Showing 72001 words to 75000 words out of 149166 words

Chapter 25 - Ke alkhairi ce COMPLETE HAUSA NOVEL

BIEBIE   

22 Oct 2024

25721

ina da matsala" Seebi ta gane da Rafeeq take, da Sauri tace "shi yazo?" tace "tun tafiar ki kullum sai yazo, ya tasani gaba yayi ta kallo kamar Tb, shine zai ceman wai ina da matsala, ai wallahi da ya tsaya da sai na bubbuge shi" Nasiba ta shiga tunani a ranta tace "Allah sarki Hamma, ni yake nema, i made a mistake da ban sanar dashi zanzo Kd ba" Nene tace sai ki man shiru? Dallah bani Uwar taki mu gaisa" da sauri tace "Ahh Nene ga Ummin ba sai kin zaga man Uwa ba". Daria Ummi keyi ta amsa wayar suka gaisa da Nene. Seebi kuwa ta tashi ta fada gidan Mami.

_Malali Kaduna_

Haka Nasiba zata zauna tayi ta ba Mami labarin Rafeeq, wani zubin taji tausayin shi wani zubin tayi daria, kamar yanzu Nasiba ta bata labarin Dramar Nene da Rafeeq, Mami tayi dariya harda k'walla, tace "ai Nene ce daidai shi" tana burgeni, Seebi tace "ai haka mutane ke cewa, wai Nene na na burge su, don dai basu zauna da ita bane, da tuni ta gudire su, Nene is very Annoying Wallahi, don dai kawai tana da ban daria, amma kwana daya zaki yi da ita duk zakiji ta isheki" Mami tace "ba wani nan, ni dai ba zata ishe ni ba" Seebi tace "hmm, wallahi Mami ba zaki gane ba" wayar Mami tayi ringing, Nasiba ta je ta dauko mata kan dining, Zaid England ne ya fito a Screen, Nasiba tace "Mami ga Uncle Zaid" Mami tace dauka mu rudar dashi" Seebi ta dauka wayan "Assalam Alaikum Uncle Zaid" da sauri Zaid ya duba Screen din wayan ya ga dai Mami ya kira, to ya yake jin muryan Seebin Nene? To ko kiran ya yi roaming ne ya koma numbern Seebi? Tambayoyi da dama, da k'yar ya Amsa Sallama, yace "Seebin mu nida Nene" tace "lahh ya akayi ka gane?" "your voice is always on my head, ba zan taba manta da voice dinki ba" taji kunyar maganar shi amma sai tace "arent you suprised? Ba number na ka kira ba fa? Zaid ya tashi zaune yace "Noo way" tace "Yes Way, bari ma ka gani" ta mik'a ma Mami wayan ta mata alama da bara taje gida ta dawo, Mami ta amsa tana Daria, yace "Mami how is this possible? You met Nasiba?" tace "Ehmana, what makes you think i wont find my Sister Inlaw? Or ince daughter na, don diyata ce, kai ne siriki na" yace "shhh Mami kar ta jiki" tace "kar ka damu ta je gida, mak'otan mu ne, Yayan Anan" da mamaki yace "dama Nasiba yayan Anan ce?" tace "iko na Allah" yace to Mami ya akai kuka saba da juna haka? Mami ta kwashe labarin da Nasiba ta bata duk da briefly ta bashi, labarin da shi kanshi Zaid be sani ba, ya jinjina kai, Mami tace "Wallahi Zaid baka ga yanda take son Ayman ba, yanzu haka tana bayanta ta goya ta" Dadi ya lullube Zaid, duk me son shi, to ya so Diyar shi, nan ya ba Nasiba wani matsayi a zuciyar shi, Mami tace "Allah ya sa yanda take son Ayman ta so babanta, ko da yake dan k'anina haծaծծe ne, ba macen da zata k'i shi" daria Zaid yayi yace "easy dai, sai na dawo zan sanar da ita _sirrin dake raina_" tace "sai ka dawo, yanzu sai yaushe?" yace "don sun raina mu sun k'ara mana additional 2weeks, sai next month in Allah ya yarda" toh Allah ya yarda, nan sukayi fira sukayi Sallama.

