Showing 66001 words to 69000 words out of 149166 words

Chapter 23 - Ke alkhairi ce COMPLETE HAUSA NOVEL

BIEBIE   

22 Oct 2024

25725

tare da kulle dakin da Mukulli ya bi bayan Rafeeq.

Bakin Zauren Gidan Maalesh ya doka Sallama "Assalam Alaikum" daga Ciki Nene ta Amsa, tare da cewa "Bismillan ku" Maalesh a gaba Rafeeq na bin shi a baya sai shan k'amshi yake tayi, kamar an ce dole sai ya shiga, ta Window Nene ta hango su, da sauri ta fito tana tafa hannayen ta, tana fadin "Ga Maalush ga Maalush" wani Murmushi Rafeeq ya saki ba tare da ya sani ba, suna hada ido da Nene yayi saurin daure fuska tare da dauke kai, ko meyasa be so taga Murmushin shi oho,a fili Nene tace "Chan ta Matse maka a matsatsen wandon ka"Maalesh ya fashe da daria, yace Nene ke dawa?" ya juya ya kalli Rafeeq da ya hade girar sama da ta kasa, Nene tace ni rabani da wannan Mara fara'a, Sannun ku da zuwa dai" ta bude baki tace "Seebi, fito da tabarma, ga Malush da Dunkum" Maalesh dai sai daria yake tayi, Hajjo ta fito, suka gaisa da Maalesh, tace "Rafeeq" Murmushi kadai ya mata, ya dauke kai, Nene sai ikon Allah take kallo, a ranta tace "Lallai yaro, kazo gidana ka dinga sha min kunu? To uban tauri ma yaci ubanshi" ta gyada kai ta shiga cikin kichin don ita kadai tasan me zata ma Rafeeq, Nasiba taji dadin zuwan su, ta dauko Tabarma ta fito kanta a k'asa ta shinfida musu, Maalesh ya fara zama sai Rafeeq, Maalesh ya bita da ido, ta dukursa ta gefen da Rafeeq ke Zaune tace "Ya Maalesh, Ina Wuni?" Maalesh yace "Lafiya lao Beautiful, ya Jikin Nene?" "Nene ta ji sauk'i Alhamdulilah" Kafin yace komi wayar shi ta fara ringing, ya dauka, Nasiba ta kalli Rafeeq, duk da ba ita yake kallo ba yasan shi take kallo, kamar ance ya kalleta, Idanuwan su suka hadu, ido cikin ido suke kallon Juna, a sanyayye Nasiba tace "Hamma na Ina wuni?" tsaki yayi ya dauke kansa, ko a jikinta ta tashi ta koma ciki, da sauri ya bi bayanta da ido, duk ya ji haushin da be amsa ta ba, tsaki yayi ya juya ga Maalesh, ashe tuni ya gama wayar, kallon juna sukayi, Nene ta katse musu hanzari, gaban Maalesh ta ajiye kwano, tace "Maalush dan Albarka, ga Zogale na kwandon ta maka kaci kai kadai kar ka ba kowa" ta karasa fadin haka tana kallon Rafeeq ta gefe ido, sosai ta ba Rafeeq daria, kallon Gefen shi yayi ya dinga Murmushin mara sauti a ranshi yace "Chill Tsohuwa, i cant eat this Sh*t" Maalesh yace "Kai Nenen mu kina ji dani fa, duk wannan ni kadai?" Ehmana dole nake ji da kai, wasu ko kallo basu isheni ba ai" Rafeeq ya kawar da kanshi gefe don yana gudun kar daria ta kubuce mai, wai don shi tsohuwar nan ke habaice habaice, lallai tana da damuwa, ta shekara tanayi ko a jikin shi, haka Maalesh ya zage sai cin Zogale yakeyi, da yake shi yana son abubuwan gargajia, Nene ta dauko kujerar tsakar gida ta zauna, don ta na ta Rok'on Allah sa Rafeeq ya nuna yana son ci ta k'are mai tanadi. Ga Mamakin ta har Maalush ya gama Rafeeq be dago kanshi ba, Rafeeq ya zunguro Maalesh, ya k'agara su tafi, Maalesh yace "Nene, bari mu tafi, gobe zan koma kano InshaAllah" Nene ta hau suburbuda mai Adduo'i kala kala, ta kwalawa Seebi kira tace kuzo kuyi bankwana Gobe zai tafi, ta fito ta raka su har Waje.
"Ya Maalesh a kano kake aiki? Yace aa, Service nakeyi, befi wata 2 in gama ba, sai in samu aiki sai in fito a sa bikin mu ko? Dariya tayi sosai tace "you are funny" yace "you think so ko?" ya kalli Rafeeq yace "Guy, tell her ba wasa nakeyi" tsaki Rafeeq ya buga tare da bude mota ya shiga, duk ba su damu ba don sun san saran Rafeeq na tsaki, sai da sukayi Sallama kafin ya Shiga mota suka wuce.

