Showing 54001 words to 57000 words out of 149166 words
aka zalunta" yace "Amin" horn akayi da k'arfi, jiki na rawa yace ina zuwa ya shiga gidan da sauri ya wangale Gate din, Meema ce da Aneesa cikin wata katuwar Mota, Meema ta harari megadi tace uban me ya hanaka bude gate da wuri? Yace "kiyi hakuri" tsaki ta buga ta figi motar da Sauri Nasiba ta ja baya don kiris ya rage su bi ta kanta. Saida ya kulle gate din ya dawo gun Nasiba tace baba su waye wannan? Yace "Kanwar Saude ce, da diyarta, in sukayi wani abun sai ki rantse su 'yayan alhaji ne, ita Aneesar naji labari har ta koma Aneesa Habib Lema a Makaranta" Nasiba ta jinjina kai tace "baba barin wuce" nan sukayi Sallama.
Tun kan hanya Nasiba ta hau tunanin yanda zata fara wannan Mission dinta har ta je gida tana sak'a da warwara, ta rasa yanda zata yi, amma abun da ta kudirta a ranta, Zata taimaki Rafeeq, zatayi yanda Rafee'ah ta bukace ta da tayi, nan Allah ya cire mata duk wani tsoron abun da zai je ya dawo, ta san its not an easy thing, amma haka kurum zuciyar ta ta amince da duk halin da zata shiga, zata yi sacrificing kanta, she's willing to take the risk, bayan jin ta bakin Baba Maigadi, da hujjojinshi na Zargin Matar Baban su Rafeeq,komai zai zo mata da sauk'i, nan ta gane ba Rayuwar Rafeeq kadai zata shiga ba, Rayuwar Gidan Lema gaba ki daya zata shiga "So help me God". To tambayan shine "Ta yaya zan shiga Rayuwar su Gaba ki daya?" zuciyarta tace "barin jira Rafee'ah a mafarki".
Da daddare sai juyi take don tayi Mafarki, amma Shiru ba Rafee'ah, washegari ma kwatakwata batahi mafarkin komai ba, kwana 3 ta jera tana jira tayi Mafarki da Rafee'ah amma shiru, tace ma kanta " it seems like i am on my own, Allah ka taimake ni."
*5:50pm*
"Sannu Nene" Nasiba tace cikin damuwa, tun kwana 2 da suka wuce Nene ke kwance, ta rasa me ke damunta, ta k'i yarda suje Chemist, kuma ta k'i yarda Nasiba ta gaya ma Abban ta, Nasiba duk ta shiga wani yanayi, a iya wayon ta, ba ta taba ganin Nene tayi ko da ciwon Kai ba, cikin rashin kuzari Nene tace "Wai uban meye zaki tasani gaba ki zabga uban tagumi kina kuka iyi? Ko kinga na mutu ne? Nasiba tace "Nene nifa ban taba ganin kiyi ciwo ba" Nene tace da yake ni Waliyya ce sai in k'i ciwo, ko kullum in banda lafiya sai inzo inyi kwance kamar wata ke a gurin, to Nasiba ko ciwon Ajali ne me zuwa ma mutu farat daya, to barin bar miki wasiyya" da sauri Nasiba ta tashi ta shiga daki ta bar Nene kwance tsakar gida, don ta san Nenen k'arfin hali kawai takeyi tana maganar nan, kuma idan ta biye mata sai ta sa ta kuka don Bakin Nene ba ya shiru. Nasiba ta rasa yanda zatayi, ba ta san kiran Abban ta don ta san shi da damuwa, yana iya kamo hanyar Katsina da Marecen nan, ya zatayi? Bata gama tunanin ba Wayar ta ta hau ruri da sauri ta dauka + ta gani wato lambar waje ne, ta dauka da Sallama, a dayan bangaren "Waalaikum Salam Seebin mu ni da Nene, ya kike ya karatu? Tace " Uncle Zaid, Alhamdulilah, ya Aikin? Yace "Alhamdulilah, ina Nenen?" kamar jira take ta fashe da kuka, lokaci guda Zaid ya rude, "me ya faru? Me ya same Nene? Wani abin yake faruwa a katsinar? Ki min magana Nasiba" daga jin muryar shi kasan hankalin shi a tashe yake" ta dan tsagaita tace "Uncle Zaid, Nene ba ta da Lafiya, tun kwana 5 da suka wuce, ina tsoron wani abu ya same ta, ban taba ganin ta haka ba, amma ta k'i yarda muje Asibiti ko nagaya wa baba na" Zaid yayi dan shiru yace "no wonder, randa na kira naji muryar ta wani iri, ashe ba lafia, kuma bata gaya min ba" "ai ba zata gaya maka ba, don Nene wata irin mata ce me Zurfin ciki, nima don ta kai kuri na san cewa bata jin dadi, har yanzu bakin ta ya ki mutuwa" Zaid yace "ki kwantar da hankalin ki, ki tashi kuyi shirin Asibiti aje a dibo ta" Nasiba tace Uncle Zaid " ba zataje ba, Nene is so stubborn" yace "trust me on this ki kai mata wayan".
