Showing 111001 words to 114000 words out of 149166 words
rangada Guda, bayan ta Nade Mami cikin lafaiyarta,Ummi na rike da Hannun Mami, Mom din Maalesh da hajjo suka iso gidan, dama Maalesh ya kirata lokacin da suka shigo KT yace "tazo gidan su Rafeeq tarban k'awarta" ta rungume kawarta suna hawaye, Nene tace "Hajia yau ba ranar kuka bane yau ranar kunsawa wasu bakin ciki ne" kamar ya?" matsa ki gani, wanda be da hanci ya ja gefe, Nene ta shiga rangada guda, Hajjo ta tayata gabaki daya suka kama hanyar shiga gidan.
"Meema me nakeji haka?" Sis guda ne!" anya gidan nan ne kuwa? Jin gudar na matsowa kusa ne ya sasu tabbatar da hakan, Saude ta sauko da kgar daga kujera don zuwa ganin ikon Allah, Meema tace "Sis ina zakije da wannan kafar taki duk ya ja ruwa" Bata kulata ba, ta shiga dangyasawa tana cije baki ta fita daga dakin, ji tayi gudar na kusantosu, sai ganin Nene tayi da wasu mutane biye a bayanta,banda Seebi ba wanda ta shaida, Saude ta daka wata uwar tsawa "Ke jarababiyar tsohuwa, wani salon iskanci ne wannan? Zaki shigo mana gidan kina guda, sai kace gidan biki wanda suka dauko Amarya" Nene tace "banda abunki ai duk inda akaji guda an sna da Amarya a gun" Saude cikin rashin fahimta tace bangane ba, ina fa zaki gane bayan kanki cunkushe yake da duhu, to Amarya ce aka kawo, Amarya Habibu Lema, Kuma ta shigo kenan, ba boka mallam tuggu, kisisinar da zai fiddata, ta shigo kenan, mutu ka raba takalmin kaza, wanda be iya ganin hakan sai fita dan uban mutum" gaban Saude ya yanke ya fadi, ta kasa gasgata zancen Nene, Alhaji ba zai taba yi mata haka ba, amma ta lura akwai wacce aka lullube, ta maida hankalinta kan wacce ke lullube da farin lafaya, a ranta tace Amarya? Zuciyarta na dukkan tara tara ta taka har gaban su, ta sa hannu ta yaye mayafin,
Yanda kukasan taga Dodo haka ta sake mayafin da sauri tare da ja da baya, gani takeyi kamar Gezau, wata ta gani kamar Aishatu, haba ba ita bace, idonta ne, Na kan tudu yace ba zata sake taka gidan ba, jin muryar Nene tayi inda take cewa " ita din dai ce, Nana Aishatu Masoyiyar Asali, wacce k'addara ta rabata da gidanta, kuma Allah ya maidota, bawani dan buta uban da ya isa ya fidda ta kuma" Saude cikin kidima ta sake ihu tace "Aishatu, kai k'arya ne, ba ita bace" Mami tayi murmushi tace "Nice Saude, Nice" Luuuuu Saude ta fadi k'asa sumammiya.
_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
This page is for all Members of JUST NOVELS, Baby nice and above all Sadeeqah Ummu Sudais, ILY'lls Oceans and Galaxies❤
Pg5⃣6⃣
Duk sukayo kanta, Alhaji Habib yace "Ku taimaka a kaita Asibiti" Nene tace "wani Asibiti? Ai kawai ruwa zaa yayyafa mata" Meema tayi saurin dibo ruwan fridge, Nene ta karba ta watsa mata ruwan sanyi nan, Saude ta farfado idonta fes kan Mami, sake zabura tayi zata tashi, Meema ta maidata ta kwantar a k'asa, Mami ta tsugunno zata dafa Saude, Saude tayi zumbur tare da nunata kar ki tabani, wallahi kar ki tabani, Aljanna ce ke, it cant be, ance ba zaki sake dawowa ba?" duk kallon mamaki suke mata, Meema tayi saurin cewa "Wallahi Daddy tundazun Sis ke ta sambatu, ina jin Zafin ciwo ne, don wani Katon Maruru ya fito mata a guiwa" Daddy yace Allah ya kyauta, ai sai ki mikar da ita ki wuce da ita daki, Ya shigewar shi ciki, Zaid yace da su "ko muje Asibiti ne?" da sauri Saude ta girgiza kai tace "ai taje" Nene ta ta6e baki tare da cewa "mun rike Allah da Annabi, ku mu shiga daga ciki ko?" Mom din Maalesh ta ja Mami cikin gidan bayan Mami tayi adduar shiga Gida.
