Showing 15001 words to 18000 words out of 149166 words

Chapter 6 - Ke alkhairi ce COMPLETE HAUSA NOVEL

BIEBIE   

22 Oct 2024

25715

a tunani na wasu yan ta'ada ne sukayi gaba da Dukiyar maraya, Ashe shi da kanshi ya dauke kayansa. Ran Baba Tj ya baci yace "kai Zaid meyasa ka dauke Ma'ajiyar ka ba tare da sanin wan ka ba? Zaid ya girgiza kai yace "Baba, banda masaniyyar abunda ya faru, ku yarda dani wallahi"

Habib ya jefe shi da mukullin motar sa. Yace "ni kana bata min rai idan kana rantsuwa a kan karya, tsaya kaji Zaid, ni ba ka ban haushi ba don ka bukaci hakkin ka ba, da ka gaya min kana da bukata da da kaina zanje na dauko na damka maka komai kamar yanda na ma danuwan ka, amma kai kaje ka dauko, ka tada min hankali, yanzu kuma kana ta rantse rantse ka ki amsa wa." Zuciyya ta dau Zaid, yace Yaya shi kenan, na dauki Save dina, ina da bukkatun na shiya sa na dauka, ka yi hakuri idan na tada maka hankali. Yana kaiwa nan ya tashi ya bar musu parlon.

Aishatu tace "anya Baba anyi ma Zaid adalci? Ai ya kamata ayi bincike, Habib yace wani bincike kuma? Bakiji ya amsa laifin sa ba? Tace ya amsa ne don bai da mafita, bayani yake muku amma ba ku son yarda, hasalima da ya fara bayani kuke katse shi, be da wata mafita in banda ya amsa laifin da bai aikata ba. Idan ana maganan irin wannan tarin dukiyar, be kamata ace an bar magana haka ba, what if Zaid bai dauka ba? Shikenan dukiyar ta salwan ta? Nidai ina ganin ayi bincike" Hafiz ya shiga hararrar ta a ranshi yana kiranta 'munafuka' Baba Tijjani yace kuma maganar ki Aisha abun dubawa ne, dole a yi bincike kam. Hafiz yace "toh a fara da dakin shi mana?" Zaid yace "wani gun zai kai ai ba zai aje a daki ba" Hafiz yace muje dai mu duba, dukkan su suka nufi waje don zuwa dakin Zaid, dakinshi ne na farko sai na Hafiz, Hafiz ne a gaba suna bin shi a baya har Aisha. Zaid na ciki yana kuka yana ganin su ya tashi ya matsa gefe, Hafiz ya shiga neme neme a wardrobe, Habib na daga katifar Gado sai ga Save na kallon su, gabaki daya suka sake sallati. Habib yace "Ahap, ai na gaya muku, ni na sani gashi nan dai, Habib ya ciro save din ya bude password din 'Zaid Lema' wayam ya ga save din, ko allura babu, Zaid ya hadiye wani irin mugun bakin miyau, ya san bai da wata mafita. Habib yace kagani ko Baba? Ba komai cikin Save din, ya salwantar da su. Baba Tijjani ya girgiza kai, yace "Zaid, ka bata wayonka" ya fita, Habib da Hafiz suka bi bayan shi.

Aishatu ta kalle Zaid cikin ido, hawaye ne malale kan kumatun shi, fuskar nan tashi tayi Ja, tace "Zaid why?" girgiza kanshi yayi yace "Aunty wallahi i didnt do it" gyada kai tayi tace "i believe you".

