Showing 57001 words to 60000 words out of 149166 words

Chapter 20 - Ke alkhairi ce COMPLETE HAUSA NOVEL

BIEBIE   

22 Oct 2024

25746

ya raba ta gaban ta ya wuce, ta an kara da hakan da sauri ta rik'o hannun shi, yana waigowa a fusace ya haska ta da wata irin hadaddiyar mari, ji kake tass, Ya nuna ta da yatsa, *"kar ki k'ara gigin tab'ani, idan ke maiyace to ki ci kanki, banza dangi Mayyu"* ya idasa motar sa, ya fada ya danna wani uban horn Baba Maigadi ya bude gate, a sittin Rafeeq ya bar gidan. Zo ku gane min Fuskar Saude, yanda ku kasan Zakkanya, sai huci take tayi, Meema kuwa zaro ido tayi sosai tana Mamakin Rafeeq, wato sune dangin Mayyu? Alhaji kuwa dafe kanshi yayi don kunya, Aneesa kuwa tana ganin fitar Rafeeq ta fashe da wani irin kuka, A gudu Saude ta karisa ta rungumo ta, ta ma kasa cewa komai don Rafeeq ya gama kashe ta, Alhaji ya matso yace *"Anee Baby kiyi hakuri, kema tunda kinsan halin Rafeeq, ki daina kulashi"* Waiyo Allah zo ku ga takaici kwance kan fuskar Uwar Aneesa, wato ba zai yi fada ba ko? Gaskian hausawa da suka ce Naka Naka ne, Hajia Saude ni barin wuce, da kyar tace *"Allah ya tsare Hanya"* be tsaya wata wata ba ya fada mota direba Ya ja motar suka bar gidan, kamar jira suke ya fita Meema tace *"JarUban chan, Sis kina kallo? Ya zaayi ya mare Aneesa?"* Saude da haushi ya mata katutu tace *"Bari dai Meema, ina mamakin wannan karfin halin Rafeeq, Ko ni uwarta ban mareta ba, sai shi lallai Ya Tafka babban kuskure, this is the last time you will hurt my daughter Rafeeq, i know What to do with him"* sai a sannan Aneesar ta dago, tace *"No Mom, you are so not doing anything to him, if anything should happen to him, i'll hate you for the of my Life"* ta ruga a guje ta koma cikin gida. Yanda kuka san an shuka Saude haka ta tsaya, saboda Rafeeq Aneesa ke cewa zata tsaneta? Lallai kam dole ta dauki mataki kan Rafeeq, Meema sai tunzurata take tayi, ita kuma sai hawa take, ta cika tayi Pam.

Tuk'i takeyi cikin kwanceiyar hankali, kamar ba abunda ya faru, ko kadan beyi tunanin abunda ya faru gidansu yanzu ba, ko a kwalar rigar shi Burin shi kawai ya sake ganin ta, tsintar kanshi yayi da zuwa Crispy, yayi ordering breakfast leda 3, Chips egg and Plantain, aka mai packaging, ya biya ya koma mota, ya kunna yana tunanin yaje ko kar yaje, zuciyar sa me tunzura shi ga mai yanayi da Rafee'ah tace yaje, haka kuwa akayi, don Rafeew Asibiti K Dara ya nufa, cikin minti k'alilan ya isa, ya kwaso leda 2, ya fita yana tafian nan na shi, sai gashi gaban Dakin da aka kwantar da Nene, ta window ya lek'a su, inda Nene ke cewa *"Kinga dai ki shirya ki wuce Makaranta ko? nace miki zan iya zama har ki dawo, ba abunda ke man ciwo "* Nasiba tace *" ni fa na gaya miki ba inda zanje, ni da Makaranta kuma sai kinji sauki kinyi garau abunki"* Nene ta sausauta murya tace *"kiyi hakuri Jikata, ki tafi DonAllah, bana so ki samu matsala da Makaranta"* Seebi tace *"Wallahi ba zanje ba"* Nene ta buga tsoki da k'arfi tace *" Nifa bana son mutum me shegen taurin kai da kafiyyar tsiya"* Seebi tayi daria tace *"Ai fah, ni barin je in siyo mana Kalaci"* Rafeeq na jin haka yayi saurin Aje ledojin gaban k'ofar dakin, da sauri ya bar gurin. Ta na bude k'ofa ta ci karo da wadannan ledoji ta tsugguna ta dauka, tace wannan kuma fa? Wani Kamshi da tayi amanna na Rafeeq ne taji, da sauri ta juya ko zata hango shi,amma wayam ba ta ga kowa ba, tabbas wannan ledojin Rafeeq ya aje su, ta hau tambayan kanta, to meyasa be shigo ba? Ohh na manta he is R-Lema, he cannot come in, ta saki wani Murmushi, tace *"R-Lema i'm Coming for you"*.

