Showing 123001 words to 126000 words out of 149166 words
ta tafi kenan don baccin ya fita daga idonta, a hankali ta bude idonta ta sauke su kan mutanen da ke tsaye kanta, cikin hanzari ta mik'e tsaye tana mitsitsika ido,ta bisu da ido, ta kai dubanta ga Nenenta tace "Lafiya Nene?" Nene tace "Sambatu kikeyi cikin bacci Seebi, kamar kina magana da wata cikin mafarkin ki, ina Sallahr Dare naji kawai kin fara maganganu, na zo daka miki duka amma ko shurawa bakiyi ba, haka na tsaya kanki jin kina ta turanci na dinga miki addua, dana ga abun ba me karewa bane ya sa na je na kwankwasa ma su Aishatu nace baki da lafia, tun kafin su karaso ta kira Dunkum da Zaidu bawan Allah tace su zo a kaiki Asibiti, shine ma fa mukazo dob cicinbar ki, sai Mukaji kina wani magana Sai Zaidu yace a tsaya yaji kamar ana son Isar da Sak'o a garesu, tsaf muke jin Amsar da kike badawa amma ba ma jin abunda ake ce miki" Seebi ta tashi tsaye tana salati, Mami ta matse hawayen ta tace "Nasiba da Rafee'ah kikayi mafarki ko?" kanta a kasa ta daga kai alamun Eh" Mami tace "For howlong kike mafarki da ita, saboda yanda naji kike magana kamar you two are so close to eachother" "Nayi mafarki da ita So 4 ko 5" Allahu Akbar, inji su, Rafeeq ya matso kusa da ita, ya tsura mata ido, yace "Naseebah tell us everything you know, kar ki boye mana komai" Nasiba ta kwashe komai tun farkon Mafarkinta da yanda ta nemi Alfarma taje ta biya mata bashi a makaranta, da yanda tasa bincikar Rayuwar R-lema, da yanda ta sa ta shiga rayuwar shi, da yanda ta taimaka mata gun tona Asirin Saude har zuwa rana ta yau da duk sukaji komai" Allahu Akbar kakeji da kirari ga Ubangiji Allah, abun Mamaki kamar Almara, ba su taba jin irin haka ba ko a Mafarki. Rafeeq ya rasa tunanin me zaiyi ya rasa sukuni, Wacce iri ce Naseebah? She did alot for him, how he wish he could show her love and Appreciation, he loves her so much, and after this wani girmanta ya karu a idonshi, wani sonta ya sake ratsa shi, wani kaunarta ya shige shi, hawaye ya zo mai da sauri ya juya ya bar dakin, Zaid ya bishi da ido ya na tunanin wannan abun Mamakin" Daddy yace "Nasiba My Child, Allah ya miki Albarka, naji Sakkon diyata Rafee'ah kuma InshaAllah gobe zan fara aiwatar da yanda tace Allah Kuma ya gaffarta mata ya sa Aljanna ce makomarta" duk suka amsa da Amin, Daddy yace "Oya muje mu kwanta is getting late" Mami tace "No, i'll sleep close to my daughter today" Daddy yace "Babanta kuma fa?" Mami tayi daria tace "yaje hutu" duk suka sa daria, Daddy ya fita, Mami ta kwanta gefen Seebi tana shafa kanta, Nene ta shimfida Bargo a k'asa tace "ki maidata ciki karshen shigewa jikinta".
Akwati Set1 (Guda 6) Mami ta hada, komai ya ji, Mami tace " idan zaka wuce Kaduna sai ka tafin ma su Ummin Anan dashi, duk da tace ba sai an kai ta gani ba, amma yakamata a bata hakkinta na uwa" Nene tace "Ni da kun bi ta tawa tunda Ran Jumaa zasu zo ba sai an sha wahalar kai kaya Kaduna ba" Mami tace dai a kai musu su gani.
