Showing 27001 words to 30000 words out of 149166 words
Numfashi me nauyi, tunda yazo Office ya kasa tab'uka komai, yana tunanin Zancen su da Sauda na jiya, ya na tsoron ta fito masa ta bayan fage,ya na gudun ta ma 'yan uwan shi wani mugun abun, har ranshi yana shakkun Sauda, be gama tunanin shi ba ta turo k'ofa, da Sallama, firgigit ya amsa, zama tayi a kujerar da ke fuskantan shi, tace "Good Morning Baban Aneesa, da fatan kayi baccin da ka dade bakayi ba" Hafiz yace "Sauda, ki bar wannan maganan, i'll pay u ko nawa kike so, just disappear from our lives" tace "sam, hakan ba zai faru ba, Dole ka dau responsibilityn diyar ka, dole ka bata rayuwan farin ciki, dole ka inganta mata rayuwar ta, idan ba haka ba, wallahi ba zaka ji da dadi ba" a dan tsorace yace "me zakiyi" ta yi daria tace "zan kaita gaban Yayan ka, ince ga diyar Hafiz lema, shekaru 16 da suka wuce kayi min fyade, ka ga ko zaka koma gidan jiya, yanuwan ka za su kara tsanan ka, su tsangwame diyar ka, niko ina iya hallaka duk wanda zai tsangwami diyata ko yayi gigin kiranta da Shegiya".
Zufa ya shiga keto ma Hafiz, ba zai so Sauda ta tona mai asiri ba, yana tsoron Sauda ta ma Yanuwan shi wani mugun abu, jikin shi duk yayi sanyi, ya karaya sosai. Hafiz ya ja goron numfashi, yace "Sauda, ni zan aure ki, muyi rayuwar mu da diyar mu tare ba tare da kowa ya san diyata bace, Muyu aure Sauda please" ta fashe da wani mugun daria tace "Hafiz, na fi karfin ka, Wallahi ni ba tsarar ka bace yanzu, yayin ka ya riga da ya wuce, ni Habib Lema nake son aure" Hafiz yace "wai Sauda mesa kike haka ne? Bawan Allahn nan be miki komai ba" ta mik'e tace shikenan, tunda kaki yarda da deal din da na maka offering, bari inje in sanar da su gaskian lamarin, barin fara da uwar dakinku Aisha Lema, tana cikin Office ma yanzu haka"
Cikin zafin nama ya damk'ota yace "aa dan Allah Sauda, kar ki min haka" cikin daga murya tace "ka sake ni" a hankali yace "OK, i will do what you want" tayi murmushin cin nasara tace yauwa ko kai fa, zama tayi tana mai duban shi cikin yanayi na yaudara, ta ciro wani kullin takkarda daga cikin jakkarta ta mik'a mishi, tace "ka sama yayan ka a abinci ko abun sha, make sure ya ci ko ya sha" ya kalleta cikin rashin fahimta, tace Amsa mana ko kana tunanin zan yi poisoning din shi ne? Son shi fa nakeyi, idan ya mutu ya zai aureni? Ba zan taba kashe shi ba coz ina sonshi, so cire wannan tunanin a kanka" ya amsa yace "Sauda, i dont want anyone to get hurt" ta mike ta dauki jakarta tayi hanyar fita, har ta kai bakin k'ofa ta tsaya ta dan kallo shi, tace "noone is getting hurt, i promise".
Haka Hafiz ya dinga juya maganin nan, ya na sak'e sak'e a ranshi.
Daily Tea din da Alhaji Habib ke sha da daddare Mami ta kawo mai, yana karatun Jarida, yace "thank u Shatu na, u ar d best" tayi daria, tace "kafin a min amarya ko?" yayi daria yace "ke kinsan ba wata bayan ke" tace "ahhh bansani ba" ta mik'e tace bari inje in dafa ma Rafeeq ko indomie ce, nasan Rafee'ah ba zata dafa mai ba" "Indomie kuma? Ba abinci ne? tace "kasan yau Taliya akayi" "Assha, ni wannan abu na Rafeeq bangane mai ba, zai ci indomie amma ba zai ci Taliya ba? Toh meye maraban Dambe da Fada?" tayi daria tace ai kai ka shagwaba shi haka" yayi daria yace barin min first Son dina" tayi daria ta shige kicin".