A kan Sitiyarin Mota ya kifa kanshi Ya shiga magana a zuciyar shi shi kadai, *"She cannot start skipping School"* guntun tsaki yayi ya tada Mota, ya bar Asibitin, me makon ya wuce Makaranta, sai ya wuce Gidansu Maalesh, yana shiga gidan ya wuce Cikin Gidan straight, kai tsaye ya shige ciki, Mom din Maalesh ya gani zaune kan 3 sitter, ta hade kafa daya kan daya tana kurban Koko a cup, Hajia Maryam kenan{Om Eman} kallo daya zaka mata zaka san cewa Yar boko ce, zatyi tsarar Mamin su Rafeeq, k'awarta ce sosai, da k'yar taji sallaman Rafeeq, ta dago ta kalleshi, ta amsa da fara'a tare da mik'a mai hannu ta mai nuni da yazo ya zauna kusa da ita, tana son dan Aniniyarta sosai, Zama ya zo yayi kusa da ita a hankali yace "Mom barka da Safiyya" tace "Son Ka tashi Lafia?"* kai kawai ya daga mata, Murmushi tayi a ranta tace oh ni Rafeeq when will you ever change? Shiru ya dan gifta, tace zaka sha Koko? Girgiza kai yayi alamun Aa, tace "to me kakeso in hada maka?" da kyar yace *"bakomi"* chan ya kamo hannun ta yace *"Mom, Hajjo zaki bani"* (Hajjo Mai aikin su Maalesh ce, tsohuwa ce, tun Maalesh na jariri take gidan) ta kalleshi da alamun tambaya, yace *"Jinya zatayi a Asibiti"* Mom tace Jinyar wa? Waye be Lafiya? To anzo gurin, idan akwai abunda Rafeeq ya tsana be wuce ya bude baki yayi bayani ba, baya son dogon surutu, be san ta inda zai fara bata bayanin nan ba, kawai sai ya mik'e zai fita tayi saurin kamo hanun shi, *"haba Rafeeq, ya zaayi ka fara magana kuma sai ka tashi ka fita?, jinya wa Hajjo zatayi?* Tsaki mara sauti yayi yace *"ki bari kawai, na fasa"* Girgiza kanta tayi tace "Rafeeq you are very Stubborn" ta harare shi ta mai umarni da ya zauna, ta shiga ciki ta iske Hajjo na kakaci, tace da ita Hajjo, idan ba matsala Rafeeq ke so kije Asibiti kiyi jinya, kinsan hali na tambaye shi waye be lafia,da ya min bayani ya gwammace a barshi, Hajjo tayi dari tace kna ruwan dan gidana, ba komai Wallahi, zanje, kinsan akwai ladan masu Jinya, ina kwadayin shi, Barin tashi in shirya, Mom ta mata Godia, ta koma parlor inda ta bar Rafeeq, ta daure fuska tana hararar shi, shi ko sai Murmushi yake tayi, dan yana jinsu ita da Hajjo, ba jimawa Hajjo ta fito da ledar kayanta, ta ma Mom Sallama, Rafeeq ya kamo hannun Mom tayi saurin fizgewa, a hankali yace *"Mom, Nene ce bata da lafia, Kakar erhm ya ma sunanta? ya tsaya yana son tuno sunan da yaji ana kiran yarinyan, yace toh na manta sunan, i've said enough mun tafi"* be jira cewar ta ba ya fita, ita kuma Murmushi tayi, tana me tausayin Yaron Aminiyyarta.