Haka ta mik'e ta kaima Nene Wayar, Nene ta amsa da Sallama, Zaid ya gaida ta, "lahh, Zaidu bawan Allah, kaine Ya Ingilar?" yace "Alhamdulilah, ashe ba kiji dadi ba?" saida Nene ta wurga ma Nasiba harara kafin tace "Kai kalau nake" "Aa Nenen mu, ga muryar ki nan, ni dai ki tashi ki kimtsa gashi na turo a zo a kaiki Asibiti, donAllah kar kice Aa" ba yanda zatayi tace "Toh Zaidun Seebi, tunda yanzu maganar ta kadai kake ji" duk sukayi daria, ta mik'e da k'yar ta shiga bandaki, yace "Nasiba, ku shirya za a zo a kaiku Asibiti" tace "Uncle Zaid ina iya kaita, ba sai an zo ba" yace "don't be silly, zan sake kira inji ya jikinta" dif ya katse wayar. Nasiba tayi murna, tace "Allah Sarkin Uncle Zaid, Our Guardian Angel."
A karo na 3 Ya shiga lalluben layin Rafeeq, sai ya kusa shiga sai ya datse kiran, don yana fargaban abun da zai ce mai, Rafeeq be son irin haka, amma ya zaiyi? He is his only choice, chan dai yayi shahada ya sake kiran wayar Rafeeq, ringing biyu Rafeeq ya dauka ya kafa a kunne ba tare da yace komai ba, Zaid yace "hello son, ya kake?" kamar ba zai yi magana ba yace " Barka da Yamma" Zaid yace "Kaci abinci?" "Uhm" kadai yace, Zaid yace "Rafeeq ka tuna Nene? Wacce kama granddaughtern ta Assignment last week? Kamar ba zai tanka ba yace "yeah" " she's sick wallahi, she's been sick for days" a ranshi yace to why are u telling me? Allah ya sa ba cewa zaiyi inje in gaishe ta ba don ba zuwa zanyi ba, shiru be ce komai ba Zaid yace "Kaji ai?" da kyar yace "Allah ya bata lafia" "Amin, Rafeeq i want you to do something for me, DonAllah ka dauke ta ka kaisu Asibiti" cike da mamaki yace "What??" Zaid yayi saurin kwantar da kai, donAllah they need help, kaisu Asibiti kawai zakayi, this is all i'm asking for, Please" dif Rafeeq ya kashe wayan, takaici uwa ya kashe shi, shi be san meyasa Uncle Zaid ke sa shi yawan magana ba, in banda neman Magana shi zai kaisu Asibiti? Why they need help, shi First Aid box ne? Kai akwai Sakel, shi be kai kanshi Asibiti ba zai kai wasu? Ga Maalesh baya nan, to ko dai ya kira musu Ambulance? Amma Uncle Zaid ya fi k'arfin ya sashi abu ya k'i yi, be da wani Zabin da ya wuce mik'ewa ya shiga mota.
