Showing 3001 words to 6000 words out of 149166 words
hannu ya sa a aljihu ya zaro makulli ya bashi, yace " room 108, Allah huta gajia" ya maida duban sa ga abokinshi yace "Night Maalesh" ya juya ya bar Zaid da Maalesh a gurin. Zaid yayi murmushi ya tsaida shi ta hanyar kiran sunan shi "Rafeek Lema " Chak ya tsaya.
_Bibilicious biebee_
👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
Pg4⃣
Uncle Zaid ya tako har gaban shi ya, yace "kana da matsalan wani abu? Do u need anything?" girgiza kai rafeek yayi, yace No, nothing, Zaid yace "nawa aka kama min daki? Rafeek yace "na riga na bada" kayan abincin ka fada kudi? Rafeek yace "akwai saura" karatu fa? A takiace yace "Lafiya " Zaid yayi daria yace "baka tambayi Mami ba" Rafeek ya dago jajjayen idon sa ya kalli kawun shi, Zaid ya fara daria don ya san ya kure hakurin shi, tunda har ya sa shi magana haka, yace to "ka tafi ko?" kamar jira yake ya fara tafia part dinshi, Zaid ya juya gun maalesh, Mahmud ya abokin na ka? Maalesh yace "Uncle Zaid, akwai improvement, don yanzu yana zuwa lectures, daga chan muke wai yayi lectures 4-6", Zaid ya kalleshi yace "good, kai yaushe kake gama service din? Maalesh yace"karshen wata" Zaid yace yayi "kyau copper, ka kawo min CV dinka kafin na bar katsina" Maalesh yace nagode Uncle Zaid.
Kamar daga sama yaji muryan Rafeek nace wa "erhm, nace ba?" Zaid da Maalesh suka kallo shi, Zaid yace "naam, kace mene?" Rafeek ya danyi guntun tsaki yace " kace ma wannan yarinyar ta daina shiga harkata, ta daina kula ni" tsaf Zaid ya gane yarinyar da ya ke magana, amma sai yace "wace yarinya kenan?" Rafeek ya bata rai yace "Aneesa" Zaid ya dan murmusa, yace "haba Rafeek, ya zaayi ta daina kula ka? Ai ko ba komai zumunci ya hada ku, ba wani abu bane don ta kula ka, besides ai kanwar ka ce, duk da ba a saba ganin fuskar shi da murmushi ba, amma kallo daya zaka mishi yanzu kasan ranshi ya baci, ya daure fuskar nan tamau, zuciyar sa na tafarfa sa, da karfi yace " she's not my Sister, she's Nothing like my sister" Maalesh ya tsorata da yanayin abokin sa, don ya dade be ji ya daga murya haka ba, kuma uncle Zaid ya ke ma ihun nan? Kai Rafeek be cikin hayyacin sa"
Rafeek ya runtse ido gam, Zaid ko sai daga baya yayi da na sanin cewa Aneesa kanwar Rafeek ce, tunda ya ga haka, ya san ran shi ya baci, kwata kwata be son ganin tillon dan yayan shi a damuwa.Rafeek ya bude ido a hankali ya sauke su fes kan Zaid, dan gajeren tsaki yayi yace "I am sorry" Zaid yayi murmushi yace "je ka kwanta Rafeek" Maalesh kai ma ka wuce gida Allah ya bamu Alheri" ya fada motarsa, Maalesh ya shiga motarshi ya tada, a ka bar rafeek tsaye yana kallonsu, maigadi ya bude gate Maalesh ya fara fita, daidai Rafeek uncle Zaid ya tsaya, yayi winning glass ya miko mishi takarddun Kilishi guda 2, yace a hanyar K'ank'ara na siya " Rafeek ya amsa yayi murmushi da gefen bakin sa, Zaid yace "Baka tambayi Ayman ba" Rafeek ya dan gajeren murmushi, yace "she's fine, she is always" Zaid ya jinjina kai yace "Good night Son" Rafeek ya daga mai hannu ya wuce.