Hajjo Ta ishe shi da surutu cikin mota, idan ya tanka to wanda ba sa wurin sun tanka, yayi shiru ya maida hankalin shi kan tuk'in sa, har suka iso Asibitin, ya ciro paper da biro yayi rubutu, ya mik'a ma Hajjo, yace *"ki basu, Daki na Goma Sha Biyu"* Hajjo ta san halin shi sai kawai ta kwashi kayanta ta shiga cikin Asibitn, da tambaya aka nuna mata dakin su Nene, ta shiga da Sallama Seebi ta amsa mata tare da gaida ta, ta amsa mata, Nene ta dago tana Kallonta, ta mata ya jiki, da ta lura suna mata kallon rashin sani sai ta ciro takardar da Rafeeq ya bata ta mik'a ma Seebi, ta amsa kallo daya ta ma rubutun ta san nashi ne, don ta yi mastering rubutun shi, duk inda ta gani zata gane, ta fara karantawa *"She'll be staying with Nene Until she's discharged, and you,,,, you are so not skipping classes, Come out now"* ta karanta letter ya fi a kirga, wannan wani irin Letter ne? Ba gabas ba yamma, sai orders din da yake badawa, to ko wannan matar yake nufi da zata zauna da su har sai an sallame ta? Ita kuma ba zata yi missing School ba kuma ta fito waje ta sameshi? Haka yake nufi? Indai haka ne, to it means ya ji me suke cewa da Nene dazun, hakan na nufin ya damu da lamarin su? He cares for them this much? Lallai he's doing more than enough for them, its time ta fara cika Alkawarin da ta daukar ma Rafee'ah, Allah ka taimakeni, nan taji wani kwarin guiwa, tayi saurin fita, Nene tace "ke kuma ina zakije?" ina seebi tayi gaba, Hajjo ta riko hannun Nene tace "Ni zan yi jiyar ki kawata" Nene tayi murmushi kawai.

Inda yayi parking Jiya ta nufa, sai ko gashi zaune kan mota, ya cire rai da zuwan ta, shi kuma ya ki tafiya, sansayar muryar ta yaji tayi Sallama tare da cewa *"Hamma Rafeeq"*da sauri ya diro daga kan motar, yana me kallon ta, Murmushi ta mishi tace "Hamma na ina kwana?" kawai sai ya ga ta chanza ta koma Rafee'ah, da sauri ya lumshe ido ya, chan ya lula duniyar tunani, *"Kai Rafeeq wannan ba Rafee'ah bace, Rafee'ah ta rasu, She's never coming back, dont let this girl mess with your head, you cant let her play with your mind "* ya bude ido tare da yin guntun tsaki, ta gaban ta ya wuce ba tare da ya kalle ta ba yace *" Get In The Car"* ya shige ya barta tsaye, na take wasu tunanin suka zo mata, Anya zata iya? Zata iya da Zafin kan Rafeeq? Anya zata iya da halin shi? anya zata iya jure komai? Ji tayi wani abu ya k'arfafa mata zuciya, taji wani irin Kwarin Guiwa, A baiyane tace *"I Can and I will, I musnt give up, not now not ever, Rafeeq Lema da yardan Allah sai ka dawo daidai"* tana kaiwa nan ta fada motar.

(Please Lovers❤ Ignore all the Typos and Errors👏🏽👏🏽👏🏽)
_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

This Page is for you Hauwa Nayaya❤.

