Showing 48001 words to 51000 words out of 149166 words

Chapter 17 - Ke alkhairi ce COMPLETE HAUSA NOVEL

BIEBIE   

22 Oct 2024

25724

sauri ta rik'o hannun shi har cikin Gida, tace da Nasiba "ke dauko Tabarma ko darduma" da sauri ta dauko ta shimfida mai, "Zaidu Sannu da Zuwa, kazo lafiya?" Nasiba dai ta bisu da kallo, tana ta kallon ikon Allah yanda Zaid da Nene suke ta labartawa, "Nasiba baki san shi ba ko?" ai Shine Zaidu bawan Allahn da bakina ya kasa daina ambaton shi, wanda ya taimaka mana randa muka kusa Gobara, Nasiba tayi murmushi tace "Allah Sarki, Nene ta bani labarin abun da ya faru, Mungode da taimakon da ka mana, Allah ya saka maka da Alheri" har ranshi yaji dadin adduarta gareshi, yace ai Seebi mun taba haduwa kece dai ba ki gane ni ba" tace "ni? A ina?" yace wata rana ba a wuce Sati 2 ba, na dauko daga wajen Umaru Musa, na a je kawarku wurin Motel, ku biyu kuma kukace in sauke ku a Salamah, kin tuna? Nasiba ta zaro ido, Tabbas kaine, na tuna, dama nima ina ta tunanin inda na sanka, nan fira ya barke, idan kaga Nasiba, Zaid, da Nene na fira sai ka rantse sun dade da sanin juna, Nasibar da ta ke da wuyar sabo, bata da saurin sabo, sai gashi nan da nan taji ta sake da Zaid, haka kurum taji Zaid ya samu gurbi babba a zuciyar ta. Sai da Zaid yaci Burabiskon Da Nene tayi kafin ya musu Sallama ya wuce Gidan Yayan shi.

"Assalam Alaikum" bakin shi kadai ya kalla ya san ya amsa Sallamar, da ka kalleshi ka san yaji dadin ganin Zaid, amma ya kasa nunawa, Zaid dai ya Zauna, yace "R-Lema" da k'yar Rafeeq yace "Sannu da Zuwa?"" yauwa Rafeeq ya kake? Ya skul? Sai da ya dauke shi Seconds kafin yace "Alhamdulilah" "Kaci abinci?" kai kawai ya daga mai tare da nuna mai Ledan take away din da yayi a Crispy. Zaid ya jinjina kai yace "akwai wata matsala? Ko akwai abunda kake so?" Rafeeq ya girgiza kai alamun aa, Zaid ya mik'e tare da dafa Rafeeq yace "Good" bari in k'arasa cikin Gidan isowa ta kenan, Rafeeq bece komai ba, har sai da Zaid ya kusa barin dakin ya cire baki yace "Ya Rafeeah-Ayman? Zaid ya juyo da murmushi yace "Shes fine, tana Gaida Yayan ta" Murmushin gefen kumatu Rafeeq yayi, ya dauke duban shi daga Zaid don kar ya mishi wata magana da zai bata mai rai (kun dai san Maganar ko? Maganar Mami).

