Showing 6001 words to 9000 words out of 149166 words

Chapter 3 - Ke alkhairi ce COMPLETE HAUSA NOVEL

BIEBIE   

22 Oct 2024

25708

sosai, bayan sun huta, Abba ya kebe da mahaifiyar shi, Nene tace "Ya akayi ne Mahammadu? Cikin ladabi yake maganan, yace " Nene, gidan nan ya tsufa, katangar kamar zata fado, shine nace ko zaki koma chan gidana na layout, tayi saurin katse shi "kai tsaya, ni da gidan nan mutu ka raba, shekaru sama da 30 ina zaune da yan unguwan nan lami lafia, kawai sai kace na tashi? Too don naki Garin Gwamna (Kaduna) shine kazo da wannan salon? Toh ba zan tashi ba, ina nan ni da gidan nan mutu ka raba, idan katangar ya tashi fadowa ya fado kaina, kaga nayi mutuwar shahada kenan". Abba ya ja numfashi ya san a rina. Ya sadda kansa kasa yace " Nene, ba wai gaba ki daya za ki koma chan ba, gyara zaayi, idan an gama daga katangar sai ki dawo, tace kai yaro ni zaka yi wa wayau? Ko da nake kauye ba a riga na zauna ba, ka fita idona. Abba ya girgiza kansa ya ciro waya ya kira yayar sa Fatiti, ringing biyu ta dauka, ya mata bayanin kudirinsa kan Nene, tayi na'am da maganar, ya mik'a mata wayar itama tayi tayi amma Nene tace aa. Ummi ma ta sa baki, Sai da aka kai ruwa rana kafin ta yarda, tace ni abunda ke batan rai shine unguwar nan shiru kamar ta mayyu baka ganin kowa awaje don bakin hali. Daga Abban har Ummin ba su tanka ba don kar ta chanza raayinta. A ranan Abba ya kira masu mota suka kwashe kayan Nene na bukata suka kai Gidan layout, A rannan Nene batayi kwanan Kofa Ukku ba".

Abba ke raka Nasiba Registeration. A gurin reg. Ne ta hadu da Ushee da Miemee. Hussaina Umar(Ushee) Aisha Saliz (Miemee) kawayen juna ne, tun JS1 suke tare, Ushee da Miemee suna da kirki sosai, suna son junan su, Miemee ta fiye surutu da kaudi, Ushee kam akwai jan mutane a jiki.
Wurin signing course form suka hadu, Inda Nasiba ta tambayi Miemee da ke bayanta a layi Biro, tace "donAllah ara min biro na rubuta mat.no dina nawa ya tsaya, Miemee da murmushin ta ta ciro ta bata, Miemee na son kyawawa, tace keme MCB kike? Tace "eh" Sunana Miemee, wannan kawata ce Ushee" Seebi tayi murmushi ta mika musu hannu sukayi musabaha tace"its nice meeting u all" nan suka dinke da labari har ya kai su da exchanging numbers, a nan ne suka gano gidan su Ushee be da nisa da gidan Nene. Haka Abotar su ta samo Asali.
Wannan Kenan..

_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS
ASSOCIATION(NWA)

Pg7⃣

"Kinsan jiya sai da nayi mafarkin Azababben Guy din nan?" Miemee ce ke maganar nan, Ushee da Seebi suka yi daria, Ushee tace ai ya hadu ne ba karya, Seebi tace ku ma kuka ga fuskar shi, ni jiyan nan ai a tsoroce nake, Miemee tayi tsaki, "ai wlh kina bada mu, kiyi ta wani nok'e nok'e kamar wacce tayi karya". Seebi tace banyi karya ba amma ai KUNYA ADON MACE (Na feedon biebee). Miemee ta kada idanuwa tace "story for the gods" Ushee tayi daria tace "ya isa, ku tashi muje Library mu fara Assignment din Wagini, Seebi tace "wallahi yunwa nakeji, daure wa kawai nayi aka gama first lecture" Ushee tace kinsan dai gobe za'ayi submitting, kuma gwara mu yi mu dawo before 12 kafin Mr Ola ya shigo, kin dai san rules dinshi ba a shiga idan ya shiga" Seebi tace "ba zaki gane yunwa Da nake ji bane, ku je ku mana Assignment din, Miemee tace "aa muje dai tare, sai mu fito mu ci abincin sha biyu saura minti talatin (11:30) Seebi tace "i can manage har time din muje".

