Showing 18001 words to 21000 words out of 149166 words
gudu ya nufe shi ya je ya rungume shi, shi ko Zaid ya daga shi sama yana "Oyoyo my boy" i've missed you so much, look at you" Rafeeq dan shekara 5 yace "welcome home Uncle Zaid" yace "Thanks son, ina baby Rafee'ah? Cikin hausan shi da be fita Rafeeq yace gata chan tana fushi wai ka daukeni" Zaid ya sauke shi yace "Ohh my baby come here" da gudu ita ma tazo ya dauketa, suka ida shiga parlorn, Sai da ya durkusa har K'asa ya gaida Aishatu da ke ta faman jera mishi sannu da zuwa, kafin ya kalli Yayan shi yace "Barka da Rana Yaya" Habib baki sake kamar soko yake kallon Zaid, kwata kwata ya chanza kama, kamar wanda aka ma wankan Engine yayi Jazir yayi kyau. Suka gaisa, kafin kace kwabo Aishatu ta cika shi da abinci.
Kamar daga sama Hafiz ya fado Parlorn, da Zaid ya ci karo, kamar wanda yayi Gamo da Aljan yayi saurin juya wa, ashe Habib na kallon shi, yace "Hafiz ina zaka, baka lura da danuwan ka bane? Ba yanda zaiyi dole ya dawo.
Wani murmushi ne kan fuskar Hafiz mai wuyar fassaruwa, yace " Hello brother, its good to see you again, welcome home"
Zaid ya hadiye miyau, ya shiga tunanin baya, komai ya dawo mai sabo, ya sake hade wani bakin miyau, be san murmushin da Hafiz keyi na meye ba, a ranshi yace Allah ka min tsari daga Sharrin me sharri" a fili kuwa yace "Thanks, its good to see you too".
A year Later(Bayan Shekara 1)
Zaid ya gama bautar kasar shi a shekarar shi ta 23, Hafiz kuma a Shekara 24, Zaid Ya zama wani Azabbaben Guy, tun yanzu mata ke kawo mishi hari, Aishatu ta mishi maganan Masters yace, sai yayi settling. Rafeeq da Rafee'ah na ta zuwa school, da aji daya Rafeeq ya fi Rafee'ah, Dukkan su Allah yayi musu Baiwa na Kokari...
"Kutumar Uban chan" Hafiz ya lailayo wata ashar, wa nake gani kamar Anas? Anas da ya koma wani Giant, Giya ta hura shi yayi daria yace "ni ne fa" Hafiz ya diro daga kan mota suka rungume juna, yace ashe "rai kan ga rai"? Rabo na da kai tun kafin in dawo Nigeria, kuma na yi ta kiran wayan ka baya shiga, gashi bansan gidan ku bare naje(wai duk abun nan, Hafiz bai san Gidan su Anas ba, What a fool😆). Anas yayi daria yace " wallahi na koma Porthacourt da zama" chan nake sana'a" Hafiz yayi shewa "da kyau maza, wannan wace irin sana'a ce da yayi transforming dinka lokaci guda? Duk ka koma wani Don? Anas yayi darian yan bariki, yace " abun sirri ne" Hafiz yace haba mutumen, kar ka min haka, ka fada mim hanyar samu nima in karu, Anas yace "Zaka iya?" Hafiz yace koma menene zan iya, indai har zan samu kudi" Anas yace "haka ne, kasan sai da kudi ake neman kudi, akwai kudi gurin ka? Hafiz yace "aa babu, kamar nawa ake bukata?" Anas "yace half million(#500,000). Hafiz yayi jim, sannan yace Ba matsala, i'll find a way, like always."
Rana Dubu na Barawo....
Babu inda Yaya Zai ajiye Safe dinshi da wata kadarar sa, indai ba a bank ba, toh defintely a Office din kusa da dakin Baccin su ne, tunani Hafiz ke nan, ya zaiyi ya shiga ciki ba tare da kowa ya ganshi ba? Anas ya kira don shawara, Anas yace "kar ka damu, ina da master key din da zai iya bude ko wani kofa, kawai dai bari sai daren, sai na zo muyi operation din tare.
