Showing 138001 words to 141000 words out of 149166 words

Chapter 47 - Ke alkhairi ce COMPLETE HAUSA NOVEL

BIEBIE   

22 Oct 2024

25741

baki yace "Ina da Zainab din?" Rafeeq yayi daria. Alhaji Habib ya shigo, bayan gaisuwa Zaid yace "Yaya yanzu fa zan wuce Kaduna" 'Ba ka bari sai Gobe?" da sauri Zaid yace "Tab" Alhaji Habib yayi daria yace "toh kai wani Gida ka zaban ma dan naka? Gwara tun wuri a je a gyara ayi furnishing ya dauki matar shi su koma chan" Zaid yace "Yaya Akwai dan shirin da nake musu, nan da lokaci kadan zakaji" "Alright" inji Alhaji Habib, Suka fice, Uncle Zaid yace da Rafeeq "kai kuma kayi ma Seebin magana, in ta amince to, in bata amince ba sai kuje ku dawo, duk dai yanda kukayi sai ka sanar dani" Ya rungume shi yace "Thank you, You are the best" "shuttup boy" sukayi daria, tare suka hau sama wurin Mami Uncle Zaid ya mata Sallama, ya ma Seebi da Aneesa Sallama, ya wuce Gidan Nene ya mata Sallama, ta mai Addua Sosai, ya dauki Abii da Ummi da Anan suka wuce Kaduna.
A yau Lahadi yan Nesa suka koma garinsu, yan biki aka watse. Nene ta tarkata ta koma Gidan Lema don kwana daya da tayi ba Seebi duk sai ta ji ba dadi Sabo turken Wawa.
Karfe tara na dare taji sak'o ya shigo wayarta, ta bude "Baby, I'm hungry" ta kalli Nene da ta bude baki sai surutu take mata tana bata labarin 'yan biki" ta dan muskuta, ta mik'e tace "Nene ina zuwa" Nene ta tsuke fuska tace "ina zaki da daren nan?" "Hamma zan dafa ma Indomie" Nene ta tabe baki tace "Ke Seebi ki fita idona, ke baki iya dan jan ajin nan ba, Miji ya kiraki jiki na rawa zaki kai kanki, tun kafin ki tare, wayace miki haka akeyi?" Seebi ta bude baki cike da Mamakin Nene, tace "Nene meye haka kike fada?Yunwa fa yakeji? Meye laifi don zan kai mai Abinci? Ai mijina ne ko?" Nene ta bude baki "Ehh lallai Seebi wuyan ki ya isa yanka, idon ki ya fedare, ke kin auri Dunkum, zaki gayan magana ke me Miji, ke dadi Miji, ke danubanki Mutunci nake neman miki" Wayar ta ya sake Ringing din, da sauri tayi hanyar k'ofa tace "Ni abinci nace zan kai mai ba wani abu ba" Nene ta daga murya tace "Ke kika sani, indai Dunkum ne gaki gashi". Kitchen ta wuce, tana shiga ta hango SlicedBread, tace " Yauwa" Ta bude fridge ta dauko Sardines da butter, da bama ta hade su gu guda, a gurguje ta shafa ma bread dinnan tayi toasting guda 4, ta Zuba mai Pepper Chicken din da ta ganj a cooler ta ciro Kwalin Exoctic a fridge ta sa a tray da Cup tayi k'asa dakin Rafeeq, a k'ofar Dakin tayi Sallama.
