Showing 135001 words to 138000 words out of 149166 words
wurin Dinner, idan baka nuna ba, ba zaa barka ka shiga ba" Nene tace "ina wai?" Mami tace "Dinner kamar Walima aka hada, zaa hadu duka a ci Abincin Dare don murnan Biki" Nene tace "Tab, Munafurci ya sa ba a a gaya min ba? Ya ake abu ne ba a sanar min?" Ummi tace kiyi hakuri, dama katittikar mu ne nanz shine yanzu zan kai gida a shirya a tafi" Nene ta harari surukar ta tace "bani su nan" da sauri Ummi ta mik'a mata IV's din duka jiki na rawa, Nene ta zaro daya ta mik'a mata, tace "muje gidan, zan ba wamda ya dace yaje don kar muje su ba mu kunya, sai wanda yayi wankan Suwaga(Swagger) zaije" duk sukayi Daria, Mami tace "to Nene ku je ku shirya da anyi Sallahr Ishai zaa tafi, Nene tace bari mu je da sauri suka fita ita da Surikarta Ummi.
Mami kuma ta wuce Parlorn Daddy inda aka ma Nasiba Makeup, Sanye take da Turquoise Blue Wedding gown, da dogo Veil dinshi wanda Houseofkaya suka dinka mata, Rigar ta hadu iya haduwa, Aneesa ce ke koya ma Nasiba yanda zatayi tafia gun dinner din, Mami ta shigo da Sallama, Nasiba tayi saurin Sadda kai, Mami ta isa gunta ta rungume Nasiba tace "MashaAllah Seebi kinyi kyau sosai"Murmushi kawai tayi, Wayar Mami yayi k'ara, ta dauka " Yeah Okay, we are ready as well" Mami ta kalli Lynaz me Makeup tace "Thank you Lynaz, you've transformed my daughter" Lynaz tace "thats my job maam, we bring out the beauty in you" Mami tayi Murmushi suka tarkata kayansu Aneesa tace "i'll show you the way out" Mami tace daga nan ki kira min Wayr Maalesh, Rafeeq yazo ga EventsUnlimited(masu hoto) nan sunzo, yazo ayi Post wedding pictures kafin a tafi dinner din, Aneesa tace "Ok Mami" Mami ta tsura ma Nasiba kyau, duk kunya ya kamata ya sadda kanta k'asa, Mami ta kamo hannunta tace "Nasiba Wallahi ina sonki ina jinki kamar Rafee'ah, kinyi kyau sosai, Allah ya Albarkaci Rayuwanku duka" a hankali ta amsa da "Amin".
Ta k'ofar baya aka shigo da Masu hotunan, don kar a dauki hankalin mutane, aka bi dasu ta baya suka hau sama Parlorn Daddy. Bayan gaishe gaishe suka hada kayan hotunan su. Mami ta fita waje don kiran Rafeeq ko Maalesh ta ko ci Sa'a wayar Rafeeq ta shiga, " "Hello Feeq kana ina? Mam ina tsakar gida, Oya ka shigo ciki ka hayo Sama, ga Eventsunlimited nan, kazo ayi Postwedding pitures, ya marairaice kamae zaiyi kuka, Mami ta ya zan shigo, Mutane da yawa, tace "ta baya fa zaka shigo" "ni Mami i cant" tace "Ina Maalesh ya rako ka mana?" Mam Lesh yaje tattaro Friends dina yanda zasu a kwashe mutane a tafi at once" tace "Alright gani nan zuwa in taho da kai".