Bayan Sati 2.
"Haba Habib, meyasa kake haka, don me zaka biya ma Hafiz kudin makaranta ka ce ba ruwanka da Zaid, ya biya ma kanshi? Naga dai da Hafiz da Zaid duk daya suke a gunka?" yace "Aisha, Ni Zaid ya sire min, ya bata wayon shi, ya ban kunya, shi yasa na zame hannu na kan lamarin Zaid, tunda yana da kudi sai ya biya ma kanshi duk makarantar da ya ga dama a fadin duniyan nan" tace "wai shin in ma haka ne, ai naga Hafiz shima an raba Gadon nan an bashi, shima yana da kudin nan, ai sai ka biya musu duka, ko ka k'i biya musu duka, duk su biya ma kansu, yace "hakan na ga daman yi" tace "kana raba daya biyu, na fa lura da kai, tun bayan da abun nan ya faru ka ke kyaran Zaid, ko gaisheka yayi baka amsa wa, ko yaranka ya dauka sai kayi ta mishi fada,kana hantarar sa, haka akeyi? Kar fa ka manta kaine uwarshi, kaine ubanshi. Habib yace "ke Aishaba abunda ya dameki, ko taro ba zan sake kashewa kan Zaid ba, and baki da hurumin yi min magana kan Zaid, duk randa kika sake cewa na ma Zaid kaza zaki fuskanci fushi na, this is my decision, and its final" ya tashi ya bar mata parlorn, Hafiz na jinsu, a ranshi yace wannan matar na shigar min hanci amma zan fyato ki...

Tafiyar Hafiz ta kankama, yau suka tafi Abuja shi da Habib, inda Jirgin su zai tashi zuwa kasar Malaysia, Zai fara karatun shi fanni Computer Studies.

Zaid ya ci kuka da ya ga Hafiz ya tafi, dagaske Yaya Habib yake kenan, dagaske ya zame hannun shi daga lamuran shi, toh shi ya zaiyi? Shi kenan ba zai yi karatu ba? Burin shi na zama Injiniya ba zai cika ba? Wa zai sponsoring dinshi? A yau ne yayi kuka sosai, a yau ne yake kukan Maraici. Ji yayi ana share mishi hawaye, ya dago kai da sauri, Rafeeq ya gani da sauri ya dauki yaron ya rungume shi yana hawaye. Aishatu tace Zaid tashi share hawayen ka. Ya dan zabura, ashe ba Rafeeq kadai ya shigo dakin ba, ya dan kwakulo murmushi yace Aunty tun yaushe kike nan? Tace "tunda ka fara sambatu" anan ne ya fuskan ci zancen zucin da yakeyi ya fito fili. Yace "Aunty yaya ya dauke Hafiz ya kaishi Malaysia, ni ina nan, ba sanaa ba karatu, ni ina ga zan fara aikin karfi kamar Welda ko Kanikanci, idan na tara sai na siya Jamb in cike ko ABU Zaria ne. Aishatu tace "kai Allah ya sawwake, Wallahi kafi karfin yin Welder ko Kanikanci. Aunty ba yanda zanyi, dole zan nema sana'a dole inyi karatu, ina son cin burin,tunda ba wanda zai dauki nauyin karatu na dole in tashi tsaye don neman yanda zan cigaba da karatu na. Aishatu ta mike tsaye, tace Zaid, ni Zan dauki nauyin ka, Zaid ka nemo duk makarantar da kake so a fadin kasar nan, in har be fi karfi na ba, Zaid zan tsaya maka da ga farkon karatun ka har karshen shi.

"Zaid i will Sponsor you if let me". Zaid da mamakin furucinta yace "Aunty, kar ki damu, bana son daura miki wani nauyi, ba kuma na son ki samu matsala da Yaya" Aishatu tace "Kar ka damu, ba wani nauyin da zaka daura min, ko ban auri Habib ba ni me iya daukan nauyin ka ne, Babana ya gaya min irin Halaccin da Marigayi Lema ya mishi, kaga ko ban fadi ba duk abun da na maka. Kuma maganar Habib, ai ya amince kayi karatu, yace dai kwabon shi ne ba zai yi ciwo ba a kanka, to kar ya damu kwabon shi ba zai yi ciwo ba, kuma zakayi karatu a Turai. Muje muyi searching relevant Schools before its late" ba ta jira amsar shi ba tayi waje. Cikin farin ciki ya dauki Rafeeq yana wulla shi sama yana cewa "Rafeeq maman ka wace iri ce?"

