Showing 117001 words to 120000 words out of 149166 words

Chapter 40 - Ke alkhairi ce COMPLETE HAUSA NOVEL

BIEBIE   

22 Oct 2024

25734

"Yaya a yanke kawai zan ma fi samun kwanciyar hankali, nagaji da wahalar da kafan nan ke bani".
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
A GURGUJE
Bayan An yanke k'afar Saude ta dan yi kwanaki a Asibitin ta dawo Gida, an bata Crutches na tafiya, har yanzu Aneesa ba ta sauko ba, Daddy ma ba ruwanshi da ita, sai da Mami tayi dagaske kafin ya lekata so daya, shi bek'i ya saketa ba, don ya mugun tsanarta, Mami ta shaida mai Ai don Diyarta zaiyi.

Saude tayi mugun shiga taitayinta, yanda taga Alhaji ya banzatar da rayuwarta, ya nuna mata cewa da ita da banza daya suke, ita har ga Allah tana sonsa.
Mami ta samu Aneesa a daki wata rana bayan ta dawo daga School, Mami tace "Aneesa, komai yayi zafi maganin shi Allah, nasan Saude ba ta kyauta ba, ba kya tunanin cewa abubuwan zasuyi mata yawa? Kin dauki gaba da ita, watan ta kusan 1 a Asibiti ba kije kin dubo ta ba, Sannu be taba hadaki da ita ba, Aneesa horon da kika mata yayi tsanani, Uwa uwa ce, ko ya take, donAllah kije ki sassamta da ita ko ta samu sauki, nasan hankalinta a tashe yake, i was once in her shoes, Rafeeq turned his back against me, banji da dadi ba please Have Mercy on her, go talk to her" Aneesa ta share hawayenta ta san tana matuk'ar Son Mamarta, amma what she did was unforgiveable. Ok kawai tace ma Mami.
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
"Kanaji ko? Kwana 1 na baka, ko ka kawo min cikon kudina, ko wallahi in sa Guys su min gunduwa gunduwa da kai, you cannot run away from me, wherever you go, i will find you and i will Kill you, i want my Money" Ya hadiye wani mugun bakin miyau, duk Iskancin shi ya san Steve ya fishi, yayi dana sanin Shiga Chachar nan, da beyi Chacha ba k'ila da ya rage Bashin 2million din da Steve ke binshi yace " Sorry Iga Steve, i'll get you your Money, kayi hakuri" Steve yace "Ka sanni, kasan me zan iya yi, get my money Ready or else, hmm" ya kashe wayar, cikin shi ya duri ruwa, da sauri ya lalubo Numberta.
"Fatara me tada Tsohon Bashi, Aminiyata ya kike?" a tsure tace *Mak'ale, meyasa ka kirani, we dont have any Bussiness left, kar ka sake kirana, You might get me into trouble, danAllah kar ka sake kirana" dif ta kashe wayar, tana waigen bayanta Allah yasa ba wanda ya jita, wayarta ya sake ringing har ta katse bata dauka ba, ya sake kira ta dauka a masife " Ke Sauda, butulu, ni zaki kashe ma waya? Kar ki kawo min Iskanci mana, haka kurum da ina kiranki ne? Kudina zaki ciko min, na sha miki aiki kina bani rabi baki ban rabi ba, nasan ina binki bashi fiye da 7million, amma na bar miki 5, ki bani 2million ciki, i need it, its an emergency, kuma ina sonshi kafin gobe" cike da rudu tace "Makale me kake cewa ne? Are you insane?, banda sauran Alaka da kai, please ka rabu dani, i am a born again person, ina so in saita rayuwata, i want to start new, so Please ka rabu dani, kar ka sake kirana" wani mugun daria Mak'ale yayi yace "Nice Joke Sauda, kinsan dai na fiki tasha ko? Ni zaki cema you are a born again hahah Sauda bani ke da wuta ba amma na san ke 'yar wuta ce komin tuban da kikayi, kin dade kina tsula tsiyarki, mtsww, yanzu ba wannan ba, Kudina nake so, someone is threatening me, if i go down i promise to drag you down with me, idan baki son Asirin ki ya