Ta sauka kasa ta ga Rafeeq, sanye yake da shiga irinta Nasiba, manya kanya Turquoise Blue ga hularsa yayi kyau fiye da tunanin me tunani ga wani k'amshi yana zubawa, Mami ta rungume shi tare da mai kiss a kumatu, tace " Yaro na ya girma " Sake rungumeta yayi ta ja hannunshi har Sama ta sada shi da Parlorn Daddy ta turash ciki. Sandarewa yayi da ya hango Sanyin idaniyar shi daga chan gefe ana kashe mata hoto, Kallonta yakeyi cike da so da k'auna, ya shagala da kallonta sai ji yayi Me daukar hoton tace"The Groom is here, come over here" Hankalin Seebi ya koma kan Rafeeq, gani yakeyi Yafi ko wa Dace tunda yana da Seebi, itama hakan ne, don yau ya mta kyau matuk'a, a hankali ya taka har gunta yana mata kallo kasa kasa, ta sadda kanta k'asa ya sa hannun shi ya dago fuskarta ya kai bskinshi kan kumatun ta ysyi kissing a hankali, daburcewa tayi Lokaci guda ya sa hanayenshi duka hya ya rike kafadunta, idonta a runtse ta bude su a hankali, Cikin muryar rada yace "Calm down baby, i got you" Me hoto tace "Oya Romeo Shall we?" kao Kawai ya gyada mata, nana aka fara kashe musu hotuna kala kala.
8:10pm
Ko wacce ta samu gurinta a Mota, Motoci aka kawo sun fi 20, yawancin Manyan duk sun tafi, Mami da Aminanta sun wuce, yanmatan ne dama suka rage, Rafeeq da Seebi a bayan Motar Uncle Zaid, Miemee da Maalesh a gaban Motar, Usheey na motar wani friend din su Maalesh Faisal, tun farkon biki suka hade, kuma da alamu suna son junan su,
Nene ta shigo gidan, Da sauri tana murnan ga motoci nan basu tafo ba, dama sai da ta tabbatar ta sallami kowa a gidanta kafin ta fito, Daga dan Nesa ya hangota, a zuciyar shi yace "Neh-neh? ina take tunanin zata?" wata zuciya tace "Dinner"da sauri ya girgiza kai, In har ka bari Matar nan taje Dinner dinnan, to sunan ka sorry, zata kwafsa maka, ta bada kai gaban Friends dinka, zata ba ka kunya gaban Manya mutane, you have to stop her from coming, unless yiur name will turn to Apology" gargadin da zuciyarsa ke ma sa kenan, da sauri ya bude k'ofa yace "i'll be right back ya fice" ba su lura da ita ba, da sauri ya tare ta, ta yashe baki "Ahh su dunkum da manya kaya, ka ga kyan da kayi?" yayi Murmushin yak'e yace "ban Kai ki ba" Nene akaji dadi tace "Allah ko? Ni naga k'auna, ga motoci nan bari in dirje In shiga"Da sauri Feeq yace "No No Neh-neh, Mami tace " ki tafi mata da wasu kaya" Nene tace wasu kaya kuma dunkum?" ko dar yace ina jin kayan da zata raba wa mutane ne" suna ina? Yace Suna daki, kaje ka dauko min kar a tafi a barni" yace "wa zai tafi ya barki, ke ke da Ango" Nene ta ji dadi tace muje mu kwaso, suka jufa hanyar dakin Rafeeq, Rafeeq ya bude dakin shi, Nene ta shiga tace "ina kayan suke?" yace duba kewaye, aiko tana shiga yayi saurin fita ya sa Mukulli ya kulle K'ofar, ba ta lura ba illa ma cewa take "Ina kayan suke dunkum?" yana fita ya ma motovin gaban gida Signal da su fara tafia, aiko duka motoci suka kumna Motar su, da sauri ya hau tasu, Maalesh ya tada Motar suka bar haraban gidan fuk suna masu kunna fitilar motocin su, abun za kyau Convoy din ya hadu.
Haka su ka wuce NYSC hall, inda a Nan ne zaayi Dinner.
*******
"Bara'uba Salatin gwarawa" cewar Nene da ta fuskanci Dunkum ya kulleta a Dakinshi.