*MAFARKI*
"Assalam Alaikum Nasiba" Murmushi tayi tace "Sai yau Ko Yaruwa ta Rafee'ah?" "Afuwan Ukhti, Ya Hakuri da Hidima?" Nasiba tace "Toh mungode Allah" Rafee'ah ta fara magana cike da natsuwa "Da farko zan fara da gode miki, kin aiwatar da Aikin Farko da na saka ki, ina me miki albishir da kin riga da kin shiga Rayuwar Rafeeq, kinyi Namijin k'ok'ari, ina jinjina miki, abu na gaba shine, kinsan ance duk yanda mutum keso ya ci Nasara, ya kuma samu Albarka da Ribar Rayuwa, to ya bi Mahaifanshi, Musamman Mahaifiya, duk yanda kake son samun Nasarar Rayuwa, Idan baka bi Mahaifiyar ka ba, to ba zaka taba ganin daidai ba, duk me ka taba zai ruguje, kai ko da ka samu to bazaiyi Albarka ba" Nasiba ta jinjina kai tace "Haka ne" Rafee'ah ta cigaba "Toh abu na gaba shine, ki daidaita tsakanin Rafeeq da Mahaifiyar shi, indai kina so Rafeeq ya gama Makaranta wannan Zangon, to dole sai ya samu Albarkar Uwa, ba wannan ba dai, Duk da yana cikin Duhu, ya nemi gafarar Uwarsa, don ko yau ya fadi ya mutu sai Allah ya tambaye shi, don be nema samun Haske ba, ki Daidaita tsakanin su, Nasiba" Nasiba cikin Firgici tace "Ta ya zanyi haka? Kinfi kowa sannin kafiyar Rafeeq, ina zan nema Mahaifiyar ku? Ina zan ganta? Ta ina zan fara?" *Ke Alheri Ce* *Ke Alheri Ce* *Ke Alheri Ce Nasiba Muhammad* bat ta Rafee'ah ta bace, a firgice Nasiba ta farka daga Baccinta, "ki taimake ni Rafee'ah, atleast give me hint ya zanyi? duk ta bi ta jike da zufa, Minsharin Hajjo ya tunasar da ita Mafarki ne tayi, da sauri ta sauka kan Gado ta fita daga Dakin, ta dauro Alwala tazo ta kabbara Sallah, sai da tayi Raka'ah Shidda kafin ta dukufa da Adduoi, Alkah ya shige mata gaba, ya kawo mata komai a Sauk'ak'e.

*9:45am*

"Ki tsaya kiyi Kallaci Seebi" "Aa Nene zanyi a Makaranta, sauri nake kar bus ta tashi" "to Allah ya taimaka, a gaida miemo gayu" "Zataji sai na dawo" da sauri ta bar Gidan ta na ciro yar Tecno dinta a jakka ta latso number Usheey, "Usheey, kin isa National? Akwai Bus? Usheey tace " Eh Seebi, biyu sun tashi saura daya, kiyi sauri kar ta cika mu tafi" Seebi kamar tayi kuka, tace Gani nan na kusa bakin Titi, zan samu Napep" "Okay to sai kinzo" Ji take kamar tayi gudu, don in Last bus ta wuce bata san yadda zatayi ba.