****
"Yo ai tunda ba a kai ga shara da gyaran dakinta ba ai ina ga dakin Mijinta kawai zaa safketa ko?" cewar Nene, Maman Maalesh tace "hakan ne daidai, in yaso a gyara mata daki daga baya ta koma" Dakin Alhaji Habib suka shiga da ita, bayan sun dan jima suka mata Sallama, Uncle Zaid ya dauki Ummi Da Ayman ya kaisu gidan Baba Tj don chan za su zauna, Nene da Seebi da suka shiga dakinsu don huta gajia.
********
"Na shiga uku na, tawa ta same ni, Meema ya zanyi da mutanen nan? Aishatu ta dawo, komai ya jagule, nasan yin wannan Shegiar tsohuwar, nayi nadamar sawa a kona gidansu don yanzu Reshi ya juye da majuyi. Ni gaskia ba zan iya bari Aishatu ta kwanta da mijina ba, zuwa zanyi in lumama ta wuk'a ta mutu, na tsaneta na tsaneta" Saude ce ke wannan furucin cikin yanayin da ya firgita meema, bata ta6a ganin Yayarta a wannan yanayi ba, Firgici da Tsoro take gani kwance a idonta, tace "Sis ki k'okarta ki kwanta, komai zai zo a sauk'ak'e, gobe zanyi maganin abun, trust me Sis". Saude ta dan jigina da pillow kamar me bacci".
******
Aneesa batayi wani tashin hankali ba data dawo daga makaranta taji labarin dawowar Mami, hasalima murna tayi don ta tuna da, Mami ta kasance me kyautata mata, har Parlorn Daddy taje ta rungume ta, tana mata sannu da zuwa, Daddy yace " kice ma Saude bayan Isha'i tazo ina nemanta" tace "ok Daddy" ta fice ko da ta sanar da Mummynta Saude ta haruzka, don me Aneesa zata je gun Aishatu, tayi fadan ta zage Aneesa tas, karshe ma Aneesa ta buga tsoki ta bar dakin, ko a jikinta don ita bata tsoron fushin mamarta.
Sak'e sak'e saude ke tayi, bata san me zatayi ba, idearta duk ta k'are, duk wata dabararta ta bace bat ta cije yatsa ta datsa lebe duk don ta samu sausauci amma a banza, Meema ta bata shawara tayi acting kamar ba matsala kafin da safe ta nemo mafita.
Har wurin k'arfe 9 ba Saude ba Labarinta, Alhaji Habib ya latsa wayarshi ya kirata, K'in dauka tayi sai da Meema ta rada mata wani abu a kunne, kafin ta dauka tana cika tana batsewa, yace "Saude ina nemanki a dakina" a takaice tace "banda lafiya" yace "SubhanAllah, kafar ne har yanzu? Gani nan zuwa" ya latse wayar ta kalli Meema, Meema tace "lets use this opportunity ki kwanta ki ta juyi matsayin baki lafiya, kinga zai tsaya wurinki" ta dan mata rada a kunne" Saude ta jinjina kai tace "Plan dinnan zaiyi aiki".
****
"Shatu nah, Saude ce bata ji dadi ba ina so in je in dubota" Mami ta dan hade wani bakin miyau tace "Haba Habibi, matarka bata Lafiya shine sai ka tsaya tambayan wani izini, donAllah tashi muje mu ganota" Daddy ya ji dadi tare da rik'o hannun Mami suka nufi Dakin Saude.
