Showing 114001 words to 117000 words out of 149166 words

Chapter 39 - Ke alkhairi ce COMPLETE HAUSA NOVEL

BIEBIE   

22 Oct 2024

25733

daga gira "yadai Dunkum ya da mana lek'e?" ya danyi tsaki yace "Ya jikin Naseebah?" ta ta6e baki tace "ni bansan wata Naseebah ba" ya dan kalleta da mamaki tace "nadai san Nasiba Seebin Nene" cikin rashin gane inda ta dosa yayi tsaki zaibi ta gefenta ya wuce tace "ni dai bansan ko a Amuruka a ka haifeka ba, naga iyayin ka ya soma yawa, in banda fi'ili da felek'e sunayen mu na da turanci ake fadansu, kace Mam, Neh-neh, oh ni Aminene diyar Mamman, har Nasibar ma da turanci kake fadarta? Wai Naseeebah" ta kwaikwayi muryarshi tana gyatsine, tsaki yayi me Sauti ya wuce ta tace "woo dangin tsaka".
*******
Kasa hak'uri yayi, ba inda zaije cikin daren nan, ga Maalesh yaje Kano, yana son sake ganinta, yana son Sanin in jikinta yayi sauk'i,ya kalli Mami, "How's she?" Mami tace "Taji sauki kam don yanzu nan ta bar Parlorn Nan" "wai Naseeebah?" inji Nene ta fada tana daria, yasan shi take kwaikwayo bece komai ba ya mik'e ya fita, Daddy na cewa "Nene sai na hadaki da Zaidunki, kin sa ma danshi ido" sukayi ta daria.
*******
Saude ta kulle kanta cikin daki tana ta kuka ta k'agara ta ga dawowar Meema taji yanda suka k'are, tana fatan dacewa, Aneesa tace "Mommy, wai ba zaki bari a kai ki Asibiti ba? Wannan kurjin sub ki warkewa, sai karuwa suke tayi suna fashewa ga wari, nidai gaskia bazan kara matse miki ba" Saude tace "Sorry my Baby, nasan gaji, karki damu Auntynki kawai nake jira, da ta dawo komai zaiyi daidaita, trust me my child".
*********
"May i come in?" da bata saurara da kyau ba, da bataji me yace ba, da Sauri ta latse wayar da takeyi da Miemee tace "Hamma shigo" tana dan gyara dankwalin kanta, ya shigo kan stool din madubi ya zauna cikiciki yake magana kamar ance dole sai yayi, yace "cikin ya bari?" cike da kunya tace "Eh ya bari" yace "Sannu fa" tayi murmushi yace "I'm hungry" da sauri ta mik'e tace "i'll cook you dinner" ya yamutsa fuskar sa yace "No no no, bana son cin Solid food at night, tashi ki rakani in har kinji sauk'i" da sauri tace "i'll just get ready" smilling yayi yace "good girl" ya fita. Ta bishi da ido tana mamakin shi, duk ya bi ya sauya, damuwarshi k'arak'ara a kanta, ta bude Sif ta ciro Hijab ta bi bayanshi.