_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

Pg1⃣6⃣

A parlor ya iske ta ta ciro Latop dinta ta shiga yanar gizo, tace "wacce Kasa kake da burin karatu, kumae kake so karanta?" Ya danyi jim alamun tunanin yace "USA, ina son karantar Engineering". Murmushi tayi ta fara searching Relevant Schools a USA; tace " zo ka gani Zaid, ga wani Havard University Cambridge nan" ya matso, details din School da komai ta duba, tayi naam da makarantar, shima haka ama ba laifi makarantar zaiyi tsada.

Nan da nan ta fara ma Zaid processing, bayan Sati daya ta tura wani Yaron babansu da Zaid American Embassy dake Abuja don neman Visa. Komai ya kankama, don saura kwana 2 tafiyar Zaid Makaranta.

A ranar Habib ya dawo gida Bayan ya sada Hafiz da makaranta, ya mai Wa'azin da ko kofar kunnen shi be shiga ba, Habib ya tabbatar mai da cewa duk wata zai dinga jin Alert na shigo mai, Hafiz yayi godia Sosai.
Zaid ya zo mishi sannu da zuwa amma ko tanka shi baiyi ba, Aisha tace ya yan makaranta? Yace "Hafiz dan Malaysia ana chan bawan Allah, da zan taho harda kukan shi, ya ban tausayi". Aishatu tace "Allah Sarki, Allah ya bada Sa"ar karatu" yace Amin.

Tace "Shima Zaid dai ya kusa tafiya" ya dan zaburo, ina zai tafi?" tace "yo karatu mana a USA, ko nan zai tsaya ya lallace?" Habib yayi tsaki, yace kinga abunda nake gaya miki ko? Shi ya dauke dukiyarsa,in ba haka ba, waye zai biya mishi karatu a Havard University? Aisha tace "nice nan,ni na dauki nauyin shi, zan tsaya mai har sai inda karfina ya kare" cikin mamaki Habib ya kalleta yace "Ke Aishatu, ina mai umartan ki da ki janye hannunki kan Zaid, tace ita sam, ita ta sa kanta Shin ba kai kace ba ruwanka da duk wanda zai taimaki Zaid ba? Kaine dai kwabon ka ba zaiyi ciiwo ba?Toh ni zanyi sponsoring dinshi, i'll endorse him, Deal with it Habibullah! Ta fice ta barshi zaune da mamaki.

Kwana biyu ba zaman lafiya tsakanin Habib da Aishatu, Zaid yayi takaici, don a ganin shi shine sillar faruwan komai, har ya sameta yace "Aunty, tunda Yaya ya haneki da taimaka min, a bar maganan karatun nan kawai, Allah ya biyaki". Tace sam Zaid, karatu kamar ka tafi ka gama ne, i've spent alot on it, ba zan yi hasara ba, so make me proud, kaje kayi karatun ka, ta mishi yan nasihu da waazi.

WasheGari Zaid ya je Gidan Baba Tijjani ya maj Sallama, Ya dawo gidan yayan shi ya durfana gaban sa ya na hawaye yace "Yaya ka yafe min, kar kayi fushi dani, kaine Ubana, kaine Uwata, fushinka kamar na Iyaye ne, Yaya kayi wa Allah ka samin Albarka a karatun nan da zanyi"
Sosai ya ba Habib hakuri, shi yasan yana son kaninshi, amma fushi ya rinjaye shi, a ranshi ya sa ya yafe ma Zaid, yace "tashi ka tafi Zaid, Allah bada saa, a kula, know where you come from".

Rannan tafiar Zaid da kyar aka banbare Rafeeq jikin shi, kuka yakeyi kamar ana zare mai rai, Ko Rafee'ah da bata san komai ba sai da tayi kuka, Aunty Aisha ma ta koka.

