Showing 63001 words to 66000 words out of 149166 words
ja motar shi yayi gaba" Su Miemee suka bi motar da Ido baki a hangame.
_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
Pg4⃣0⃣
A tsorace ta dan kalleshi, ko bi ta kanta beyi ba ya hau titi kanshi a tsaye, Maimakon suyi hanyar Asibiti, sai bani tayi ya dauki hanyar *Sally's Cuisine* ba tace da shi komai ba har ya iso yayi parking, fita yayi ya shiga, nan ta samu damar amsa Wayar Usheey da tun da suja aje su take ta faman kiran ta, "Hello Seebi ina zai kaiki?" tayi daria tace "Asibiti" "haba har hankalin mu ya kwanta" tana ganin ya fito tayi saurin katse wayar, Hannun shu dauke da ledoji 4 ya aje mata 3, dayan kuma ya aje a seat din baya yaja mota sukayi Asibiti.
Ko da suka isa Asibtin, har ta bude murfin mota zata fita, Zuciyar ta ta bata shawara, ko bazai amsa ba, ki masa godiar dawainiyar da yake tayi daku, Abinci lunch da dinner baya fashin kawo muku, ga kai ki makaranta da dawo dake duk da ba kullum ba.
Ta juyo ta gyara zama yanda tana fuskantar sa tace *"Hamma Rafeeq, Yau Dr ke sa ran Sallamar mu, mun gode kwarai da dawainiyar da kakeyi da mu, Allah ya biya ka, Allah ya saka da Alheri ya, Allah ya ji kan Magabata, Albarkaci Rayuwar ka, Allah ya kuma Saka maka duk Zalincin da aka taba maka, wanda ba za ka iya yafe su ba"* tana kaiwa nan ta fice daga motar, bata tsaya sauraren abun da zai ce ba, Yanda kuka san Hoto, haka Rafeeq ke zaune a gun, ko yatsar shi ya kasa dagawa, be san lokacin da ya furta *"Ameen*" ba.
Haka kurum yaji dadin Adduointa, Shi be san meyasa ba, amma yana jinta a jikin shi, kawai yaji ya bata babban matsayi a ran shi, jinta kamar FEE'AH.
Da k'yar ya kunna mota, saboda jikin sa ya mace gabaki daya, ji yayi ya kasa tafiya, guntun tsaki ya sake ya duba Aljihun motar shi ya ciro paper da biro, rubutu yayi sannan ya fita ya shiga Asibitin, daidai Dakin ya chokara a jikin kofar yadda in an bude zaa gani, yayi tafiayar sa.
Seebi na idar da Sallah ta dauki Abincinta, Su Nene har sun gama da Abincin da Nasiba ta shigo dashi,nan zaman jiran Sallama sukeyi, Nasiba tace "bari inje in ga Dr, k'ila ma ya mance da yace yau zai sallame mu" Nene tace "E danAllah, na k'agara inga nayi juyi kan Gadon K'arfe na" sukayi daria duka.
Tana murda kofa wata kaaramar Takarda ta fado, duk'awa tayi ta dauka, ta na budewa tabi rubutun da ido, Murmushi tayi a hankali tace "R-Lema" a nutse ta fita daga dakin ta fara karantawa ga abun da yace
_"Ameen to your Duas. Idan an sallame ku, ga number na ki min text you DONT have to Call just TEXT"_.
Seebi tayi murmushi ta sake karantawa, tace *"R-LEMA kenan Allah ka bani ikon taimaka ma beautiful soul dinnan"*. Tasa kai ta wuce office din Dr. A hanya suka hadu da Dr da Nurse Sai suka juya suka koma dakin.