Da daddare misalin 12:30 na dare, Anas da Hafiz basu sha wahalan shiga Personal Office din Yaya Habib ba. Suka shiga neme nemen, Hafiz ya jawo wata yar durowa, sai ga wata tamfatsetsiyar Agoggo Swatch ta fado, murna ya hau yi, Drawer na biyu kuwa wani Safe ne a jikin tare da kwado, Hafiz yace "Anas look what i've found, it got a small lock" Anas yayi daria yace "worry not, i gt a small key" ya sa dan karamin key, tsaf kwado ya bude.
Wurin bude Safe suka ji gam, insert password ya nuna musu, Hafiz yayi murmushi, yayi typing, *Habib Lema* lock ya ki buduwa, ya yi typing *Habibullah* incorrect password, yayi tsaki ya yi typing *Habib* a nan warning alert ya fara, Anas yace "meye matsalar? Dama baka san password din ba?"
Cikin barci yaji Alert mai karfi, a firgice ya tashi don ya jima da kwantawa, ya kunna bedside lamp, ya duba gefen shi ya ga Aishatu na barshi, still Karan na kara yawa, wayar shi ya shiga lalube, don a zaton shi Alarm ne, duk da beyi tunanin yayi setting Alarm ba, Ya duba ya ga ba wayar bace, ya dan fara bubbuga Aisha don Karan na kara yawa, ta tashi tana mutsitsika ido, "yadai Daddyn Rafeeq?" yace tashi"ki kashe Alarm din nan na wayar ki" cikin mamaki tace "Alarm dai"? Ta kalli Agogon dakin taga 12:40am, tace kai "Aa, ban sa wani Alarm ba".
Habib ya Sauko daga kan Gadon, nan yaji karar ta wurin bedside drawer ne, ya dan matsa gurin. Zuciyar shi ta ayyana mishi *Brief case*Da sauri ya nufa Brief Case dinshi, don ba tantama *Warning Alert* din Safe din shi ne.
Da sauri ya bude pincode din ya dauko wani dan karamin Machine kamar dan Ipad, Aishatu da dawo kusa dashi, Habib ina tunanin ba mu kadai ke gidan nan ba, ka hanzarta kiran Polisawa, yace Aishatu whoever this is, he's among us, in ba haka ba, wa ya san ina da office cikin Gida?.
A Zuciyar shi, ya ce Zaid ne, aiko zai dauko mummunar mataki kan Zaid, yace "ba sai na kira police ba, i can handle this, idan nace miki Zaid na da Halin banza bazaki yarda ba, bari na nuna miki proof" wasu danne danne yayi a jikin machine din sai ga Fuskokin Hafiz da Anas sun bayyana, suna ta fama da saka incorrect Passwords. A hankali Habib ya furta "Hafiz? No it cant be" Aishatu ko batayi mamaki ba.
"I dont know where the problem is, amma for sure Yaya sunayen mu yake sa as passwords, misali kaga zaiyi naming password after the owner, kamar ka ga da na dauki Safe din Zaid, karon farko na saka Zaid lema Safe ya bude, toh ban san mesa wannan yaki budewa ba, na saka Habib, na sa Habibullah duk sunki budewa, could it be possible ya sa Sunan First Son dinshi?" Rafeeq? Yes thats it! We are rich bro, password din is Rafeeq"
Habib najin Haka ya zabura a guje yace Shikenan Aishatu ya gano Password din, Da Karfi Habib yace *Hafeeeeeeez*!! Sai da Gidan Ya amsa.
_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg1⃣8⃣
Ihun da Habib yayi ne ya tashi Zaid da Mdaga bacci, da sauri ya fito suka fito daga dakin baccin shi, yayi cikin Gidan don ya san tabbas ba lafiya.