tonu ki hada min kudina kafin Gobe wallahi in ba haka ba, komi zai iya faruwa" dif ya katse kiran,Zufa ya fara jike kayan Saude, ya zatayi? Ai ba zata taba bari asirinta ya tonu ba, wanda ya tonun ma tsautsayi ne, tana cikin tararrabin nan ne Meema ta shigo dakin tana zuba uban k'amshi, Saude a razane ta kalli Meema tace "Meema akwai Matsala, i need your help, Makal'e ke min barazana, wai zai tona min Asiri idan har ban bashi 2millionn ba donAllah ki taimakeni, bana tunanin a Account dina zan samu ko da 100k" Meema ta kalli Saude galala tace "Sis are you crazy?ke matar the great Habib lema baki da kudi sai ni? Please stop this nonesense now" baki wangale Saude ke kallon Meema da mamaki, yau ita Meema ke ma magana Gatsau? tace "Maryam nike ma magana haka?after all i've done for you? I took care of you tun kina k'arama and now don banda wata mamora kike min magana yanda kika ga dama" Meema tace "nifa kin dameni, haba, gori zaki min don ina zaune a gidan Mijinki? To karki damu i'm leaving and never coming back, dama son Zaid ne da burin samun Shi ya sa ni zama a gidan nan all this while, amma naga banda chance din samunshi kwatakwata bana gaban shi, to banga amfanin zamana a gidan nan ba, bayan inada Sugar daddies din da zasu ingata rayuwa na da kuruciyata, da kyau na, na hakura da Zaid, ba zan lallace kanshi ba bayan inada Future , so zamana a gidan nan be da amfani" ta juya da sauri saude tace "No No Meema donAllah Dont Go, dont leave me like this, i need you now more than ever, you are the only one i have left, kema ni kadai gareki, pleaee kar ki tafi" Meema ta kalleta a tsaye tace "Sorry sis, i cant do anything for you" Aneesa tace "Aunt Mee, you are leaving? Why?" Meena ta daga kafada tace "Anee take care of your Sis, ni na shiga dunia, i'll come back when i acheived what your Mom wasnt able to Acheive" ta banga k'ofa ta fita, Saude ta rushe da wani irin kuka, Aneesa ta karasa gunta don lallashi..
******
"Saude kin hada min kudina ko kuwa?" jiki na rawa tace "Kayi hakuri i need more time" da tsawa yace "I dont have any time left, once 2 yayi clocking it would be the end of me, and you are my last hope, so i ask You nicely ina zanzo in karbi kudina?" cike da tausayin kanta tace "Mak'ale, inada ATM's biyar, ina jin kudin cikin duka zasu kai 400k, ga Sark'a na da yan kunne sai a saida, na san zasuyi 500k, in aka harhada nasan zasuyi 1million, ina kuma da Gona duk sai in baka ka har hada" Mak'ale yayi Murmushi yace "Good Girl, yanzu kikawo min, ina ta wurin Magama" Saude ta fashe da kuka yace yadai? Tace "Mak'ale banda k'afa, k'afa ta daya, an gundule dayan?" cikin halin ko in kula yace "Really? Yanzu ki ba Meema kayan kawai ta kawo mun" "Meema left me Jiya" haan to ya zaayi? "Ya zan samu kaya na ne? Ina diyarki?" da sauri tace "keep my daughter outof this" "So tell me how can i get my Shit?" tace "Shi nake tunani ni idan na fito they'll be suspicious" yace "i'll come get it" tace "no you cant come over" yace "like you have an option, nagaya miki need to get the whole shit kafin 2, and this is past 12, the earlier the better, if you are worried i'll be caught kar ki manta waye mak'ale, i'll gt everything under control like always, ki tuna duk aikin da kika sani bantaba failing dinki ba, so dont worry i gt my ways" ba dan hankalinta ya kwanta ba tace "Ok".