Hafiz ya shigo da Sallama, ya zauna tare da gaida Yayan shi, Yaya Habib yace "Oga Hafiz, ya aikin yau?" yace "Alhamdulilah yaya, Tea zaka sha? Yace eh, as usual, ai nafi 20years ina shan tea duk dare" Hafiz yace "haka ne, nima barin dauko cup inzo mu sha" ya mik'e don zuwa kitchen, ya samu Opportunity ba zai yi watsi da hakan ba, a kitchen ya iske Aishatu, yace ahh Mami Abinci kikeyi?" tace Hafiz an shigo? Wallahi dan rigimar nan nake dafa ma indomie kafin ya shigo gidan" Hafiz yayi daria yace "dan Zaid dan rigima, ina baby na?" tace "tana daki, tana sanaar ta, kasan in ta dauki wayar ta" yace na ma kusa chanza mata waya, Iphone6s, tayi chatting din da kyau" tayi daria yace "ina mugs dinnan nima yau zan bi yaya in sha Shayi?" tace Shayin Ibada,tare da miko mai Kofin tangaran".
Ya faki idanun yayan shi da yake ta duba jarida ya juye maganin nan tas, ya tsiyaya ruwan zafi cikin kofin, yace yaya "bismillah" wai Hafiz kai ka zuba min tea din? Ai da ka bari Maminsu ta zo ta zuba min" yace "no yaya bakomai", shima ya tsiyaya ya zauna suna shan shayi suna Fira.
Asuban ci ta ma Garin Jigawa gun bokan na kan tudu, kasancewar yau Weekend: Bayan ta gama ma boka kirarin da ta saba mishi, tace " na kan tudu aure zanyi" ya kalleta yayi daria yace "naga hakan saude" tace "ai ni nasan akwai nasara, abunda nake so da kai na kan tudu, bana son a samu mishkila, kar ko ya tambayi dalilin ko ba'asin auren nan, kar kowa yace don me, inshort a rufe ma kowa baki kan Auren nan" daria ya tuntsure da, yace "an gama" yayi yan tsubbace tsubbacen shi yace komai daidai ne" ta ciro kudi masu yawa ta dire mishi tare da yin godia.
Hankalin Hafiz ya dan kwanta don yaga kwana biyu har sun wuce ba abunda ya samu Yaya Habib, tabbas kam Sauda ba wani mugun abun zata ma yaya ba.
Ji Yayi kawai ya na son zuwa Office din da matar shi ke aiki, Zuciyar shi na tunzura shi, yace da Driver "mu tafi Office din Madam" Direba Yayi mamakin Umarnin Alhaji, amma be tanka ba yayi Ofishin Madam for the first time da Alhaji.
Alhaji Habib ya fita ya nufi cikin Office din ba tare da yasan me zaiyi a ciki ba, yayi knocking bakin k'ofar Secretary, Sauda da ke ciki tace "yes come in" Alhaji Habib ya tura kofa tare da Sallama. Zurum Sauda ta mik'e tsaye, gabanta ya yanke ya fadi, Duk yanda take zaton Alhaji Habib lema, ya wuce tunannin ta, yayi ne ta ko wani fanni, Kwarjinin shi ya cika mata fuska, shima kallonta yake yi da murmushi a kan fuskar shi, lokaci guda ya ji ya kamu da son ta, Sai da ta daidaita natsuwan ta da yaudarariyan murya tace "Welcom sir, i'll tell the Director You are here" cikin sark'ewar Murya Alhaji Habib yace "no i'm here for you" murmushi tayi ta gefen kumatu don ta san tunda ya sha maganin nan dole zai zo neman ta. Tace sit please, ba tare da jin komai ba ya zauna suka dan fara magana, har ya mata maganan aure, ba da bata lokaci ba ta amince mai.