Bude wa yayi ta shiga da tray din kanta a k'asa, Hijab ke jikinta amma sai ta mishi kyau sosai, hannu ya sa ya karbi tray din hannunta ya ajiye kan stool, ya riko hannunta ya zaunar da ita kan Gado, yace "Thank you" da sauri ta kwace hannunta ta mike ta isa ga Tray din ta mik'a mai Sandwich din tace "kaci, you are hungry" ba gardama ya amsa, ta tsiyaya mai lemun ya kurba, yanda yake taunawa a hankali cikin aji, sai taji ya burgeta, guda biyu kawai yaci yace ya k'oshi, ta so ya k'ara amma ya shaida mata ya ishe shi, ta mik'e ta kwashe kayan tace "to sai da safe" da sauri ya mik'e ya karbe tray din ya dire a k'asa yace "Baby i want to talk to you about Something" jin yanda yayi maganar ne ya sa ta gane maganar Muhimmiya ce, wuri ta samu ta zauna, k'asa ya zauna yana me fuskantar ta, a hankali ya fara magana;
Baby, i know we had a rough start, i kept the way i feel for you for a quite a long time, ,kin shigo Rayuwata as a Blessing, you Sacrificed and did alot for me, And nagode miki for all that, Yanda Allah ya tsara, you are now My Wife, I know be kamata na sa ki ki min wani abu ba bayan abubuwan da kika min a baya, na son ba kya min son da nake miki, i'm not even sure if you love me at all, well I dont care about that, Ni ina sonki, ina kaunarki which is why nake so ki taimaka ba danni ba, ba don bakya so na ba, idan Wannan shine abu na k'arshe da zaki min ki min shi, ba zan tilasta miki kiyi abun da bakya so ba, but i'll be happy if you grant my request. DonAllah". Yanda yake magana ya sa taji tausayinshi, to me yake bukata daga gareta haka har yake rok'on ta? Kuma wai a ganinshi bata sonshi?" muryar Mimi ya fado kanta a lokacin da take ce mata "Seebi, sai kin cire kunya zaki iya zaman aure, he is your husband, take care of him or Someone will" runtse ido tayi tace
"Hamma, ka daina cewa bana sonka, ko ban sanka ba ai ba zance bana sonka ba, balle kuma Yanzu da kai Mijina ne, and Please ka daina rok'ona haka, ka fadi ko me kake so, InshaAllah zan maka shi in har befi karfina ba" Sosai maganganun ta suka mai dadi, ya samu k'arfin guiwan yi mata magana, hannunta ya sake kamawa yana mursawa a hankali yace "Baby, ina so ki dauki Zuwanki UMYU Matsayin Zuwa na ba zuwan karatun ki ba, ina nufin Don ki hadu dani ne kikazo Garin Katsina Gabaki daya, i want you to Sacrifice the 1year you spent in UMYU for me, ina so Ki Hak'ura da karatun da kikeyi a UMYU" idon Naseeba ya kawo ruwa, Tayi saurin maidasu, a ganinta kishinta yakeyi shiyasa be da Raayin tayi Karatu, amma Feeq beyi kama da Mazan da ba son Matansu suyi karatu, k'ila yana da reason dinshi, Sonshi da takeyi zai sa tayi mai komai, Ko don ta k'arasa ladarta, ko ba komai Aljannarta na tafin k'afarshi, a hankali tace "Hamma na, ba sai ka rok'eni haka ba, nafa kawai Umurni ne, umurni kawai zaka bani, kace Nasiba kin gama makaranta, ba zaki koma Makaranta ba, kai Mijina ne, ba sai ka rok'eni haka ba, ko da a ce ina Level 400 ka bukaci da na yanke karatu na, wallahi ni me yi ne, balle Level 1, ban ma gama sanin kan makarantar ba, Allah ya sa hakan yafi