Showing 93001 words to 96000 words out of 149166 words

Chapter 32 - Ke alkhairi ce COMPLETE HAUSA NOVEL

BIEBIE   

22 Oct 2024

25765

gurin su" Rafeeq ya mik'e tsaye yace "Idan anyi hutu kaji" ya kalli su yace "Ina so in koma Katsina yanzu" Mami ta zaro ido tace "Feeq 5 saura fa" yace "eh Mami" Abbii yace "da dai ka bari gobe" yace "Gobe zanyi test karfe 8" nan dai suka mai Allah ya tsare hanya, ya ja hannun Mami suka wuce Gida, sun dade suna magana, tace "R-Lema anya ba zaka bari sai gobe? 6 har tayi fa" yace "zan tafi dai, your prayer keeps me moving" bmya rungumeta kafin ya sake ta ya shige mota da sauri don ganin zata fara kuka. Nan ya dauki hanyar Katsina ta bishi da Addua "Rafeeq Allah ya tsare hanya ya kaimin kai lafiya, yasa ka iske su lafiya Amin"

_Layout Katsina_
11:45pm

A gajiye likis ya shigo Unguwar, duk ya gama gajia, ya wahala Mota ta tsaya mai gurin Dabai, Unguwar Shiru ba ka ganin kowa waje, abunka da Unguwanin yan gayu kowa na Gidan shi ya kulle, daga nesa ya ke hango hayak'i na tashi kan katangar wani Gida, yace "toufa, wannan hayakin daga ina, ko da ya kusanto gidan sai ya ga Gidan Nene ke ci da wuta, ai be san lokacin da ya fita daga motar ba, Gidan na ta ci da Wuta, ya rasa me zaiyi, da sauri ya dinga kiran wayar Nasiba, tana ringing baa dauka, duk ya bi ya damu, ya nufa k'ofar da niyyar ya bude ya ji wani irin zafi, ya ja da baya, ya fashe da kuka, Uncle Zaid ya fara kira, Zaid be dauka ba a lokacin yana toilet yana wanka, Yayi tsaki cikin kuka ya kira Maalesh, Maalesh ya daga " Guy howfa u never sleep?" cikin rudani yace "Nasiba, gidansu na ci da wuta" "What" inji Maalesh, gani nan zuwa, ya latse wayar, Rafeeq ya dinga kwankwasa ma makotan su Nasiba don suma Katangar ta hau ci da wuta, nan yayi tunanin yan kwana-kwana(Fire fighters), ai kafin ya samu taimako daga Makota k'ila gidan ya k'one kurmus, hannu na rawa ya latsa numbern Daddyn shi" a lokacin yana kwance ba dai bacci yakeyi ba, yana tunanin Wani abu ne da be san meye ba, ya ga kiran Rafeeq, ya daga da Mamaki "Ibn Zaid ya akayi da daren nan haka?" baki na rawa cikin kuka yace "Daddy, Daddy" Ya tashi a firgice yace "What isit son? Calm down and Talk to me" da k'yar yace "its Nasiba and Neh-Neh" zumbur Daddy ya mik'e yace "me ya samesu?" gidan su na ci da wuta, Daddy bansan me zanyi ba" Inalillahi wa ina ilaihir rajiun, Stay still son gani nan zuwa, i'll make some phone calls" ya tashi ya zumbura malummalum dinshi kan dogon wandon da ke jikinshi, ya dialo numbern shugaban Fire Fughters ya sanar dashi komai suka bashi tabbacin yanzu zaa su fito don ceton su"
Zaid ya kira Rafeeq bayan ya fito daga wanka, amma Rafeeq be dauka ba, a lokacin makocin su ya bude gida ya fito da yaranshi maza sun fara zuba ma Gidan Nene ruwa, amma kamar ana k'ara rura wutan, Maalesh ya kira Zaid ya sanar dashi, hankali tashe ya bar Hotel din ya nufo gidan Nene, a tare yan Fire fighters da Daddy suka iso, sai Maalesh, Rafeeq ya rasa sukuni, tuni Yan kwanakwana suka kuna injin suka kashe wutan Gidan Nene, Hankalin su a Tashe, Rafeeq ya dinga bubbuga gidan Nene amma ba alamun akwai me rai a ciki, Da K'arfi yace duk sun mutu kamar wani zautace, Maalesh cike da tashin hankali yace "Noo ba su mutu ba, we just need to get in" Rafeeq ya kalli yan kwanakwanan yace "Someone should break the Goddam Door" sai ya fashe da kuka, Zaid na fitowa daga motar ya nufo su, Rafeeq na ganinshi ya rungume shi, Zaid ya dinga bubbuga bayanshi yana kiran they'll be fine, Rafeeq yace "Noo Uncle, i cant loose them both, i cant" Daddy ya taba bayan Rafeeq yace "Rafeeq ka gani an 6alla kofar, yanzu zasu firdosu a kai su Asibiti, InshaAllah they are going to be fine" Rafeeq ya waiga ya ga Jamian sun 6alla k'ofar a sittin ya ruga gidan ana rirrikeshi yana fizgewa ya kutsa kai ciki, Zaid bi bayanshi Daddy da Maalesh suka rikeshi, Zaid cikin tashin hankali yace "No he cant get in there be da facial mask, Rafeeq ka fito please" Attishawa ya fara yi amma be fasa kutsa kai ba, ko da ya isa har ya ga sun dauke Nene kan Gadon marasa lafia sun saka mata Oxygen zasuyi waje da ita, sauran kuma suka nufa Nasiba, bangaje su yayi ya nufe ta yana Attisahawa da Tari ya Ciccibi Nasiba kamar jinjira, ba alamun numfashi a tattare da ita, fadi yake "Hey hang in there, i cannot loose you too, i lost Rafee'ah" kamar mahaukaci yake sunbatu ya fita da ita, be tsaya ko ina ba sai motar shi, baya ya sakata, ya shiga ya ja Motar, Maalesh na kwala mai kira amma ina sam baya ji, Officer yace da Daddy "ku tsayar dashi, she needs First Aid, Oxygen zamu saka mata, she needs it now, Daddy yace i'm sure Asibiti zai kaita" Officer yace "i'm afraid kafin a kaita Asibiti maybe ta mutu".