Su Miemee da Usheey sunzo ganin lefe, suna ta murna don Seebi tayi Goshi, kaya sai sambarka, nan suka ritse Uncle Zaid a Parlor suna zolayar shi, dariya kawai yakeyi, Miemee tace "Uncle Zee ya maganar Dinner? Kasan dai biggest hall of them all zaa kama mana, Soli Center nake ma bayani, yayi daria yace "Kar ku damu, ga Son nan kuyi magana dashi, zai yi komai" Meemee ta waiga taga Rafeeq na shigowa Fuskar nan murtuk'e, a ranta tace "kai dai ka sani".
Bayan Kwana Biyu
KADUNA
"Yaya Destiny brought Nasiba And Rafeeq Together, They belong to eachother, Ba ka tunanin dalilin da ya sa Allah ya kawo Nasiba garemu don ta auri Rafeeq ne, Nasiba da Rafeeq suit eachother, ko ban fada ba ka san Nasiba na Son Rafeeq, Mami kinsan dacin rabuwa da masoyi, please lets not deprive them of their chance to be Happy, lets help them be together, if you are worried and concerned about me, kar ka damu, i'll be fine eventually, mata da yawa a gari, i'll get one" Alhaji Habib yace "Zaid nagaya ma Times without Number cewa zan aura ma kowa Rafeeq but not Nasiba, Nasiba taka ce, Rafeeq is not worth her, he'll only hurt her da miskilancin shi, and Shes like a daughter to me, ba zan sa rayuwarta cikin kunci ba, shiyasa zan aura mata kai, kaine zaka kula min da ita" ran Zaid ya fara 6aci yace "Yaya you always tell me that you'll do anything for me, and Mami kullum cewa kikeyi kina so ki biyani for all i did to you, you all want to make it up for me, So this is what you'll do to make it up for me, Get Rafeeq married to Seebi, haka kurum zakuyi ku biyani duk abubuwan da na muku" Mami da Daddy suka kalli juna, Daddy yace "Zaid why are you so Stubborn, ban san ka da haka ba, i'm sorry i cannot do this" Mami ma tace "Sorry, Zaid ask for anything but not This" Rafeeq da ya shigo dakin Daddy ya gama jin duk abunda suka tautauna kasancewar wayar a Handsfree yake yace "ko sun amince ni ba zan amince ba, ba zan taba hada kaina da kai ba" cikin bacin rai Zaid yace "waya sa bakin ka Rafeeq? Who is asking for your opinion, shut the hell up boy, God!! you all make me sick" Dif Zaid ya kashe wayar ya cillar da ita kan kujera yana safa da marwa cikin Parlo, why is it that noone seems to understand? Shi gaskia ba zai shiga tsakanin masoyan nam ba, ya lura da irin son da Nasiba ke ma Rafeeq, ya lura bata sonsa, kuma ko kadan beji haushinta ba, ko kadan be ji kishin Rafeeq ba, tsaki yayi ta yanda zai bullo wa Yayanshi da Matarshi, ko ta halin k'ak'a bazai auri farincikin Rafeeq ba, a fusace ya bude fridge din Parlorn shi ya ciro kwalbar ruwa ya bare marfin ya cillar da ita ya kafa kai ya fara kwankwadar ruwan.