****
A Convoy suka isa har NYSC camp Hall, suna isa Maalesh ya kira Mom dinsa yace sun iso, Mom din ta sanar da MC Lubna Sufyan, nan MC ta buk'aci kowa da ya mik'e tsaye don shigowar Amare. Dj ne da Makadi(Mai Asharalle) nan da nan DJ ya sa wak'ar Nura M Inuwa na Amarya, Mom ta fita ta hada kan Amaren, Layi ne biyu, daya dogo na mata, daya na maza, in twos zaa shiga, Feeq da Seebi a tsakiya, ofcourse Miemee ce a gefen Maalesh su ne a gaba, Ushee kuma da Faisal a bayan su, Maalesh yayi kyau sosai, kayan shigen na Rafeeq ya sa, Abokan Ango Masu jiji da kai, duk ba zasu wuce shekarun Rafeeq ba, sai shan k'amshi sukeyi, ko don sun ga suna da kyau sun hadu ne oho, Kawayen Amarya kuwan sun sha kyau sun gaji, Anko suka yi na wani atamfa mai touches din Ja, sun daura Head Ja, ga kuma Amarya da Ango sunyi turquoise blue abun duk sai ya bada color, Mom tace da Miemee oya Yarinya na ku fara shiga da taku kunji?ta kashe ma Maalesh ido, nan suka fara taku sukayi hall din, aiko sauran suka bisu a baya, Fuskar Rafeeq ba yabo ba fallasa, shidai ba Murmushi yake ba, shi kuma ba daure fuska yayi ba, Suna shiga hall din Gaban Seebi ya fadi, ganin haduwar Hall din, ga Idon Mutane kan su, Hall din babba Ne kuma cike yake Mak'il, Rafeeq ya lura da ita, a hankali ya sak'alo hannun shi cikin nata, dumin hannun shi kawai taji a nata, da sauri ta kalleshi tare, ya kashe mata ido, a hankali yace "I got you" idonta ya kai kan Ummi, Mami Abbii da Daddy a chan gaba, duk kunya ya lullubeta, Zata zame hannunta Rafeeq ya matse hannun, ya ja ta suka cigaba da tafia har sai da sukaje suka zauna wurin da aka tanada domin su, kafin aka fara gudanar da Shirye shirye, Daddyn Maalesh aka bukata don bude taro da Addua, Alhaji Habib ya zo yayi Welcome Speech(Sannu da zuwa), sannan aka bukaci Baban Abokin Ango da K'awar Amarya su fito don bada takaicecen tarihin Ma'auratan, Muhawara ya kaure tsakanin Miemee da Ushee, Miemee tace "Oya Ushee tashi jeki yi Jawabi kan Amarya" Ushee tace "Tabdi, kinsan dai bazan iya magana gaban crowd ba, ai ke zakiyi, so kije dont waste time"Miemee ta harareta tace "don ace baki da hayaniya ko?" sukayi daria, Maalesh ya taso ya zo kusa da Miemee, suka jera sukayi kan Stage din a tare, abun sai ya burge Mutane.
Maalesh ya fara magana; "My name is Mahmud Ali Umar, and Rafeeq is a brother from another Mother, we've been together for 20years, Rafeeq is a•••••••• nan Maalesh ya shiga koda Rafeeq tare da mai Fatan Alheri, Rafeeq ya taso ya rungume Maalesh tare da bubbuga bayan sa ya rada mai a kunne "thank you brother".
Miemee ta fara bada bayani kan Seebi, ta fadi kyawawan halaiyarta ta kare da mata fatan Alheri" aka tafa musu, MC tace kafin su tafi sai sun taka rawa, nan Surajo mai Maalesh ya fara wak'e Malesh babban aboki, da Maryam Miemee yar gayu, sin dan taka zasu koma MC tace da su "Are you a couple?" Maalesh yace "yeah we are" tace "You suit eachother" sukayi Murmushi aka tafa musu suka koma mazaunin su.
Aka gayyaci Ango da Amarya a fili, Marok'i sai kirari yake ma Ango, Mom ta hau sama don Rafeeq da Seebi sunki tashi, Ita kunya, shi kuma be son hayaniya, sai da Mom ta je ta sauko dasu, Wannan karon karon Dj ne, Wak'ar Work-Rihanna ft Drake aka samu su, dukkansu tsaye sukayi, ba me rawa, Mom ta rada ma Feeq a kunne Spray her, Ta wuce ta zauna aka barsu su kadai a fili, hannu ya sa cikin Aljihu, ya ciro bandir din1k ya fara lik'a mata, kanta a k'asa, ya dinga spraying, Yana mata liki'i, nan Daddy da Abokansa suka zo suka lik'a musu kudade masu yawa, gajiya Rafeeq yayi, ya kama hannun matarsa ya ja ta suka koma mazaunin su, nan aka ba Abokan Ango da Kawayen Amare fili suyi rawa.