"Sauda ga wannan files din ki shigar da shi cikin documents din-- bata rufe baki ba idon ta ya kai kan mijinta dake zaune yana ta kyalkyale daria shida Secretary. Shima ya dago ya kalleta da murmushi "Shatou nah" tace "Habibi what a suprise, what are u doing here? Yace "gani nan dai, har nayi gamo" tayi daria tace gamo kuma? Da mene? Ba tare da yaji dar ba yace "da matar aure" dammm gaban Mami Aisha ya buga, firgici da tsoro suka baiyana a fuskar ta, ta zaro idanuwa tare da dafe kirji tace "a ina?" yace "a nan, Secretary dinki Sauda" take firgici da tsoron fuskan ta ya koma murmushi tace "ai sauda na da kirki, Allah ya tabbatar da Alheri" Wani shuumin murmushi Sauda ta saki.
Bayan Wata Daya
Abu kamar wasa, Yau ake daura Auren Alhaji Habib Lema da Amaryar sa Sauda Ahmad. Zaid da Matarsa sunzo tun shekaran jiya,Manyan mutane daga wurare daban daban sun hallara, har yau ba wanda ya daga kai ya ce don me Habib zaiyi aure? Ba abun da ya damu kowa da bikin nan, Rafeeq ko har Dinner ya hada ma Baban shi.
Muje zuwa
Bibilicious Biebee
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg2⃣4⃣
Zaman Lafiya akeyi a gidan Alhaji Habib Lema, Har yau Amarya Sauda na nan a matsayin Secretary na Mami Aisha, da Mami tayi maganan a chanza mata wurin aiki tace "aa, ita dai a barta nan don ta saba, haka mijin su ya barsu don yana jin dadin yanda matan shi suka hade kansu.
Hafiz ma girma yake basu duka, ba za ka ta bacewa sun san juna shi da Sauda ba, don da ga gaisuwa ba abunda ke hada su, Aneesa kuwa in kaga tayi wani abu sai ka rantse da Allah ita ce diyar Habib Lema ba Rafee'ah ba. Rafeeq kuwa be da matsala, idan ya shigo gidan be da aikin yi sai tsokanan Rafee'ah da Aneesa fada..
Bayan Wata 2 (Bakin Rana)
Gidan Shiru kamar ba kowa a ciki, Rafee'ah na Kaduna Gidan Uncle Zaid, taje taya Aunty Safiyya zama don ta na da juna biyu, kasancewar hutu, Aneesa na BUK wurin Aunty Maryam, Rafeeq na chan suna flexing da su Maalesh, Hafiz da Alhaji Habib sunje wani Bussiness trip . Sauda ta kirashi a waya tace " Alhaji ya Lagos? Yace "Ohh, banso kika kira ba, coz suprise nake so na muku, sai dai kawai ku ganmu, yanzu ma in less than 2hrs zamu shigo katsina" daria tayi cikin salon yaudara tace "kace yau da mun sha Suprise" yace "ina Shatou na?" ranta ya sosu, ta tsani taji yace "Shatou din shi" gashi shi be jin komai gaban kowa haka yake ce mata, zai sani, itama zata sani, don kawai ta barsu suyi enjoying time dinsu ne for the main time kafin ta fara operation dinta, ta daure dai tace "ni dai duk yau ban ganta ba, k'ila ta fita ko kuma tana daki" yace "to ki dai sanar mata da zuwan mu" ta murguda baki kamar yana ganinta tace toh sai kun kar'iso."
Dakin Mami Aisha ta shiga da Sallama, tana zaune kan gado tana latse laptop dinta, ta amsa mata cikin sakin fuska, tace "Sauda kin tashi lafiya?" "lafiya lao Yaya Aisha" suka yi shiru, har saudah zata gaya mata dawowan Alhaji sai wata zuciyar tace kar ki gaya mata, sak'esak'en da ta jima ta nayi ya fado ranta, ta tambayi zuciyar ta "to ko damar ce ta samu yanzu? Bari inyi amfani da damar nan" ta mik'e da sauri tace "bari in dan hada mana Sobo" Mami Aisha tace kamar kin san ina marudin shan Zobon ki. tace "karki damu i wont take long".