Nurse ta gwada Bp da Temperaturen Nene, komai daidai, Likita yace "Mama, kin ji sauki sosai, zan sallame ku, Amma donAllah ki rage cin Jan Nama" Nene ta bishi da kallon kai gaja, tace *"yaro wani Nama ne Ja?"* yace "Naman Sa, ko na Awaki" Nene ta tuntsire da daria, tace "Su balangu da tsiren da nake ci kake son hanani ci ko? Yace " Mama saboda Lafiyar ki ne, bawai ina son hanaki bane" ta tabe baki tace "toh dai bari kaji Ubana *Mamman* Shanun shi 31, duk bayan wata ake kashe mana daya, ba saidawa ake ba ci mukeyi, kuma ban taba jin ance wani naman Shanu yasa shi ciwo ko wani abun Allah sauwak'a ba, toh nidai _Aminene Mamman_ da bakin ciki ya kashe ni gwara Dadi ya kasheni Ehe" Nasiba tayi saurin cewa "I'm so sorry, She's always like this, InshaAllah she'll regulte it" Dr yace "Dont worry i have someone exactly like her at home" Nene ta cika tayi fam tace "Oho dai, Sai ka sallame mu yau, Ke kuma ni zaki chanzawa ko? To in ma zagina kukai da Ubanki Mahammadu kuke" Dr ya fashe da Daria yace "yi hakuri Mama ga takardar sallamar ki" yafi maka don yau ko baka sallameni ba gida zan kwan" Nasiba ta girgiza kai cike da takaici, Hajjo kuwa sai daria take tayi.
Dr na fita Nene tace " _kinga latso min Zaidu bawan Allah a waya, ba gardama Seebi tayi yadda nene tace, Yana ganin kiranta ya yanke ya sake k'ira
Zaid yayi Murna kwarai da jin Sallamar su Nene, kuma ya bata shawaran bin yanda Likita yace, jin shi kawai Nene tayi don ba ta da Mak'iyi kamar me son rabata da Nama, nan dai ta hau yi mishi Godia da Adduoi, Ya tsaidata ta hanyar cewa Haba Nene, Kun wuce nan, babu godia a tsakanin mu. Sukayi Sallama. Bayan Seebi ta karba wayar ne yace mata zai turo a maida su gida, tace ai "Hamma Rafeeq yace in gaya mai idan an sallame mu" da Mamaki Zaid yace "Rafeeq dai?" tace "eh shi" shi da kanshi yace haka?" tace "eh" "Rafeeq yana zuwa ne?" tace "Duk da ba shigowa yake ba, amma yana kawo mana Abinci Rana da Dare, sometimes ya na aje ni makaranta" Allahu Akbar zo ku ga jin dadi gun Zaid, Ashe Rafeeq na da sauran Mutunci da tausayi a tattare dashi? Be taba ganin Rafeeq ya damu da lamuran wasu ba kamar su Seebi lallai akwai Improvement, yace da Seebi "to sai kun koma gida mayi waya" sukayi Sallama. Duk zaton Nasiba da Nene Zaid ne ya sa Rafeeq dawainiya dasu, duk abunda yake yi saboda Zaid ne, nan suka gane cewa ashe Rafeeq ne ya sa Kanshi, ba kowa ba. Nan Nasiba ta k'ara samun wani k'warin guiwar Aiwatar da Kuddirinta.
Seebi ta kwafi numbern da Rafeeq ya bata, ta masa text din as he demanded. Ga abun da tace;
_"Assalamu alaikum Hamma Rafeeq anyi discharging din mu, mun shirya, we are good to go"_
Yana wanka yaji wayarsa alamar shigowar sak'o, bayan yayi Sallah, ne ya daga wayar ya ga message daga new number, ya bude ya karanta, dan guntun tsaki ya ja (Ikon Allah! sak kace bashi yace ta mai ba).
Key kawai ya dauka ya fice daga gidan sai Asibiti, yana isa ya mata text "Ku fito".
Seebi na jin shigowar text ta duba taga Shine, ba su wani dau lokaci ba suka fito harabar Asibitin da kayan su. Inda yake aje Motar shi sukayi, ta na zuwa ta iske Booth a bude, be fito ba haka Seebi ta shiga saka a kayan boot sai da ta gama, sannan ta bude gaba ta shiga ta zauna su nene kuma sun shiga baya.