_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

Kin chanchanci Yabo a guna Masoyiyar Asali, Wannan page din naki ne Ag😘

Pg5⃣1⃣

Yana tuk'i yana kallon bayanshi hawaye na zuba, sambatu yakeyi, "DonAllah kar ki tafi ki barni, Rafee'ah ta yafi, kema kar ki tafi, bansan me zanyi ba in kika mutu, Ya Allah kar ka dauki ranta, Allah ka dauki nawa instead" ireiren maganganun da Rafeeq keyi kenan, Sanyi ACn Motar ya sa Nasiba farfadowa, tari ta hauyi ai da sauri ya juya ya kalleta, wani murmushin da be san lokacin da ta subulo ba ya sake tare da taka birki ya tsaida motar, fita yayi ya koma baya, hannunta ya rik'o Yace "Naseebah, Naseeba are you Ok?" tari ta shiga yi ba sassautawa ta zame hannunta daga nashi tace "I'm fine, ina Nene?" yace "Tana chan gurinsu Uncle Zaid" Nasiba ta shiga tuno abunda ya faru tiryan tiryan, tace "Hamma mu koma donAllah, Nene na chan ban san halim da take ciki ba" yace"karki damu nasan Asibiti zasu kawota, right now i need to take you to a hospital" tace "please mu koma, i'm fine now, i just need Water" da sauri ya dauko mata ruwa a gaban Seat, ya bude ya bata ta kwankwada" cikin sigar lallashi yace "Listen to me, zan kaiki Asibiti a duba ki, Neh-neh kuma is in safe hands, barin kira su in gaya musu kin farfado mu hade a Asibitin" Maalesh ya kira, "Maalesh kuna Ina?" cikin damuwa yace gata nan zamuzo "Alheri Clinic don ya fi kusa" "bata farfado ba?" Wallahi kuwa feeq, gatanan ko numfashi batayi" Rafeeq ya cije hak'oranshi, yace mu hade Asibitin ni na kusa ma" sukayi Sallama, Seebi tace ya jikin Nenen? Rafeeq ya fita ya koma matukin direba tare da cewa "gata nan zasu kawo ta wanchan Asibitin".
*****
Daidai isowar Ambulance, aka fito da Nene aka shiga da ita ciki already Daddy ya kira Dr aka yi da Nene Emergency, da kyar aka samu suka tsaya daga waje,Seebi kuwa ta k'i yarda a bata gado acewarta ba inda ke mata ciwo, Dr's suka buga nan suka ta6a nan ba alamun Nene Zata motsa suka dukufa da aikinsu a matsayinsu na Kwararrun likitoci.
Bayan 'yan mintoci Likitoci suka fito fuskar su ba Annuri.
Dr Sami yace "i'm so sorry, we couldnt save her" luuuuu Nasiba ta zame k'asa ta zauna dabas, Inalillahi wa ina ilaihir rajiun inji Daddy, Zaid Ya dora hanayensa duka biyu akai, Maalesh ya fara matsar kwallah, Wtf? Inji Rafeeq, ya chakume shi, what do You mean by you couldnt, save her huh? Dr Umar yace "kuyi hakuri, kamar tana da Athma, kuma ta shaki hayak'in Sosai, kuyi hakuri Addua kadai take buk'ata" Bangaje shi yayi ya shiga dakin duk suka biyo bayanshi banda Nasiban da Hawaye ke ambaliya a fuskarta, Nene ta rasu? Nenenta? Inalillahi, Nan da nan ta chanza kammanni sabida kuka, tausayi Mahaifinta da Goggonta da ke Jigawa ya kamata, suna mugun son Nene (kamar yanda Iyalan Zailani keson Tsoho, lols) kuka takeyi sosai me hade da Sheshek'a, ta kasa yarda da Nene ta Rasu. Rayuwar da sukayi ya fara dawo mata, ta mik'e Zumbur ta shiga dakin.
Kwance ta ga Nene an rufeta da zanin Gado, Uncle Zaid ta fara kallo, har yanzu be sauke hannunshi daga kansa ba, yana kuka mara sauti, Alhaji habib be daina Salallami ba, Maalesh na kuka, Rafeeq na kwance kan jikin Gawar Nene yana kuka, Neh-Neh DonAllah ki tashi, DonAllah, Neh-neh kin zama wani Jigo a cikin Rayuwata, na k'i yarda kin mutu, in kika mutu bansan ta yanda Zan cigaba da Rayuwa ba ke a cikinta, Neh-Neh Ina sonki, ki tashi na yarda ki cigaba da cemin Dunkum, zan amsa sunan, ba zan k'ara miki tsaki ba, zan dinga shan Maganin nan, zanyi duk abunda kikeso, DonAllah ki tashi, Allah kar ka kashe min Neh-neh nah, Allah ka tada min ita I love you Neh-Neh. wani kukan me tsuma rai Nasiba ta fashe dashi, duk sun tausaya ma Rafeeq, Wai dagaske Nene ta Rasu? Shikenan ba Nene? Numfashinta taji ya kusa daukewa itama.