Soli Center suka nufa, "oya fito" ya umurceta, cikin sanyinta ta fita tana tafia a hankali, duk ta raina kanta ganin irin mutanen da ke wurin, bata tunanin a garin Katsina akwai irin wuraren nan, ko don bata fita ne oho, tana bin ko ina da kallo, wurin ya hadu, tana ganin yanmata da samarin su, Har suka iso Shawarma&Pizza Spot, yayi ordering, Pizza da Shawarma, tace "Hamma ba yunwa kakeji ba, kwadayi kakeji" murmushin gefen baki kawai ya mata, yace "Muci Anan?" ta marairaice tace "No please" don ta raina kanta da kallon da 'yan gurin ke binta dashi, ya lura yace "Oya rik'e, i am not your Boy" ta amsa ledojin hannunshi, Rafeeq be da tausayi, suna tafia yace "do you need anything? Tace "No Thanks" suna tafia zasu koma cikin mota Sukaji ance "R-Lema" a tare suka juya, wata hadaddiyar budurwa suka gani Rafeeq ya zaro ido yace "Nanjeee? Omg" ai ko wacce aka kira da Nanjee ta rugo da gudu ta rungume Rafeeq shima rungume ta yayi suna jin dadin ganin juna,
Gaban Nasiba ya yanke ya fadi, meye wannan? Wacece wannan rungume da Hamma Rafeeq? Zuciyarta na bugu da sauri, duk ta dabarce ta shiga yanayi ganin Rafeeq da wata, hankalinta yayi matuk'a gun tashi, da sauri ta dauke ido ta matsa gefe don kirjinta na barazanar fitowa " OMG R-freaking Lema, What are you doing here?" murmushi kawai yakeyi ya kasa cewa komai don be san me zai cemata ba, mamaki ya cika ta, don ta san ba haka yake ba, ya cika surutu a da, amma yanzu sai basarwa yakeyi, tace "lookat you, what happened to you kamar ba R-leman da na sani ba" share maganan yayi yace "Yaushe kika dawo daga States? tace "wallahi last week nagama Masters na and all, ina Maalesh? Maalesh na Kano Wallahi, "I've missed you guys wallahi" "same here" "who is she R-Lema, your girl? Ya tsina fuska yayi Shaf ya mance da Seebi da ke tsaye kamar gunki, ba tare da ya kalleta ba yace "She's so not my type ke kin sani, shes my cousin" Seebi na jin haka, No reason taji hawaye na sauka daga fuskarta, Nan aka kira wayar Rafeeq ya matsa gefe yana receiving wayar, Nanjee ta matso kusa da Seebi, ta sa hannu tana share hawayen Fuskar Seebi, tace "Haba k'anwata why are you crying?" Seebi ta wayance tace "Aa ba kuka nakeyi ba" dont lie to me, i caught you crying, tell me you have feelings for R-lema huh? Tell me" daburcewa Seebi tayi tana girgiza kai, tace "No No is not what you are thinking, wani abu ya shigar min ido ne" Nanji tayi murmushi tace "bansan ya kuke da R-lema ba, but i can say you have feelings for him, You got Jealous when you saw us together, dont worry, i am not a threat, R-lema was my Bestfriend, and Maalesh was my crush lokacin muna Secondary School, so you dont have to worry about me, Kina sonsa, i can say that for sure" Nasiba ta rasa bakin magana, bata taba zaton wani ko wata zai fuskanci abunda takeji game da Rafeeq ba, tayi Alkawarin barin abun a ranta har mutuwarta, tace "Sorry Aunty is not what you are thinking" Nanji tayi murmushi tace "kanwata think about it, Rafeeq ya min yaro da na miki snatching" ta fada tana daria ita kuwa Seebi ta rasa yanda zatayi, Feeeq ya dawo yace "Oya lets get going Mami ta kira tana tambayarki" Nanji Babe bari mu tafi, sukayi shaking hands tareda exchanging Numbers, Seebi ta kallesu ta gefen Ido, Allah ya sauwake kuna diyan musulmai kuna taba juna kamar muharamai" ta murguda baki, fuu ta wuce gun mota don wani abu da takeji me kama da Kishi, Nanji na kallonta tayi daria ta wuce gun Saurayinta dama tare suke.
**********
Tun a mota ya ga yanayinta ya chanza, ba kamar da sukazo ba, amma yanzu ta hade rai sai fushi takeyi, ko me aka mata oho, yaso ya mata magana amma ya shareta har suka zo Gida, yana parking ta bude k'ofa zata fita yayi saurin rik'o hannun ta yace "Whats your Problem?" a dan masife tace "i dont have any" baki bude ya kalleta, ashe ta iya fushi, to me yayi zafi haka? Tab" ta wuce ta bar mai ledojinshi, ya daga kafada yace "matsalarki" ya wuce Dakinshi.