Meema na ganin Zaid da zuro a guje zata rungume shi, da sauri Zaid ya ja gefe yace lafia? Cikin kissa tace "Uncle Zee, naji dadin ganin ka ne, nayi ta kiranka ba ka dauka ba, na Kuma kace mana zaka zo ba, da kyar yace "i was driving" ya yi saurin hayewa Sama don ya k'i jinin Meema, wani irin warin Man bleaching da gashin doki takey tayi. Meema taje ta barbade jikin ta da turaren da boka ya bata, wanda yace "idan har Zaid ya shak'i kamshin, to sai yanda tayi da shi, Zaid juwa ya shiga ya gauda Yayan shi, Sauda na zaune tace " a kawo maka abinci?" ya danyi murmushin yak'e yace "aa Nagode" ta kalli Mijinya cikin Kissa tace "ka ganshi nan Alhaji, ni bansan me na mishi ba be cin abincina, be taba ci ba, haka zai kamo hanya tunda daga Kaduna, amma ko ruwan Gidanka be sha" Zaid ya dan wayance yace "Wallahi sai na cika ciki na kafin nake k'arasowa nan" Alhaji Habib dai ya murmusa yace "kun fi kusa" yauwa Zaid, ya karatun Rafeeq? Kasan idan be ci Exams din nan ba Spilling na 3kenan zaiyi ko?Mates dinshi daga masu Service sai masu Aiki" Zaid yace " Yaya, Rafeeq zaici Exams dinnan da yardan Ubangiji, this is his last year a School, just have faith" Alhaji Habib yace "Allah shi yarda" Sauda a ranta tace "sai mu gani" Zaid ya musu Sallama ya sauko k'asa.
Meema na ganinshi ta k'araso, Da sauri Zaid ya toshe hancin shi saboda wani irin warin tashina hankali da ya ziyarcin hancin shi, Meema meye ke wari haka kamar Jab'a?" tace "Jaba kuma?" Zaid yace "sai anjima idan na tsaya a nan Kaina zai min ciwo" da sauri ya bar gurin takaici ya hana Meema bincshi, wai ita ke warin Jab'ar ko turaren? Ta fashe da wani kuka mai tsuma rai.

*UMYU KATSINA*

Jugum jugum sukayi suna neman mafita, Awan su 3 a Library, suna neman yanda zasu yi Solving wannan Assignment dinsu na Calculus, gashi 5 ta wuce, gashi da Sassafe karfe 8 zaayi Individual Submission a Office din Course tutor, kuma yace idan suka kwafa na juna zai gane, Ana tsoron Malamin da Course dinshi kasancewar dangin Maths ne, ana samun Carry Over da yawa, hankalin daliban da keyi a tashe, ko wannen su ya dage yana iyakar k'ok'arin shi, gashi 5 har ta wuce, ba yanda Miemee Usheey da Seebi zasuyi illa su wuce Gida don Maghrib ta k'arato, Miemee tace zata ba lesson teacher din k'annenta ya mata Solving, Usheey kuma tace " Zata duba cikin Note book din brother dinta shima yayi Course din lastyear, idan Allah ya sota ta samu, Nasiba da idon ta ya ciko ruwa ta kasa magana, don bata da wata mafita, ta tsani CarryOver amma ta sadakas ta fadi course dinnan, dole sai ya dawo mata Next Year. haka suka wuce Gida.

K'arfe 7 Zaid ya Shigo Gidan, tunda ta gaishe shi bata sake magana ba ta cigaba da Kallon Takardanta kamar ansa zai fito, Zaid ya zauna kusa da Nene, yace "yau Seebi boko ake ta sha? Yau ba a ma Nene Fira?" Nene tace rabu da ita 'yar nema, ka ganta nan tun dazun nake ta magana ta min banza, tunda ta dawo take ta rubuce rubuce tana yaga takarda, ko abincin kirki ta kasa ci, shine kagan mu zugum zugum kamar kurma, ina ta Addua Allah ya kawo mun kai. Yayu daria, yace "Seebi Assignment ne halan?" tace "Wallahi Uncle Zaid, part of our CA test ne, kuma ban iya ba, tun dazun nake ta solving amma na kasa, yace "mugani" da sauri ta mik'a mai ya bude baki "lalala, Calculus, tabdi, ai ko lokacin da mukayi Calculus da k'yar nayi passing course din yanzu ko ko kasheni zaayi ba zan iya cewa ga yanda akeyi ba" hawayen da take makalewa suka gangaro, Zaid kadai ne hope dinta, gashi shima be iya ba, Zaid ya lura da yanayin da ta shiga yace "yaushe zaayi Submitting? ta fashe da kuka, Zaid ya rude yace " Calm down ki kin magana" tace "Gobe da Sassafe before 8, kuma individualy yace don zai gane idan mun kwafa daga junan mu".
Zaid yayi shiru for sometime, wani tunani yazo mai, amma yana gudun abunda zai faru, amma kuma dole ya taimaki Nasiba don tana bukatar taimako shikuma yana da halin taimaka mata, ba tare da tunanin me zai faru ba ya ciro wayar shi ya latso Numbern Rafeeq.