4Years Later(Bayan Shekaru 4)

Abubuwa da yawa sun faru, cikin shekaru biyar nan, Ciki kuwa harda gama makarantar Hafiz da Zaid, ya kamata ace Hafiz ya gama ya dawo gida tun last 2years saboda Course duration dinshi 2and half year ne, amma shashanci da Iskanci ya hanashi dawowa, Hafiz ya kware a fannin Chacha da harkar cocaine (Gambling) duk Malaysian Gambling center sun san da zaman Hafiz, duk ya karar da kudin Zaid, kuma kullum shine tambayan Habib kudi, gashi duk bayan Wata 5 yake zuwa Nigeria, abun ya damu Habib amma bai yi magana ba.
Hafiz shine drugs, duk wasu kayan maye Habib ba wanda be sha. Amma abun alajabi shine, hafiz beyi kama da mai shan ko da sigari bane. Yanzu dai Hafiz ya talauce, baida kudin Chacha, baida kudin Cocaine, ga Bashi ana binshi na wurin Gambling, wasu thugs ke barazanar daukan rayuwar shi, sunce ya biya su, yace Yayan shi zai turo, shiru sukeji don tunda ya ma Habib maganar kudi shiru kakeji, zaman shi Malaysia baida wani amfani, Returning ticket dinshi yaje yayi renewing don zuwa Nigeria, Ogan Yan Chacha ya had Hafiz da wani yaron shi don ya bishu Nigeria ya taho musu da kudin su. Hafiz beyi gardama ba, don shima yana da bukatar kudi, dole ko yazo Nigeria Alabasshi idan ya kara hada wasu kudadden ya dawo.

Tunda Zaid ya tafi USA ya fara karatun shi cikin kwanciyar hankali, Kullum suna waya da Aishatu, Rafeeq da Zaid sun yi wani irin Shakuwa kamar yana Nigeria, da ya dawo school har ya san ya bude datan maman shi ya shiga Skype don suyi Video Call da Uncle Zaid, Rafee'ah tayi ta kuka kan Hamma Rafeeq ya bata wayar amma haka zaiyi banza da ita ta yita tsala ihu har sai Mami tazo ta amshe wayan ta bata ko shi Rafeeq din ya ga daman bata wayan. Duk wata Aishatu na raba Albashin ta ta tura ma Zaid rabi, Habib kan kira shi su gaisa, amma bai taba tura mai ko taro sisi ba itama Aisha bata taba tambayn shi ba. Wata sa'in idan ba a ma Aishatu Albashi ba, ba ta da sukuni, ta dinga zirga zirga kenan, ina zata samo kudi ta tura ma Zaid? Zaid ko yana fuskantar ta duk da ba ta fito fili ta gaya mishi damuwar ta ba ya kan fahimceta. Yace Aunty kar ki dinga damun kanki, zan sanu part time job a nan ko da Cafe ne, zanyi serving as Waiter. "Waiter? kar ka sake inji Zaid, kafi karfin nan, kar ka damu, i'll find a way to make money kaji?" yace "naji Allah rufa asiri" Jin ta kawai yayi, ba zaiyi kwance tana mishi komai ba, shima zai tashi don taimakon Kanshi.

Tun tafiar Zaid Shekara Biyar kenan be taba dawowa gida ba, a ganin shi takura ne ga Aishatu ko kudin Jirgi matsala ne, shisa duk yanda taso yazo gida fir sai yaki yace har sai ya gama toh gashi dai ya gama sai shirin dawowa.

BAYAN DAWOWAR HAFIZ.
Tunda ya dawo ya ke sak'e sak'en inda zai samu kudi, yaje Warehouse be ga komai ba, da alamu Habib ya chanza ma'ajiya. Tunanin mafita yakeyi, gashi ba zai iya tambayan Habib kudi ba. Wani tunani ya fado mai, da sauri yayi murmushi.

Karfe sha dayan dare(11pm), bayan Yara sunyi bacci, Aishatu ta dauke su ta kai dakin su, ta wuce dakinta ta tsala wankan ta, ta saka night gown ta fito ta jawo kofar tayi dakin Mijinta Habib, da sallama ta shiga, yace "Shatou na, har yaran sunyi bacci? Tace eh sunyi, Rafee'ah da rigima wai sai dai kar hamman ta ya Kwanta a cinyana, Habib yayi daria, yace "ina ruwan kishiyoyi, yauwa Shatou, dauko bargon dakin ki, jiya naji sanyi wallahi, tace kamar akwai bargo a nan, yace "eh yayi k'ura, gobe zan bada a wanke" tace "toh bari naje na dauko" ta juya ta fita a hanzarce.