*******
Dawowar shi daga School kenan, a gajiye yake don a yau ya ga Project dinshi, Cikin gida ya shiga, ba kowa a Parlorn k'asa Sai Saude da mak'ale yace ta harhada mai komai gashi nan zuwa, ganin Rafeeq a wannan lokacin ya tada mata hankali, amma ganin be nuna ya ganta ba ya sata dan kwantas, hayewa sama yayi yana kiran "Mam".
Doguwar riga jallabiya ce jikin Mak'ale, yayi rolling da gyale, ya k'wama bakin glass wanda ya mamaye fuskar sa, ba ka taba gane shigar maza yayi, a bakin gate yace da Baba Maigadi suna ciki? Yace " Hajia babba ko karamar? A takaice yace babbar yace eh ta na nan, Makale ya shiga gidan yana taku kamar mace, kai tsaye Saude tace tana Parlorn kasa da ya shigo zai ganta, kawai sai ya amsa ya ware, a saukake batare da kowa ya ganshi ba, kan Mak'ale a kasa ya shiga, ko magana basuyi da Saude ba ya amsa k'aton Envelop din hannunta ya juya ya fita, Saude ta sake ajiyar Zuciya ganin ba wanda ya ganshi har ya bar Parlorn, a ranta tana tunanin dabara irin ta mak'ale.
Da sauri sauri Makale ke tafiya a farfajiyar gidan, karaf ya ci karo da wani abu, ko da ya dago wata tsohuwa ya gani, Nene ta yashe Baki tace "ikon Allah, saurin me kikeyi ne haka da baki kallan gabanki in kina tafia? Iye? Makale ya sadda kai, Nene tace" ko da yake ya zaki ga gabanki bayan sanye kike da wannan bakin tabarau din?". Daddy da Uncle Zaid suka shigo gidan dama tare suke da Nene ta dai riga su shigowa inda sukuma suka tsaya a waje suna dan magana, daga gidan Nene suke, su ne dubo Ginin ne, A k'asa sukaje. A lokacin kuma Fitowar Rafeeq kenan daga cikin gida, ya sa Mamin shi dafa mai indomie, ya ga Nene na ma wata Mita, tsaki kawai yayi yace "this woman, she annoys everyone, har bak'in ma bata barsu
ba" yayi hanyar Dakinshi ya ga Rigimar Nene wai sai ta cire gilashin Matar nan, ya tsaya ganin ikom Allah wannan karfin halin Nene na bashi mamaki, ina ruwanta da Glass din da matar ta saka? Makale na dan karewa ba dama ya sa hannu ya bangaje Nene don kayan dake hannunshi, Nene ta ci nasarar cire Glass din fuskar Mak'ale.Nene na daria tace"Diyata ya na ga fuskarki kamar ta gardi?"
Fuskar da bazai ta6a mantawa ba ko anyi shekara dubu, fuskar da ta jefa rayuwarshi cikin Garari, Fuskar da ta sashi cikin K'unci da Ukubar Rayuwa. Tafia yake be ganin gabanshi idonshi a rufe, ba abunda yake gani sai bakar ranar da bazai taba mantawa ba, komai ya dawo mai sabo, ba su san da zuwan shi ba, sai da Mak'ale yaji an rike mai k'ugu anyaye gyalen kanshi, Nene ta dan daka tsalle tayi baya tare da karanto "Summa Alaiyna bayana" na shiga uku me zan gani haka? Gardi da shigar Mata, Idon ryafeeq ya kada yayi Jazir, tabbas shine, aiko Mak'ale ya zubda kayan hannunshi zai Arta a guje Rafeeq ya damk'o shi ya sauke mai nushi, Nene tace "Barawo ne ko dunkum? Ci Uwarshi Wallahi" Alhaji Habib daUncle Zaid suka karaso, "Rafeeq meye haka?" Rafeeq be bashi amsa ba Alhaji Habib ya hada ido da Mak'ale, baki na rawa Ya nuna shi da yatsa "me kakeyi anan?" Mak'ale ya kaima Rafeea Nushi, da sauri Rafeeq ya cikashi shi kuma ya zabura zai gudu, Nene ta hango dan gatarin da kwanaki taso ladabatar da dunkum a gefe da sauri ta dauko ta wurga ma Mak'ale, cikin saa ta sameshi a Bayan kai, Mak'ale ya zube a k'asa, Rafeeq na is gunshi kamar ance ya sa hannu a bayan wandon Makale, yana sawa kuwa sai ga Bindiga.