Sai da suka bar Asibitin, da kyar yace " Ya Jikin?" Nene ta murmusa a ranta tace Uban Kasaita, a fili kuma tace "Alhamdulilah, na watsake" kamar ba zai ce wani abu ba yace "Sannu Fah" tace "yauwa" a hankali tace kamar dangin Maguzawa wai sannu" Hajjo da Nasiba kadai suka jita, Murmushi kawai sukayi, tun daga nan ba wamda ya sake magana har sai da suka iso gida, ya juya ya dan kalli Hajjo yace "Hajjo Mom tace ki k'ara Sati daya sai ki koma gida" tayi murmushi tace "ba damuwa"
Tare da taimakon Hajjo suka shiga da kayan su ciki, sai da ya tabbatar sun gama kwashe wa ya danna horn, ta lek'o ta window, ya mik'a mata manyan ledojin Abinci, yaja motar sa yayi gidan su Maalesh.
*England*
Zaid ne kwance kan tafkeken Gadonsa yana waya da Mami, inda aka bashi Ayman ta dinga mai gwaran cin ta, har sukayi Sallama sannan ya kira Nasiba,
Suk gaisa ya tambayeta ya jikin Nene ta amsa masa da sauk'i.
Suka danyi hira sannan ya gaisa da Nenen itama ya musu Sallama.
Nan ya hau tunanin wanda zai sa ya musu Grocery shopping, don ya tabbatar suna da Buk'ata, baya son takura wa Rafeeq, Saboda abunda ya fahinta, Rafeeq has done more than Enough, kuma baya so ya k'ure shi .
Maalaesh ya fado ransa, Take ya kira wayansa, Ringing biyu ya dauka "Hello Mahmud" nan take ya gane Uncle Zaid ne, don shi yasan shi kadai ke kiran shi da sunan shi na Asali, "UncleZee ina wuni" suka gaisa, yace "Mahmud ina so donAllah ka min Shopping na kayan Abinci, da kayan buk'ata na Gida, ina so ka kai wani Gida na nan ku sa da gidanku na Layout(Gidansu Rafeeq yake nufi) Nan ya mishi kwatancen gidan. Malaesh yace "Angama, anything for you uncle Z" barin je yanzu ma, "barin maka transferring kudin" da sauri yace "Noo akwai kudi hanuna Uncle Z" "dont be Silly Son, i'm sending now" Murmushi Maalesh yayi yace "Nagode" suka yi Sallama, Nan take Zaid ya mai Transfer din 100k.
2:47pm
Seebi na zaune bisa kujera yar tsugune, tana yi wa Nene tsifa, i Nene da Hajjo na kan tabarmar k'asa, Sallama suka ji, da sauri Seebi ta zaro Mayafin ta kan Igiyar Shanya, Nene ta daura dankwali tare da Amsa Sallama, Maaleah yace "donAllah nan ne Gidan Nene?" da sauri tace Eh Yaro Shigo, nice nan Aminene, yace toh ina zuwa, Yara ya samu ya sa su kwasan kayan ya ce suka shiga gidan nan, Mamaki ya rufe su Nene, ana haka ne Maalesh ya bi bayan su ya shigo, yana ganin Hajjo ya bude baki "Laaaah Hajjo, kece nan?" tace "Maalesh yaushe a gari?" yace "jiya na shigo, na tambayi Mom kina ina tace ba kya nan" tace aiko dai gani anan, ya durkusa ya gaida Nene, ta amsa mai cikin Fara'a, yace "kece Nene daga gani" ta nuna kanta da Yatsa tace "Nice nan Aminene Yar Mamman, duk duniya ba wata Nene sai ni" ta nuna Nasiba da hannu tace "Nenen Seebi kake ji" ya juya ga wacce aka cema Seebi, ya ga shi take kallo, tsaf tagano shi, shine wanda kwanaki da zai basu Lift yace sai ta cire Nikab, kuma Shine Abokin R-Lema, ta dai maske ta gaishe shi, "Lord have Mercy" inji Maalesh, tuni Nasiba tayi gaba da Imanin shi, da kyar ya amsa mata fuskar shi cike da Annashuwa.