Kamar ba zai daga wayan ba ya dauka ba tare da cewa komai ba, Zaid yace " Hello Son" chan k'asa Rafeeq yace "Yeah" yace "kana Ina?" da kyar yace "gani nan zanje gidan su Maalesh" "donAllah i need your help" Rafeeq yayi saurin cewa "Menene are you ok?"don yaji Uncle sounds so serious, Zaid yace "i'm fine, i need you to come back, daidai kwanar Gida kafin kaje Salamah, Please" be bari yace komai ba ya kashe wayar shi ya na rok'on Allah ya sa yazo" Nasiba ta tsare shi da idanuwa, yace "Nephew dina ne, ina ganin Zai iya miki Solving problem dinki" Dadi ya lullube Nasiba, Mintuna 45 suka shude, ba Rafeeq ba alamun shi, Nasiba ta damu kwarai, Zaid kuwa ya cire rai da zuwan Rafeeq, don har yace ta miko mai ya gani yayi trying solving din. Kirrrrrr Wayar Zaid tayi Ringing, da sauri ya dauka ganin Rafeeq, "Hello" Chan k'asa yace "Nazo kwatacen" da sauri Zaid ya zura takalma yace gani nan fitowa.

Daga nesa ya ga Rafeeq, da sauri ya k'arasa gunshi, "Rafeeq thanks for coming" Rafeeq be ce mai komai ba illa binshi da yayi da ido, alamun ka min bayani, Zaid kuwa yak'i cewa komai don ya san Halin Rafeeq, yana iya ce mai wata zaiyiwa Assignment yace ba zaiyi ba ko kuma yace be iya ba k'arshe ya tafi ya barshi, shiyasa Zaid be ce komai anan ba, k'ila idan a chan ne yaji kunyar Nene da Nasiba ya mata, duk da ya san ranshi sai ya baci, yace "please ka biyoni, ganin asarar cewa ina zamu?ko me zanyi? Yasa Rafeeq bin Zaid a baya ba tare da ya ce uffan ba, har Soron Gidan Nene, Zaid yayi Sallama, cikiciki Rafeeq yayi Sallaman shima Nene ta amsa, Zaid na gaba Rafeeq na biye dashi kan shi a k'asa, Nasiba na ganin R-Lema tayi Zumbur ta tashi tsaye, Nene tace "Lahh Zaidu Bawan Allah, wanene wannan me kama da kai?" kallo ba ta ishe Rafeeq ba, Zaid yace "Rafeeq ba ka gaida Nene ba" ba tare da ya kalleta ba yace "ina wuni"ciki ciki Nene ta amsa tana mai wasa, dauke kai yayi ya sauke shi kan Nasiba, kallo daya ya mata ya dauke kamar be taba ganin me irin halittar ta ba, Rafeeq da ya k'osa yaji me ye amfanin zuwan shi gidan nan ya kalli Zaid cikin tuhuma, Zaid ya k'i yarda su hada ido, don yasan shi yake kallo, ba tare da ya kalli Rafeeq ba yace "Son, Assignment ne ya gaggari Seebi, nima na gwada tawa fasahar na kasa, nasan you are in good in Calculus, shine nace bari in kiraka ka taimaka mata DonAllah" Waiyo Allah kuzo ku ga bakinciki kwance kan fuskar Rafeeq ji yake kamar ya dora hannu a kai ya sa ihu saboda takaici, wai me ya sa Uncle Zaid ke mishi hakane? Zaid kuwa har yanzun ya ki kallon Rafeeq din balle ya san halin da yake ciki, "I am sorry" ya furta a hankali don ya san Rafeeq din shi yake kallo.
(Readers me kuke ganin Rafeeq zaiyi? K'ila tafiar shi zai yi ba tare da yace musu komai ba, don da Alamu Uncle Zaid ya gama kashe Rafeeq)