Alheri Amin" ta mik'e tsaye zata tafi,tausayinta, Sonta da k'aunar ta suka k'ara shigar shi, nan ya sake bata babban Matsayi a cikin ranshi, yace "Baby, baki gama karatu ba, yanzu dai zaki fara, i have plan for us, Abun da ya faru a baya tsakaninmu da Saude and All, hakan ya sani tsoron Mutanen mu, baka san wanda suke kewaye da kai ba, ba ka san ma su nufar ka da Sharri ba, hakan ya sa na tsani fara sabon rayuwa a k'asar nan, ina tsoron sharrin Mai sharri, ina tsoron Hassadar mai Hassada, Ina so muyi Nesa da k'asar nan, ina so mu fara Sabon Rayuwa inda ba wanda zai matsa mana, ba wanda zai cutar da mu, inda zamu gina Rayuwar mu cikin Aminci da k'aunar juna, Na gaya ma Uncle Zaid bukata ta, sai ya sanar dani dama Zai shirya mana Honeymoon a London mu hudu, sai yace in tambayeki idan kina da raayin Zama chan, zai Samo mana gida, ki fara Karatunki, And ni in fara Masters dina, idan baki da raayi, sai muje muyi 3weeks mu dawo, toh Alhamdulilah kin Amince, So help me Lord! I'll make you Happy, you wont regret this I promise, i'm going to shower you With Love and Care For the Rest of our Lives" kallo daya zaka mata ka ga Murnar da takeyi a zuciyarta ya baiyana, Dadi ya mamayeta, Farinciki ya ziyarci zuciyarta, ina zata saka ranta don Dadi, Alhamdulilah ta gode ma Allah a cikin ranta, ji take kamar ta rungume shi, ta bashi tukwicin wannan Albishir da ya mata, wai ita yau Seebin Nene zata je London? Bata taba zaton zataje ko nan da Airport ba, Amma da yake baka cire rai daga rahamar Allah gashi Aure zai kaita London. Kashe mata ido yayi yace "Baby, we'll be there, alone, just me and you, Just Us, then i would teach you how to love me" a hankali tace "You dont have to teach me how to love you, because i Do" Wani dadi yaji a ranshi cikin wata murya me sanyi yace "You What?" gangar Soyayya ta shigeta, bata son lokacin da tace "Yes Hamma, I believe In Destiny, My Destiny is to Meet you, Marry you and be with You, I love you So much" Dadi ke mai chalugude a k'irji, Farinciki da jin dadi ya ziyarceshi, takowa yayi ya matso gaf da ita, har suna iya jin hucin Juna, a hankali ya zare Hijab din jikin ta, nan da nan ta daburce, idonta ya juya don tsoro, shikam yana son yanda idon ta ke juyawan nan idan ta tsorata da abu, murmushi yayi ya Rungumeta sosai, ido ta runtse saboda tsoro, a hankali ya rada mata a kunne "Shhhh, keep calm, I got you" lamo tayi a jikinshi, shikuma ya sa hannu ya ware ribbon din da aka daure gashin kanta, gashinta ya zubo, ashe tana da gashi haka, a hankali ya dago ya tallabo fuskar ta, bata bude ido ba har yanzu ya kai bakinshi kan nata ya bata light kiss, kafin yace "I Love you Baby, with every fibre of my being, I will love you always and Forever" murya chan ciki ciki tace "I love you More Baby"