Da fushi ta shiga gidan tana ta mita cikin zuciyyarta, ba kowa a Parlorn K'asa ta hau sama daidai Dakin Saude taji ana magana k'asa k'asa, ta so wucewa don lab'e haramun ne, amma zuciyarta ya haneta, ta kasa kunne sosai ta gane Aunty Meema ce da Saude ke magana amma bata jin me suke cewa, a tsorace ta dan tura k'ofar a hankali, ta kutsa kai ciki ta labe tsaf takejin Su, jikinta ya fara rawa sakamakon abubuwan da kunnuwanta suke jiye mata:
"Wallahi Sis cikin kwanaki Shidda gidajen Boka shabiyar naje garuruwa daban daban, duk magana daya suke gaya min, wai ba abunda zasu iya miki" da Sauri Nasiba ta ciro wayarta ta danna record.
"Yanzu shikenan tawa ta sameni, yanzu ya zanyi da Alhaji? Gashi Aishatu ta dawo na san sai yanda tayi dashi, Matsalata Aneesa, ya zanyi da ita? Yanzu idan Alhaji ya fadi ya mutu bata da gadonsa, ya zanyi in sa ya bata k'addarorinsa, da ace ta hanyar Sunna muka haifi Aneesa da nasan tana da gadon Hafiz, gashi Hafiz be bar mata komai ba, kai ni tau na shiga uku" da sauri Nasiba ta toshe bakinta, tana fadin inalillahi wa ina ilaihir rajiun, yanda ta shigo haka ta fito a tsorace, jikinta na rawa ta ci karo sa Nene, Nene tace "meye haka jikin ki ke rawa kamar Mazari? Ya akayi? Ko gamo kikayi? Seebi ta ja hannuj Nene zuwa daki, ta rasa me zatace, Nene tace "wai meye? Zaki gaya min ko sai na je dakin Sauden naga me kike ma rawar jiki don naga da ga chan kike" da sauri tace "Aa nene, kar kije bari kiji" ta mata Playing abunda tayi recording, "tohhhh maganar kenan? Shi Hafiz din waye? Seebi tace " Yayan Uncle Zaid ne, ya rasu" toh Shine Uban Aneesar kenan, kuma Shegia ce, to ko sun sani? Anya bana tunanin sun sani, bari dai muga" Nene ta mik'e Seebi tayi saurin kamota, ina zaki? Haba Nene tada fitina zakiyi tsakaninsu? DonAllah kar kije, Nene ta lailayo ashar ta watsa ma Seebi, tace "Uban meyasa kikayi rakodin din, ni ban guri dalla" ta fita da wayar Seebi a hannu" Seebi ta daura hannu a kai "La i'llahailallah lahu take maimaitawa Hafiz Lema ne Baban Aneesa? Kuma ba ta hanyar Aure suka haifeta ba? Gashi Nene ta je fallasa asirinsu, anya tayi daidai kuwa da ba Nene wayar? Da sauri ta bi bayan Nene.
Nene bata tsaya ko ina ba sai dakin Aneesa,
Aneesa ta kalleta galala tace " Meye? Zaki shigo min daki? Nene tace "yi hakuri, DanAllah zuwa nayi ki latsa min inji wannan rakodin din" kamar ba zata karbi wayar ba ta karba, ta yi playing recoding din da tagani" K'arara muryar Mamarta taji tana wannan furucin ta zaro ido tace da Nene meye wannan? Ko Kinsan Babanki Shine Hafiz Lema? Ko kinsan ke Shegiya ce? Ihu Aneesa ta rusa, Na shiga Uku, ni Shegia? Ai ko a sittin ta diro daga kan gadin ta fita waje tana bige Seebi da ke kokarin riketa, wucewa tayi dakin Saude, Saude da Meema na kan Gadi, Aneesa ta danne kan Saude, duk ta chanza kamar wacce Aljannu suka shiga, tace "Saude Aminu ki gaya min da babanki, Ni diyar Hafiz Lema ce? Hafiz Lema ne Baba na? Dama ni shegia ce?"

_Bibilicious Biebee_
(donAllah kuyi hakuri, kunji ni shiru kwana biyu, hakan ya faru ne sakamakon Makaranta da muka koma, Karatu ya tasoni gaba wallahi ga matsalar wuta da muke fama da ita, kuyi min uzuri, nima so nake nagama wallahi, kunsan halin Karatu. DonAllah ku cigaba da Hakuri nagode..)

👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

Pg5⃣7⃣

Cikin k'ak'ari Saude tace "Aneesa ki dagani, You are hurting me, ki cika min Wuya" Meema tayi tayi ta k'waci Saude daga hannun Aneesa amma ta kasa, Nene a ranta tace "ku k'arata chan" Mami da Daddy suka shigo da sauri, Daddy yace "Meke faruwa nan ne?" ai Nene ta mik'a ma Daddy wayar Nasiba yayi Playing recording din nan, idan shi ya kada yayi jazir, ya Kalli Saude da Aneesa cike da Tsana, Daddy ya juya ya bar Dakin, Mami ce ta k'arasa gunsu tana ririk'e Aneesa, Aneesa Calm down, let your Mom go, please" a hankali Aneesa ta zame k'asa tana gurshek'en kuka me tsumma rai, Sauden ma Kukan takeyi, tace "Aneesa my child, ki saurareni" Aneesa tace "Saude ki daina min magana, ni ba diyarki bace, ashe ni shegia ce? Ba ta hanyar aure aka sameni ba? Kikayi min k'arya Babana ya rasu, Allah ya isa, Allah ya isa, na tsaneki Saude, i wish i have a different Mother" Mami tayi saurin taran Aneesa tace "Haba Aneesa, ki daina magana haka, Musulmi na kwarai shine wanda yake rungumar k'addarar sa da hannu bibiyu, me kyau ko mara kyau, DonAllah muje ki sha ruwa ki huta, kar ki sa abun a ranki". Fuu ta fita kamar zata tashi sama, Mami ta kalli Saude ta dan yi mata alamun tayi hakuri kafin ta wuce, Saude ta daura hannu a kai ta rusa ihu, Shikenan Asiri na Ya tonu, banda sauran Mutunci a idon kowa, Meema tawa ta k'are ya zanyi?" Meema ta hau lallashinta.

Safa da Marwa Alhaji Habib ke tayi a tsakar dakinsa, Wannan wani irin musiba ce, ya zaayi Saude ta iya wannan cin Amanar? Ta yaya Saude zata musu haka? Taya zata Aure shi bayan tasan cewa Hafiz ne Baban 'yarta, Mami ta shigo ta dafa kafadar shi "Habibi, donAllah ka kwantar da hankali, daure ka sha ruwa gashi nan" Alhaji Habib yace "Shatu Sauda taci Amanata" "Shhh, ka sha ruwan nan, everything is going to be fine InshaAllah" ya karba Cup din hannunta ya kurba, "Sakinta zanyi, ba zan iya zama da ita ba wallahi" "DonAllah dont make any descision yet, you are Angry, kar kayi abunda zakayi dana sani" "da nasani? Shatu da nasani fa? Don na saketa? I never loved her, God i didnt even know why i got married to her, itama kwadayi ne yasata Aurena, idan ba haka ba meye zata dinga maganar Gado, gaskia ba zan iya zama da matar nan ba, ta zalunceni, Sakinta Zanyi, and Hafiz? How could he do this to us? "DonAllah ya isa Habibi, Hafiz ya rasu, please dont say bad about him, Allah ya gafarta mishi ya rahama mai, and if you have the slightest respect for me, ba zaka saki Saude ba, zaka cigaba da Aurenta ko don Aneesa, diyar k'aninka" "Shatu kar ki man haka" Mami ta rungime Mijinta tana shafa kanshi kamar k'aramin yaro tace "Please Habibi, do it for me, Please".
*******
A daren Ranar, Saude, Aneesa, da Daddy ba su samu sun runtsa ba, Washegari Aneesa ta ki bude k'ofa, Mami tayi kwankwasawr duniar nan, amma taki ta bude.
K'arfe 11:30 Uncle Zaid ya shigo gidan, Tun daren Jiya Daddy ya kirashi ya sanar dashi, abun ya firgita Zaid Sosai, amma beyi wani mamaki ba, ya Umurta duka 'yan gidan Su hallarci Parlorn Daddy, har su Nene karere, bayan Meema ta gunguro Saude kan Kujerar guragu, Duk ta fita hayyacinta, kafar nan ta faara rubewa, ga wani wari, Zaid yace "Ina Aneesa?" Mami tace ta kulle k'ofa tun jiya" Zaid ya mik'e ya wuce Dakin Aneesa ya shiga kwankwasawa, "Anee open the door, Uncle Zaid ne please" "Go away i dont want to see anybody" Anee Please kizo ki bude mim k'ofa, nine Uncle Zaid, K'anin Babanki" a hankali ta bude kofar tare da Rungume Zaid, be hanata ba, kuka take tayi sai da tayi me isar ta kafim ya jata har toilet ya wanke fuskarta kafin ya rik'o hannunta har Parlor inda suke Jugum jugum kamar Gidan Rasuwa.
*******
"Uncle Zaid bana son ganin wannan Matar a rayuwa ta, Na tsaneta, na tsaneta, tayi Zina ta haifeni, ni bazan zauna rumfa daya da ita ba" Aneesa ta fashe da kuka me tsuma rai, duk sai ta basu tausayi, Saude ta gungura kekenta gaban Aneesa, tace "ki yafe min, ki sani whatever i did, was because of you, i did it for you to have a better life, i did it because i Love you" cikin tsawa tace mata "k'arya kikeyi, Makaryaciya, you never loved me, coz if you do, you wouldnt have given birth to me, you were a slut, and thanks to you, i'm a bastard" ta juya zata bar Parlorn da gudu Saude tayi saurin mik'ewa zata bita, ta turgude ta fadi, wani ihun wahala ta sake Mami, Meema da Seebi sukayi Kanta, Daddy Dauke kanshi yayi, Rafeeq dama latselatsen wayan shi yakeyi, Zaid yace "Feeq je ka fiddo mota, mu kaita Asibiti" Feeq yayi kamar be ji ba" Zaid ya sake cewa "Rafeeq Lema, i said je ka dauko mota zaa kaita Asibiti" Rafeeq ya mike tare da zare earpiece din kunnen shi, ya kalli Zaid yace "No Uncle Zaid, ni ba zan dauko Mota akai any bitch Asibiti ba, besides I never liked her" ya wuce ya bar Parlorn, Zaid yayi saurin Kallon Alhaji Habib, Shi ko ya daga kafada alamun be damu ba, shima ya mik'e ya shige daki, Zaid ya kalli Mami yace "barim dauko mota, kuyi k'okarin sauko da ita".