Nasiba, yau ba darasi ne zaki tashi ko sai kin makara? Nene, na gama makara wallahi, amm dai shiryawa nakeyi, na kusa gamawa, Nene tace" kin san nafi kowa son karatun nan, so nake naga kin zama dapta" Seebi tayi daria, tace"Nene Doctor ake cewa, kuma ai Nene ai ba karatun da nakeyi ba kenan" Nene tace "ke dalla rabani, duk daya ne, tunda ance zaki iya aikin asibiti da karatun,dama ni buri na in ga yar jikalle na aikin asibiti, idan naje ba ruwana da bin layi" Nasiba ta fito tana daria, tace "Oh Nene akwai abin daria, nikam bari in tafi don na san nayi latti." Nene tace "ga kalacin ki chan, yanzu na siyo miki kosai, ga koko na dama miki" tace Wallahi na tsaya kalaci latti zanyi, ushee na chan National ta na jirana, idan naje makaranta zan siya, Nene ba ta ji dadi ba, amma ba yanda zatayi, ta ciro #200 a hab'ar zaninta tace "gashi kin kara" Nasiba ta rungume kakarta, tace "nagode Nene sai nadawo" har waje ta rako Seebi ta na mata addua.
Ya shigo gidan Cikin shiga k'ananun kaya, yayi kyau matuka, a parlo ya zauna yana neman layin Rafeek, ringing na 3 ya dauka "Barka da Safiyya" Zaid yace "Rafeek, ka tashi lafiya?" eh kawai yace, ka tafi school din ne? Rafeek yace "Eh, ina da lectures ne yanzu" Zaid yaji dadi sosai, yace "ni gani nan zan wuce Abuja, sai na dawo kaduna, ko na biyo ta makarantar muyi bankwana?, Rafeek ya girgiza kai yace ba sai kazo ba, Allah ya tsare hanya, ina gaida Ayman dina" Zaid yace "Ayman dinka zataji, amma ita kadai? Rafeek yayi saurin cewa "Safe journey" tare da latse wayan.
Aneesa ce ta saukko taga Uncle Zaid zaune, bude murya tayi tace "Aunty Meema, ga Uncle Zaid" ta karasa gunshi "good Morning Uncle Zaid, Zaid yayi dan murmushi yace "Aneesa kin tashi lafia? Lafiya lao Uncle Zaid ba dai yau zaka tafi ba? Yace yanzu kuwa "yaya ya tashi ko?" Eh ya tashi, Uncle Zaid, ina da matsala" Ya dan kallota na me fa?, ta gyara Zama "Uncle Zaid, Yaya Rafeek ne, ba ya son in rabe shi, kullum da ya gannin kamar ya ga mutuwar shi, rannan har mari na yayi don na je dakin shi" ta karashe maganar ta tana kwalla, Zaid ya sauke numfashi, shi ma besan ta inda zai bullo ma lamarin Rafeek ba, kullum sai fadin rai, ya kasa manta abunda ya faru a baya, ya kasa cigaba da rayuwar sa kamar yanda wasu ke cigaba da rayuwar su idan wata k'addara ta fado musu. Ya daure yace " kiyi hakuri Anee, kinsan halin Rafeek, Miskili ne, ki daina shige mishi, kar wata rana ya illata ki, ki yi hakuri, ki taya shi da addua Allah ya shirya shi, da ina da ikon chanza shi da na chanza shi, amma Addua kadai yake bukata. Da sauri Aneesa tace Uncle Zaid wallahi zan iya chanza, ina son shi, zan iya zama da shi ta ko wanne hali, ku aura mishi ni, ni ce ALHERINSA.
_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
Pg5⃣
Zaid ya yi mamakin maganar Aneesa, banda yarinta ya za'ayi tace a aura mata Rafeek? Uncle Zaid baka ce komai ba, Aneesa ta katse mishi tunanin.
Yak'e yayi, yace "banda abunki Aneesa, wa zai ma Rafeek aure yanzu? Rafeek fa yaro ne, he is just 24" tace "Uncle zai- ya katseta ta hanyar daga mata hannu yace "please anee, no one is getting Rafeek married now" tayi raurau da fuska, tace"Wallahi ina son Rafeek, zan kuma jira shi, zan jure duk wani wulakancin da zai min.