Kwance take kan gado tana ta mutsumutsu, ya k'arasa Gadon ta tare da kiran sunanta, ta rungume hannunshi ta na wani kukan munafurci, Mami ta kauda kai, yace "Sannu Saude, k'afar ne? Allah ya sauwake ya baki lafia" Mami tace "Sannu Sauda, Sannu" Alhaji yace "Ko muje Aisbiti?" cike da makirici da kissa tace "A bari da safe sai aje, i'll b fine cike kawai dai Alhaji Please stay with me, kar ka barni ni kadai" ya dan kawar da kai gefe, yace ba ga Meema da Aneesa ba?" Saude ta marairaice tace "Please Alhaji, dare daya ne" cike da makirci Saude ta kalli Mami tace "Yaya ba zaki damu ba ko ya kwana a nan, ina bukatar taimako da kulawarsa" Mami tayi murmushi tare da mikewa tace "karki damu, yana iya tsayawa, mudai burinmu ki warke ki samu sauki, Allah ya baki Lafiya sai da safen ku" ba tare sa ta kalli Daddy ba tayi hanyar fita, Ji yayi kamar ya kurma ihu, meye hakan Aishatu tayi? Shi da yaci burin daren yau, ya zaayi ta amince ma Saude haka? Aishatu batayi missing dinshi ba, tunda bata damu dashi ba, ranshi na k'una, zuciyar shi na tafasa, da ta san yanda yayi kewarta da bata tafi ta barshi zaune ba"
*******
Tafiya takeyi kawai bata san inda take jefa kafarta ba, saboda wani bakin kishi da ya turnike ta, tayi kewan Habibinta sosai, ba halin kasancewa tare dashi a wannan daren ji tayi an dafata" a dan firgice ta dan kallota, Nene ta daga mata gira "Yadai? Ina zaki kika bar mijin ki? Ashe ke sakarya ce? Nazata ke wayis ce ashe ke kauyis ce, mtsw, wai nan fa bariki akai miki, an kwace miki miji a wayance don kar ku kasance tare, Aishatu, na gaya miki BARIKI IYAWA" Mami dai ta kasa ce ma Nene komai, Nene ta ja hannun Mami suka koma dakin Saude da Sallama" Saude da har ta mik'e Zaune tana ma Alhaji Shagwava shikuma yana ta basarwa, tana ganin Mami da Nene ta hade rai, Nene tace "Alhaji ya na ganka anan? Daga zuwa inje in dawo" Alhaji yace "Wallahi jikin Sauden ne" tace "to ai gani na dawo, kasan ni ta aika a ka kira mata, wai jikinta na ciwo ko akwai dabarar da zan mata namu na tsofi, shine naje neman Robb don zan shafe mata a baya don ta samu saukin ciwon jikin ashe har ka zo mata bankwana, to ai sai ka tashi ka bi amaryark dare nayi" baki wangale Saude ke jin K'aryar da Nene ke shatatawa, Mamakin wannan duniyancin tsohuwar nan takeyi, zatayi magana Nene tayi saurin cewa"Toh ku tashi Alhaji, ina so in shafe mata jiki, don taji dadi, InshaAllah zuwa Safiyya ta warke" Kamar jira dadsy yakeyi yayi zumbur ya mik'e, Saude zata mik'e Nene tayi saurin danna mata harara, Da sauri Alhaji yace "Sai da safenku, Allah ya sauwake" ya fita da sauri,Mami na mamakin yanda Nene take rarafk zance, Nene ta katse mata tunani tace "Zaki bi mijin ki ko sai kin gama sakin bakin? Sum sum Mami ta fice, Nene ta juyo ga Saude ta kashe mata ido, ta juya ta fita.
Ihu Saude ta sake, ihun takaici, ihun bakin ciki, ta na tsananin kishin mijinta, gaskia ba zata iya barinshi tare da Mami ba a wannan dare, dole tayi maganin abun amma ta yaya?