Daga gidan su zuwa gidan su Nasiba yayi tsaki yafi dubu, gashi yanzu fi Minti 5 yana tunanin yanda zai shiga gidan, Kamar yayi kuka, Ya ciro wayar shi ya tura ma Zaid text, "i'm there" don be son mishi magana a halin yanzu, Zaid yayi saurin kiran Nasiba, yace "ku fito yana waje" ta shaida mai da yanzu zasu fita. Ya tura ma Rafeeq da cewa "there are coming now, kindly greet the sick person please, Please Rafeeq, for me" tsaki ya buga Wannan Uncle Zaid din yana sani abun da ban yi niyya ba, takaici ya hana shi tsayuwa, ya koma motar shi ya Zauna" ba ayi minti Daya ba Nasiba ta fito rik'e da Nene, ta waiga ta waiga bata ga kowa ba, daga chan taga wata jan mota mai bakin Gilashi, da alamu ba kowa ciki, "to ina wanda Zaidun ya aiko?" "inaga bai karaso ba, mu koma daga ciki" duk wannan lek'e lek'en da sukeyi Rafeeq na kallon su, ganin zasu koma ciki ya sa shi yin horn, Nasiba ta juya inda taji horn, ta ga haske a ta cikin motar nan zuciyar ta ya bata, R-Lema ke cikin motar chan, ta tsinci kanta da murmushi ko ba komai zata samu ta shiga rayuwar shi, tace "Nene, ga motar chan" "wanchan mota kalar jini, ga bak'in windo shi kike nufin mu shiga?" cike da takaici tace "toh, ko Uncle Zaid din ne zai sa a cutar da mu?" da sauri tace "ni ba haka nace ba muje muje kar ki kaini gaba" su ka karasa har inda yayi parking, har yanzu be fito ba, Hannu ta sa ta bude k'ofar baya, Nene ta shiga da Sallama ita ma ta bita ta shiga ta rufo kofar, Nasiba ta kalleshi tace "ina wuni?" be amsa ba, shi dai ya tsinci kanshi da cewa "Ya jiki? Sannu da jiki" Nene ce da fara'arta tace "Naji sauki sosai" be sake magana ba ya ja motar, cikin nutuswa yake tuk'in shi, Nasiba na karantar duk wani abu da yakeyi, tausayin shi take ji sosai, ba tasan lokacin da hawaye suka soma zubo mata ba, tayi saurin sharewa don kar Nene ta gani ta tara mata mutane, be zarce ko ina ba sai Asibitin K-Dara, ya shiga yayi parking, shiru shiru be ce musu komai ba, Nasiba tace "Nene anzo fito mu shiga"suka fito, ga mamakin ta shima ya fito yayi gaba hanyar entrance din, suka bishi a baya, Nene na mata mitar "shi kuma wannan haka yake dunkum?" Seebi dai bata ce komai ba, Rafeeq ya tsaya ya yanki kati, ba layi, ya kira Dr Daran, yace "Baba gamu gaban Office dinka" yace to Rafeeq ku shigo, hannu kawai ya nuna ma Nasiba Office din ya samu guri ya zauna, Nasiba kuwa ta gane me yake nufi, ta sake rik'e Nene suka shiga cikin office din, yace kune Patient din Zaid? Nasiba tace "eh" ai ya kirani ya sanar dani zuwanku" ya shiga yi ma Nene tambayoyi, da gwajegwaje, kusan Minti 45, kafin yace " Inna Zamu baki daki, Hawan jinin ki ya tashi" Nasiba ta zaro ido tace "hawan jini Dr?" meyasa ta samu hawan jini? Yace "Ke kuwa ta tsufa, ai tsufa ce, don ma jikinta me kyau ne kuma tana regulating din shi,amma still zamu bata gado don kar ta kamu da Diabetes, don na fara ganin Symptoms din a tare da ita, kar ki daga hankalin ki, yanzu barin na muku processing gado, Suka fita waje da Dr din, Nasiba ta leleka bata ga Rafeeq ba, a ranta tace "ya ma yi kokari da ya kawo mu" Dr ya rubuta aka basu Gado, A ka kaisu har dakin, Nasiba na tunanin yanda zataje Gida kwaso kaya.