"Tunda maganan Soyayya akeyi, bari kuji labarin rai na"
Meema ce ke fadin haka a yayin da ta ke sauko wa daga bene har ta karaso gaban su, sanye take da shara-sharar rigar baccin da ko guiwar ta bata rufe ba, Zaid ya dauke duban sa daa kanta, masauki tayi kan kujerar da yake zaune, fari take mai da ido tace "Uncle Zee, kasan irin son da nake maka? Ni bansan yanda akayi na fara sonka ba, kuma na sha mafarkin mun yi aure mun haifi kannen Ayman, Uncle Zaid ka aureni please.
"Ya Salam!" Zaid ya furta a hankali tare da dafe kanshi, wasu irin mata ne wannan? Masu tallan kan su, Ya cije ya kalli meema da ke ta wurwulla idanuwa don ta burgeshi, wani takaici ya tokare mai wuya, ya san Meema na son shi, tun kafin yayi aure, amma ba zai iya auren ta a haka ba, sam rayuwar su basuyi kama ba.
Alhaji Habib Lema da matarshi Hajiya Saude suka sauko kasa, da sauri Zaid ya tashi ya nufi gun yayan shi, yace "Barka da safiyya" Yayan yace "lafiya lao, Engr. Har anyi harramar tafiya?" Zaid yace InshaAllah "ya juya ya kalli matar yayan sa yace "Madam an tashi lafia?" fuska sake tace "lafiya lau Uncle" yayan yace "Zaid muje daga waje akwai wata maganar da nake so muyi, yace "toh yaya" Zaid ya musu Sallama da ga chan zai wuce, ba haka hajia saude ta so ba, ta so taji maganar da Alhaji zai gaya ma Zaid, ta so taji me zasu tautauna a kai.
Meema ta kalli yayar ta rai a bace tace na "Nagaji Sauda, ya za'ayi na dinga mishi tallan kai na ya na ba dani? Nifa na fi karfin wulakanci da namiji" H.saude ta murmusa, tacd dadi na dake Maryam gajin hakuri, ai komai sai an bi a sannu a ke dacewa ko? Kiyi laakari da yanda ni na samu Alhaji, ki kara hakuri komai ya kusa zuwa karshe" Aneesa tace "Mummy ni kum-- Hajia saude tace " shhh, Matsalarki Rafeek ko? Nima shine kadai matsala ta, bana jin Zaid, Rafeek nakeji, amma kar ya damu idan ya sn wata be san wata ba, ku bar komai a hannuna kunji?" Meema da Aneesa suka chafe hannu cikin murna suna fadin "sai ke mata daya rak a gidan Habib Lema" ita ko dadi wannan kirarin ya mata dadi ta haye sama.
A hankali yake tuk'insa, yana tunanin maganar da yayan sa ya gama mishi yanzu, a kan karatun Rafeek ne, inda yayan ke cewa "kaga Zaid, ni sai nayi wata da watanni ban daura Rafeek a idona ba, be yarda mu hada hanya, anya yaron nan be shaye shaye? Da sauri Zaid ya girgiza kanshi, yace " wallahi Rafeek be shan ko Sigari"
Yayan yace "Zaid na kasa yarda da hakan shekara ta uku kenan Rafeek na Spill over a makaranta, last upper year spill over from nowhere, be gyara ta ba, last year ma be gyara ba, ina tsoron wannan shekarar abun da ya faru ya sake faruwa don da alamun abokan banxa yake bi suke bashi wasu k'wayoyin da ke taba mai kwakwalwa, shisa ya kasa kwantar da hankalinshi yayi karatu" da sauri Zaid ya katse shi, ta hanyar cewa "aa yaya, ka fadi Alkhairi ko kayi shiru, kowa ya san Rafeek mai k'okari ne da hazaka, kar ka manta tunda Rafeek ya shiga UMYU shine over roll dinsu, 4+pointer, komai ya dagule ne sakamakkon k'addara da ta riga fata, amma InshaAllah komai zai daidaita. Alh. Habib ya jinjina kai yace "haka ne Allah shi kyauta, amma kasan har yanzu ba ya min magana? Zaid ya tashi yana daria yace bari na tafi "Yaya sai na dawo karshen Sati"
Alh. Habib yayi daria "wato ba ka son laifin shi ko?" Toh Allah ya kiyyaye.