Kamar a sama ta ga Motar Rafeeq a gabanta, bata san lokacin da ta sake Murmushin da ke kara ma fuskar ta kyau ba, ba watawata ta zagaya ta bude K'ofar ta shiga, k'amshin sa ya sa ta lumshe ido, ta bude baki zata gaishe shi, sai kuma ta tuna wani abu sai ta fasa, har ya ja motar shi shiru shiru bata gaida shi ba, ya saurara yana jiran ta gaishe shi amma bata ce ko 'a' ba, a ranshi yace ko lpy? Ta gefen ido ya kalleta sai hura hanci take yi, tana girgiza kaf'a tana kallon window, yau kuwa meye Haka? Guntun tsaki yayi yace ma kanshi "why do i even care?" ya dauki hanyar Makaranta, kusan minti 10 ba wanda yace da danuwan sa k'ala, Nasiba tayi wani shu'umin Murmushi, sun kusa Makaranta daidai Daji-dajin hanyar, Nasiba ta daddage ta buga tsaki da k'arfi, har cikin kunnen Rafeeq, da sauri ya dafe kunnensa da hannu daya, be yi magana ba, Tsut ta k'ara jan wani tsakin da ya fi na farkon k'ara, Haushi ya cika Rafeeq, kamar yayi me, be dai tanka ta ba, ya tsani Tsaki (kuji mun Rafeeq, wai ya tsani Tsaki) Nasiba na lura dashi, ta k'ara jan wani dogon tsaki daidai ta taka burkin Motar da Rafeeq yayi ji kake k'iiiiiiii, Nasiba ta tsorata sosai, ta kalleshi cike da tsoro, ba tare da ya kalleta ba yace "Get Out" Nasiba ta juya ta kalli dajin nan ga sanyi, gashi bata tunanin zata samu na Allahn da zai karasar da ita Makaranta, har zata bashi hak'uri, sai kuma ta fasa, bude k'ofar tayi ta fita, kamar jira yake ya ja motar shi ya wuce, ya barta nan tsaye, hawaye suka soma kwaranyowa, tayi dana sani, meyasa take son k'ureshi? Ita dake son fiddo shi daga yanayin da yake ciki, Meyasa ta k'osa, to gashi ya direta kan hanya, kuma ba zata iya takawa ba, don tafiar da saura, ta rasa yanda zatayi ta zauna gefen Titi ta na me rokan Allah ya kawo Bus ta tsaida su ko a tsaye sai ta tsaya.

"Mtswwww" tsakin da Rafeeq yayi kenan Karo Na 8 bayan ya dire Nasiba, meyasa zai ajiye ta bakin hanya? Yanzu if shes not careful Mota ya bugeta fa? Tsaki ya sake yi tare da kallon Mirror dinshi, chan ya hango ta zaune gefen Titi kamar Almajira, Tsaki ya sake yi yasa trafficator yayi U Turn ya koma Baya, horn ya mata da sauri ta dago ta sake Murmushi, a ranta tace "Ba zai iya bari na anan ba" kawar da kanta tayi gefe kamar bata ganshi ba, tsaki yayi da k'arfi, ya danna mata horn, ko dagowa batayi ba, takaici kamar me, wai shi yau ake ma haka? Allah Allah take kar yayi zuciya ya barta nan, amma wani zuciyar ta bata karfin guiwa, Matso da motar yayi kusa da ita ganin zai take mata k'afa yasa ta tashi ta hau kan dakali, da k'yar yace "Get In the Car" A takaice tace "No thanks" tsaki yayi yace " Nace ki shigo ko? So kike kiyi Missing Lectures?" a tsiwance ta murguda baki tace" What do you care idan nayi missing lectures? Werent you the one that dropped me here? Ba zan shiga ba" ta sake murguda bakinta, kamar Tv ya ke kallonta, mamakin ta yake, yaushe ta koyi Rashin kunya? Yaushe ta samu guts din mai magana haka? Yau Shi R-Lema ake ma haka? Lallai Yarinyar nan bata sanshi ba, be san me ta taka ba. Abun Mamaki be daddara ba yace "ki shigo motar nan" ta juya tace "ba fa zan shiga ba nace" kamar zaiyi kuka, besan lokacin da yace "Will you Please get in the Car now? Please".

