Showing 105001 words to 108000 words out of 149166 words

Chapter 36 - Ke alkhairi ce COMPLETE HAUSA NOVEL

BIEBIE   

22 Oct 2024

25761

key ya fita daga gidan, Nene ta bishi da ido tace "toufa Allah ya sa lafiya"
******
Zamewa tayi ta zauna a k'asa tana maida numfashi, tunda uwata ta haifeta, bata taba ganin abu makamancin na yau ba, ta sha jin irin labaran nan a littatafai, amam bata yi zaton haka abun yake ba, Mallam yace "Sannu Nasiba, kinyi k'ok'ari, ina mai murnan sanar dake cewa Asirin da akayi don Alhaji ya kare, Zuri'ar Lema sun yi dacen samunki a rayuwansu, kina musu wannan hidimar ba tare da sanin su ba,KE ALHERI CE NASIBA, Nasiba ta share hawayen da ke gangarowa ta k'ak'alo Murmushi tace "Nagode Mallam, Allah ya saka maka da Mafificin Alherinsa, ya raya zuri'ah" yayi murmushi ya amsa da Amin, Sosai yaji dadin adduointa, yace "tashi ki tafi gida" sukayi sallama ta wuto gida.
********
Guiwarta ta shiga Sosawa, don ta soma jin k'aikayi a wurin, da k'aikayin yayi yawa ta daga doguwar rigarta don ganin me yasameta a guiwan, wani k'urji ta gani a gurin kamar fitsarin gwauro, tayi tsaki ta shiga lailaya gurin don k'aikayin ya soma yawa, Meema tace "Sis lafiya kuwa? Ya naga kina soshe soshe? Tace "ke wani dan iskan kurji ya fito min a guiwa, sai dan banzan k'aikayi" Eyyer sannu Mom, barin dauko miki piriton kisha, zai bar kaikaryin" cewar Aneesa tare ea mikewa.
*******
"Habibullah Lafiya? Yau kaine a gidan nan? Lafiya ma dai? Ya naganka haka da Farar Saffiyar nan?" baki na rawa yace "Mama ina Aishatu?" Mama ta murtuk'e fuska tace wata Aishatun?" cikin rawar jiki Alh Habib yace "Mama ku gafarceni, nasan nayi laifi gagarumi, amma ki taimakeni ki gaya min inda take, wallahi ina da bukkatar ganinta yanzu" Mama ta kalleshi galala, tacs "Habibu kenan, tin randa ka saki Aishatu shekara da watanni kenan baka ta6a zuwa gun mu gaishe mu ba, baka zo ka ga lafiyar mu ba, balle kace tana ina, ka tambayi lafiarta, ko makamancin haka, ai inace Habibu ko da baka auri Aisha ba mu Iyaye ne a gunka, amma da yake ba mu isa da kai ba, dukda Rabon da Allah ya baku na 'ya'ya, bamu ci albarkacin su ba, so hakan ma yanzu ba ruwanka da mu, ba kai kayi aure ba? Ba ka dauke mu komai ba, sai ka je chan, ba kai ba Aishatu" Hawayen da yake 6oyo ne suka shiga reto a fuskar shi, Muryan Baba Tijjani yaji inda yake cewa "Ke Lami, ya da daga murya da Sasafen nan?" ganin Alhaji Habib durkushe gaban Maman Mami ya sa shi mamaki, "Habibullah a gidan nan?" Yauwa Alhaji ka ganshi nan, don ya raina mu, ya raina mana azziki sai yau ya zo neman Aishatu, dube shi nan"nan ta cigaba da zazzaga Masifa, ta inda take shiga ba ta nan ta ke fita ba, da Baba Tj ya ga abun nata yayi yawa ya kalli Daddy yace "yi tafianka Habib, zan neme ka" kamar wani k'aramin yaro ya rausayar da kai Alamun a tausaya mishi, Baba Tj yace "kar ka damu, Zan kiraka" jiki ba k'wari ya fice sum sum. Nan Baba TJ ya tasa Mama gaba yana mata Nasiha, bw kamata tayi haka ba, godia ya kamata tayi da ga maido Habib kan turbar gaskia, shi dama ya san ba yin shi bane, nan ya cigaba da mata Nasiha.
*********
Hawayen kunci yake tayi, Ji yayi ba zai iya wani kwanan ba tare da ya Dora Aishatu a kanshi ba yau duk inda take sai ya ganota, he'll be with her again ya fada toilet dom yin wanka, dole zaije duk wani Gidan da ya san Aisha na zuwa nemanta.
Nasiba ta fito daga wanka ta na shafa mai Nene ta shigo dakin, tace ke kuma daga ziddo shara kikayi wani gurin, ina kikaje ne?" Seebi tace "ina fa? Ina nan mana" Nene ta harareta tace to banfi minti 10 da barin dakin nan ba, na ga bakya nan, na fita har k'asa nemanki, ban ganki ba, don ki renan wayau zakice kina nan" Seebi dai tayi shiru ta cigaba da shafa man ta, don tasan ta k'ara magana tsafe Nene zata dago ta. Nene ta fice daga dakin ta sauk'a k'asa gun Baba maigadi, don taya shi zama, bayan 'yar mahawarar su, ya kece mata ya lura Alhaji na cikin Matsala, dazun ya fita da damuwa, yanzu kuma ina ganin damuwar shi ta k'aru, bansan me ya auku ba ,Nene tayj dan jim ta mik'e tace ina zuwa.
*****
Hannu bibbiyu ta iske shi yayi tagumi tace "Alhaji Lafiya? Ya na ganka haka?" kamar jira yakeyi, ya fashe da kuka, yace "Nene nayi kuskure, nayi kuskure babba, wallahi bansan ya akayi na saketa ba, bansan ya akayi ban nemeta duk tsawon lokacin nan ba, bansan ya akayi na mance duk wani abu da ya dangance ta ba, bansan ya akayi na daina tunanin ta ba, gashi ban san inda take ba yanzu, bansan inda zan shiga nemanta ba, bansan ta inda zna fara ba" Nene ta tausaya mai sosai, ta shiga lallashin shi, tana bashi baki, chan kuma ta danyi jim sai tace "wai wa kake nufi? Wai Mamin su Dunkum? Jin yanda take magana ya sashi daga kai, yace "eh ita" ta shiga tafa hanayenta tace "toh share hawayenka, kakarka ta yanke sak'a, na san inda take" zumbur ya tashi baki na rawa yana mamakin ina Nene ta san Aishatun shi? Ya kawar da mamakin shi ya shiga tamabyar ta inda take, Nene tace "ai ni sai dai in mutum be gaya min matsalar shi ba, da ikon Allah zan magance mai" ba wannan yake son ji ba, yace donAllah ki gaya min, tana ina? Wani hali take? tace "ina zuwa" ta fita daga Parlorn sai gata ta dawo da Seebi, Seebi na tambayarta lafiya? tace "Ke ko ba Mamin dunkum kike bani a waya mu gaisa ba?" Seebi ta kalli Nene ta juya ta kslli Alh Habib da ya zura mata ido yana neman jin Amsarta, ta gyada kai tace "itace" Nan ya rude, "tana ina? Ya take? Is she alright? Seebi my child, tell me where is she now? Where can i find her please?" Nasiba tace "Daddy calm down, shes fine, tana Kaduna" "Kaduna? Gun wa? DanAllah kice min batayi aure ba" Nasiba tace "batayi Aure ba, she's been waiting for you all this while, tana nan tana jiranka Daddy" Wani Murmushi ya sake yace "I am coming for her, tell me ina kika santa?" tace "Mak'otan mu ne a Kaduna" Allahu Akbar, i shall go to Kaduna now" har ya juya cikin daki ya juyo ya kalli Seebi, yace "KE ALHERI CE a gareni Seebi thank you" Nene tace "Kadunan zakaje? Aikuwa dama ina so inje inga Mahammadu, ko zan biyoka?" cikin Nishadi yace "me zai hana, ai kawai kije ki shirya Nenenmu", "wani shiri zanyi? ai a shirye nake" Seebi tayi raurau kamar zatayi kuka, tace "Nene na zaki barni a nan ne?" Nene ta zaro ido tace "Rufa min asiri in mutu maza su rufeni, ya zanyi gigin barinki gurin dangin matsafa? Ai kafata kafarki, muje ki shirya" Seebi ta zaro ido tace bangane dangin matsafa ba, Nene ta tabe baki, tace "Zan shak'a miki muje mu shirya".
Parlorn sama ya iske su, yace "kun shirya? tace "ai sai tafia kawai" yace "to bismillah" yace "bari in shiga inyi ma Saude Sallama in gaya mata na tafi Kaduna" da sauri Nene tace "ai ta fita yanzu tace sauri takeyi shiyasa ba zata tsaya kuyi bankwana ba, amma tana mana Allah ya tsare" Baki Sake Seebi ta tsaya kallon Nene da take ta karanto k'arya, Sauden da ke cikin daki ita da Aneesa sun koma Baccin safe, Meema kadai ce ta fita, ran Alhajk ya 6aci, baya son fitan da Saude ke yawan yi, tsaki yayi yace "mu tafi" Nene kuwa Allah allah takeyi su tafi don bata san Alhaji ya gana da Saude, gudun kar a samu Matsala balle idan ta san gurin tsohuwar matarshi zaije. Nan suka fito a tare suka shiga bayan Sienna, Alhaji ya kwalawa direban shi kira, Baba maigadi ya wangale Gate, Nene ta wangale baki tana ma baba Maigadi Byebye. Waya ga kauyus a Sienna.

