Showing 147001 words to 149166 words out of 149166 words
Uncle Zaid, Rafeeq ya kanga mai fuskar Baby, Zaid da Aunty Zee sukace "MashaAllah, Rafeeq ka sa na tuna randa aka haifeka, you look just like him" Feeq yayi Murmushi yace "Zaid Rafeeq lema, open your eyes and see your Grandpa, Your Dad's Hero, your Dad's Saviour, Your Dad's Favourite, Your Dad's Best" Farinciki ya maimaye Uncle Zaid, bakinshi ya k'i rufuwa, don dai ya tabbatar da abun da kunnenshi yaji sai yace "What did you just called him?" Rafeeq yayi Murmushi yace "Zaid Rafeeq Lema" ya kalli Aunty Zee yace "Ga Miji nayi miki" tayi daria tace "Aikam nagode dama wannan ya tsufa ga sabon Jini" sukayi daria Hafiz ya lek'o yana ta cewa "Baby baby" duk sukayi daria. Nene tace "Zaidu Bawan Allah yaushe zaku zo?kace da ta haihu xaku zo?" yace "Eh Nene, zamuzo ranar Laraba dukkanmu Har su Yaya da Abbii, Mahmud kuma sai Jumaa shi da Iyalinshi InshaAllah" Rafeeq yace "Meye Laraba?" duk yanda ta so tayi shiru ta kasa, tace "Kai Rafeeq, ka fita idona, Kar kaga kwana biyu na sa maka ido ka dinga min wasu kamkamba da iyayi, ba fa tsoronka nike ba, don Tsiya Laraban ne baka sani ba? To bature yaci buraubashi" daria sukeyi sosai, yace "dagaske bansan meye Laraba ba" ganin iyakar gaskiar shi Yake fadi, Seebi tace "Wednessday ne Laraba baby" yace "yauwa Baby you the best, Uncle Zaid bari na baka short story, nan ya basu labarin yanda sukayi da Nene a Airport aiko suka fashe da daria, Nene ta ja kunnenshi ya tashi da sauri ta bi Rafeeq da throw pillow suna Zagaye parlorn tace " ni za kayi wa Bariki da turanci? Ashe ba saida ni kayi ba kasa na daga hankali na? Ya Rungumeta yace "ya zanyi in saida uwargida na, kinsan ina sonki Sosai" itama Rungume shi tayi tace "I lobiyu too" duk sukayi daria, tace "Zaidu BawanAllah idan ka gama murnan Takwaran da aka ma, kaje ka biya min Makarantar Yaki da Jahilci, da na dawo Turanci zan fara zuwa in koya, saboda kar Baban Zaid ya sake min irin haka" gabaki daya suka sa Daria.
5 Years
Ayman yar kimanin Shekara 10 zaune tana kallon CN ta k'ura volume, Shafeeq da Shafee'ah kuma da Aishatu(diyar Aneesa),suna game Hide and Seek, duk sunyi kachakacha da Parlorn, nan pillow nan remote nan ball nan teddy, sun cika gidan da Hayaniya Zaid na gefe zaune Kawai, Ihun su ya fara isan Rafeeq dake daki, tsaki yayi ya daura Pillow kanshi, ihun Yan biyu ya cika ma Rafeeq kunne, kamar zaiyi Kuka ya zaro Wayan shi ya latso Maalesh, Ringing daya Maalesh ya dauka Rafeeq ya balbaleshi Da fada "Lesh wani irin abu ne haka?" Maalesh yace "Guy ya akayi ne?" cikin Masifa yace "Some noisy kids are Disturbing my peace, for crying out loud Today is my only Holiday in ban huta yau ba sai yaushe? Gashi Baby tana gidan ka in sun hadu da wannan Usheey din kamar kar su rabu" Maalesh Yayi Daria yace "Yanzu ya kake so ayi Oga? Ni kazo ka kwashesu duka ku tafi Gidan ka" Tabdi so kake su tsorata min Jaririyata yar kwana 2? Ka bar su nan, ai hutu suka zo ma" Dif Maalesh ya katse wayar, Rafeeq yayi tsaki ya lalubo wayar Uncle Zaid, "Hello Son yadai? Uncle Zee Yaushe zaka koma Katsina kuma?" "Katsina dai? Jiya fa nadawo kasani, what is it? Kamar zaiyi kuka yace " Uncle Zee yaran nan suna son tarwatsa min kai, suna da hayaniya, tun dazun nake so inyi bacci sunki bari na, and I'm very tired, nidai Katsina zan maidasu Gobe, ba zan iya ba" Zaid yace "Haba Son, Jiya fa suka zo, kuma Seebi ta matsa su zo muku hutu, da k'yar Mamin su ta bari na taho dasu, amma kwana daya kachal sai kace zaka maida su haba Yarona" kamar zaiyi kuka Feeq yace "Nidai i want to rest, ba kuma zasuyi shiru ba" To bari in sa Driver yazo ya daukesu akai Su Bambinos, kafin Zee ta dawo daga gidan Mahmud" Rafeeq bece komai ba Ya kashe wayar. Bayan 'Yan mintoci sai ga Sam yayi knocking, Amina mai aiki ta bude k'ofar, yace "Oga yace yazo ya tafi da yara" Amina tace oya ku shirya Uncle Zaid ya aiko a tafi dasu, da murna su ka tashi za suje Bambinos, "Adda Ayman ki bari in zauna gaba" cewar Shafeeq, Ayman ta harareshi tace "Go back my Friend" Lil Zaid yace"Aunty Angel in zauna a gaba? tace "Eh zo ka zauna My boy" Murmushi Kawai yayi ya zauna, "Aunty Angel yaushe Ammi zata dawo? Ta shafa kanshi tace "taje Gidan Aunty Mimi, Aunty Mimi ta haihu, ba zata dade ba kaji Yarona?" kai kawai ya gyada don shima yana jin wuyar Magana, haka suka tafi.