Tayi Sallama ta shiga Cafteria, tsirarrun mutane suka amsa ta dinga raba idanuwa, don yau kadai ta zo CAF ita kadai, dalilin hakan kuwa shine " ba su gama samun Assignments din ba gashi har sha biyu saura minti sha biyar(11:45), Miemee tace "tunda kin fi mu jin yunwa, kije ki yi sauri kici abincin, sai mu hade a class kiyi sauri fa, don muma duk ta kare tafiya zamu yi" Seebi tace Ok, muje ko Ushee? Miemee tace wlh ba za taje ba, ni kadai za a bari nan? Ki tafi kawai don you are waiting your time" Seebi ta harari Miemee tace "in kun ga dama kar kuyi sauri" Suka yi daria duka.

Seebi ta wuce straight wurin reception desk, tace "Sannu ko" yaron ya amsa da mai "za'a kawo miki?" tace nikam bani koma meye sauri nikeyi aji zan shiga yanzu" yace" toh" ya shige ciki da sauri, don sauri ma ta kasa zuwa ta nema gurin zama. Jim kadan sai gashi ya fito da tray yace "hajia baki zauna ba?" tace "mik'o min kaji?" tray din ya bata, FriedRice ne da cowslow sai pure water. Nawa ne kudin? Yace "Dari Uku (#300)ne" ta ciro ta bashi ta amsa tray din Sai dai me?

Juyawan ta ke da wuya ta ci karo da wani, ba ta san sadda ta sake tray din abincin ta ba, duk kayan ciki ya zube, ta dago idanuwan ta da suka kada suka yi ja ta kalli wanda ta buge, shi ko tunani yake wani me kasadan ne ya zubar mai da abinci a jiki? yana dagowa suka hada ido, tsaf ta gane shi, shine na gaban motar jiya, haushi ya turnike ta da ta tuna wulakancin da suka musu na k'in daukar su don tana sanye da nikab.

Rafeek yayi dan guntun tsaki, da zai yi magana sai kuma ya fasa, ya juya don tafia, Nasiba tayi saurin shan gaban sa ta na huci tare da rik'e kugu, ranta a bace matuk'a, ga haushin ta zubar da abincinta, ga haushin yunwa, ga haushin missing lectures din da zata yi, ga haushin bata da wani kudin siyan abinci. Idonta ya kawo ruwa ba tare da saninta ba hawaye suka fara zuba daga idanuwan ta. Ido Rafeek ya kura mata, so yake ya tunkude ta yayi tafiar sa, ba halin shi bane tausayi, be damu da damuwar kowa ba, amma abin mamaki sai ya tsinci kanshi da ce mata "Me kike so?"

_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS
ASSOCIATION(NWA)

Pg8⃣

Ta sa bayan hannun ta ta share hawayen ta, tace "ba kaine ka tsaya a baya na ba na kifar da abinci na, ka juya zaka yi tafian ka, ba ka ban hakuri ba, gashi yunwa nike ji, abun da ya fi ban haushi shine zanyi missing lectures dina."

Kallon ta kawai yakeyi, ba wai ya fahimci bayyanan da take mishi bane, don shi ba ma'abocin sauraron korafe-korafen mutane bane, yana iya maka laifi ya fi ka zuciya, amma dai ya ji dai tace zatayi missing lectures. Mutane sai kallon R-lema sukeyi don da wuya kaga yana magana da namiji balle mace, in ka ganshi cikin CAF to takeaway yazo yi.