Rafeeq ya shiga Office din Dr, ashe Sallan Maghrib ya je yayi, ya ga basa nan, Dr yace "nayi admitting din su ne,suna room 12, HBP ne da ita, and a minor Diabetes, shine muke so ta samu rest, zan kira Zaid in sanar dashi don yace duk me ake ciki in kira shi, Rafeeq ya danyi gajeren tsaki yace " Me ake so?" Dr yace wannan taje ta dauko musu kayan bukatar su, don zasu kai 3-5days, payment kuma zan tura ma Zaid, Rafeeq yace "a ina zaayi?" yace a gun Cashier, Rafeeq be sake cewa komai ba ya fita, sai da yaje yayi payment kafin ya fita daga Asibitin, Jifatu yaje, ya siyo kayan Amfani, Su kayan Tea ne, fruits, karton din Ruwa, Bargo, Sallaya, da duk wani abun da yasan zasu buk'ata, Rafeeq shine da tsaywa siyan Kaza, ya koma Asibiti, Irin leburori yasa suka kwasan mai kayan, yayi gaba suna binshi a baya, har gaban dakin room 12, umarni ya musu da su shiga da kayan, shi kuma ya juya, daidai nan Nasiba tace Nene barin je in dauko kayan bukatar mu, don ba musan har yaushe zamu tsaya anan ba, Nene tace "toh akwai kudin Nape hannun ki?" eh akwai. Tana bude k'ofa ta gansu tsaitsaye da kaya nik'i nik'i, ta bude baki, sukayi sallama tace wannan kayan kuma fa daga ina? Suka ce wanchan ne yace mu shigo da su nan, Nasiba ta lek'a don tava wasu ke nufi, ga mamakin ta Rafeeq ne yana tafia da sauri, da sauri ta bi bayanshi, gudu gudu amma ta kasa cimma shi, daga nesa take ta kwada mai kira tana "R-Lema, R-Lema dan tsaya don Allah" shi kuwa yaji wannan kiran da ake mai, amma be tsaya juyowa balle ya ga ko waye, a tunanin shi irin mutanen nan ne da suke binshi a school, be juyo ba balle ya tsaya ya cigaba da tafian shi, ita kuwa bata fasa binshi ba, ba ta fasa kiran shi ba, bata damu da yanda ake kallon ta ba, "Rafeeq Please tsaya" wani tunani ya zo mata ta dan daga murya tace *"Hamma Rafeeq"* Chak ya tsaya, gaban shi ya yanke ya fadi, Muryan K'anwar shi yaji, a hankali ya furta "Rafee'ah?"...
_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
*Sometimes, its hard for you to figure out what to write when you want to tell someone how much you Appreciate them, but it does'nt matter, i'll say it and write it anyhow. She's more of a Mentor, A Role Model, a Teacher, A Guide, A Respected, Loving and Caring Person, She's one who always wants to share, she's Determined and Confident, Her Support and Advice has helped lotta people, she has touched lives, ofcourse she's touched Mine and lotta people i know, She's Simply Amazing coz She's her, She's AUNTY SIS.*
*This page is for you Aunty Sis*
Pg3⃣7⃣
A hankali ya juyo, suna hada ido da Nasiba, yayi saurin dauke ido yana waige waige, kamar me neman wani abu, a hankali ta sake furta *"Hamma Rafeeq"* Mamaki ya lullube Rafeeq, tabbas ya san shi muryar Rafee'ah yaji, duniya ita kadai ke ce mishi Hamma, a ranshi yace *"to wannan kuma fa? Why is she sounding like my sister?"* a hankali Nasiba ta fara magana *"Mungode Sosai da wannan hidima da kayi damu, Allah shi saka da Alheri, Allah ya biya ka"* ta na kaiwa nan ta juya ta koma cikin Asibitin, shikuma yayi tsaye kamar an dasa shi, ya kasa motsi, shi beyi gaba ba, shi beyi baya ba, mamaki da tsoro ya kama shi, ya shiga tambayan kanshi, *"Meyasa wannan take magana kamar Rafee'ah, there's something about her, i just dont know how to describe it"* da kyar ya shiga mota ya bar Asibitin Jiki a Sanyaye.