*Katsina*
Nene ina kika shige ana ta kira? tace kai dai bari, gani ina ta Soya Farar da Anan yace a soya mai in ka dawo da Seebi in baka ka kaimai" Abbi yace "kema dai Nene, sai ki biye ma Anan don yace yana son Fara, shi yanzu haka ya mance" tace "Tiya biyu na siyo mai, baka ga bak'ar wahalar da naci a kasuwa ba, kuma ina dawowa na gyara ta, yanzu har na soya tiya daya, gani ina soya gudan tiyar" Abbi yace "Taya b'era b'ari".
Yau be jira amsan Sallamar ta ba ya shigo ciki, sakamakon wani k'amshin da yaji, ya na tunanin k'amshin meye wannan? Wannan dai ya fi karfin suyan kaza, tana waya ta ganshi tsaye, tace " yau kuma Sallamar da akeyi k'asa k'asa baa samu damar yi ba? Ko muryar ce ta ida daukewa? Ni tashi min akai ga kujera chan" Abii yace "Nene ke da waye?" tace "ni da Dunkum" "wanene kuma Dunkum?" tace "ka tambayi Seebi waye Dunkum dangin Tsaka" Inaaaa Sam Rafeeq be san tana yi ba, hankalin shi na kan Soyayar Farar da ke cikin gwagwa, ya hadiye wani mugun miyau kamar tsohon maye, rabonshi da Fara shekari sun fi 10, tun suna zuwa Islamiyya, nan Rafee'ah zata siyo musu, suyi taci, har Farar dari 2 suke siya, haka kurum yaji yana son cin Farar nan, ko don tuna baya, yana son cin farar nan for times sake, kuma dai yana so. Nene ta sauke kaskon ta hadeshi da na gwagwan, tana dagowa taga idon Rafeeq tsam kan gwagwar Fara wani shu'umin Murmushi tayi, a ranta tace"Yau ranar Nene ce" Ta dauki soyayyar cinyar farar nan ta sa a baki, ta wani lumshe ido tace "kaii wannan fara zad dadi, kamar kunne na ya tsinke" Rafeeq ya sake hadiye miyau, suna hada ido da Nene yayi saurin shan mur ya dauke kai, a ranta tace "yaro da ni kake zance" ta shige daki ta zauna tana kallon shi ta windo, a ranshi yace "na san wannan tsohuwar ba bani Faran nan zatayi ba, kuma gashi raina ya biya, i want, i will just take it" be tsaya wata wata ba ya durkusa ya dibi guda biyu ya sa a baki, waiyo dadi, yana kara sa hannu yaji an damk'o bayan rigar sa tace "Yihuhu Na chafko shi, na chafko b'arawon fara ta" a hankali yace "Akwai matsala Lord Have Mercy".