"kai ni Dallah daga ni,ka wani danne min kahon Zucciya, ko sai ka k'ara sani?" da mamaki ya dago ya kalleta yace"Neh-Neh??" tana yunkurin tashi Maalesh yayi saurin taimaka mata ya zaunar da ita, murna gun Rafeeq baa magana ya subuce da dariar murna "ku Bata mutu ba Wallahi bata mutu ba" Sujjudushukur Nasiba da Uncle zaid sukayi don godewa Allah, Alhaji Habib ya fita don kiran likita yana hamdala, daya bayan daya ta bi su da ido tace "wai ya? Ko cema ku akayi na mutu ne da kuke ta wannan abun? Dr Sami da Dr Umar suka shigo da mamaki, sun tabbatar da zuciyarta bata bugu kafin suka sanar da Yanuwanta, to ya akayi haka? Ikon Allah ne, Dr Sami ya soma dube dube a jikin Nene, Yace "Blood of Jesus has healed her, she is a strong fighter" Nene ta katse shi tace "wai gwajegwajen nan na meye? Kalau fa nike, zaka zo ka tasani gaba kana man turanci, Daga gani kai kace musu na mutu, haka kurun ka tada wa 'yan jikokina hankali" duk sai da sukayi Daria banda Rafeeq da ya daure fuska wai ba abun daria bane(ikon Allah ku ji min Rafeeq da ya gama fita hayyacinshi don ance ta Mutu) Dr Sami ya kalli abokin aikinshi yace "Dr Umar what is she saying?" Dr Umar yace "Shes thanking God that Shes still Alive, go to the Office i'll take it from here" Dr Sami ya fita daga Ofishin.
Ya kalleta da Murmushi yace "Sannu Mama, kiyi hakuri dogon Suma ne kikayi, Wallahi mun dade a kanki, Duk wata kafa ta sadarwa ta tsaya a jikin ki, saida muka samu tabbacin hakan kafin muka sanar dasu" tace "da kuka tabbatar kaine a zaune yanzu? Nace kaine a zaune? Toh ban mutu ba, bawai tsoron mutuwar nike ba, ku dai san aikin ku, ku san me zaku dinga fada ma mutane, yanzu da bakin labarinku ya sa Zuciyar Jikata bugawa ta shek'a lahira fa? Ni na mik'e ita ta mutu to me akayi kenan? Anyi ba ayi ba, ana muku kirari da likita bokon turai, to bokon kashi dai tunda ba ku san aikinku ba" nan ya shiga bata hak'uri tace su zaka ba hakuri, sai in yafe maka" yayi murmushi yace da su "Daddy suyi hakuri" murmushi sukayi sukace bakomai. Bayan nan aka fara diramar sama Nene Drip tace kwatakwata ita bata san Zancen ba sai dai a sallameta, Seebi tace "Wai Nene ki tsaya mana a sa miki drip din" tace "naki, ke ki zo a saka miki" Rafeeq ya daure fuska, "Uncle Zaid please talk to this Stubborn Old Woman" yayi daria yazo yace "Nenenmu kiyi hak'uri ki bari a saka miki drip din, kinga ko an sallameku yanzu ba inda zaku zauna a gidan don kusan komi ya k'one, da lallashi da lalama Nene ta yarda aka sa mata drip din.
"***
A dan tsorace Rafeeq yace "Ku tsaya ku tsaya? Ku tsaya! Ina Ayman? Nene tace sai yanzu ka tuna da ita? To kar ka damu tana gun Kakar ka, dazun Baban ta ya kaita kwana, ashe Soyayyar k'arya ake mata tunda sai da aka Neh-neh ta watsake aka tuna da ita, Rafeeq ya murtuk'e fuska, Zaid yace "kaii Nene, kinsan in ka rude abun da ke gabanka kawai kake gani, amma ba me tantaman Soyayyar Rafeeq ga Ayman, Nene tace sai ni don ya fi so na, yau naga tashin hankalin su O'eh, Maalesh yace "a fadi suna mana", tace "da Dunkum nike ai yasan dashi nike, tashin hankali yau Su dunkum har da su i lobi me Neh-neh, to nima i lobi you Dunkumeh, ai na rok'i Allah kar ya kasheni sai ya nuna mana auren mu" Alhaji Habib na daria yace "Aurenku ke dawa? Tace "yo ni da Dunkum mana, ai sai na Auri Dunkum" Duk suka fashe da Daria banda Rafeeq da ya hada gabas da Yamma kamar be ta6a daria ba.