Hafiz na ganin Shigewar Aishatu dakin Habib yasan ita da fitowa sai gari ya waye, sadaf-sadaf ya shiga dakinta, drawern madubi ya je ya jawo be ga wani abun dauka ba, side drawer ya koma ya bude, dubu biyu da dari biyu ya gani (#2200) ya gani ya zare ya sa a aljihu yace ko sigari na sha. Yana jawo na kasan ya ga wayam, kamar ance ya ciro dirowar ga baki daya, yana cirowa sai ga wani dan case a kasa, ya ciro case din hannu na rawa, yana budewa ya ga wata dankareriyar Saitin Sarka da yankunne, da abun hannu da zobe, tsaf ya gane sarkar ce da ya siya ma yayan shi a matsayin gudummuwa lokacin bikin Aishatu, ihun murna ya sake harda yar hamdalan shi, yayi daria yace "wannan shi ake cema ja ya fado ja ya dauke" yayi sauri maida Drawern ya tura case din cikin rigar shi ya mik'e don fita. Juya wan da zaiyi wa zai gani? Aishatu ce tsaye kikam tana kallon ikon Allah hannayen ta kan kirjinta.

_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

Pg1⃣7⃣

Iyakar tsorata Hafiz ya tsorata, ga case rike a hannun shi ba wurin boyo, amma da yake Hafiz namijin duniya ne sai yace "Aunty, ashe baki kwanta ba" kallon kai dakata ta mishi, tace "meye a hannunka?" yayi dan murmushi yace "Oh wai wannan? Sarka ne da yan kunne da na ba Yaya Ajiya kwanaki na dauki kayana" baki bude take kallon shi, tace "kai Hafiz kaji tsoron Allah, ajiya ka bashi ko kyauta? Ina cewa kayi ya sa a Lefen sa, shine gudumuwar ka?, kasan daukan abun wani ba tare da Izini ba Sata ne? Ya kalleta shek'ek'e, yace "Sata? Ta ina ya zama sata? I bought it da kudina, don na dauki abu na shine sata? Its mine anyways. Tace " its fine kai ka siya, i knw that, don ya gaya min, Hafiz Ka riga ka bashi, shi kuma ya bani, ko shi baida iko akan shi, its no longer yours". Yace "Madam, its mine, noone can get it from me, not even your husband, saboda haka sai da safen ki, idan kin isa ki gaya mishi ya zo ya amsar miki". Ya wuce ya barta tsaye.

Aishatu da dafe kai, wai Hafiz ke gasa mata magana haka? Duk Habib ya ja mata, da be amsa ba tun farko, da wannan ranar ba tazo ba. Tabbas ta san duk cikin Sark'ok'in ta ba wanda ya kai na Hafiz? to ya za tayi tunda ya bukaci abin shi? A fili tace "Allah shi kyauta" Zuciyar ta ta ke waswasin gaya wa Habib? Toh tace mishi me?Ta haddasa fitina tsakanin su? Balle shi Habib dake matukar son Hafiz, ko Zaid be so haka.
Kuma bata son wani abu ya kara shiga tsakanin ta Hafiz, don tsakaninta da Allah tsoron Hafiz takeji, yanayin sa na bata tsoro, a ranta ta kudiri cewa ba zata gaya ma kowa ba, idan yayi wari sa ji, ta dauki Blanket dinta ta datso kofar ta, tayi dakin mai gidan ta.

Da Sassafe Hafiz ya je kasuwa don saida Sarkar nan, kasancewar ta tsaddadiyar sarka tun shekara biyar da suka wuce, da aka auna Kadan ne babu cikin Miliyan, Naira dubu dari tara da goma(910).
Hafiz ya cire 650 ya ba yan Malaysia ya rike sauran da niyyar zai je Lagos Gambling kila ya ninka kudinshi so biyar (Allah ya shirya ka Hafiz.)

Matashi dan kimannin shekaru 22 yayi sallama a kofar parlon Habib da ke zaune shi da iyalan sa, Habib ya dago kai tare da amsa Sallaman, kallon shi kawai yake yi yana son tuno fuskar, Aishatu ce ta mike tace "Zaid?" Rafeeq ya sake Ihu da karfi, da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login