°1:23am°
Saude ta kasa bacci, abun duniya ya mata yawa, idanunta sun soye duka, ba alamun bacci, kallo daya zaka mata kaga tsantsar tashin hankali a tattare da ita, gaskia ba zata iya ba, Allah kadai ya san me Habib da Aishatu keyi, wani abu ta tuna, shaidan ya mata huduba, zumbur ta tashi, ta manta da maruran da ke kafarta masu mata Azaba, tana dangyasawa ta fita ta nufi kitchen, Wuk'a ta zaro, don ita Wallahi kashe Aishatu zatayi, haka ta dinga hada hanya don gani tayi wurin da duhu sosai, bawai don ba wuta ba a tunaninta k'ila Bulb din corridor din ne ya mutu, tana jan k'afa har k'ofar da zai sadata da Dakin Daddy, dagowar kanta ke da wuya ta ci karo da gamon ta, Wani halitta ne tsaye daidai k'ofar parlorn Daddy kamar Maiguard, sanye da Likafanni Fari, fuskar nan bakirkirin ga wani abu saman kan kamar k'aho, daskarewa Sauda tayi don Firgici, Tsuuu kakeji Saude ta saki Fitsari, wannan halittar ta fara kusanto Saude, habawa k'afa me na ci ban baki ba, Saude ta arta a guje ta shige daki a sittin bayan ta jefar da wukarta, ta datse da mukulli tana maida numfashi, Nene ta fashe da daria ganin yanda Saude ta tsure, tace "Shegia, ashe k'aryar iskanci takeyi, harda tsula fitsari, to ina nan ina gadinsu, ba abunda zaki musu, ni zanyi gadinsu har sai sunyi kwana 7, sai sun murji amarcin su" Nene ta sake fashewa da daria ta shige dakin su, tare da cire farin Kayan jikinta ta fada toilet don wanke fuskarta da ta sha Bak'in gawayi.
Haka Saude tayi kwanan Zaune a tsorace.
Bayan kwanaki 5
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Yan Kaduna sun koma, banda Ayman da ke gurin Nasiba, cikin yan kwanankin nan Daddy ya dan yi kiba, an gyara ma Mami Dakinta, har ta tare, sai Amarcinsu suke sha kamar wannan ne aurensu na fari hankalinsu kwance Allah na karesu, Nene na gadinsu ba tare da saninsu ba.
Meema ta bar gari ta zage gun bin gidajen bokaye don samo ma Yayarya mafita, Saude kuwa ta fara zarewa don duk a lokacin da tayi niyyar kulla ma Mami Sharri tsakar dare sai ta ci karo da Nene wacce tayi badda kama zuwa wannan mumunnar Hallitar da Saude ta ma lakabi da Fatalwa,
Saude ta fara Zarewa, ta fara susucewa, Ga Maruran kafanta sai girma suke k'arawa da yawa, abubuwa sun rinchabe sun ma Saude Yawa duk ta sa damuwa a ranta, ta fige ta fita hayyacinta.
*UMYU Katsina*
Ki kirashi donAllah ya maidaki Gida Seebi, ba fa ki da lafia, baki ta dan cije alamun tana dan jin zafin ciwon tace "Ku bari kawai, zai daina with time, haba abunda an riga da an saba" Usheey tace "Tab, dama ana sabo da ciwo? tace "bari nidai sai na kirashi in ma Zagina zeyi yayi, ta dauki Wayar Seebi ta latso Hamma na ta kira, Ba yanda Seebi zatayi da Miemee da Usheey. Yayi ringing har ya katse bai dauka ba, Usheey ta sake kiran layin shi, a ringing na 3 ya dauka, yabkara wayar a kunne ba tare da yace komai ba, Usheey tayi saurin cewa "ina wuni?" ya danyi jim, wannan ba muryan Naseeba bane, yace "Yeah" "um um dama Seebi ce bata dan jin dadi, tunda safe take fama da ciwon ciki har yanzu, kuma lectures zamuyi 4-6 tace zata tsaya amma ya kamata ace ta sha magani ta dan huta a gida"cike da damuwa a ranshi yace "Oh Allah why is she sick" a fili kuwa cewa yayi "kuna ina?" da sauri tace "Bayan theatre" dif ya kashe wayar, Miemee tana na Usheey daria tace "ai gwara da ke ce kika kirashi, dani ce ya katse ma waya da yaji ba dadi" Usheey tace "Toh ko we should get her on a bus, sai in rakata, na yafe Lectures din yau din" Miemee tace "muje Kawai, mayi attending nextweek" Seebi tace "ku barni please, zai daina, kar kuyi missing lectures saboda ni pls" kafin daya daga cikinsu ya k'ara magana Wayar Seebi tayi ruri, Usheey ta dauko wayar ganin Hamma ya sata dauka da sauri ji tayi yace "ku matso da ita" ya katse wayar, ya yace? "Cewa yayi a matso da ita, which means yana kallon mu, Miemee tace ga motarshi chan, Usheey tace "Oya Seebi, kiyi k'okari ki tashi ga R-Lema chan yazo, suka taimaka mata suka nufi motar, Idonshi fes kanta, cike yake da damuwa, ji yake kamar ya fito ya taimaka mata, ya dai daure ya zauna cikin mota ya k'wama Glass a ido yanda ba zasu gane yanayin yake ciki ba.