*******
Baba Maigadi yazo da Igiyar Shanya, aka daure Mak'ale tsaf, Rafeeq ya shiga dukkanshi, Alhaji Habib ya kira jamian Tsaro, Rafeeq yayi tsaki yace "we dont have time for this, ya shak'o wuyan Mak'ale, "Uban me kakeyi a dakin Mamina 3/12/2014?" Mak'ale yayi shiru, tare da kawar da kai gefe" Daddy yace "ka bamu amsa kafin police suzo, sukazo ba zakaji da dadi ba" Mak'ale ya ki magana, Nene ta kwala mai wannan gatarin a taakiyar ka, tace kana magana ko sai na rotsa ka?" Mamakin tskhuwar nan yake, anya Mace ce kuwa, wani riko da ta mai dazu ya zata kattai suka kamashi. Akai akai mak'ale yayi magana yayi shiru, Zuciyya taci Rafeeq ya zaro bindigar Mak'ale ya nunashi da ita, yace "Iswear to God, ka fadamin me kake yi ranar a Dakin Mami na kuma waya saka ko in harbeka" a tsorace Zaid yace "Feeq, calmdown hand the gun over" Rafeeq yace "tell me or i shoot" Mak'ale yayi murmushi yace " You cannot shoot me Boy" "İ Am no Boy, i am Rafeeq Freeking Lema" Rafeeq ya saita kafar Mak'ale ya harba ji kake tasssss, İhu Nene ta sake, Mami da ke kitchen tayi salati tare da kashe gas ta sauko, Aneesa a kidime ta firo daga dakinta tayi kasa Gaban Saude ya yanke ya fadi, what the hell just happened? Gabanta na dukan chalugude ta lek'a window abunda idonta ya gane mata ne yasa ta sakin fitsari, shikenan "Asirinta ya tonu, ya zatayi? Mafitar ta daya, ta bar gidan kafin su ankara da ita, Crutches dinta ta hau dogarawa cikin sanda ta hau saukowa, inshaAllah kafin Mak'ale yayi wata magana ta bar gidan.
Mami Ta tsure ganin Rafeeq yayi harbin, burinta taje ta kwace bindigar hannushi da yake sake kokarin harbin wani, Daddy ya janyeta ya rungume.
Rafeeq ya saita zuciyar Makale "Dont underestimate me,Tell me now or i wont miss your Heart, start talking" cikin jin zafi da Azaba Mak'ale ya fara magana "Sauda ce, Sauda ce, itace ta sa mata magani a drink dinta tayi bacci, ni kuma na shigo dakin nayi acting kamar wani abu ya shiga tsakanin mu, itace ta sani, itace ta sani na kawo mata poison don ta sama yaran mijinta har macen ta mutu, itace ta sa na Kashe Hafiz Lema, itace ta sani na sa ma wani Gida wuta last 2months, itace..... "İnallilahi wa ina ilaihir rajiun kawai kakeji" kuka Mami, Aneesa, Uncle Zaid da Daddy keyi Sosai banda Rafeeq da idonshi ya k'ekashe, "Jaruban chan" cewar Nene.
Cikin karaji Rafeeq yace "Saudeeeeee yau zan kasheki da hannuna" murya na rawa Aneesa tace "Yaya Rafeeq, Yaya Rafeeq, ga Saude chan, gata chan zata gudu" dum a tare suka kalli hanyar gate, ashe suna tsaye ta zo ta wuce ta gabansu, gashi har ta bar gidan, da gundulelen kafarta take cilla kafar da crutches tana tafia sauri sauri, Rafeeq ya danna a guje Mami na kwala mai kira ko waigiwa beyi ba, Mami tace Habibi ku tsaidashi kar yayi kisa donAllah, Zaid kuje, Daddy da Uncle Zaid suka bi Rafeeq a baya.
Kuka takeyi tana dogara Sandarta tana tafia da sauri, daga gefe taga wani Me Keke Napep na fitsari hango makullan tayi jikin Napep din, da sauri ta k'arasa gun Keke Napep din ta shige, ta tada, tayi ribas ta bar gurin a Sittin, Me Napep ya ji Alamun an tada mai Abun Hawa da gudu ya zira wandon shi, kafin yayi aune sai gani yayi wata mata Me k'afa daya ta sace mai Machine" Jamaa ku taimakeni ta sacen a daidaita sahu" Rafeeq ya karaso ya shiga halbin tayar Napep dinnan amma ina be sameta ba, ya harbi iska da hannunshi, dan Achaba ya tsaida, shima ya janye shi ya wurgar dashi a kasa ya hau kan Machine din ya burka ya bi bayan Saude Mai Keke Napep.(Lols)