Ya kalli mai bada abincin yace sake zubo abincin, ya samu wuri ya zauna, be kara bi ta kanta ba, tsaye tayi tana murza idanuwa, cleaner yazo don share gun, chan sai ga shi an kawo wani tray din, kallon ta yayi yace "zauna" ba musu ta zauna ya tura mata tray din gaban ta, ta kalli abincin ta kalle shi, tsaki yayi a ranshi, ya miqe ya fita, haka ta gyara zama taci abincin ta, wannan karon har da Orange juice. Tayi hamdala ta zaro wayarta, ta ma Ushee text "Lecturer ya fara? Jim kadan sai ga Ushee tayi reply da "eh ya shiga, kina ina?" ta mayar mata da "ina CAF, yana bari a shiga? Ushee tayi reply da " wlh bai bari, yanzu ya wulakanta su Chinyere, kuma ya kulle kofa" Nasiba ta hadiye kukan da ya so zuwa mata, ta ma Ushee reply da "ni na wuce gida, sai Allah ya kaimu Gobe" ta mike tare da daukar jakkarta tayi waje.

Ba ta lura dashi ba har ta dan gifta yayi dan tsaki yace "erhm, nace ba? Ta dan juyo a firgice ganin shi ya sa ta sauke ajiyar zuciya tace "Wlh har na tsorata, kace mene?" kamar ba zai yi magana ba don yanda tayi maganar ta tuna mishi d wani abu, chan yace "Meyasa zakiyi missing lectures?" nan da nan idon ta ya kawo ruwa, tace "nayi latti, yana daga cikin ka'idojin malamin, na idan ya shiga aji ba wanda ya isa ya shiga, 12 yake shiga, gashi yanzu 12:19, kaga ko gwara na tafi gida akan naje ya hanani shiga karshe kuma ya wulakanta ni" Rafeek yace wani mallami ne wannan? Tace Mr Wagini ne. Yace ina kuke lectures din? Tace "Science Theatre" a takaice yace "biyo ni" be jira bin ta bakin ta ba yayi gaba.

Babu yanda zatayi dashi da ya wuce ta bi bayanshi, tafia yake a nutse kamar be son taka kasa, fuskar nan tamke tamau duk inda suka wuce ji kake ana "R-Lema" mutane ba su damu da yanda yake basar da su ba idan sun kira sunan shi, ita ko Seebi ta kasa dauke idanuwan ta daga kallon shi, karantar shi take yi, komi nashi daban, ba kamar wasu mazan ba, ta tabbatar da wani ne suka jero haka sai ya isheta da magana, amma shi ko wannan ko kallo bata ishe shi ba, haka suka iso bakin Lecture hall din, Nasiba ta ja ta tsaya, tana kallon yan latti nan suna leke ta window, Rafeek ya taka har gaban kofar ajin da ke kulle ya sa hannu ya kwankwasa.

Daga ciki Mr Wagini ne ke tunanin wani me kasadan ne ya ke kwankwasa mai, bayan shi da hannun shi ya kulle kofar, rai bace yace da na kusa da kofar"open the door" da sauri yaron ya je ya cire sakatar kofar ya bude, idon kowa a kan kofar, so suke su ga mai karfin halin kwankwasa ma Mr. Wagini.

Shigo wa yayi yana tafian nan nashi,ya na bouncing a hankali, ba Matan ba harta mazan sai da su kaji ya burge su, kowa ya shiga tofa albarkacin bakin sa, da yawa za su so Mu'amala ko da ta gaisuwa ce ya hada su da Rafeek, Miemee tayi saurin tabo Ushee "OMG, ga wani Azababbe nan, ya tafi da imani na" Ushee tace "ni baki ji nayi shiru ba? Ai ya hadu ne over, mu dai kalli draman da zasuyi da Wagini".

Har gaban Lecturern yaje, da alamun akwai sanayya tsakanin su, magana suka danyi kafin Rafeek ya juya ya bar Lecture hall din, Nasiba na tsaye inda ya barta, ta gaban ta ya wuce ta bishi da kallon mamaki, shi kuma wannan lafian shi kalau kuwa? Ko be gane ta bane ya wuce ta gaban ta ba tare da ya kalle ta ba? Ko kuma ya na nufin ta bishi ne? Duk a zuci take zancen nan, ba ta gama zancen zuci ba taji ana cewa "Mr Wagini yace duk na waje su shigo aji" da sauri suka fara tururuwar shiga ajin. Wuri ta samu ta zauna ta na tunanin Wannan Bawan Allah me tarin ban mamaki har a ka gama lectures ba ta fahimci komai ba.