Ta shiga dakinta da sauri, tana sak'esak'en abun yi, ta yanke hukuncin kiran Mak'ale, ringing daya biyu ya daga, cikin muryan yan iska yace " Hello Matar lema ya akayi ne?" tace "mak'ale kana ina ne?" yace gani wurin Goruba road" tace "donAllah yi sauri kazo akwai aiki" yace "to gani nan karisowa" "yauwa idan kazo ka kirani"
Ta gama hada tsobonta tsaf, ta ciro wani k'ulli daga habar zaninta, ta ware, magani ne na gari ta zube shi a cikin cup din ta karkada, sai kuma ta ciro wasu k'wayoyin magani ta zuba a ciki, ta karkada sosai ta dauka ta nufi dakin Mami Aisha. "Lahh har kinyi me?" tayi daria tace "har na hada, ai ba wuya" ta dire mata jug da cup din, Mami tace "nagode sosai" tace "haba ai bakomi bari inje in daura sanwan rana" ba jira ta tsiyaya sobon a kofi ta sha, ta kara tsiyaya wa ta shanye, ya cigaba da aikin ta a kan computer. Saude da ke Labe bakin k'ofa ta daka tsalle ta na murnan ta sha, da sauri ta koma dakin ta ta kira Mak'ale tace "wai ya? Kana ina? Yace wallahi gani nan bakin gate dinku yanzu nake shirin kiran ki" tace "toh bari in fito in shigo da kai" ta yafa mayafi ta fita da kudi a hannu.
"Baba ina kwana?" Sauda ta gaida baba mai gadi, Cike da faraa da rawan jiki ya amsa da "Mun tashi Lafiya Hajia?" tace "Alhamdulilah, dama dan Ganyen Latas (lettuce) ke so ka siyo min" yace "toh toh ba matsala, barin samo yaro ya siyo don ba a bar gate din haka ba ba kowa" "aa baba kai zaka je ka siyo, sauri nakeyi" tace a dan fusace, ya danyi shiru sai yace "to, barin in yi sauri in je" nan ta tsaya har sai data ga ficewan shi, ta lek'a taga yayi nisa. Ta hango motar mak'ale daga nesa ta kira shi a waya yace "hello baby?" tace ka shigo mak'ale" yace "toh gani nan".
Tare suka shiga cikin gidan, parlo ta tsayar dashi tace ina zuwa, lek'awa dakin Aishatu tayi taga tayi daidai kan Gado tana sharar bacci. Murmushi Sauda tayi, ta janyo laptop din tayi shut down, ta maida cikin jakkar ta ajiye kan side drawer, ta kwashi sobon ta da cup ta fita dashi, ta dawo ta dinga bubbuga Mami Aisha, amma ko shurawa batayi ba, kamar matatta haka take kwance. Saude ta danyi ihu taga ko zai tada Aishatu, amma ko ta motsa, Sauda ta saki murmushi tace things will go as planned.
Bayan Minti Talatin(30 mins Later)
Bakin Gate Hafiz ya dinga Horn, ba alamun Baba mai gadi, to ko ina yaje? inji Alh Habib, daidai nan Rafeeq ya danno motar shi kwanar Gidan, ya k'araso, Ganin Motar Uncle Hafiz tsaye ya sa shi fitowa daga nashi motar, zuwa yayi ya k'wank'was kofar side din Uncle Hafiz, yayi winning "Sannun ku da zuwa Uncle Hafiz, Daddy Sannu ya hanya? Bamu san yau zaku dawo ba" Suka amsa mishi gaisuwan su, Uncle Hafiz yace "mu kam Rafeeq bude man gate dinnan, Bansan inda Baba yaje ba" Rafeeq ya kalli Gate din yace "to ko ina yaje? Its unlike him" ya karasa tare da shiga gidan don bude Gate, Uncle Hafiz ya shigo da motar sa, Rafeeq ma yaje ya shigo da tasa. Sauda na jin dirin motar su ta fara tsalle, ta gyara zaman kan kujera tarw da rafka Uban tagumi hannu bibbiyu.