_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

Pg3⃣4⃣

Kusan Mintinu Biyu Rafeeq na tsaye, shi be ce komai ba shi be tafi ba, Nasiba ba tayi mamaki ba, don ta san halin Rafeeq na shariya da k'yaliya, Nene kuwa ido ta sa ma Rafeeq ta kasa gane me ke shirin faruwa, har Yanzu idon Zaid na kallon Gefe, Rafeeq da takaici ya gama rufe shi ya hau tunani, tabbas da wani ya mai abunda Uncle Zaid ya mishi da ba abun da zai hanashi barin gurin, Amma Uncle Zaid ne, ya fi K'arfin Wulakanci a gunshi, ajiyar zuciya yayi ya mik'a ma Nasiba hannu kamar me rok'o, Nasiba tace me zan baka? Rafeeq ya dan yi guntun tsaki, Zaid yayi saurin kallon su yace da Nasiba "bashi question Paper din, da sauri ya dauko ta bashi, ya amsa ya karanta, a ranshi ya yi tsaki yace Question din is straight forward, i dont knw why some people are dumb, ba su san komai ba, ji wannan simple Question din,(ni bibi nace ba kowa bane kamar ka ba dan rainin wayau) wata zuciyar tace harda Uncle Zaid fa, a ranshi yayi dariya, amma a baiyane fuskar nan tamk'e tamau.
Kan tabarman ya hau, ya ciro biro cikin wandon shi, ya duk'a ya fara solving question din, tunda ya fara rubutu be dago ba sai da ya gama, yana gamawa kuma ya mik'e ya zira takalman shi ya bar Gidan. Zaid ya bishi da sauri, Nene da Nasiba suka bishi da ido, ita Nene Mamakin Wannan yaron Zaidu BawanAllah take, a ranta tace ko kurma ne? Nasiba kuwa Mamakin da takeyi yanda tafi Awa 5 tana kokarin yin wannan Assignment din ta kasa, amma shi cikin mintinan da basu wuce 7 ya gama komai, lallai ta jinjina mai, shiru-shirun shi ba a banza ba tunda ya san abunda yakeyi, haka kurum taji Rafeeq ya burgeta, ta durkusa ta dauki Papern, rubutunshi ta bi fa ido, neatly kamar irin rubutun Computer, tabi steps din da yabi, taga abun very clear, kawai sai ta tsinci kanta da Murmushi a hankali ta furta R-Lema. Nene da ta zuba mata ido, tace "Toooooooh, ke kuma gamo kikayi? Nasiba ta fashe da daria.

Ko da ya fito har Rafeeq ya kai bakin motar shi, Zaid yace "Rafeeq" chak ya tsaya ba tare da ya juyo ba, Zaid ya iso har gabanshi yace "ka saurareni, nasan na maka laifi, na maka karambani, kayi hak'uri" dan guntun tsaki Rafeeq yayi ba dan komai ba don Zaid zai sa shi magana yace "ka isa da ni ne, bakomai, stop apologising" ya shige mota ya ja ya bar Zaid tsaye, Zaid kuwa dadi ne ya lullube shi, lallai Rafeeq is improving, shi a zaton shi fushi zaiyi dashi, amma Rafeeq ya bashi mamaki kuma yaji dadi, a ranshi yace"Allah ka kawo ma Rafeeq Sauyi" ya juya ya koma gidan Nene. Ya na shiga Nene ta tare shi da maganar Rafeeq, "Nace Zaidu Bawan Allah, shi wannan fa?" Zaid yace "Dan Yaya na ne" Nene tace baya magana ne? Ko kurma ne? Zaid yayi murmushi yace "yana Magana" Nene tace "to ya na ganshi haka kamar wani Zararre, ji uban gashin da ya ajiye, ko ni Mace ya fini, shi ko bai da lafiya ne?" Nasiba ta kasa kunne don jin me Zaid zaice don ta na san sanni meyasa Rafeeq yake haka, Zaid yace "haka yake, miskili ne" Nene ta jinjina kai tace "Lallai kam naga Alama, Shekaru na 68 ban taba ganin Miskili kamar shi ba, ya ci a bashi Sarkin Miskilai" Daria sukayi duka, Nene tace "Bari in tashi in zubo maka Tuwon Masara miyan kuka da na dafa maka" Zaid yayi murmushi yace "yauwa Nenen mu ni da seebi kadai".
_Bayan kwanaki Biyar_.