Tagumi ta rafka hannu bibiyu tana tunanin irin dukan da zata ma dunkum idan ta samu ta fito, ita zai ci ma fuska? Don kar taje lanchin (luncheon)din shine zai kulle ta don bakin hali. Agogon dakin ta daga kai ta kall 9:15, ji tayi ana bude k'ofar dakin da Mukuli, da sauri ta mik'e ta la6e bayan labule don yau watan cin uban Dunkum ne ya shigo, fitowa tayi daga Bayan labule tace "Zaidu bawan Allah, kaine anan bakaje gun patin ba?" da mamaki yace "Nene, me kikeyi anan?" tace "ba wannan shegen yaron bane ya kulle ni a dakin don ya tsane ni, wai don kar inje partyn" Zaid yace "Wa kenan?" cikin fada Nene tace "Wa fa banda fitsararen Danka Dunkum" Zaid yace "shi Rafeeq din ya kulle ki? Saboda me to?" tace "Af Sabida ya tsanan mana" "aa Nene ki bar cewa Haka, bari in dauki abu mu tafi" ta yi Murmushi tace "Yawwa Zaidu Bawan Allah" da sauri Zaid ya bude Wardrobe ya ciro wata Envelop yace "muje Nenenmu, kai Nenen mu kinyi kyau wallahi" dadi kashe Nene tayi ihun murna tare da juyi tace "Ai nasani wallahi, kaima kayi kyau Sosai dama Zainabu ta na nan sa ta ganka" yana tafiya tana bin shi a baya yace "ai ta ganni" tace "ta ina? Ko ta zo ne? Yace " Aa Wallahi, ta Video Call, itama ta sa na makara" Nene tace "Miye Bidi'o kwal?" suka shiga Mota Zaid ya fara mata bayanin Video Call.
Yanzu lokaci ne na Nishadi(Entertainment) inda aka gayyaci Baban Cinedu da Baba Ari su fito don sa Mutane Nishadi, Baba Ari ya fito ya amsa Mike ya dinga Ma Feeq Ango kirari, ya dinga zazzafo zance, har gaban Feeq yaje ya na surutai, cikin Muryar shi yace Ango Rafeeq ka sha k'amshi, me zaka ce game da wannan Rana? Ya sa mai Microphone din daidai bakin shi, kamar ba zaiyi magana ba, chan kuma sai yace "Kana da Hayaniya" aiko duka hall din aka kwashe da daria. Baba Ari yace "Abun yazo inji me tsoron wanka, Amarya Nasiba, sai kin yi dagaske don Mijin naki, erhm erhm... Aka sake kwashewa da daria banda Rafeeq da ya murtuk'e fuska, Naseebah ta kalleshi ta sake daria, ya sa hannu ya tsinguleta tayi dan ihu me k'ara.
Yana daga ido idonshi ya kai kan Nene da Uncle Zaid baki bude a hankali yace "Akwai Damuwa" bacin ran Nene duk ya 6ace data ga Tsaruwar Hall din, da manyan Mutane da ke ciki, Ihu ta hada da Shewa da ta ga haduwar da Seebi da Feeq sukayi, ai da sauri ta k'arasa gunsu, tana washe Baki, Seebi ta mik'e ta rungume Nene, ta fara kwalllar farinciki, Nene ta bude baki tace "kwalliyar dubu dari da hamsin din zaki jika da hawaye? Maza Share hawayenki, ina nan tare dake" ta kalli Rafeeq tana mai Murmushi don ya mata kyaun da be taba ba, da tuno Abun da ya mata nan da nan ta galla mai harara. Mai hoto da gurbataciyar Hausarta tace "Mama siya a maka photo" Nan Nen ta pose aka fara kashe mata hoto, Nene har da rike su K'ugu duk Cikin style, sannan ta tunkude Feeq ta zauna a tsakiyar su aka musu hoto, har da dundu ta sakar mai ta baya ba tare sa Seebi ta gani ba, takaici ya hana shi Motsi.