"Assalam Alaikum" wata zazzakar murya tayi sallama a k'ofar parlon tare da shigowa lokaci guda, fesar da ruwan bakinshi yayi tare da sakin robar a kasa sakamakon kwarewar da yayi, wata hallita ce tsaye da Bak'ar Jallabiya, kamar Maman Ayman, sai dai wannan tafi Maman Ayman haske, tafita kyau, tafita dan kauri da tsawo kadan, kamar Balarabiya, dam Gaban shi ya yanke ya fadi sakamakon hada idon da sukayi, lokaci guda ya ji shi a wani yanayi me wuyar fasaltuwa, rabon da yaji irin wannan yanayin an jima, yayi ta maza ya saita tunanin shi ya taka daf da ita, kamshinta ya bugi hancinsa, ya lumshe ido wani natsuwa na shigar shi, Ya tsura mata ido yana son gane wani abu game da ita, , itama shi din take kallo da sauri ta kawar da tunanin da takeyi game dashi, don duk yanda take zaton shi ya wuce nan, ya zarta tunaninta, da ta ga Kallon ba me k'arewa bane ta cira baki tace "Ina wuni, donAllah ina neman Zaid Lema" cikin sanyin jiki ya lumshe ido yace "Ni ne, how may i help you?" a tsaye tace "Sunana Zainab Sani Sister din-- bata karasa ba yace "Sistern my late Wife, Safiyya" tace "Exactly" yace "Ban sanki ba, but i've heard about you from her, and da kika shigo ina ta kallon ki, da kikayi magana kuma na ga tsantsar kamar da kikeyi da Ita" cike da k'asaita tayi Murmushi, da ya lura 'yar aji ce, sai shima ya ari fuskar dansa Rafeeq (lol) yace "So why are you here? ta kalleshi da mamaki tace " I'm not here for you, i'm here for my daughter, i came to take her with me, its time for her to Live with her Mother's Family". Da mamaki Zaid yace "What??".
_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
Pg5⃣9⃣
(This Line is for all the Amazing Sisters that Sacrificed their Happiness for their Nieces and Nephews, i'm talking about the Sisters that gt Married to their Late Sister's Husband. Only Allah Can Reward them💙)
"Eh kaji ni sarai, nazo in tafi da Rafee'ah Aymana ne, jiya na dawo k'asar, an gaya min cewa Aure zakayi, Ba zan yi gangancin barin ta wurin ka ba, ba zan bari ta fukanci wahalar MATAR UBA ba, ba zan bari tayi kukan rashin uwa ba, shiyasa zan dauketa. Kallonta Sosai Zaid keyi, Sosai ta burgeshi, yanayin maganar ta, bata shakka ko tsoro, yanda ta nuna son da take ma Ayman ya burgeshi, da ta ga kallon da yake mata sai tace "Mallam ka dauko min diyata, sauri nakeyi" Zaid ya murmusa, yace "Ga dukkan alamu kina Son wannan diyar taki" tace "So fiye da kaina ma" yace "Good, amma kiyi hakuri, ba zan iya ryauwa ba Ayman ba, na rasa Mamarta ba zan iya juren Rashin ta ba itama, kiyi hakuri ba zan iya baki ita ba" Zainab ta bata rai tace "Bangane ba" ya yi Murmushi yace "Baki gane hausar ba? Oh ashe balarabiya ce, gashi ni ban iya turanci ba balle larabci, hakuri kawai zakiyi, ba zan iya naki Ayman ba, Kuma idan nayi aure Amarya ta zata rik'e min ita, yanzu haka ma ba ta tare dani a garin Kaduna, tana chan garin Katsina tare da Amaryar tawa" Idon Zee suka ciko da hawaye, ta sausata murya tace "Please ka taimaka ka bani ita, ina so in kasance tare da ita, ina sonta Sosai" Zaid ya girgiza kai tare da Murmushi yace "Nope, ai ina jin ganinta ma zai miki wahala balle ta zauna tare da ke, kinga ba ma lallai bane Mijinta ya Amince da ita ba" da sauri tace " Wallahi banda aure, kuma kafin inyi sai na tabbatar Mijin da zan aura ya amince zai riketa ya dauketa a matsayin Uba" yace "Tabdijam, da Mahaifinta a raye, har sai an nemi izini wani? Wannan ma na daya daga cikin dalilan da zai hana in baki ita, ba zan baki ita ba gaskia" ran Zainab ya gama 6aci tasan in ta k'ara bude Baki zata iya fashewa da Kuka, ta sa6i jakkarta ta juya ta bar Parlorn ranta a jagule, Zaid kuwa Murmushi yayi Sosai.