_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

(Afuwan Habibties, Ina k'ara baku hakuri a kan rashin jina da kukeyi akai akai, Makarata ke boyeni wallahi, karatu ya fara Zafi, i spend more time in School than in House, nima na k'agara na gama wallahi, So ku cigaba da hakurin da kukeyi dani, Nagode, Saura Cinguli👌🏼)

Pg5⃣8⃣

Wuta kawai Saude ke ba ma Napep dinnan, ita kanta tana Mamakin yanda take Sarrafa Napep dinnan, ta madubi ta hango Rafeeq na binta a acha6a, sosai ta k'ara gudu, Abun ya ba Rafeeq mamaki me k'afa daya da Jan Napep haka shima ya kara gudu, Round din dandagoro(hanyar Barin Katsina)Saude tasha inda tayi tafia kadan kafin ta fita daga cikin Katsina, Relay sukeyi sosai ita da Feeq, har sai da suka bar Katsinar baki daya, Jamaan Annabi sai binta sukeyi da Kallo, wasu suce ko Lafiya?, ganin zata mai nisa ne ya sa shi k'ure gudun babur dinnan, a lokacin sun bar gurin taron Mutanen, cikin ikonAllah ya kamo Saude, aikuwa ganin hakan yasa ta fita daga Napep din tana neman guduwa, daidai wani Kango take nufa, Rafeeq ya sauka daga kan Machine din, ya bita a baya, to k'arfi ba daya ba, gata da k'afa guda, nan da nan Rafeeq ya isketa. Cikin Saude ya kada, ta kalli Gabas da Yamma, bata ga halitta ko daya ba, tasan tata ta k'are bata ga ko digon imani a idon Rafeeq ba, tasan kasheta zaiyi, yana ko Chapkota ya wanketa da Marin da bata taba tunanin a iya rayuwarta wani ya taba mata irin shi ba, yace "Wannan na Mamin mu ne" ba ta gama tunani ba ta sake jin wani Mari a dayan kumatun yace "This is for Rafee'ah" ya kai mata Nushi a ciki yace "This one too, is for Rafee'ah" ya kwashe kafarta ta zube a k'asa, ta saki ihu sanda gulalliyar k'afar ta daki k'asa, yace "Wannan ma na Rafee'ah ne" ya zaro Bindiga daga cikin Aljihun shi ya saita kanta dashi yace "And this one also is for her" Tsuuu Saude take Fitsari, yau ta hango k'abarinta, baki na rawa jiki na 6ari ga Azabar da takeji a jikinta, tana kuka ta ke cewa "Kayi man Rai Rafeeq, kuyi hak'uri ka gafarceni" Idonshi ya rina yayi Ja, wannan Family is the First and the Last Family da zakiyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login