Hafiz a kidime yace " Akwai Matsala" Anas yace "mu ware kawai" Hafiz yace "aa its too late, lets just act smart" daidai nan Habib, Zaid, Aishatu suka shigo dakin.
Zaid ya damke Anas, Habib kuwa bai yi sanya ba ya chakumo wuyar rigar Hafiz yace "What have you turned yourself to? A monster? A heartless, selfish person? Me ya sa ka dauke Safe din Zaid? Bayan kowa an bashi Kason shi? Ka k'ulla mai sharrin shi ya dauka, Wannan wani irin cin Zali ne?" Zaid ya kalle su cikin rashin fahimta, yace "whoa!, wani Safe aka dauke nawa? Hafeez cike da borin kunya yace " I dont know what You're talii about, let me go" Habib ya kai mai nushi a baki, ya ja wuyar Rigar shi har gaban TV din Office din ya kunna, ya kara jan shi har gaban Safe din ya saka Password din, Safe ya budu, dan karamin security camera da ke jone da Safe din Habib ya danna, sai ga fuskokin Hafiz nan da Anas tunda suka fito da Safe din, duk abubuwan da suka fada sai da suka gani kuma suka ji kamar a film, Zaid ya dinga maimaita Inalillahi wa ina ilaihir rajiun, Be son sanda ya sake Anas ba ya nufa Hafiz cikin zafin nama, Anas na gannin haka ya arta a guje. Zaid na zuwa ya daga hannu ya faska ma Hafiz mari har kala 2, yace "how dare you Hafiz?" dama kai ka dauki Akwatin nan kace nine? Ka sa Yaya ya tsane ni? Ka sa ni cikin Halin Kunci? Hafiz me na maka? Ni da kace ka na son kudin wallahi zan mallaka maka halak malak, amma sai ka bi ta bayan Gida, Hafiz i wont forgive you "
Hafiz ya fashe da daria cikin borin kunya wacce aka ce da hauka ake nadeta, yace " *So what? Now that y'll know my deepest secret, what are you going to do? Ehh? Ya kalli Yayan shi what are u going to do Habib Lema? Hand me over to the police? Go on you never cared dama, ka kira min polisawa su tafi da ni, kaga ko ba wani Abu bane don dan kishiya ya tura kaninsa gidan kaso(jail)*."
Zaid yace "Kar ka damu Hafiz, ai daga nan Police station kayi, naga you are so eager ka ganka behind bars(bayan kanta.) Hankalin Habib ya tashi ba zai taba tona asirin Gidansu ba, hada Hafiz da police kamar tona ma marigayi mahaifinsu asiri ne, Habib ya kalli Zaid yace "Zaid, so kake Hafiz ya biya ka kudi da kaddarar da ya satan maka?" Zaid yace "ni ba abunda zanyi dasu, Burina Allah ya ji kan mahaifa na, ya ji kan yanuwa na" Habib yace "Madallah, let him go" a tare Zaid da Aishatu sukace "what?" Habib yace Hafiz is our Family, kar mu tona asirin junan mu, mu taya shi da Adduan shiriya" Zaid be tanka ba ya bar office din, Aishatu ta bi bayan shi, Habib ya kalli Hafeez cikin sanyin murya yace"Jeka kwanta its late" Hafiz kunya da tausayi suka lullube shi, ya sa hannu cikin aljihun shi ya ciro Agogon Swatch din da ya sata, ya mika ma Habib yace "da a ce baba na da rai, he'll be very oroud of you Yaya" habib ya sa hannu ya amshi Agogon ba tare da yace komi ba, shi ko Hafiz ya sauka kasa zuwa dakin shi.