Kusan kowa zancen gayen da ya shigo aji dazun suke, wasu suce daga ganin shi dan zafin kai ne, wasu suce ya burgesu, Miemee ta kalli Seebi tace "kinyi missing, ba ki ga wani Azababben guy da ya shigo ji dazun ba" Ushee tace ni abun da ya daure min kai shine, yau Mr wagini yayi abun da be ta bayi ba shine barin late comers su shigo aji, Miemee tace "kuma fa immediately after fitan wannan ne yace ace su shigo" toh ko shi ya rok'i alfarmar abar su su shigo? Miemee tace wane shi? Be yi kama da lecturers ba, yaro ne student kamar mu, da kwai abun da ya kawo shi" kawai muce yau yan kirkin Mr Wagini suna kanshi" Ushee tace "gaskia kam" ta zunguro Seebi da kwata-kwata ba ta tare dasu, tafiya kadai takeyi, Seebi ta dan firgita ta k'akalo murmushi tace "Uhm" cikin zuciyarta kuma tunani take "Is it possible shi ya roke Mr Wagini akan a barsu su shiga?" Meyasa fuskar sa fa ba annuri? Meyasa da ya fito ko kallon ta beyi ba? Meyasa ko sunan ta ya kasa tambaya? Meyasa fuskar sa yake cikin yanayi na damuwa ko rashin walwala ne bata san ya za ta sa abun ba? Tambayoyi da yawa da take bukatar amsoshin su. Haka kurum taji tana son sanin Wanene wannan R-Lema?

Nima biebee nace waye Rafeek Habib Lema??

_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

Pg9⃣

ASALIN LABARIN:

Anyi wani Attajirin mai kudi a garin Katsina mai suna Alhaji Ibrahim Lema, Matan aurensa 2, Karime da Hajjo. Karime ce Uwargida 'ya'yanta 4, Babba danta mai suna Habibullah, sai Aisha da Farida sai autan ta Zaid. Hajjo Amarya na da daya mai suna Hafiz. Alhaji Ibrahim yaso 'yan'yan shi su fi haka yawa amma da yake haka Allah ya tsara sai ya hakura.

Zaman lafiya akeyi a gidan Alhaji Lema don yana bawa kowa hakkin sa.
Habib shine babba a gidan, yana da kwazo don shine yayi gadon mahaifinshi don tsufa yazo mishi, a yanzu Zaid da Hafiz suna Secondary School matakin aji 5(SS2).

Kasancewar Alhaji Ibrahim Lema sannane ne yasa abokan gaba ke kawo mai hari, hakan ta faru Yau Ranar Juma'a da misalin karfe 1 na dare yan fashi suka dira gidan Alhaji Iro Lema, Bacci yakeyi sai jin karar bindiga daga waje, da sauri ya diro ya fito waje, ganin diyarsa Aisha kwance shame-shame cikin jini hankalin shi yayi mummunar tashi, be ankara ba sai jin yayi an dora bindinga a kanshi ana fadin "if u make a move i will burst ur brain" "Inalillahi wa ina ilaihir rajiun" ya shiga maimaita wa, da kakausar murya aka ce ina kudin da kaddarorin ka gaba ki daya nake so ka tattaro min cikin mintuna da basu wuce 5 ba, kayi yunkurin wani abu yara na zasu fasa kwakwalawar matanka a gabanka kamar yanda aka ma diyarka. Hankalin Alhaji ya tashi, yace kar ku taba min iyali na, zan baku duk abunda kuke buk'ata, ba tare da bata lokaci ba ya tattaro musu kudadden da ke cikin gidan nan, da wasu k'adarori. Yan ta'adan nan suka kwashe komai suka fice, ashe sun dasa bomb cikin Gidan, cikin mintuna da basu fi 3 ba gidan ya tashi ya kone kurmus ba wanda ya tsira.
Abunda yan taadan nan basu sani ba shine, fashin da suka ma Alhaji, basu taba kaso daya daga cikin goman dukiyar sa ba(1/10)