_Bibilicious Biebee_

šŸ‘§šŸ½KE ALHERI CEšŸ™‡šŸ¼ā€ā™€

NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

*This is for y'lls Members of Miemee Bee šŸ‘„Novels, You guys are Simply the best, I see lotta _ā„¢Nasi-Feeq_ , lotta _ā„¢Nasi-Zaid_, too bad no ~ā„¢Nasi_Lesh~ , lolsšŸ˜‚ ILY'llsā¤ā¤ā¤ Together we keep it movingšŸ’‹ *#1love*

Pg4⃣2⃣

"Oh shit" ya fada da ya tuna abunda yace, yau shine da cewa please? Kuma ba amfanin shi ba, sai na wanda ya ce ma wa? Lallai in har bata shiga motar nan ba zai tafi kuwa ya barta, a 6angaren Seebi kuwa, kalmar 'Please' ta maimiata cike da mamaki, Yau Shi R-,Lema ke cewa please, aah akwai cigaba, akwai nasara, amma me tasan in ta tsaya jan aji tafia zaiyi ya barta, kuma ba lallai bane ya dawo a wannan karon, a sakwan da be wuce iku ba Rafeeq yayi shawaran tafia, sakwan da be wuce biyu Nasiba ta fada motar, be tsaya jira ba ya hau kan titi, ko kallon shi batayi ba, shima bai kalleta ba, har suka zo Makaranta, ya kawo ta bakin Department dinsu, ya na parking ta fita tayi banging door shi kanshi ya firgita, ya bi ta da ido yana mamakin Wannan bak'uwar Halin da shi be san da ita ba, to ko dai tana da damuwa ne? Saboda ya san ta kullum ta shigo Motar shi sai ta gaida shi, in ko yayi dropping dinta sai ta zabgo mai addua tana mai Godia, amma yau ba Sannu bare Nagode. Tsaki ya ja yana fadin "Matsalar ta, i dont need her thanks, greetings whatsoever" ya ja motarshi yayi gaba.

Zaune take kan lallausan Rug dake kusurwar dakin ta, jingina tayi kan luntsuma luntsuman throw pillows da aka wa bangaren ado, Grapes take ci a k'asaita ce, Meema ta shigo ta zauna kusa da 'yaruwarta, ta daga kai sama tana kallon POP din dakin, da Walpaper, da wakeken gadon ta, ga madubi shak'e da turarruka masu yawa. Ta dafata tace "Meema, ji yanda kike kallon dakin kamar yau kika fara shigowa" Meena tace "Hmm Sis, ina mamaki ne, rayuwa na gudu, a wani lokaci, ko gidan kanmu ba mu da, ba mu da Sanaar da ta wuce saida Abinci, amma in one time, God has buttered our Bread" Sauda tayi saurin cewa "You mean My Bread?" daria sukayi gabaki daya, tace " Tabbas ke mai sa'a ce, don kuwa duk abunda kika sa a gaba, ba makawa sai kin cimma sa, ga ki da hangen nesa da kuma hikimar magance Nesa tun kan tazo kusa" Saude tayi wani shu'umin murmushi, tana jin dadin yadda kanwar ta ke k'oda ta. Meema ta cigaba da cewa "saidai wannan karon na rigaki hango nesan da zata iya kawo miki cikas, da sauri ta gyara zamanta tace "yi magana Meema" Meema ta gyara zama tace " kin taba tunanin yadda Rayuwa zata kasance miki idan Alhaji Habib yau ya fadi ya Mutu? Tace "Da sauri tace "bangane ba Meema, yi min bayani dalla dalla"
Ina nufin yau in Alhaji ya mutu, in banda tumunin takaba ba abun da zaki tsira dashi? Kina da labarin Yau Alhaji ya mutu tsinke ba za a ba Aneesa ba? Don bata da Gadon shi? Komai zaa tarkata a ba Rafeeq, be fi a baki kaso daya cikin takwas ba, sauran kuwa na Rafeeq ne, shi zaa ba komai" tace Meema ina son Habib, ba na ma tunanin mutuwar sa, kuma ni bazan kashe shi ba sabida Gadon sa be dameni ba" Meema tace "ai ba ina nufin ki kashe shi bane, ina nufin in ta Allah ta kasance ya mutu yau, da me zaki tsira, ai bana tunanin zaki tashi da abun azziki, gashi diyarki bata da gadon sa balle a sa rai zaiyi yawa" Saude tayi zuruuu tana nazarin Maganganun Meema, tabbas tayi Magana kuma abun a duba ne "toh Meema yanzu, meye abun yi?" Meema tace kawai sawa zakiyi ya Mallaka ma Aneesa wasu k'adarorin sa, da dukiya" Saude tayi Murmushi tace "i know what to do, bari ya dawo daga tafiar nan".