"You cant sleep with them you know?" Cewar Maalesh, "Why cant i?" inji Rafeeq, Daddy yacei "Aa Rafeeq gida zamu tafi, ga Nasiba nan she cant look after her" yace "She's not well too, itama she needs someone to look after her" "Aa Hamma i can, i'm fine ba abunda ke damuna" Rafeeq yace "Shuttup you are not fine" Zaid yace "IkonAllah" Rafeeq be sake magana ba ya zaro wayar shi daga Aljihu ya latsa waya, ringing biyu ta dauka cikin magagin Bacci "Hello Mom" Mom din Maalesh tace "Son ya akayi ne da daren nan?" "sorry na tadaki, Hajjo fah?" ta kalli Agogon gefen gadonta tace for goodness Sake Rafeeq shes Sleeping, baka duba agogon bane kafin ka kira, this is 12:15am, guntun tsaki yayi yace "sorry mom, but you need to wake her up, an sake kwantar da Neh-neh kla Asibiti Maalesh yanzu zaizo daukanta, thanks Mom Love you bye" be jira ta amsa ba ya kashe wayan tare da kallon Maalesh, Maalesh kaje ka dauko Hajjo, Dad Uncle Zai ku tafi gida, I'll be here har sai Hajjo tazo". Kamar Shine Babba duk sukace Okay Maalesh ya fara tafiya, Kafin su Daddy, dama Nene Already tana bacci. A waje Daddy ke cema Uncle Zaid Rafeeq ya damu sosai, damuwar da yayi kan Nene da Seebi ya ban Mamaki, Zaid yace "ba wani abu bane kawai dai ya girgiza da Gobaran nan, na san Mutuwar Rafee'ah ta dawo mai Sabuwa, ya zata zai sake wani rashin ne, don kasan Ya dauki Nasiba kamar 'yaruwarshi, kuma duk da ba sa shiri da Nene, yana sonta Sosai" Daddy ya jinjina kai. A lokacin Zaid ke ba Daddy labarin abun da ya faru tsakanin Saude da Nene, yace " tohh abunda ya faru kenan, dazun naga bakinta ya kumbura da na tambayeta sai cewa tayi a tayi da bango ashe da walakin goro a miya, ta san basu kyauta ba shiyasa bata gaya mim abun da ya faru ba, bakomai Nenen tayi daidia" sukayi daria.
*****
"Ya ki ke jin kanki yanzu, akwai abunda ke miki ciwo, ko yake damunki?" tayi murmushi tana mamakin wannan hali na Rafeeq, lokaci daya zai nuna damuwarshi kan abu, a wani lokacin kuma sai ya nuna shi be da damuwa ko kadan, kamar yanzu ne, yanda yake tambayar ta kamar ance sai ya tambayaeta dole, tace "Ba abunda ke damuna Kar ka damu" a takaice yace "ban damu ba" tayi murmushi tace "Liar, ka tabbata baka damu ba?" ya mata shiru, itama tayi shirun chan sai yace "Naje Kaduna" da sauri ta kalleshi, "da gaske kaje Kaduna?" be amsata ba yace "Anan yace in gaidaki, Murmushi me sauti tayi sannan ta fara hawayen farinciki, yace "Maminki na gaida ki, wai ku maida mata Babynta haka, she's missing her enough" dariyan farinciki ta fara tana Hamdala, tace " Thank you Hamma Rafeeq" a ranshi yace "meyasa take min Godia?" ta sake cewa "I'm proud of you" Murmushin gefen baki yayi ya tashi ya barta zaune ya koma chan kusa da Nene ya zauna, ko wannen su da sak'e sak'en da yakeyi.