Tunanin wannan dawainiyan da Rafeeq ya musu take tayi, komai ya tanadar musu, ashe yana da kirki? ashe Zuciyar shi bata ida macewa ba? Ashe yana da sauran kirki tattare dashi? Toh in ko haka ne, ba zai wuyar tankwaruwa ba, Allah ya bata saa Amin, ta kalli Nene tace *"Zaki ci Kaza?"* Nene ta kalle ta da mamaki tace *"bangane zanci kaza ba, naga dai don ni a ka kawo shi"* Seebi ta girgiza kai tace *"naga dai marasa lafia ba su fiye cin abinci ba, nama ma bai dame su ba"* harararta tayi tace *"ni ya dameni zubo min"* dariya sukayi gaba ki daya.
*Rafeeq* zaune yayi tagumi hannu bibiyu, ya lula duniyar tunani, shi fa be fiye tunani ba, amma tun da ya dawo daga Asibiti ya ke tunanin wannan yarinyar, mamaki yake mesa take abubuwa kamar Rafee'ah? Mesa take kiran shi da sunan da kanwarsa kadai ke kiransa da shi? Ko ta san fee'ah ne? Maganar ta komi na yana mai kama da na Fee'ah, haka kurum yaji a ransa yana son sake ganin ta.
*WasheGari*
Rafeeq ya shirya don yana da Morning lectures, ya fita daga dakin shi, a tsakar Gida ya ci karo da dukka 'yan gidan, dauke kai yayi kamar be gansu ba ya chanza hanya ya nufa motar sa, Alhaji Habib ya ciri baki yace *"Rafeeq"* kamar ba zai juyo ba ya juyo yana kallon su one by one, Daddy, Saude Meema sai Aneesa ne a tsaye, wani gololon bakin ciki yaji da ya hada ido dasu duka, dadi kamar ya kashe Aneesa yau tayi tozali dashi, kwana biyu ta lek'a dakinshi sai taji a kulle, a hankali ya tako gaban su kallo daya ya ma Baban shi, da kyar yace *"Daddy Barka da Saffiya"* Alhaji Habib da murmushi a fuskar shi yace *"Ibn Zaid ka tashi lafiya?"* kai kawai ya gyada mai, yace *"Zanyi tafia, zanje Abuja , zanyi kwana biyu"* yace "Sai ka dawo" "yaushe Baban ka zai dawo?" a k'agare yace *"Upperweek"* *"baka gaida Auntyn ka ba"* da sauri Rafeeq yace *" na makara, na tafi"* ya wuce ya bar su tsaye a nan, Saude ta bude baki cike da mamakin Rafeeq, Alhaji ya wayance *"Rafeeq kenan, an samu yau zai je school"* Aneesa tayi saurin bin shi a baya, "Ya Rafeeq jira ni nima makarantar nayi, sai ka ajiye ni" be tanka ba, burinshi ya fada motar sa, *"Ya Rafeeq mana"* tayi saurin shan gaban shi haushi ya kama shi, shi dai ya tsani Aneesa,cikin hargowa yace *"zaki matsa min ko sai naci Ubanki"* Duk diramar da akeyi akan idon Saude,Meema da Alhaji akeyi , ita kuwa Aneesa dadi ya kama ta, yau wace rana Rafeeq ya mata magana, ita ba ta k'i ya dinga lailaya mata Ashar kullum ba, indai shine hanyar maganar shi gareta, Rafeeq ya lura kwata kwata hankalin Aneesa be gun shi, ta tsura mai ido tana zabga murmushi, tsaki yayi