Kwanci ta shi ba wuya gun Allah, su Seebi Semester ta ha, don yau suka fara hutun Mid-Semester break, haka kurum taji ita ta na son Zuwa Gida gun Iyayenta. Dama Safiyyar Yau Hajjo ta koma gida, don Nene tace ta koma bakin aikinta ta ji sauki, Nasiba ta shiga gun Nene, "Nene barka da hutawa" Tace "yauwa Seebin Nene" tace "mun dan samu hutun kwana 7, shine nace mu shirya mu tafi Kaduna mu dan chanza guri" Nene ta yi Kamar bata ji ta ba, Seebi ta sake maimaita mata, tace" KE nasiba ki fita ido na, shin ni tsarar kice? Nasiba ta kalli Nene da mamaki, tace me nayi? Nace wani abu da ba daidai ba? Nene tace ki kalle ni ki ce man in zo muje Kaduna hutu, ni yar firamare ce? Sai inje in ma Uwaki zaune cikinem gida, yan unguwa su tacewa Uwar miji ta tare Gidan D'a to ba haka nake ba, in ma Mahammadun ya aiko ki to shima zan gamu dashi" Nasiba ta kalli ta Nene cike da mamaki, shin me yayi zafi haka? Girgiza kai tayi tace "Wallahi you are always out of point" Nene tace "Eh baturen ma yaci kutumar ubanshi, nan gani nan bari" Nasiba ta shige daki tana mamakin Nene, ita in anyi gabas to yamma zatayi, ta gurgiza kai ta hau hada kayanta.

WasheGari
Tun da farar Safiyya Nene ta shiga kasuwar 'yar kutungu, tayo ma su Ummi Siyayya, su garin Alkama, Sansamin yaji, Kuka, busasshan kubewa, daddawa da dai sauran su. Sauri take ta dawo gida, tana shigowa taga Nasiba na kalaci, ta sauke ajiyar zuciya, tace lafiya Nene? Nene tace "Allah Allah nake kar ki tafi, don nasan ki da d'oki, tace "ya zanyi in tafi ba muyi Sallama ba?" Nene tace "yo nasani? Da kin tafi da sai kin raina kanki wallahi" tayi daria, "Me zai faru da na tafi" tace "Wallahi mota zan shiga in biki har kadunan, in lakada miki na jaki, sannan in juyo in dawowa ta Katsina" me Nasiba zatayi in banda daria, daria har da hawaye, Nenen ma Dariya tayi.
Tayi shirin tafiya, Nasiba tace da Nene "kinga ki shirya mu tafi, ya zaayi ki zauna ke kadai a nan, hajjo ba ta nan, DonAllah Nene nah" Nene tace "Shin in tambayeki, Shekaru 21 da daya da nayi nikadai cikin gida me ya cinye ni? Me ya kama ni? Eyi? Nasiba tace " Wanchan Unguwar akwai mutane, kina jin motsin mutane, wannan fa? Tace "Ke ni rabani, ba fa inda zani, Ina nan kinji Nenen Seebi? Allah ya kaiki lafiya ya dawo mun dake lafiya" Amin Nene na, tace to Nene ga wayata nan zan bar miki, sai mu dinga gaisawa muna jin lafiyar Juna, ba musu ta amsa, sukayi Sallama har tasha Nene ta raka Nasiba gaban ta suka tashi. Ta musu fatan Allah sauke su Lafiya. Ba ta bar tasha ba sai da ta ma wani Conduster tatas don yace mata "Hajiya tafia ne?" tace "aa uwarka ce". Tunda ta fara masifa bata yi shiru ba, wai ya mata rashin kunya yana mata maganar Yan tasha, Da k'yar wani mutumi ya lallabata ya Ya fidda ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login