**********
Tana isa Gida ta fada kan Mamanta ta fashe da kuka, Maman ta hau lallashi tana cewa "Zainab me yasa ki kuka? Me ya faru? Wani abun ya samu Aymana?" cikin kuka tace "Umma, cewa yayi ba zai bani ita ba, wai Amaryar shi zai ba ita, yanzu haka Aymana na Katsina ita zata kular mishi da ita" Umma tayi Murmushi tace "Zainab dama sai da na gaya miki Zaid ba zai yarda ya baki Aymana ba" "wai ma Umma tun da Safiyya ta rasu mesa baki gaya min ta bar diya ba? Eh Umma? Meyasa kuka boye min ta bar diya, haka Aurenta, sai dai naga hotuna a IG, gashi har diyarta ta fi shekara, haba Umma me ya sa kuke min haka ne?" Umma tace "Zainab hakuri zakiyi, umurnin babanku ne, ya san halinki, kina iya cewa zaki dawo, kuma Lokacin kina tsaka Da rubuta Jarabawa, kuma in kika dawo kika ga Aymana kina iya cewa ba zaki koma ba, ko kuma ki nemi a baki ita ki tafi da ita, shiyasa yace in har aka bari kika dawo, sabon tashin hankali kowa zai shiga, kuma Zainab ki kwantar da Hankalinki, Zaid mutumin kirki ne, yana da Amana, ya kan kawo mana Aymana shi da Marikiyar Ayman, mutanen kirki ne wallahi, kar kiji fargaban komai, Zaid zai kular miki da diyarki" "Umma ba shi nake ji na, ina tsoron Matar Uba, ina tsoron Kar ta sha wahalarta, shiyasa nake so ya bamu ita, ai mu ke da hakkin riketa" Aa fa Zainab, shi ke da hakki, sai yanda yayi da ita" kafin Zainab tace komai sai jin Sallama sukayi, k'anin Zainab ya shigo yace "Umma ga Yaya Zaid nan a waje" Umma tace "Bismillan shi, ya shigo" Zainab ta 6ata rai tace idan be bani ita ta dadi ba, zan maka shi Kotun Musulunci" Daidai da Shigowar Zaid fuskar nan kamar kullum dauke da Murmushi, A ladabce ya durkusa har k'asa ya gaida Umma, Umma ta amsa mai cikin sakin fuska da girmamawa. Zainab ta hadiye fuska ta na karkada k'afa. Murmushi Zaid ya sake yi yace "Umma ashe 'yan makaranta sun dawo?" Umma ta kallo Zainab da ta hade girar sama da k'asa tace "Aiko dai su Dr Zainab an dawo" Zaid yace "Ahhh ashe Dr ce" Umma tace aiko Likita ce, jiya ta dawo ta kammalla karatun Likitamcin ta gaba ki daya, saura Housemanship da zatayi a Barau Dikko" Zaid yace "Allah sa Alkhairi" "Amin Amin" Abba ba ya nan ko? Umma tace "Ya je Government House" su ka danyi shiru na wani dan Lokaci kafin Zaid yace "Umma sai gashi Likita ta zo min da wani zance" Umma tace "ina ruwan Zainab, jiya ta dawo, daga ce mata Mijim Marigayiya Safiyya ma zai yi aure nan da Sati biyu, Kai Mu'allim sai kace nan za a kawo mana Aymana? Sai ta tambaya wacece Aymana, kasan ba a gaya mata Safiyya ta bar diya ba, ai fa tun da ta ji ance Diyar Safiyya ce take ta ruwan Wulakanci tun jiya, wai zata je ta daukota, ya zaayi mu bar maka yarinya, wacewace ita sai ta amso ta" Zaid ya fadada Murmushin sa, yace "Umma zan bata Aymana idan tana so" Umma da Zainab suka zuba mai ido, Zaid ya maida dubanshi ga Zainab da ta zuba mai idanuwanta, yace "kwarai kuwa, zan baki Ayman ki rayu da ita, har girmanta, har tsufanki, Aure kawai zai