Pg3⃣8⃣

Yana jin shigowar ta amma be dago kai ya kalleta ba, illa tada motar da yayi ya ja motar suka bar Asibiti, ba wanda ke cewa danuwan sa k'ala, gaban Seebi sai faduwa yake tayi, shi kuwa jefi jefi sai taji ya buga tsaki, ko tsakin me yakeyi? oho! Ga mamakin ta sai gani tayi ya sha kwanar Unguwar su, tayi saurin kallon shi, sam be san iskar da ya dauko ta ba, don ko ta gefen ido be kalleta ba kuma yasan Shi take kallo, daidai gidan su Seebi yayi parking, be ce da ita komai ba, har kusan minti 3, ganin ba zai mata magana bane yasa ta fita daga motar, tana fita kuwa yaja motar ya tafi, baki hangame ta bi k'urar motar da ido, shi kuma haka yake? Yanzu da bata dauko jakkar da ta ajiye makullan gida ba ya zatayi? duk yanda take zaton Rafeeq ashe ya wuce nan, ya wuce tunanin ta, a baiyane tace *"R-Lema, you are full of wonders"* zata bude gidan kenan ta hango Baba Maigadi, da sauri ta k'arasa gun shi, da faraa suka gaisa, yace *"Nasiba, Aminene shiru, dazun da naje siyan k'osai na biyo tanan na ga k'aton kwaddo, shin lafiya?"* Nasiba cikin damuwa tace *"to da sauk'i dai, jikin ne, amma tana asibiti"* *"Allah sarki wani Asibiti kenan?"* *"Asibitin Dr Dara"* ya tabbatar mata da zaizo, sukayi Sallama ta bude gidan ta shiga, sai da ta share gidan kafin ta shiga tayi wanka, tana fitowa ta shirya, ta dauki litattafai ta sa cikin jakka, ta ciro waya ta kira Ushee, ringing daya ta ծauka, bayan gaisuwa Seebi tace *"Ya Karfe nawa zaa fara lectures?"* *"11 ne"* *"Okay to gani nan zuwa, Allah sa in samu Mota a National"*(School Bus Stop).
Ta fito ta rufe gidan, ta fara tafia, tsaki tayi don tasan ba zata samu Napep din da zai kaita National ba sai ta kai bakin Titi, na Nene tace Unguwa kamar Mak'abarta. Tafia take da sauri, sai ji tayi mota na mata horn, k'in tsayawa tayi sai ma saurin da ta k'ara, daga cikin motar yayi tsaki ya k'ara gudun motar har ya sha gaban ta, kallo daya ta ma motar ta shaida me ita, ta tsura ma Bak'in gilashin windon motar ido kamar tana ganinshi, shima anan ya samu ya k'are mata kallo, abunda ya kasa ganewa shine, meyasa take rinewa ta koma mai Rafee'ah? Mesa idan suna tare yake ji kamar yana tare da Rafee'ah? Ya lumshe idonsa a hankali ya bude, chan kuma ya buga guntun tsaki. Nasiba da ta gaji da tsayuwa a gun, Har yanzu dai be fito daga motar ba, be sauke windown shi ba, gashi kuma ya tare mata hanya, to me ya ke nufi ne? Ko yana nufin ta shiga motar? ta yanke hukuncin shiga motar, ta yi jihadin bude motar ta shiga, dama abunda yake jira kenan, ya yi ribos ya dau hanya ba tare da yace mata k'ala ba.