_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

Pg4⃣4⃣

Ya dago fuska a daure kamar bai taba dariya ba, ya bi hannunta da ido, yanda ta rik'e mishi bayan riga, a hankali yace da ita "Sakeni" tace "nak'i na sake ka din, nace nak'i" yace "me na miki da zaki rike min riga?" "tambaya kakeyi? To Sata kai man, ka satar min Fara" ya sake tamk'e fuska, wai wani irin Sata?" wanda ka min mana, ai daukan abun da ba naka ba Sata ne, ni kuma ban baka Fara ta ba ka dauka" ya nuna farar da yatsa yace "wanchan abun zanci, Allah ya kiyaye in ci k'waro" tace "Kai Dunkum, ka fita idona, ni da na ganka durkushe, in ba ci min Fara kakeyi ba meyasa zaka durk'usa a gun? Ruku'u kakeyi?" da k'yar yace "da ki ka ganni Durkushe k'andagare na ga zai hau, shine na kore shi, dana sani da na barshi ya hau" tace "Ayiriri nanaye, kai Dunkum ka raina ma kanka wayau ba ni ba, Shekaru na Goma so Shidda da dori (60+) kasan ko ba kalar barikin da ban gani ba, tunda ka ci min Fara ta, ina so ka amsa laifin ka, ka bani hak'uri a wuce wurin" guntun tsaki yayi ya juya zai bar gidan, da sauri ta jawo rigar shi, tace "Sai fa ka ban hakuri" a k'agauce yace"Goodness, Wallahi kina da Damuwa, ga ki da Hayaniya" tace "zaka ga damuwa idan kaji ka a *Jakar Magori*" kallon Rashin Fahimta ya mata, tace "Too, ba ka san Jakar Magori ba ko? No radio a gida? To wurin da zan kai Labarin ka ne, k'arfe 11 dare in ka kunna Radio zakaji ance "Jakaaaar Magori, Dunkum ya Saci Farar Nene a garin Katsina" a ranshi yace "this Woman is Unbelievable, zata aika" ganin idan ya biye mata zasu ta Fafatawa ne, gashi kuma yau ta sashi magana fiye da Sentence 10, kanshi har ya fara ciwo, juyawa yayi zai fita, Nene ta sake Chafko Rigar shi, Tsoki ya buga da k'arfi yana cewa "wai ke wace iri ce?" "sai fa ka bada hakuri"

Daidai nan Maalesh ya shigo da Sallama, Nene na ganin shi tace "Yauwa Maalush, zo kayi Shaida, Dunkum ya min satar Fara" Maalesh da Murmushi kwance kan fuskar shi yace "Nene, ban gane ba?" tace ka tambayi "Dunkum ya maka bayani" ya juya ga Rafeeq ya ga irin rik'on da ta mai kamar wanda ya saci Mota, daria ya kubce mai, yace "Guy howfa? Looks like you've fall into the Old Woman's trap, what did you do?" Rafeeq cikin k'uluwa, yace "Tell her to let go" dak'yar Maaldsh ya sa Nene ta sake Rafeeq, tace " yo Maalush, ci min Fara yayi, kuma ni ban bashi ba, kuma ya k'i yarda ya ban hakuri, ni ko na kamashi kamar na kama Aradu" Maalesh ya fashe da Daria, ya juya ya kalli abun da aka kira da Fara, ya yamutse fuska kamar ya ga kashi, ga kalli Rafeeq da mamakin ta ya ya ci wanchan abun me kama da kyankyaso, yace "you ate that? Rafeeq yace "You are crazier than she is, i cant eat that" kamar ta san abunda yake cewa tayi saurin cewa "Karya yake, a shinshina hannun shi" Maalesh ya shashantar da maganar ta hanyar tambayar Nasiba tace "ai Nasiba kwananta 4 Kaduna Jibi zata dawo" "Lord of Mercy" inji Rafeeq, so All this While Nasiba na Kaduna? Yake bata lokacin shi on this Woman? Yazo ya sha zaman banza amma bata ce mishi Nasiba ba ta nan ba? (Ka tambayeta ne?) dogon tsaki yayi ya fincike mukullin hannun Maalesh ya fita, Nene ta bishi tana dariya tana fadin "Dunkum tsaya kaci Fara, tsaya a k'ulle maka Leda" daria takeyi sosai, don ta san yau tayi maganin Dunkum, Maalesh yayi Dariya, yace "ranshi ya baci, barin je" tace ranshi ne ya baci? To ya sa omo ko kilin ya wanke shi" Maalesh yayi dariya, yace barin je Nene zan dawo Anjima nima iso wata kenan" tace "Allah huta gajiya" ya fita amma be ga komai ba sai k'urar Motar shi, Murmushi yayi ya taka zuwa Gidan Lema a k'afa.

Yana shigowa dakin ya fada Toilet dinsa, Shower ya sakar ma kanshi, tunani kala kala, wai me ke kaishi gidan Nene ne? Zuciyar shi ta bashi amsa da "Kana kewar wannan Yarinyar ne" da sauri yace "Noo, ba ita nake missing ba, i only miss seeing my Sister in her" tsaki yayi yace "stop getting to my head i dont want" haka ya cigaba da magana shi kadai kamar zararre.