A tare su 3 suka shigo parlorn, Alhaji Habib na ba Rafeeq labarin Bussiness trip din su, suka shiga da Sallama, Ta dago ta amsa a sanyaye, Sannun ku da zuwa Alhaji, Hafiz sannu" "sannu ya gidan? Rafeeq yace "Auntyn mu lafia naganki haka?, u look disturbed" tace "Rafeeq, wallahi Mami ce naji ta shiru, tana daki tun da na tashi, na kwankwasa na kwankwasa shiru, na zata ma ta fita ne amma baba maigadi ya bani tabbacin kai kadai ka fita yau" Rafeeq yace "toufa, its unlike her baccin Safe, This is just 12:30" Sauda tace "nima dai haka nagani" Hafiz maybe she needed the sleep, shes just sleeping" Alhaji Habib da yaji Hankalin shi ya ki kwanciya, yace "kaii Rafeeq, je ka tado ta, Azahar ma ta kusa" Rafeeq ya haye sama, Sauda ta cigaba da cewa "tun dazun da mukayi waya da kai na lek'a don in gaya mata dawowan kuamma shiru na jita wallahi".
K'wank'wan "Mami kina ciki?", ya murda k'ofan sai dai damk'e ya jita, yace "mammy, ki bude Rafeeq ne, ko duk baccin ne haka? "Mammy mana, ki bude Daddy ya dawo" nan ma shiru, duk ya rude ya shiga k'wankwasa kofar iya karfin shi.
Alhaji Habib ya dan daga murya yace "Rafeeq Har yanzu ba ta bude ba?" daga sama Rafeeq yace "Daddy ba ma ta magana, kuma kofar is Jammed" da Sauri Alhaji Habib ya mik'e ya hau Saman, su Hafiz suka rufa mai baya. Shima knocking ya fara yana cewa "Shatou na, kina ciki? Are you okay" Shatou taso ki bude mana k'ofa" Sama sama sukaji a na magana, da suka kasa kunne sukaji muryan namiji ne na cewa, "Mun shiga 3, Aisha ki tashi, tashi maigidan ki ya dawo, Haba Aisha duk gajiyan ne, ai ya kamata ki tashi daga baccin nan haka, ki tashi ki nemo min hanyar fita"
Rudani da firgici ya ziyarci zuciyar Alhaji Habib, kirjin shi kamar ya tsago daga rigar shi ya fado don tsoro, hannu ya sa ya toshe bakin shi don wani kuka da yaji ya zo mai, yana k'okarin lalibo adduar "Innalillahi wai inna illaihir raji'un"
"Allahumma arjirni fi museebati wa akhlifni khairin minha.
Hafiz kuwa take Ran shi ya bashi wannan makircin Sauda ne, ya kai duban shi ga Sauda yana mata kallon tuhuma, da ta lura da kallon da Hafiz ke mata, ta girgiza kanta alamun ba ruwan ta, tayi saurin kawar da kanta daga duban shi.
Rafeeq ko da be fahimci komai ba ya cigaba da k'wank'wasa kofar, "Mami na Open up please, you are making us worried" ji yayi an taba k'ofar, ya matsa baya yana murmushi ya kalli Daddyn shi, yace "Dad, she's opening up, she's fine". Bawan da yace da shi komai, sai k'ofar da suka tsura wa ido.
Mak'ale na cire key ya murda kofar ya danna a guje har yana buge Alhaji Habib da ke kan hanyar shi, duk suka bishi da ido, Hafiz yayi yunkurin binshi da gudu Alhaji Habib yayi karfin halin rik'o Hafiz, ya girgiza mai kai alamun rabu da shi, Rafeeq cike da alamun tambaya yace "Daddy waye shi?" Alhaji Habib be ce komai ba face hawayen da ke zuba daga idanun shi, ya matsar da Rafeeq gefe yaym shiga dakin Aishatu, burin shi ya ga Aisha ta ce mishi "mafarki yake, this is not true" don so yake ya tashi daga wannan mummunan baccin da yake, Hafiz ma ya bi bayan shi, sauda ma ta rufa musu baya suka kutsa dakin Mami Aisha.
Rafeeq da shifa kwatakwata k'wak'walrshi ta dode, be gane komai ya bi su a baya. Hafiz yayi saurin dauke kanshi daga duban Aisha, Sauda kuwa daura hanayenta tayi guda biyu a kai, Alhaji Habib ya zame k'asa tare da fashewa da wani