Sun so sata a baya amma tak'i bata so ya gano me ke damunta, tace su sata gaba,haka sukayi, suka rufe, be ce musu komai ba ya ja motarshi ya tafi, kallo daya ya mata ya dauke kai, Seebi na da dauriya, haka ta dinga cicijewa tana mutsitsika baki alamun zadi, har ranshi ya ke jinta, Da alamu tana shan wahala, ya na tausaya mata sosai, ya dinga driving, Seebi duk'e a gaban mota idonta lumshe Rafeeq ya dan juyo ya kalleta, kamar yayi kuka yakeji, a hankali yace "Sannu Kinji?" tadan kalloshi ta gyada kai, gani yayi gwara ya tsaya ya sai mata magani, don in taje gida kwanciya zaa sata tayi ko kuma wannan lunatic grandma ta bata wasu maguna marasa dadi, a hankali yace "Naseeebah, Me ke damunki?" ta dago a daburce ta rasa me zata ce mai, daure fuska yayi dan guntun Tsaki yace "Period pain ne?" waiyooo Allah k'asa bude Seebi ta shige, kunya ya rufeta ta rasa me zata ce mai, tsakin ya sake yi ya maida hankalin sa kan tuk'in sa, chan kuma ya kira Mamin sa Waya "R-Lema yadai?" Kamar bazai yi magana ba yace "Mam, First Aid for Mentsrual Pain, drugs? Anything?" ta danyi shiru chan tace "ba a cika san ana shan kwayoyi ba, its better to use natural remedy, like Hulba, Khal tuffah in hot water, hot water bottle" Mami ta shiga zanyano mai sunayen magunguna kala kala, Rafeeq ya danyi guntun tsaki yace "Mam-Mam, its an emergency, just name a thing, Mami tace "ok kane ma mata Khal tuffa cider vinegar sai hot water bottle sai ayi using dinshi" "Thanks Mam" zai kashe tace "Rafeeq wacece bata da Lafiya?" a takaice yace "Naseebah".
Waiyo Allah na is she alright?" Mami zanje in siya Mata maganin, sai mun dawo Gida" "Toh Feeq ina mata Sannu" ya kashe wayan, ya dan waiga ya ga Nasiba ta dan jingina kan kujerar, ya danyi parking ya dan rankwafo ta wurinta har tana jin saukar numfashin sa, ya kwantar mata da kujerar yace "kwanta kinji?" haka ya wuce ya siya mata duk abunda Mami tace ya kaita gida, ya taimaka mata da jakkarta, Mami ta sauko da sauri ta rungume Seebi tana mata Sannu, Nene tace "wannan ciwon Marar naki na fara tsorata dashi,Muje ga ruwan Zafi na dan dauraye ki" Rafeeq ya mik'a ma Mami ledar magungunan, Mami tayi sauri ta shiga kitchen da hado mata da dan ruwa mai dan Zafi.
√√√√√√√√√√√
Kula suke ba Nasiba kamar wata k'wai, Ba Daddy ba Rafeeq ba Ba Nenen ba, Zaid ma da ke Kaduna yana kira, binibini Rafeeq zai lek'o ya ganta tana bacci sai yayi murmushi ya juya, ya ci karo da Nene a wurin juya, Nene ta