Cikin dare Hafiz ya tattara kayan shi tas, ya ciro wayar shj ya kira Anas, Anas a tsorace ya dauka yace "hello, matsoraci kana ina,?" Anas yace kaii kaji yanda hanji na suka kada, na mugun tsorata?" Hafiz yayi dan tsaki yace "kai ni zo ka dauke ni ina nan ina jiran ka" Anas yace wa? Ba dai ni ba, bari ma turo maka Escaley kawai" cikin mintuna kadan Escaley ya kira Hafiz yace mishi yana waje, Hafiz ya kwashi kayan shi da kyar ya fita waje, Escaley ya taimaka mishi, Mai gadi na tsaye yana kallon ikon Allah, farar takarda Hafiz ya ciro ya ba mai gadi, yace ya ba Yayan shi ko Zaid da safe, me gadi yace "Oga Hafiz ina zakaje da daddaren nan, 2 ta kusa fa" be amsa shi ba ya shige mota Escaley ya ja motar.
Tare suka dawo daga Sallahr Asuba, tun a hanya ba wanda ya kula wani, Zaid fushi yake da yayan shi kan abun da ya faru da daddare, Habib kuwa ya san dole ran shi ya baci, don ba a kyauta mai ba da be dauki wani hukunci kan Hafiz ba, Zaid ba zai gane ba, be san halin mutane ba, ana iya cewa don Uwar su ba daya da Hafiz bane ya tura shi prison, Amma zai mishi bayani idan ya sakko. Suna shiga Gidan mai gadi ya ciro takarda ya mik'a ma Ogan shi Habib yace "inji Hafiz, jiya karfe 2 ya bar gidan nan" hannu na rawa Habib ya warware takardar, Zaid har yayi gaba ya dawo don yana son jin me Hafiz ya rubuta a wannan wasikar. A bayyane Habib ya fara karantawa, ga abun da ya rubuta nan ;
"*I know i'm a disgrace to this family, which is why i left you, na barku, zan shiga duniya, kar ku neme ni, ku mance kuna da wani danuwa me suna Hafiz, ba zan bari ku kara gani na ba, ku Shafe Hafiz Lema daga babin rayyuwan ku, saboda Hafiz Lema doesnt exist, Enjoy your lives without me brothers"
Ba Habib ba harta Zaid sai da hankalin shi ya tashi, tsakanin danuwa da danuwa sai Allah, Jini ba wasa bane, nan da nan Zaid ya fara hawaye, da gudu ya shige daki Habib ya bishi a baya, Zaid ya dauko wayar shi ya shiga neman layin Hafiz sai da ya mishi missed calls nawa kafin ya dauka, A dake yace Ya akayi ne Zaid? Zaid na kuka yace DonAllah Hafiz ka dawo, kar ka barmu, Wallahi na yafe maka, ka dawo, nd i promise we'll be like Nothing wrong has ever happened, donAllah, i need You. Hafiz ya fashe da dariya, yace "You dont need me oo, idan na tsaya zan cigaba da yi muku barna ne, gwara nayi nesa daku, kar ku sha wahalan nema na, don ba za ku taba binciko ni ba" Zaid ya fashe da kuka, Habib yayi saurin karban wayan, ya kara a kunnen shi, yace "Hafiz ka saurareni" Hafiz ya katse shi, yace "Yaya kar ka bata bakin ka, i've decided, be Happy brother kafin yace wani abi Hafiz ya latse wayar. Habib ya shiga neman layin yaji swtiched off ashe Hafiz fito da Sim card din yayi ya tauna a bakin shi ya zubar.
_Bayan Shekara Sha Biyar_ *(15 Years Later)*
Gidan Alhaji Habib Lema cike makil da mutane , da Alamu Biki akeyi, Hajia Aishatu na hango zaune kan Gado cikin wata tanfatsetsiyar Leshi, kamar yarinya yar shekara 20, sam girma be nuna a jikinta ba, shigowa akeyi ana mata Barkan an daura aure lafiya, wasu mata suka shigo suna fadin "ina Uwar Ango take, taje ta fito mana da Amarya?" ta tashi tana daria, tana fadin "Ni da kaina?" suka ce " ke fa da kanki Maman Zaid tunda da bakin ki kikace Zaid ba kani bane, d'a ne" tayi daria ta nufi inda aka tanada domin Amarya da kawayen ta Amare, ta shiga da Sallama suka amsa tace ince dai kun gama kimtsa min Amarya ta? Duk sukayi daria, Amarya Safiyya ta sunkuyar da kanta, Aunty Aisha ta nufeta ta dago kanta, tace "MashaAllah, Safiyyah kinyi kyau, ku muje Filin Launcheon din, an tattaru Amarya kawai ake jira"
Ango Engr Zaid Lema Suka shigo filin launcheon da Abokan shi, İnda aka tana da domin su suka zauna, Amarya ma aka rakota har gurin Angon ta, Bayan Aunty Aisha ta bude taro da Addua ta ma manyan Baki sannu da zuwa ta koma ta zauna kusa da Mijinta Alhaji Habib Lema.