_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍

NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

K'ARSHE

Shigowa dakin tayi tana Sallalami tana tafe hanayenta, da sauri Seebi ta ture Feeq, tana sinsina kai, shikenan Yanzu Nene zatayi Shela dasu, don tasan ta gansu, ba su san Nene gwanace ba, wayyaya ce in taso, yi tayi kamar bata ga me sukayi ba ta kalli Seebi tace "yanzu ke Seebi, wannan k'aton Gardin zaki kalla ki kira da Bebi? Bebi fa? Amma an cuci jarirai da k'ananun Yara" Seebi ta sauke sigh of relief, tana jin dadi Nene bata gansu ba, abunda bata sani ba tun sanda ta shigo Nene na la6e ta window, Seebi bata tanka ta ba ta rabata ta gefen ta wuce da sauri, Nene ta galla wa Feeq harara tace "Dangin Tsaka, an zo ana mana fankama, amma an tsaya ana ma Mata k'aramar murya" Girgiza kai yayi ba tare da cewa komai ba ya fada toilet, don yau ba zai bar Nene ta bata mishi Mood ba, yau ya na cike da farinciki mara Misaltuwa, Nene ta durkusa ta kwashe tray din ta wuce tana Murmushi, a baiyana tace "a ganin su ban ga suna Sumba ba?" lols.
Rafeeq na fito wa toilet ya ciri Waya ya kira Uncle Zaid, Ringing daya ya dauka "Rafeeq Lema, why are you calling me in the Middle of the Night?" "Uncle Zaid, its to 10 fa, dare yanzu har yayi?" Oh God, did You forgot? I have a Wife Stupid" dariya yayi yace "Ohh Sorry, na manta wallahi, i thougbt har yau gauro ne kai" Zaid a k'agare yace "Shuttup and go straight to the point, Matata na jira na" Rafeeq ya ta6e baki yace "Su ma su Mata, Dama in gaya ma Seebi said Yes, ta amince" Ohhh Feeq ba zaka iya bari sai da safe ka kirani ba?, kar ka sake kirana sai bayan 1week" dif ya latse Wayar, daria Feeq yayi Ahh Su Uncle Zaid dokin shiga dakin Amarya kenan? Lols.

A Gurguje
Kwanci tashi ba wuya gun Allah, Rafeeq ya gina soyayyar sa a Zuciyar Seebi cikin kwanaki kadan, bai jin komai gaban kowa ya nuna mata So, in kuwa tana kusa dashi to sai fa ya rik'e hannunta, Nene tayi masifar tayi tsiyar amma a banza, don shi indai kan Seebi ne Neh-neh ta bar bata mai rai, haka dai aka Kamala komai na tafiyar su Seebi, zasu tashi ta Lagos in two days, ana Gobe zasu tafi Seebi ta fita gidansu Usheey, zasu biya gidansu Miemee ta musu bankwana, A gidan su Miemee suka kulle a daki, suna bata shawarar yanda zata rik'e Mijinta, sai ta cire kunya da sauransu.
••••••••
Tun dazun yake kiranta a waya wayar bata shiga, da sauri ya dawo gida ya haye Sama, dakin Mami ya fara dubawa don yanzu tafi zama chan bata nan, sai ya lek'a kitchen, ya L'eka dakin Nene bata nan, sai Nene ita kadai, juyawa yayi ya fita cike da damuwa, Maminsa bata nan itama, ya kira Mami waya yana me tambayar Seebi, ta shaida mai da nan ta barta da Nene, Dakin Nene ya koma, zaune ya ganta tana cin dabino, tana ganinshi ta hau taunar dabinon nan kamar Chewingum da gayya, shiru yayi na kusan minti 3 kafin yayi tsaki yace "Neh-neh ina Baby?" shiru tayi kamar ba ta ji shi ba, Rafeeq ya k'ulu sosai, amma beyi zuciya ba, to ko don Yace Baby ne tak'i kulashi? Ya dan sausauta murya ba kamar dazu da yayi kamar yana mata gadara yace "Neh-neh, ina Naseebah?" nan ma Shiru ta mai, kamar ya mak'ureta don haushi, Amma ya daure ya kai zuciyarsa Nesa yace "Neh-neh mana, please ina Naseebah taje?" mik'ewa tayi tace "Haba Dunkum, haba Dunkum, ya zaka tasani gaba kanai man tambayoyin ya Uwata ta haifeni? Kazo kana min wasu surutai a ka, kana fa da Hayaniya, Kana maganar wata Bebi, ni bansan baby ba na dai san 'yar Tsana(Doll Baby), Ajiyar Seebin ka bani? Yaushe rabon da kai man magana? Yau da yake kai ke so sai gaka kana min magana, to banganta ba, fitar min a gaba" Rafeeq ya k'urawa Nene ido, ya san dai idan ya bude baki ya mata magana k'arshe ya kai ga sa mata hannu, juyawa yayi Kawai ya fita, Dadi ya kashe Nene ganin ta k'untata ma Rafeeq, har da hayewa Gado tana murna, ko ba komai ta rama Wulakancin Da ya mata ranar Bikin shi.
Aneesa ya gani ta fito daga kitchen rik'e da Plate, tace "Yaya Rafeeq ya dai?" cikin doko yace "Anee ina Baby? Ohh taje gidansu Ushee, da Miemee" gudu gudu, sauri sauri ya sauka daga Saman. Daidai Haraban Gidan suka ci karo, tare take da su Miemee da Usheey, Tsayawa sukayi, straight gunta ya nufa tare da jawo hannunta, Ba tare da yace komai ba ya ja ta daki, Su Miemee suka bisu da kallo, tare da fadin "toufa" suka wuce cikin Gidan.
Dakinsa ya rufe k'ofar a lokacin tsoro ya cika ran Seebi, da bango ya sadata ya mata rumfa da hanayensa, ya tsura mata ido kamar ba zai tanka ba a hankali yace "Baby kin sa na shiga damuwa, your phone wasnt going through" amda sanyi jiki tace "Kayi hakuri, naje musu Bankwana ne" to meyasa baki jira na dawo ba na kai ki, i was worried about you, and your Grandma was so Annoying, i nearly Hit her" a hankali tace "Hamma, ka dai na gigin cewa zakayi hitting Nene, i know shes annoying and she loves you" kada idonsa yayi yace "And it is you i love" da sauri ya hada bakunan su, ta tureshi iya k'arfin ta tace "su Miemee na jirana" ya rik'o hannunta yace "Oya na basu time, because in two days time, its going to be The two of us alone" bata gama saurarshi ba ta fita da gudu don yanayin shi na bata tsoro.