"Hajjo tace Maalesh wannan kayan fa?" yace "Uncle Zaid yace a kawo" Nene ta chafe "Allah Sarki Zaidu Bawan Allah, Allah shi biyaka ya saka da Alheri, Malush kaima Nagode maka" Yayi daria yace Nene "Maalesh nake ba Maalush ba" duk sukayi daria, na da nan Maalesh suka dinke da Nene, k'wank'waman su iri daya na surutu, sai yi suke tayi yanda kasan sun dade da sanin juna, dama shi Maalesh saurin Sabo ne dashi, nan Hajjo ta zubo mai Burabusko ya kwasa kamar ba gobe, sai kallon Nasiba yake tayi, ita kuwa sai smilling take tayi tana jin diramar su da Nene, har kusan Laasar be da niyyar tafiya. Wayar sa tayi k'ara, ya ciro daga Aljihu ya duba, ya kalli Hajjo yace dan gidan ki ne, tayi murmushi tace "Rafeeq Ho" ya dauka "my guy howfa?" kusan sakwan 3 beyi magana ba chan yace "kana ina? Nazo gida baka nan" Maalesh yace "Wallahi gani ta wurin gida Uncle Zaid ya aikoni" tsaki Rafeeq yayi yace "ina jiranka" ya kashe wayar, Nasiba ta tsura wa wayar Maalesh ido, kamar tana jiran Rafeeq ya fito daga ciki, Nene tace "Wannan uban Yan k'asaitan ne ko?" Maalesh yayi daria yace "Nene kinsan Rafeeq ne?" ta ta6e baki tace "ai wannan sai kun hada mai da tofi" yayi daria yace barin je, sai na dawo ya musu Sallama ya kalli Nasiba yace "Bye Beautiful" ita kunya ma ya bata ta rufe fuskar ta da tafin hannayen ta.
Yana shiga Dakin shi ya ga Rafeeq kwance kan Gado, ya bubbuga mai k'afa, kamar ba zai tashi ba, ya mike sukayi side hug, Maalesh cike da doki yace "I met her, Wallahi naganta yau" da k'yar Rafeeq yace "Who?" Maalesh yace "The love of my life, Seebi, Uncle Zaid ya aike ni Gidan su yanzu in kai ma Nene sak'o" a dan tsorace Rafeeq ya kalleshi, kamar zaice wani abu sai ya fasa, be damu da Rashin Ansashi da Rafeeq yayi ba, Maalesh ya cigaba "Shes beautiful, ai kasanta, ta hadu ko? Zamu dace? Haka ya ishe Rafeeq da maganar Nasiba, yace " Guy do you think she'll like me? Wallahi ina sonta, kawai ganinta nayi gefe na kamar an jefo ta, ina ganin ta naji She's the one, wannan shi ake kira "LOVE AT FIRST SIGHT" cikin kufula da daga murya Rafeeq yace "Will you Shut the f**k up?
_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
Pg4⃣1⃣
Maalesh ya kalleshi da mamaki yace "Guy, Calm down" Rafeeq yayi guntun tsaki cikin yanayin shi yace "ban ga dalilin da zai sa ka dinga min maganar wata yarinya ba, duk ka bi ka ishe ni" Maalesh cikin doki yace "Feeq ba zaka gane ba, Wallahi ina sonta, sosai fa" kamar ba zai ce komai ba yace "She's Innocent, dont hurt her" da sauri Maalesh yace "Wallahi i wont, shes not like the rest of the girls i'm with, Wannan ta dabance, guy bani shawara ya zanyi?" chan cikin mak'ogaro yace "Tell her" "bansan mesa ba i lost the courage, ai da tun dazun na gaya mata" Rafeeq yayi shiru ya cigaba da latsa wayar shi be ce komai ba, Maalesh ya yi rigingine kan Gado, Rafeeq ya dora wayar shi kan cikin Maalesh, Maalesh ya tashi da sauri ya dauki wayar Rafeeq ya duba, kan Screen din ya ga Message ya karanta, ya kalli Rafeeq don neman k'arin bayani, guntun tsaki Rafeeq yayi yace "The girl's Number" wani irin super Maalesh yayi ya duro, ya rungume Rafeeq, donAllah numbern ta ne? Kai Nagode Breh, naji dadi Wallahi" Shi dai be ce dashi komai ba, Maalesh yayi copying number din yayi saving a wayanshi.