Da sauri ta shigo Sallama tana kwala mai kira, "Baby" dakinshi ta fada ta ganshi kwance yayi rub da ciki zuwa tayi ta hau kan bayanshi, "ohhh Baby lemme sleep" tsalle ta fara yi kanshi har sai da ya jiyo ya kalleta ta dawo kan cinyarshi, ta rataye Hannayenta a wuyansa, tace "Baby Guess What?" ya kalleta cike da shauki yace "Sister Nasiba Lema, wont you let me sleep? Kafada ta daga alamun Aa, tace "ni sai kayi guessing" yace "Baby save me the Stress tell me" murna Fal cikinta tace "Yaya Maalesh ne yace ranar suna zai min takwara, zai sa ma Babynshi suna Naseeba" Wooooow cewar Rafeeq, Yanzu mu kayi magana fa, be ce min komai ba" Wayar shi ya jawo ya sake kiran Maalesh, Maalesh na dauka yace "What?" Rafeeq na daria yace "Ashe ni zaa ma takwara, baka gaya min ba" ta yaya zan gaya ma? Ka kirani dazun kana min fada" Seebi tace "Aini Ya Maalesh ka gama min Komai Allah ya raya Baby Nasiba" yace Amin Seebi, and ki bincika sosai Feeq ya koran miki Yan hutu su duka" Feeq yayi saurin latse wayar, Seebi ta kalleshi kallon tuhuma tace "Baby ina Yarana?" ya dan sosa k'eya yace "Baby they were disturbing and i wanted to sleep" ta harareshi sai kayi me? "Uncle Zaid ya aiko a dauke su" Aunty Zee fa na gidan Ya Maalesh fa ta na duba Mimi, ni gaskia a dawo min da su, Amanar Mami ce, kuma nasan Angel na recording duk abunda kake musu, Mami na zuwa suna zasu kai k'ararka, ni ka dawo min dasu, ta fara shagwaba" Kallonta kawai yakeyi cike da So ds k'auna, shekaru sun shude amma ba abunda ya chanza na daga Kyaunta do koman ta, kaganta ba za ka taba cewa ta haifi Zaid dan Shekaru 5 ba, mayatacen kallon da Feeq ke binta dashi ya sata hararshi tace "What?" kashe ido yayi yace "Baby lets make a Baby" ta sake hararar shi tace "Bangane ba" idonshi ya k'ankata yace "I mean lets Make Mahmud Maalesh too" baki ta murguda tace "ban fa gane ba" Rungumota yayi sosia yace yanzu zaki gane, salon da ya fara mata yasata tuntsirewa da daria.
Daria Zaid keyi kamar cikinshi zai fashe, Seebi na tayashi, Rafeeq na cewa "Baby ku dagani nagaji" Zaid yayi daria yace "Papa is a Superman he cant get tired right Ammi? Seebi tayi daria tace "Right Son, Your Pa is a Superman" Feeq na nishin wahala yace "Yes i am a Superman" Seebi ta tuntsire da daria, ta san Feeq da rashin Juriya, Sauka tayi tace "Son Sauko is time to Sleep" ba gardama ya daga Rafeeq ya ma Seebi kiss a kumatu yace "Sai da Safe Ammi nah" Allah ya tashe mu lafiya, kar ka manta Adduar bacci" kai ya daga mata, yaje gun Feeq, Feeq ya daga shi Sama ya kai shi daki ya sa shi fitsari ya kwantar dashi kan Gado, tare sukayi Addua, Feeq ya mai Goodnight kiss ya kashe mai wuta ya fito.
Isketa ta yayi a Parlor, yace "Sister Nasiba Lema" ta kalleshi tace "Baby na ina sonka sosai" nima ina sonki sosai Baby na" Kinsan Nextweek ne Opening din *LEMA SPECIALIST HOSPITAL* Akwai wasu Dr's yan India da Uncle Zee ya ma magana, zasu zo and zasu dinga Partime anan, Asibiti ai ya gama haduwa, ga kuma Dr Zee Lema, ga Kuma Sister Nasiba Lema" Seebi ta tafa hanayenta cikin jin Murna, tace "ka san kafi kowa iya kiran Sister Nasiba? Thank you Baby for helping me Acheive my Goal, i wouldnt be what i am today if it werent for you" "Shhhh Baby dont say Anything, i should be saying that, ba zan taba manta Role din da kikayi playing a Rayuwata ba, role din da kike kan Playing, Baby kin game min komai, you stayed with me and love me despite my flaws and imperfections, you were there with me through my tough times, you endured all my Negativity, above all you gave me the most priceless Jewel Zaid, Tell me what more can i Say Seebin Feeq? You are a Blessing, I love you So Much i cant live without You, and Hey, you gave my life a purpose, it was all about Eat, Pray, Sleep Repeat... And now It is about Seebi and Zaid, all about The Both of you, My Happiness". Rungume shi tayi ta bashi wani hot kiss, chabal ya dauketa kamar baby sukayi daki.