RANAR TAFIYA
Bayan An musu Nasihohi da Adduo'i, Daddy, Mami Anee, Abba da Umman Aunty Zee, Abbii, Ummi da Nene suka raka Uncle Zaid, Aunty Zee Seebi da Feeq Airport din dake Kaduna a Mando, inda zasu tashi zuwa lagos, daga lagos zasu hau Jirgin da Zai sada su da England.
Sosai Seebi ke Kuka ta rungume Iyayenta Mata, ta dade Rungume da Nene, kuka sosai takeyi, duk taurin zuciya irin na Nene sai da tayi k'wallah, da taga kukanta ba me k'arewa bane, sai tace da Feeq "Kai Dunkum, zo ka janye Matarka" jin kukan yake har ranshi da k'yar ya banbareta daga jikin Nene ya doraya a kafadarsa, a hankali ya rada mata a kunne "I got you" Uncle Zaid yace "Alright ya isa hakan nan, lets get going" ya Rik'o hannun Matarshi, har sunyi gaba Nene tace "Dunkum" kamar ba zai tsaya ba, sai chan ya juyo, sai da ta harareshi tace "Ka kular min da Seebi, Kamar ba zai tanka ba yace "InshaAllah" nan suka fara daga wa juna Hannu har suka kure wa ganinsu.

LEEDS BRADFORD AIRPORT
A gajiye libis ta fito daga Jirgin, ta sha bacci a kafadan Feeq, Aunty Zee na ta mata daria, Feeq ya rik'o hannunta suka fara tafia, Kayansu su ka kwasa, Uncle Zaid ya tsaida musu Cab, suka shige inda yace akai su *Bradford Intl Hotel* suna isa Zaid ya kama musu Daki Biyu, Room 123 da 124 aka basu, 123 duk suka shiga suka baje, Feeq yayi ordering Abinci daga Room Service, sukayi Jami'n sallolin da ake binsu, sannan sukayi Nafila, bayan sun idar ne Zaid ya dafa kan Zainab kana ya Umurci Feeq da ya dafa kan Seebi shima, hakan yayi,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login