Dj ya kunna kida gida ya kaure da sauti, gudu yake yana bangaje mutane, babban burin shi ya ganshi a filin rawa, Maalesh na kwala mai kira kan ya bar gudu ya ki, har hularshi ta fadi, Maalesh yace "ka ga hular ka ta fadi, ka tsaya ka saka" ina samm bai ji ba. Sanye yake da kaya komai iri daya Da Ango Zaid wato farin Shadda Kaftan mai Malummalum, yana zuwa Filin rawan ya wani ci burki, ya fara kallon kowa one by one, ya juya ya kalli Mamin su ta girgiza mai kai alamun kar yayi, ya kashe mata ido daya(wink), Abban su kuwa murmushi ya mai, Ya kalli Uncle Zaid Ango, ya daga mishi gira alamun go ahead haba kamar wanda aka sa ma battery, ya fara takunshi daidai da sautin kidan, abun be mishi ba har sai da ya cire Malummalum dinshi ya wulla ma Maalesh ya cigaba da rawan shi yayi gaba yayi baya. Ango Zaid yace ma amaryar shi "kinga mutumin ki na cizgar rawa ko?" da yake ba kallo take yi ba kanta a kasa yake tace wanene? Zaid yace "waye in banda RAFEEQ?"
_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg1⃣9⃣
Amarya ta dan daga kai taga tabbas Rafeeq ne ke wannan chashewar, wuri ya dauu sowa sabida Rafee'ah ta tashi cikin takun ta ta biyo Rafeeq filin rawa tana mishi like, shi ko sai rawa yakeyi iya karfin shi. Sai da Zaid ya mishi alamun ya isa kafin ya tsagaita.
MC ya fara gabatar da shirin Biki, Hajia Aishatu ta bude taro da Addua, Rafeeq ya bada tarihin Ango, biki yayi biki, anci an sha, an gwangwaje, Rafeeq da Rafee'ah sun taka rawar gani, shima Ango ba a barshi a baya ba don sai da Rafeeq ya sashi rawan dole, akayi hotuna, sukayi Family Photo.
Washegari aka daure aure, aka kai Amarya Gidan ta da ke Kaduna U/rimi, da yake chan Zaid yake aiki. Part daya aka ware ma Rafeeq a gidan Zaid don Zaid da Rafeeq kamar abokai suke, ba za ka gansu kace Kawu da dan shi bane.
Rafeeq dan dangi ne,duk inda ya gifta sunan shi kawai zakaji ana kira, yanuwa da abokan azziki, manya da yara, kowa Rafeeq, tabbas Rafeeq yana da farinjini, ba don komai ba don shima he's a simple somebody, ba ruwan shi da zabe, yace ina yi da wannan ba nayi da wannan, aa kowa nashi ne, yana da son mutane, da son wasa, ya ja wannan tsokana, ya ja wannan tsokana, maza da mata, bashi da kyamar talaka. Rafeeq fari ne, bai ciki tsawo ba, bai cika gajerta ba, dan daidai, be da kauri sosai, kyakyawa ne ajin farko, har friends dinshi na mai kirari da ''all ladies eyes on Rafeeq'' duk budurwa mai ji da kanta ta na so a ce da ita budurwar R-Lema, saboda ya hadu, Arzikkin baban shi be sa shi girman kai ba ko kadan, haka fa yake a