Gabaki dayansu a Tamfatsetsen Parlon Uncle Zaid, bayan su dawo daga Zagayen lungu da Sakon Sabon Asibitin, Dan guntun Walima sukayi isu isu, aka ma Yanuwa da suka riga mu Gidan Gaskia Addua, Dr Zainab da Nurse Nasiba suka yi Alkawari ba da guddumuwa iyakar K'arfinsu domin cigabar Asibitin. Aunty Anisa ba ma son Waina da tuwo" cewar Hafiz dan Uncle Zaid, Aneesa ta rungume shi tace "me kake so babana?" Nene tayi karaf tace "Ba sa son Tuwo sai Rice" Akayi daria Aneesa tace "Barin zubo muku kunji yarana" Ayman tace "Kunsan Nehneh ta fara jin Turanci? Nene tayi karaf tace "bazasu yarda ba Aymana sai sunji munyi, ki tambayeni yaya sunana?" duk suka Zuba musu Ido suka fito gaban Kowa, Ayman tace "What is your Name? Nene harda gyara murya aka mak'aleta tace "Ma Nem Aminene Mamman" Gabaki daya Parlorn Aka tuntsire da daria.
Mami da Alhaji Habib sukayi Hamdala da suga Family dinsu a haka, taji dadi tasam cewa Burin Rafee'ah ya gama cika, sai dai su mata Adduar Allah ya sa ta huta, Baby Zaid kwance jikin Uncle Zaid inda yake mai magana yace "Grandson kaje kaci Abunci da yanuwanka gasu chan" k'asa k'asa yake magana yace "Grandpa, i am not hungry" Zaid ya shafa kanshi yace "Are you sure Grandson?" "Yes Grandpa kasan Me Papa yace min about you? Uncle Zaid yace "tell me Grandson" yace "He Said You are the best There is, you are the Best There was, and The Best there will ever Be, He loves you so much" Zaid yaji wani Dadi ya rungume Takwaranshi yace "I love you and your Pa So much" Nene ta tabe baki tace maganar kenan, kai wannan Jikan naka Zaidu Bawan Allah be son mutane, be yarda da kowa da ga kai sai baban shi, kai ko Katsina sukazo ya dinga wani ja da baya baya, da yayi Gadon Miskilancin sai ya zarce shi ko cikin yara yanuwan shi baka ganinshi, sai shegen son jiki" Su Mami sukayi Daria, Little Zaid ya tabe baki ya kalli Uncle Zaid yace "She's Noisy" Nene tace "Me yace?" Rafeeq yayi karaf yace "Cewa yayi kina da Hayaniya" duk suka fashe da Daria.
Nima Biebee Isa Dariar nayi na fito nace bari na bar ku haka.......
TAMMAT BI HAMDULILAH
Alhamdulilah! Alhamdulilah!! Anan na kawo karshen wannan k'ageggen Labari na na KE ALHERI CE, Kuskuren da nayi a ciki Allah ka yafe min kuma ku yafe min dan Adam Ajizi ne, Allah ka bamu ma su son mu tsakani da Allah, Allah ka bamu 'yanuwa masu Zumunci kamar Uncle Zaid, wanda yake Fitila k'ona kanka ka haska wanda yake so, Allah ka bamu Ladar Zumunci. Allah ka kara mana son Yanuwan mu Ameen Ya Rabb.
Ina Godia da yanda kuka kasance A tare dani tun Farkon Novel din har zuwa k'arshensa, yanda kukayi Hakuri da rashin Posts na kwanaki, ina fatan kun min Uzuri saboda Uzurorina. Ina Fatan kun Nishadantu, kun Ilimantu da #KAC, kuma zakuyi koyi da abubuwan k'warai na ciki, kuyi panchakali da mara amfanin ciki.
And Yeah to The Bibilicious Freaking Fans all over The WorldšI Love Y'lls with Every Fibre of My Being, I Heart Y'lls To Piecesā¤ā¤ā¤
#1love to All My Whatsapp Groups ā¤
#1love to Nagarta Writters Associationā¤
My Wattpad followers @biebeeisa, Thank you for Your Votes and Comments it means alot, M Sorry i dont reply some of your messages. But Y'lls are right here in my Heart⤠I love you.
Thank You! Thank You!! Thank You!!!
#KAC
#SeebinFeeq
#SeebinNene
#1love
#Ana tareš»š»š»š»š»
_Bibilicious Biebee_
#Complied by Princess Aysha Muhammad