*5:00pm*
Zaman kadaici ya ishi Nene, ta rasa yanda zatayi, gashi ita ba gwanar shiga Makota ba, don gidajen makwabtan akwai Karnuka, kuma ai ta k'wank'wasa wa ba a amsa, Wayar Nasiba ta dauko ta kura wa wayar ido tana jira a kirata, shiru, ta na ta 'yan latse latsen ta, bata san ma dai abun da takeyi ba, tsaki ta buga "ina dalilin zaman mutum shi kadai" (Nene ke kika jawo) ta jawo Gyalenta ta fita waje,tana kallon Unguwar, Mugun tsaki ta buga da ta ga Unguwar Wayam ba ko dabban da ke wucewa, Kamar a sama taga wata Mota Me kalar bula(blue) ta doso ta, ai da murna ta fara sa ma Motar Hannu.

Birki na cikin motar su ka ja k'ii, don ba su lura da ita ba, a fusace Meema ta fito, Aneesa ma ta fito, Nene da Murmushin ta tace "Sannunku 'yan jikokina, kuyi hak'uri na tsaida ku, DonAllah ku dan latso min Zaidu bawan Allah a wayar nan" ta na me mik'a musu wayar Nasiba, Meema ta kalli wayar cike da tsana tace "Ke Almajira, in banda jahilci, ba ki sanmu ba zaki tsaida mu kice mu kira miki wani? Har kina daura k'azamin hannun ki kan mota ta?" Aneesa tace "Aunty Mee mu tafi don Allah, irin wannan da su ake conspiring a maka wani mugun abun, its all a ploy" Ta ja hannun Auntyn ta, suka koma Mota, Meema ta ja motar tare da bad'e Nene da k'ura, yanda kuka san Hoto haka Nene ta tsaya, wai yau ita a ka ci ma fuska kuma ba tace komai ba, haushinta daya da ba ta ci uwar babbar su ba, amma a fili tace "Ubangiji Allah ka sake hadani da su" ta koma Cikin Gida tana jin haushin kanta.

*Malali Kaduna*

"Nasiba, kin taba ganin uwar da tayi fushi da danta? ko tayi fushi dashi na wasu lokaci ne, ko me ya ke mata ba za ta tab'a fadin Mummuna kalami a kanshi ba, tsakanin d'a da Mahaifi sai Allah, balle ni da ban taba ganin Laifin Rafeeq ba illa Laifina, nice na sakashi a halin da yake ciki yanzu". Nasiba ta kamo hannun Mami tace "karkiyi Blaming kanki, k'addara ce ta riga Fata, nidai DonAllah kice kawai ki yafe mishi duk da kince be miki komai ba" Mami tayi Murmushi tace "Toh Nasiba, na Yafe ma Rafeeq Duniya da Lahira, na yafe mishi, Ubangiji Allah ya sa ya gama da Duniya lafiya, Allah ya bashi saar karatu, Allah ya ma Rayuwar shi Albarka" da sauri ta Rungume Mami dadi kamar ya kasheta, ita a ganinta zataji Saukin komai tunda Rafeeq na tare da Adduar Mahaifiya, tace "Ameen Mami, ki Cigaba da mishi addua kullum, InshaAllah ba zai tab'a tab'ewa ba" Mami ta tsura wa Nasiba ido cike da k'auna tace "Bless you Daughter, you have an Amazing Heart, Ke Alheri Ce" Murmushi kawai Nasiba tayi, don bata son tayi magana Mami ta cigaba da kukan da takeyi, tace "Mami yaushe zakizo Katsina? Katsina na missing dinki" Murmushi tayi tace "i have no Bussiness left in katsina, Duk Wata Baba na da Mama na su na zuwa duba ni" Nasiba ta sigar zolaya tace " are you sure you have no Bussiness in Katsina? Mahaifarki ce fa, besides, your One and Only Love is there, nasan he still inside that pure heart of yours" Mami ta daburce tana unconditional Murmushi, tace "ke Nasiba maganar me kikeyi haka? Shuttup ni ba kowa a zuciya na, na tsufa" Nasiba tayi dariya tace "Is that so? Then why are you blushing?" Murmushi Mami tayi tace "How i wish zan sake ganin Habibullah" "Awwwn Mami ta tuna da tsohuwar Zuma" tace "Kinsan ana cewa Zaid me kyau ne, Hafiz Me kyau ne, amma Wallahi duk Habib ya fi su kyau, harta Rafeeq da ke kama dashi be kamo k'afar shi ba" Sosai Nasiba tayi daria tace "zai k'ara kyau idan kika koma dakin ki" Mami tace "Hmm nagaji da tsammanin Ranar nan" Nasiba tace "Dont worry Mami,Akwai Allah, gaskiya zata baiyana, zai gano gaskia da na rashin bincike ne ya sa shi daukar mataki take yanke, amma kar ki damu, Have faith" Mami tace "dadi na dake you give me Hope" Sukayi Murmushi, kuma chan sai Mami ta fara matsar k'wallah, Nasiba tace bari in kira miki Nene ki sha dariya.

