha da tun farkon Labarin Hafiz take kuka. Sai da sukayi me isar su duka kafin Hafiz ya duk'a har k'asa ya nemi gafarar su duka, Habib yace bakomai Hafiz Allah shi kyauta gaba, Allah ya sa kuma ka koyi darasi, duk wanda ya bar gida gida ya barshi. Hafiz yace "InshaAllah Yaya, ba za ku sake kamani da wani laifin ba", yace "toh Allah yasa" ya juya ya kalli Aunty Aisha yace "Aunty kiyi hakuri da duk abunda na miki, da sauri ta katse shi tace baka min komai ba, Allah ya yafe mana" Hafiz ya kalli Zaid zai yi magana, Zaid ya tareshi da murmushi yace "Welcome home Brother".
(Muma munce Welcome Hafiz Lema, Lubie maitafsir tace "Dont cause any trouble" Aisha Yau kuma tace "Allah ya sa ba tuban muzuru kayi ba😐", nidai Biebee nace ku biyoni kuji rayuwan Gidan Lema bayan dawowar Hafiz Lema)

_Bibilicious Biebee

👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

Pg2⃣1⃣

Rafee'ah ta shigo parlorn da gudu ta na kukan Shagwaba ta fada kan baban ta, Abba yace "Rafee'ah baby me ya sameki?" ta turo baki tace "Abba ba Hamma bane kece min Jaki head" Zaid ya fashe da daria, yace "kema ki dinga k'ok'ari kamar Feeq dina, kin tsaya kan makeup" Abba ya harareshi yace Zaid mind your own bussiness" Zaid ya sa wani darian, Rafee'ah ta kara tunzura, ta sake saka wani kukan, Mami tace "Yi shiru babyna, ki barni da Rafeeq da Uncle Zaid dinku, zanyi maganin su, ta mak'e kafada, nidai ba Uncle Zaid dina bane, na Hamma ne" "Shikenan baki gaida Uncle Hafiz ba, ko ba ki ganshi bane"

Zumbur Rafee'ah ta tashi, ta nufa Uncle Hafiz da ya kura mata ido, yana murumushi, fadawa kanshi tayi, tace "Welcome Home Uncle Hafiz, we missed you" ya shafa kanta yace my preety princess, nayi missing dinku duka, na dawo, ba zan sake nesa da ku ba" ta rungume shi, yace "ina Hamman naki?" ta turo baki, sai yaje dropping Ya Mahmud a gida, ke waya dawo dake? Tace shi ne fa, chan baki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login