Wata tsohuwa ya gani da ga gefe ta na sa mai hannu, yayi mamaki don ba a titi yake ba, har yanzu be fita daga cikin Unguwar ba, ya dan gangara ya sauke gilashin motar shi, yace Lafiya Iya? Tsohuwar tace Yauwa bawon Allah taimaka ka zo ka ka duba min layin wutan chan, k'auri yake yi,nafi minti 30 tsaye ko zan ga wani namijin da zai duba mun, amma tun dazun shiru, Zaid yayi shiru ya na karantar tsohuwar nan.
Can ya fito ya kulle kofar yace muje nagani, tsohuwar ta ja shi har cikin madaidaicin gidanta, daidai gurin, fuse din har ya fara spark , "SubhanAllah, kinga ya fara kamu da wuta" Zaid ya ga in dai ya bata wani lokaci wires din wurin za su fara ci, kuma baa san inda wutan zai tsaya ba, yayi jihadin sa hannun shi ya zaro fuse din ya cillar.
Tsohuwar ta sa ihun murna har da tafin ta, tace "sannu dan Albarka, Allah ya sa ba abunda ya samu hannuka" Zaid ya dago hannun shi, Cikin ikon Allah ba abunda ya samu hannun.
Zaid yace "ina zuwa, ya fita" tsohuwar ta bishi da ido, motarsa ya shige, bayan mintuna kadan sai gashi da mai gyaran wuta, Zaid ya kalli tsohuwar yace " Toh Iya, ga mai gyara nan, ni zan tafi" baki bude tsohuwar nan take kallon shi, bawan Allah tsaya, Zaid ya tsaya, tace Nagode kaji? Allah ya biyaka, Zaid yayi murmushi. "Amin Nagode Iyah, ni na wuce" tace "donAllah ka tsaya, na kwadanta maka zogale" yace "wallahi, sauri nake, kaduna zan tafi yanzu" tace toh dan jirani da sauri ta shige kitchen, sai ga ta da bakar leda ta mik'a mai, tace gashi ya amsa yana mamakin me ke ciki, tace kayan miya ne irin su daddawa, kuka, kanwa da su kanumfari" ya ce toh ni iyah-- ta katse shi ta hanyar cewa a kai wa Uwargida, idan babu kuma akai ma mahaifiya, Zaid ya sake wani murmushi, farat daya yaji son tsohuwar nan har ranshi, yace "toh nagode Iya" tace bakomai har ya juya tace "nidai, in kace min iyah, ji na ke kamar ka mayar dani wata tsohuwa, zaid yayi daria sosai, yace ai tsohuwar ce" tace "kai bawan Allah, ban wani tsufa ba" yace toh shekarun ki nawa? Tace goma-goma guda shiddada hudu Zaid(10*6+4) ya bude baki yace lalala 64 fa kenan? eh lallai baki tsufa ba" a tare sukayi daria. Yace "toh me zan dinga kiran ki dashi ? Tace "yanda jikoki na ke ce min, NENE"
_Bibilicious biebee_
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS
ASSOCIATION(NWA)
Pg6⃣
Zaid ya murmusa yace "toh nene" tace "kai ya sunan ka"? "Sunana Zaid" tace "Zaidu Bawan Allah" yayu dariya yace "toh Nene bari dai in wuce kar nayi rana". tace "Gaskia ne, ince kaduna zaka ko? Ko ka san d'a na? Hafizu Mamman? Fari dan fulani" Daria sosai Zaid yayi yace "Nene kaduna babban gari ne, ba yanda zaa yi na san shi" tace "Allah ka bincika, duk kaduna shi kadai ne" Zaid da ya k'osa ya tafi yace "Toh Nene", Kudi ya ciro ya ba mai gyara suka kara Sallama.
Har bakin motar shi ta rakashi, tana daga mai hannu tana mai addu'oin kariya. Ya tada motarshi yayi ribos,ya dau hanyar barin unguwar, Nene ba ta koma ciki ba har sai da ya kure ganinta kafin ta koma cikin gida, bini-bini sai ta saki murmushi tana tunanin Zaidu bawan Allah.