Bayan Sati 2
Cikin kwanakin nan Sha hudu, kallo daya zakuyi wa Saude ku san cewa tana cikin Azaba da Musiba, don k'afarta ya gama Rubewa, har aiki akayi amma kamar an jangwalo wani abun, don kafar tayi damadama, ko so daya Daddy be zo ya dubata ba, kullum sai sunyi Fada da Mami kan sai yazo dubata amma yak'i, Aneesa ma idan ka mata maganar dubota sai ta hau Zage zage, Mami ce d a Seebi ke kula da ita harta Meema tayi watsi da lamuran Yayar tata, sai ta ga dama take zuwa Asibitin, Mami kuwa ko so daya bata taba gazawa da kula da Saude ba, Zaid ne ke Biyan duk wasu kudin da aka kashe a asibitin.
Dr ya kira Mami Office dinshi yace "I am so sorry to tell you, k'afar Sauda Ya rube, bai da wani amfani, idan aka barshi a hakan zai yi causing trouble to the other leg ne, So ina ba da Shawarar a yanke kafar, ayi mata Aiki me kankat" Mami ta dafe k'irji tace "A yanke k'afar fa kace" Dr yace "Its the best solution, ana iya samata k'afar roba, amma kuje kuyi Shawara".
**********
Waya ta kira Zaid ta shaida mai yace" Ba matsala amma ta tuntubi Sauden, shi yana wani aiki ne idan ya samu sarari zai lek'o Katsinar" ko da ta tuntubi Sauden da maganar Sosai ta firgita, taci kukanta harta godewa Allah, wai yau ita Saude me ji da kanta, me takama da duk abunda take so sai ta sameshi ko ta halin k'ak'a wai ita ake cema zaa yanke ma k'afa, lallai Duniya Budurwar wawa, to ya zatayi idan bata amimce ba zai shafi dayan kafar, ga wahalar da take ci, gwara kawai a yanke, tana hawaye tace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login