Muryar Uncle Zaid ta kauraye hall, din inda yake ba Amarya da Ango Shawara yana musu Nasiha, Nene taji wani dadi, da sauri ta bar gunsu Seebi ta k'arasa gun Uncle Zaid, cewa take "Zaidu Bawan Allah ka bani abun maganar nima nayi".
"Assalam Alaikum jama'a, sunana Aminene Mamman" Rafeeq ya dafe kanshi da hanayenshi biyu cike da takaici, a hankali yace "Lord of Mercy! what is this crazy Woman doing?" Seebi ta dan rankwafo a hankali tace "Baby its your day, be happy dont be Sad" Murmushi yayi yace "Ina sonki kinji?" Murmushi kawai tayi, Nene ta cigaba da cewa "shekaru na Sittin da dori nice kakar Amarya wato Seebi, duk da wasu ba su so na zo gun nan ba, har kulle ni sukayi a cikin daki, toh Da yake ta Allah ba tasu ba, sai gani a cikin Fillin nan, hantar su sai ta fashe" ta karasge tana me hararar Rafeeq, shiko Murtuk ya dauke annurin fuskar shi, Nene ta cigaba da Surutan ta karshe ta Ma Maauranta Addua da fatan Zama lafiya, nan da nan hall ya kachame da tafi, da yawa Nene ta burgesu ta basu daria. Dj ya sa mata wak'a, tace "kai ni rabani da wannan wakar kafiran" Surajo kada min molimoli, aiko kamar jira surajo mai asharalle yake, suka fara kidi, Nan Nene ta fara taka rawar Moli Moli, nan da nan wuri ya kachame da tafi, Abii dai dafe kanshi yayi yana tunanin yaushe Nene zata bar abubuwan ta. Nene ta burge kowa, wani Abokin Daddy yace da Daddy i like this woman, this is what we call Entertainment" don shi a ganinshi Nene yar wasan kwaikwayo ce aka gayyato.
A tare suka Yanka Hadadden Cake din da Ummu Sudais ta Musu, cikin kunya Seebi ta sa mai a baki, shima ya guntula ya sa ma ta, nan aka hau tafi.
Dance! Dance! Dance, na Tsakiyar hall ta kacame da rawa, Yan Asharalle suyi, Dj yayi, dukkansu suna ta nuja tasu basirar, Rawa ko Nene kamar ta karya k'ugiu, lik'e kam anyi, an Watsar da kudi, (nima biebeen ku da na ga haka sai na fara rawa ina kaiwa k'asa kasa ina tsince yan dubu dubu dinnan, ban ankara ba naji Nene ta take min hannu).
Daga nan kuma aka hau Refreshment, wato cin Abincin dinner din, Babu ne kawai babu cikin kayan Abincin. Nan akayi serving kowa, Kowa ya ci ya sha. Nene tace tabb"Amma Dunkum yaso in tafka asara, da bani zaayi wannan shagalin, toh Allah ya tsare ni dai daga minahuncin shi, shege sai kyau kamar shi yayi kanshi" na kusa da ita suka tuntsire da daria, Abinci ake taci, Naga Yan Zauren Biebee Isa sai cin abinci suke, wasu har da kullewa a cikin tissue lols, Rafeeq kuwa wurin ya ishe shi, so yake kawai ya ganshi a gida, ya gaji da rawa ya gaji da hayaniyar gun. Fuska ya ma Uncle Zaid, Uncle Zaid ya bashi hakuri ta ido.
Haka taro ya tashi Lafiya, Komai yayi daidia, abun sai wanda ya gani, abun sai san barka. Sai fatan Allah ba Maauranta zaman lafiya.
Da Asuba Zaid da Rafeeq sun dade suna Magana, Sosai yake mai fada, da Nasiha, Rafeeq yayi Murmushi yace "Uncle Zee, you dont have to worry about anything, i love Baby so much, i wont hurt her, i assure you that" Zaid ya ja kunnen Rafeeq yace "In my presence her name Is Nasiba, idan a bayan idona call her anything in kaso ka kirata da Jaririya ba Baby ba" daria Rafeeq yayi yace "Are You Jealous?" Zaid ya tabe