Asalin Sunan Nene :Amina amma an fi saninta da Aminene, 'ya'yanta 6, dattijuwa ce me kimanin shekaru 65, Mijinta ya rasu shekaru 20 da suka wuce ya barta da 'ya'ya 5, a halin yanzu 2 suke da rai 3 sun rasu. Cikin wanda suke da rai akwai Fatiti, ita ce diyar Nene ta biyu, tana aure a Jihar Jigawa 'ya'yanta 3, Amina,Umar da Muhammad.
Muhammad Bishir Sunan autan Nene, yana zaune da matarsa da 'ya'yansa biyu a Malali cikin jihar Kaduna. Nasiba ce ta farko sai kaninta Anan. Muhammad Yayi aiki a National Trust fund kafin a kulle kamfanin (Company). A hanlin yanzu ba ya aiki amma yana karban pension duk wata.
Nasiba yar kimanin shekaru Sha tara a duniya(19), ba za a sa Nasiba a jerin farare ba, haka kuma ba za a sata a jerin bak'ake ba, wankar tarwada ce, me dara daran idanuwa, idan tayi murmushi kumatun ta sukan lotsa, bata fiye tsayi ba, kuma tana da dan jiki daidai ita, a takaice Nasiba ta kai macen da ake kira da masu kyau.
Tayi karatun ta na Nursery, primary harda Secondary a Kaduna Capital School(KC). Bayan ta gama ne baban ta ya siya mata JAMB, da doki tace Abba ai Katsina zan sa ko? Ya harare ta cikin wasa yace "kina nan, don ko Rigachikun ba za ki wuce ba" ta turo baki tare da bubbuga kafa tace nidai wallahi Abba bana son KASU" tun nursery dina a nan nayi Abba, Shekaru 15 ina karatu a kd, ai change of environment na da dadi, ka ga sai in kular maka da Mamanka tunda tak'i yarda ta dawo gidan nan da zama"
Umma tace "Eh kinyi gaskiya Nasiba, Nene na bukatar wani kusa da ita, tunda anyi anyi ta dawo kaduna ta ki yarda, ya kama ta kije chan kiyi karatun, Mutum ai rahama ne" Abba ya jinjina kai, yace "ko don Nene zan barki kije Katsina karatu" tayi ihun murna tace yauwa "Abban mu"
Anan yace Adda Seebi yanzu kina murna zaki tafi ki barni ko? Sai ya fashe da kuka, da saurin ta rungume tillon kaninta ita ma kukan take yi tace yi shiru Anan, ai zan dingw dawowa hutu kaji?kuma ga Abban mu ga Ummin mu ai ka ga ba kai kadai bane ko? Da kalamai masu dadi ta lallashe shi har yayi bacci, ta dauki form din ta fita don zuwa dakin ta, ta cika 1st&2nd Choice UMYUK, Microbiology course don school din basu fara Medicine ba.
Abba ya kalli matarsa yace Ummin yara, gidan nan na layout(Gidan gadon shi), ina ganin zan tada mutanen ciki Nene ta koma can, Gidan Kofa Uku ya tsufa,nan aka haifi marigayi Yaya Shehu fa, Umma ta kada kai tace lallai ya tsufa kam, kinga kuwa sai ta koma gidana na layout din, Ummi tace "toh Allah ya sa ta yarda, don yanda take son Unguwar nan, raba ta dashi sai Allah, saboda mutane da Abokan arzikkin ta ya sa ta hana a dauko mata wacce zasu dinga zama tare saboda kadaici," Abba yace ai Nene in ta kafe ba me tankwara ta, amma bakomi na san yanda zan bullo wa lamarin" Ummi tace Gidan fa? Yace "sai in gyara a zuba yan haya ciki"
Cikin Ikon Allah, Watannin da basu rufe 10 ba, Nasiba ta samu Admission a Jami'ar Umaru Musa, course din da ta zaba suka bata, Gaba ki dayan su suka zo Katsina don rako Seebi, don daga Registeration ba za ta dawo Kaduna ba.
Nene tayi murnan dawowan Seebi gunta, don ta na son jikokin ta