Tana tsakiyar su Nene suna fira, wayar ta yayi ringing, ko da ta duba New number ne, ta dauka da Sallama, Muryarta yafi komai dadi inji Maalesh, ya amsa yace "Hello, Beautiful" wani ajiyar zuciya ta sake ta amsa da Ina wuni don ta san me muryar, yace "kingane me magana ne? Cikin jin kunya tace "eh" to waye? ta yi Murmushi tace "Ya Maalesh ne" Waiyo dadi, Ya Maalesh, karo na farko bayan Rasuwar Rafee'ah yaji an kirashi ta wannan sigar, yace "Seebin Nene, you are a Blessing, kinji Voice dinki kuwa?" kunya ya bata sai bata amsa shi ba, yace "are u there? Kinyi shiru?" a hankali tace "i'm here" "Seebi will you be my friend?" Daria kawai tayi, ya kike daria? "Ba kya so in zama Abokin ki? A hankali tace "Aa" yace "Aa mene? Kina so? Will you be my friend? A hankali tace "yes" Darian jin dadi yayi yace "let me warn you, my friends usually say i'm a Sweet Soul, abun nufi shine Wata rana Abokantakar mu na iya rikidewa ya koma Soyayya" Daria kawai tayi, nan suka sha fira don Maalesh akwai Zance, sun dade suna waya inda ya shaida mata zaizo Gobe don Jibi zai wuce Kano inda yake Service.
*Washe Gari*
K'wank'wasa k'ofar yayi, sai da ya kusa minti 3 kafin yazo ya bude mai, hararar shi Maalesh yayi ya ra6a ta gefen shi, ya shige cikin Dakin, Da k'yar Rafeeq yace "Sorry i missed your call" Maalesh yace "and you cant call back?" Guntun tsaki Rafeeq yayi yace "I said i'm sorry didnt i?" Maalesh ya k'ulu ya mik'e zai fita da sauri Rafeeq ya rik'o shi, kasa magana yayi ya girgiza kanshi, Maalesh ya dawo ya zauna, Rafeeq yace "Look, wannan Aneesar banzan ce take takura min, shisa na kulle k'ofana, coz duk abunda zan mata bazata yi zuciya ba, so da ka kirani i thought itace shisa ban dauka ba" Maalesh ya girgiza kai cikin takaici, ya akayi sunana da na ta yayi kama, har da ka zata itace?" a takaice yace "ban duba wayar ba" "Oh lord have Mercy" Inji Maalesh da sauri Rafeeq yace "Kayi kyau Sosai, ina zakaje ne haka?" Don dai ya 6atar da zancen don yasan Maalesh da mita kamar Nenen Seebi. Murmushi Maalesh ya sake yace zanje Gidan Nene ne, zanje musu bankwana, Tsaki Rafeeq ya sake "Do you really have to go there?" Maalesh ya amsa da sauri "Yes My other Half is there" wani Mugun tsaki Rafeeq ya sake tare da kwanciya kan Gado, Maalesh ya mik'e yace "Feeq, barin je sai na dawo" da sauri Rafeeq yace "Wait" da Mamaki Maalesh ya kalleshi, Rafeeq ya dauke ido be so su hada Ido da Maalesh yace "I'm Bored, i'm coming with you" be jira cewar Maalesh ba ya fice daga dakin, Maalesh da mamaki ya maimaita "He's Bored?" Sabon Salo, gemu a kafada, yau Rafeeq yake cewa he's bored, shida be k'i ya kulle kanshi a daki ba, be komai, lallai kam, toh K'ila ya fara Chanza halinshi, Allah ya sa don sai nafi kowa Farinciki, ya fita