Cikin daren nan makota suka fito don ceton su, amma ba suka komai ba, sun girgiza kwarai da mutuwan Alhaji Iro Lema da iyalansa, don mutum ne mai kirki da sanin darajar dan Adam. Bincike ya nuna banda yaransa maza cikin gidan lokacin da Bomb din ya tashi, Dama Habib na lagos yaje duba wani company din baban sa, Zaid da Hafiz na makaranta Ulul Albab. Sai dai aka turo musu saqon Rasuwar Mahaifan su da yayyin su, hankalin su ya tashi Matuka don sun san sunyi Rashi Babba.

Bayan Sadakar Arbain
Alhaji Tijjani Masanawa, (Aminin Marigayi Iro lema) ya kira su duka, yace "Allah yayi yau anyi kwana Arbain da Rasuwan Mahaifainka da yanuwanka mata. Shawara ta farko da zan baku shine kai Habib, kaine Babba, ya kamata kayi aure, burin marigayi kenan, Magana ta biyu kuwa shine ka rike kannen ka da amana, ka hada kansu ka musu duk abunda uba zai ma yayan sa don kaine ubansu kaine uwarsu, ba su da wanda ya fika a yanzu,Da Zaid da Hafiz duk daya suke, kar kace wannan dakin ku daya wannan ba dakin ku daya ba, aa, duk daya suke kaji? Ku kuma, ku mishi biyayya. Ku rike maraicin ku, Ku kwantar da hankulan ku kuyi karatu ku zama abun da zamuyi alfahari daku. Maganar karshe shine maganar Gado.

Zaa tattara komai a hade, sai a raba Gadon kamar yadda Addini ya tsara, amma wani hanzari ba gudu ba, Hafiz da Zaid ba damka muku Gadon ku zaayi a hannu ba, aa Habibu za a ba ya ajiye muku har sai kun mallaki hankulan ku, kun gama jami'a sai a baku hakkinku, nan da shekaru 5 kenan ko 6. Ko akwai mai magana? Duk suka girgiza kai suka ce "aa babu"

Alhaji tijjani yace "to Alhamdulilah Allah ya ji kansu ya gafarta musu". Duk suka amsa da "Amin" yace to ku sai ku shirya ku koma bakin karatun ku ko? Suka amsa da "to baba" yace to ku na sallame ku. Hafiz da Zaid suka tashi suka tafi.

Alhaji Tijjani yace "Habibullah, wani nauyi Allah ya dora maka, ina fatan zaka rike amana? Yace "InshaAllah baba, mungode kwarai, Allah ya saka da Alheri Allah ya ja kwana" Alh. Yace "To Amin".
Yauwa Baba karshen wata zan tafi Cairo, zanje magana kan Engines din nan wanda marigayi yayi order su, har yanzu ba su iso ba" Alhaji Tijjani yace "Toh Allah shi kaimu yayi jagora Amin, Habib mata fa? Habib yayi daria yace InshaAllah baba an kusa".

_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

Pg🔟

CAIRO INTERNATIONAL AIRPORT

"Assalam Alaikum, that's my seat" ta dago fararren idanuwan ta ta kalleshi tace "oh sorry" tare da mik'ewa ta rabe ya shige ciki ya zauna itama ta zauna. Wayar shi ya ciro ya kira Alhaji Tijjani Salam Baba gani nan cikin jirgi yanzu zamu tashi" dsga bangaren Alh yace to ya an dace? Habibullah yace "Eh baba, zuwa karshen sati zasu iso" Alh yace toh MashaAllah, Allah ya kawo ku lafiya Amin"

Sanarwa akayi jirgi zai tashi kowa ya sa seat belt dinsa, duk suka yi yanda aka umarta, cikin mintuna kalilan jirgi ya fara yunkurin tashi.

Runste ido ta kusa dashi tayi, da yazo daidai tashi ta yi saurin dafa Habib

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login