rabaku da ita" ba ta san sanda Murmushi ya kubuce mata, tace "Nagode Sosai, Allah ya biya ka, Allah ya ji kan Sofie, nagode da ka Amince zaka bani ita, Allah ya baku Zaman Lafiya da Amaryar ka" yayi Murmushi tare da cewa "Amin, amma fa da Sharadi daya, i have a condition" da Murmushi a fuskarta tace "Koma meye zanyi, tell me" a takaice yace "Marry me" idanuwanta ta gwalalo, tace "What?" ba tare da wani fargaba ba yace "Ki Aureni, and Ayman is yours" ta mik'e tsaye tace "Are You in your right sense? In bacci kakeyi ka tashi, bazan taba aurenka ba, ta ya ma zaayi in auri Mijin Yayata? Tabdijam, don nace ka ban diyarka zakace in aureka? You are using the love i have for your Daughter to use me, To ba zan aureka ba, ba zan auri Mijin Yayata ba" Murmushin dai yayi yace "Ina Yayar taki? Ba ta rasu ba? Idan tana da rai zance ki Aureni ne? Ai Aure tsakanin mu be haramta ba, and kuma if theres anyone Safiyya would like me to get married to is defintely You, for the sake of our Daughter" Wani kallo ta ke binshi dashi, tace "ko ma meye ne, ba zan aureka ba, ba zaayi wannan cin amanar dani ba".
"Zaid" cewar Umma da ta gama nazarin Zaid da Zainab , Zaid ya maida dubansa ga Umma, Umma tace "Bari in dan ga Zainab" ta mike tare da jan hannun Zainab suka wuce Daki. Daidai da shigowan Abban, "Ahh Zaid Sannu da Zuwa, ka dade da zuwa? Ya na ganka kai kadai?" Zaid ya durkusa har kasa ya gaida Sirikin shi, suna ganin mutuncin Juna, Zaid yace "na dan jima, yanzu Umma ta shiga ciki ita da Zainab" Abba yace "Toh toh, barin shiga inji". Dakin Umma ya shiga, ya tarar Umma na Ma Zainab fada ko da ya tambayi ba'asi, Umma ta danar dashi abun da ke faruwa, Sosai ya ji dadi, don har ranshi yana Son Zaid, yana son sake Hade iri da shi. Zama yayi sosai yana me kallon Zainab chan yace;
"Zainab ki saurareni da kyau, wannan Mahaifiyar ki ce, Ni ko Mahaifinki ne, ba zamu so wani abu ya sameki ba, kuma Hak'k'ina ne in za6a miki Mijin Aure, Zaid Namiji ne da ko wane Uba zai so ya za6a ma diyar shi shi a Mijin Aure, Zaid na da kirki, ni ba talaka bane amma duk wata Zaid sai ya aiko da Motar Abinci duk wani nauinka Abinci yana kawo mana, tun daga lokacin da yake neman Yayarki har zuwa rana irinta yau, Zaid na da kirki da mutunci da kuma girmama na gaba, Shekarar shi daya da dori Yayarki bata taba cewa ya mata ba daidai ba, Zainab idan nace zan gaya miki irin Kirkin Zaid to zamu dade ina miki magana daya, ke ba wani tsaiyayye ba, ba kya kula Samari, ba kya sauraronsu, da ta ni ne da tun kam ki gama karatunki na miki Aure, amma saboda ba wani tsaiyaye na bari kika kammala, Zainab ba zan miki Auren dole ba, amma in kin nemi shawara ta, to Zaid Mijin Aure ne, Allah shi ya kawo miki Zaid a lokacin nan, kuma tunda shi ya bukaci ki aureshi ai ta kwana gidan Sauki, ba zaki ce ana so a hadaki da wani ba, shi ya kawo kansa, na yarda dashi dari bisa dari, sannan kuma kina maganar Zaki ci Amanar Safiyya, me ya kawo cin Amana? Kar ki manta