KADUNA

(Toh kuyi hakuri da wannan, Lokacin wahalan Wuta yazo, muna Samun matsalan wuta so ina rashin Charge, zan cigaba daga nan InshaAllah)

👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

Pg5⃣5⃣

Nene tace "Alhaji Lafia? wacece Aishatu?" Alhaji Habib ya k'ura wa Nene ido kamar me son tunano wani abu, cikin sanyi yace "Ina zuwa Nene" ya zura takalman shi, ya wawuro key ya fita daga gidan, Nene ta bishi da ido tace "toufa Allah ya sa lafiya"

Rafeeq ya iso gidan Uncle Zaid da misalin k'arfr 9:30 na safe, dauke yake da breakfast dinshi da Mami ta hada musu, shi yace zai kawo ma Zaid tunda ba zai samu zuwa yin break din ba a gidan Mami wai kanshi na ciwo. Rafeeq da mamaki ya ga Zaid garas yana kallon TV ya dai daure yace"Good Morning uncle Zaid" ba tare da ya kalle shi ba yace " Ka tashi lafiya? Ina Mahmud?" "Lesh ya tafi gaida wani Uncle din Mom a Unguwar Dosa" Zaid yace "Serve me" Rafeeq ya kalli Uncle Zaid kamar me son gano wani abu tattare dashi amma ya kasa gane komi, ya shiga zuba mai Tea a cup, ya zuba mai Dankali da wainar k'wai ya tura mai kusa dashi, Zaid ya dan gyara zama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login