Ya duba agogon hannun shi, yayi guntun tsaki, k'arfe 10 da minti 10, Lectures dinshi 8-10 ne, ya tabbatar an gama yanzu, ya maida hankalin shi ga tuk'in sa, Nasiba tace a ranta *"barin ja shi da labari yanda zai sake da ni"* jikin ta na rawa a hankali tace *"Hamma Rafeeq wani Course Kake?"* shiru kakeji ba amsa, a zatonta be ji me tace ba ta bude murya ta sake mai tambayar, guntun tsaki taji yayi irin kin dameni nan, yayi mata banza ya manna mata hauka, Waiyo Allah, Nasiba duk tabi ta tsani kanta, tana dana sanin mai magana, ji take kamar tayu kuka, Allah yaso ta ba gaban mutane take ba, da ta gama jin kunya don wannan ya kai Dizgi, hawayen ds take mak'alewa suka soma gangarowa, da sauri ta juya tare da share hawayen tana kallon window inda suke k'etara wurare don Makarantar da nisa haka suka cigaba da tafiya ba me cena danuwansa komai, a hankali taji yace *"ina BioChemistry"* da sauri ta juyo ta kalleshi, kamar ba shi yayi magana yanzu ba, ita har ga Allah ta manta da ta tambaye shi, wato sai da ya ga dama ya bata amsa ko? Muje zuwa indai zaka dinga amsa min da sauki, a ranta take waddannan maganganun, tace *"BioChemistry naso a bani,suka ban MicroBiology, na so yin change of course don course din akwai wahala"* shiru yayi na wasu mintuna, chan ciki yace *"You are so lazy, ke komai wahala, i wonder how you passed your WAEC"* ta juyo ta kalleshi da mamaki, fuskar nan tamk'e, kamar ba shi yayi magana yanzu ba, ta murmusa a shagwabance tace *"Allah Hamma Rafeeq i'm not lazy, ka tambayi Nene"* da sauri ya waigo ya kalle ta, har sitiyari na k'okari kubce mai, tabbas da da mota ko machine a gefensu da ya buge su, Muryar Rafee'ah sak yaji, ya tsura mata ido, murmushin ta mai kayatarwa take mai, zaiyi magana kuma ta fasa ya maida hankalin shi kan tuk'i, ta lura da yanayin da ya shiga, itama ta tsorata hajan yasa ta ja bakin ta tayi shiru, har suka iso Makarantar be sake cewa 'a' ba, har gaban department dinsu ya kawo ta, yayi parking, a hankali yace "MicroBiology Is a very good course, dont worry you will enjoy it with time" da k'yar take magana kamar ance dole sai yayi, da bata kasa kunnenta sosai ba da bataji me yace ba, don ciki ciki yayi maganar, murmushi tayi tace *"Nagode Hamma Rafeeq, Allah ya saka da Alheri"* dif kamar ruwa ya shanye shi duk sanda yaji ta kira sunan shi ya kan shiga yanayin da besan yanda zai fassara shi ba, ta bude murfin mota tace *"Hamma Rafeeq na tafi thanks once again"* Waiyo Allah ji yayi kamar yayi ihu har ta kusa barin motar yace *"nace ba?"* ta gyara zama tace *"ya kace Hamma Rafeeq?"* dan guntun tsaji yayi yaba takaicin tsaidara da yayi, amma dole ya kawo karshen abun tunda shike cutuwa ya sake wani tsakin yace *"Sunana Rafeeq"* murmushi tayi tace *"ai nasani Hamma Rafeeq"* an kuma, runtse ido yayi ya bude yace *" you dont have to cal my name, in kuma ya zama dole si kin kira sunana ki kirani da Rafeeq ko R-Lema not Ham-whatever"* tace *"aa Hamma Rafeeq, ba zaayi haka ba, kasan dai ka girmeni, kuma ni Ummi ta tace in dinga girmama nagaba da ni, i cant just call your name without showing some respect, So I chose to Call You _Hamma Rafeeq_ wato _YayaRafeeq_ kagane?"* Waiyo Allah, ta gama kashe Rafeeq, ya ma kasa ce mata komai, sai k'ura mata ido da yayi, gabata dayata rikide t koma Rafee'ah, yanayin maganar ta irin na Rafee'ah, har yanda Rafee'ah ke turo baki idan tana so ya mata abu wannan ma nayi, kanshi ya dau Zafi, Nasiba kuwa tsaf ta gano shi, *Hamman* ne beso tace mai, ba yanda zaayi ta daina kiranshi da hakan don ta gano wannan ne Weakness(Weakpoint) dinshi, da haka zata sa shi a hanya, bude murfin motar tayi ta wuce ce Department dinsu, tana mamakin k'arfin halin da tayi, yanda ta cire kunya ta fara mission dinta a yau, ta sara ma kanta don ta yi namijin k'ok'ari wurin sa Rafeeq magana da yawa haka.

Rafeeq kuwa kasa motsi yayi ya bita da ido har ta k'ulle ma ganinshi, mamakin kansa yake yi, wai yau shine da magana da wata mace haka, yau yayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login