Bayan kwana 3

Cikin 'yan kwanakin nan Uku, Nene ta tabbatar ita *'Yar Gata Ce* (Miemee Babe's Novel) don ko Zaid, Maalesh da Alhaji Habib na kyautata mata, Rafeeq ya rage zuwa Asibitin ya kanzo da daddare, Hajjo na kula da Nasiba da Nene.
Miemee da Usheey sunzo duba su Nene
Tun daren da akayi Gobarar Mak'ale ya kira uwar dakinshi ya sanar da ita ai ya cika aiki, ya cinna ma Gidan Nene wuta, Wutar da Suka kunna da Petir, Saude tayi daria tace "that Old witch, yanzu sai inga iskanci, dama Alkawari na miki cewa zaman katsina sai ta gagareki". Ko da safe sai da suka fita su 3 suka ga gidan Nene a k'one, murna kamar su zuva ruwa a k'asa su sha, Meema ta san aikin Saude ne banda Aneesa da tayi zaton Allah ne ya saka musu.

Zaid ya ji dadin Shiryawar Rafeeq da Maminshi, sai da yayi Azumin Godia ga Allah, dama Alwashi yaci na duk randa Rafeeq ya daidaita tsakanin shi da Maminshi, to zai jera kwana 5 yana Azumi don nuna jin dadinshi.
A safiyar Yau Nene ta sa Darun sai an Sallameta, Nasiba da Hajjo suna ta bata hakuri kan ta bari sai ta k'ara jin Sauk'i, ana haka sai ga Rafeeq da Daddy da Zaid sun shigo da Dr Umar, Yauwa Dafta, yau sai ka sallameni, Dr yace "dama Mama abun da nazo kawo miki kenan, takardar Sallama, tace "yo ni ai ko ba takardar Sallama tafiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login