*UMYU Katsina*

"Nasiba Muhammad, MCB 1220" Gabanta ya buga ya fadi a lokacin da Course Tutor ya sake kiran sunanta a karo na biyu, a hankali Miemee tace "Seebi ke fa ya ke kira" jikinta ya hau rawa sosai, idonta ya ciciko da hawaye, ai ba inda zataje, kuce bata zo ba tunda ba sani na yayi ba, cikin karaji lecturer yace "Where is Nasiba1220?" bata san lokacin da ta mik'e tsaye ba saboda ya firgita ta sosai, yace "are you Nasiba?" kai ta daga alamun eh, yace come down here, gabanta ya tsananta faduwa, bata san me tayi ba, k'ila batayi assignment din ta da kyau ba, jiki na rawa take tafia, all eyes on her, haka ta daure ta karada gaban stage, karo na farko da ta fara missing Nikabin ta, ta tsaya gabanshi, ya mika mata Marker bayan Yayi copying Question din da ya basu, yace "solve this"Nasiba tayi Adduoin ta ta fara rubutu kan Board, dama tayi mastering Solution din da Rafeeq ya mata, har sai da ta gama komai, Lecturer ya ciro scripts dinta ya mik'a mata, ta amsa ido ta zaro, *20/20* tagani murna ya ziyarce ta, yace "give her a round of applause" Aji ya kaure da tafi raf raf raf. Yace shes the only one that scored 20/20 apart frm her none of you made it to 15/20, am proud of you" A hankali tace "thank you sir" ya zaro 2000 a aljihu yace "have this" da sauri tace "no sir, you dont have to This" ya tsare ta da idanuwa ta amsa tayi godia, aji suka tafa mata, kamar ance ta lek'a window, tana lekawa ta ga Rafeeq ya zo wucewa, ta kalli Lecturerr tace "excuse me please sir" da murmushi yace Goon my dear, da sauri ta fita daga Ajin, sauri sauri, gudu gudu ta cimma shi don ta san ko kiranshi tayi ba zai juyo ba ga idon mutane a gurin, sai da tazo gab dashi ta mai Sallama, kamar ba zai tsaya ba ya tsaya tarw da juyowa, suna hada ido cikin in ina tace "Erhm, dama ina son yi maka Godia ne, anyi Marking scripts kuma nikadai naci 20/20" ta karasa tare da mika mai takardan hannun ta, ido ya tsareta da shi, ba tare da ya kalli papern ba ya juya zaiyi tafian shi, da sauri tace "Nagode Allah ya saka da Alheri, Allah ya kara basira" Chak ya tsaya, ita kuma ta juya ta ta fi, da sauri ya juyo amma har tayi gaba, ya dade rabon da yaji shi cikin Wannan yanayin, a hankali ya furta *"Me ke faruwa*?"

*MAFARKI*

"Baiwar Allah", taji wata zazzakar murya tayi kiranta, Nasiba ta juyo ta kalleta,sanye take da fararan kaya masu alfarma, fuskarta sai kyalli, tace "donAllah taimako nake so ki min, idan kika taimaka min Allah zai taimake ki, Nasiba tace wani irin taimako kike so in miki? Tace "wallah, bashi naci a wani Shago, wata rana na je siyan lemo lacasera, na bada dubu aka ce ba chanji, in tafi idan na samu na kawo, toh har yau Allah beyi na kai ba, yanzu kuma nayi nisan da ba zan iya dawowa in ba mai shago hakkinshi ba, ki taimake ni ki kai mai Nera 120, kinsan Allah na yafe hakkin komai banda hakkin mutim, Nasiba tace " bakomai, a wani shago ne?" tace " Masanawa Supermarket,Umaru Musa" toh InshaAllah zan biya miki, to ya sunanki? Don yanda zanma mai shago bayani" tace karki damu, kedai kawai ki bada da niyyar ni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login