*Washegari*
Ina Nasibar ne? Sai mun rasa Motar K'arfe 10? Ummi tace "wai ta shiga yi ma Mamin Ayman Sallama yanzu zaka ga ta taho" Abii yace ai gwara tazo mu ta tafiya.
Mami tace "Yanzu ba zaki k'ara mana hutun ba? Kin bari mun saba sosai sai kice zaki wani koma?" tace "Ayyah Mami, nima na saba dake Sosai, idan mun tafi ba zamu dade ba zamu dawo, trust me zan dawo" Mami tace "to shikenan, ga wannan kiyi using as Pocket Money" "Nooo Mami i cant accept your Money" Mami ta tsura mata ido, tace "ni na dauke ki ne a matsayin Rafee'ah, and i can do anything for you, don break my heart" "Mami kudin sunyi yawa ne ki raba biyu" " Haba Nasiba dubu Goma ne fa, ba yawa, inshort why dont you be like Rafee'ah? Be like Mami kudin sun min kadan, i need more" daria Nasiba tayi tace "Okay, I'll accept this Nagode" "Yauwa diyata" tace "One more thing" ta zaro dan karamin Zoben da ke k'aramin yatsar ta ta sa ma Nasiba a yatsa tace "this is my love for you" Nasiba ta bi zoben da kallo, tana so ta tuno inda ta san Zoben, Zoben me kyau ne sosai, kuma Azurfa. Mami tace "kinsan waya bani Zoben Nan?" ta girgiza kai, Mami tace "Rafeeq ya bani shi on my 40th Birthday, Daga Dubai ya sa akayi su Guda 2, ran Birthday na ya sa min a yatsa yace "Mamina, this is my love for you" ya bani gudan yace in sa mishi a, yace "this is the twin of your ring, even if we are far from eachother, this Ring is linked to Our hearts" daria kawai nayi nace dashi"he's Crazy" amna Nasiba yanzu Rafeeq ya tsane ni, nasan Ya dade da wurgar da Zoben shi" Nasiba tace "Aa Mami, wallahi be wurgar dashi ba, yana nan a yatsar shi, ni na san na san Zoben nan a wani wuri, a Yatsar Rafeeq na sanshi" Mami tayi dariya tace"Nasiba kenan, you want me to feel better, shikenan naji, its yours now" Nasiba tace "Aa Mami, wannan naki ne, ki ansa" Mami tace "bansan gardama tashi muje, ni ma zan kai ku tasha, kar ku rasa motan hawa" suka fita tare, a ranta tace "with this Ring Rafeeq, you'll be your Mother's Son Again". Da sauka shiga gida ne ta nuna ma Ummi kudin da Mami ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login