Showing 30001 words to 33000 words out of 149166 words
irin kuka mai tsuma rai, Rafeeq da ke tsaye kamar mutum-mutumi (Robot) don duk wasu daurar da ke aiki a k'wak'walwar shi ta dauke dif, sakamakon abun da ya gani. Mahaifiyar shi ce Kwance Zindir ba kaya haihuwar Uwarta. Rafeeq da karfi yace "Mammmmmmmiiiiiiiiiiiiiiiyy" firgigigit Mamy Aisha ta tashi.
_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg2⃣5⃣
Da karfi Mami Aisha tace "Inalillahi wa ina ilaihir rajiun, ne zan gani haka?" ta fada tare da neman abun da zata kare jikinta dashi, da sauri Sauda ta bude Closet dinta ta ciro mata zani da hijab ta bata, ta amsa da sauri ta suturta jikin ta. Ta bisu da kallo daya bayan daya, ta fashe da kuka, me ya faru dani? Aljannu suka shige ni ko? Suka min tunbur? Kumin magana" Sauda ta fara kukan munafurci tace haba "yaya, ya zaki ce haka? Kwarto fa kika kawo cikin daki, amma yanzu kina neman cema na ba kisan me kikayi ba? Zurum ta zube a kasa, don kafafuwan ta sun gaza daukar ta, a ranta tace kwarto? Ta dago taga yanda Alhaji Habib ke zubar da hawaye da sauri ta rarrafa gurin shi, ta rik'o hannun shi, Kamar wanda shocking ya taba, yayi saurin janye hannu shi tare da mik'ewa, ya nuna ta da yatsa yana kuka, "Aisha, kin cuceni, kin haince ni, kin ci amana ta, was it hard for you to wait for me?" kuka take yi sosai, ta kasa cewa komai sai girgiza kanta da takeyi, da kyar tace "kayi hakuri Habibullah" wannan magana da tayi ne ya sa shi tabbatar da zance, shikenan Aisha ta ci amanar shi, ta kawo kwarto har cikin dakin ta da tsakar rana, ba tsoron Allah. Da kyar yace "Aisha na sake ki saki daya" ya fice daga dakin, Sauda ta hau kururuwa ta bishi a baya "haba Alhaji be kamata kayi haka ba, be kamata ka yanke hukunci kana bacci ba, Alhaji ka maidota yanzu pls" tsawa ya daka mata yace "Saudat, kina so ki bita kenan? Da sauri tayi shiru kar daga neman kiba ta nemo rama. Ba ta ji dadin saki dayan da Alhaji ya mata ba, duk a zaton ta saki 3 zai mata, amna dayan ma ba laifi, zata tabbatar Aisha ba ta dawo gidan ba har abada.
Hafiz ya kalleta cike da tausayi tabbas wannan aikin Sauda ne ya rasa me zaice shima ya fita ya rage daga Rafeeq sai Mami, har yanzu tana nan duk'e inda Habib ya barta, Rafeeq ko na nan tsaye, ya kasa motsi, abubuwan ke dawo mishi kai, ya kasa yarda da Abun da idon shi yagani, da ya runtse ido Mami yake gani zindir, Mami ta dago kai a hankali ta sauke su kan Rafeeq, da jijiyoyin kanshi sun mimike, fuskar nan tayi Ja, idanuwan sa ma sun kada sunyi jazir, Mami bata damu da halin da take ciki ba ta mike ta nufo Rafeeq, yanayin da ta ganshi ya firgita ta matuk'a, ba ta taba ganin Rafeeq a haka ba.
Hannu ta cire zata riko shi don ta zaunar da shi kan gado, da sauri ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu, yace "dont touch me, Kar ki taba ni" cike da mamaki ta kalle shi, tsana da kiyayya taga ni kwance kan fuskar Rafeeq, yace "bana so in sake ganinki" baki na rawa tace "Rafeeee--q" yace "Wallahi na tsane ki" kafin ya sake wani magana yaji wani lafiyayyen mari tassss a fuska, hannu ya sa ya dafe kuncin sa, ya na dagowa ya sake ji a kara sakar mishi da wani marin da ya fi na dazu, duk a zaton shi mamin sa ce ke marin shi, dagowa yayi don sake yab'a mata wasu bak'aken maganganu, sai ya ga akasin haka, Hannun Mami ya gani rik'e da hannun Uncle Zaid da ke niyyar sake marin Rafeeq karo na 3, ta tare shi ta hanyar rike hannun.
Huci Zaid keyi, ya nuna Rafeeq da hannu "How dare you Rafeeq?" kasan da wanda kake magana? Rafeeq be bi takan Zaid ba ya kalli mami ido cikin ido, yace " i wish i had a different mother" ya juya ya fice. Cikin zafin rai Zaid yace" Rafeeq Habib Lema, come back here" Mami tayi saurin cewa "Zaid, laifi na ne, na mishi babban laifi, na ma kowa babban laifi, i dont know what exactly happened but i know i didnt do what they are accusing me of'' Zaid yace " Mami wai meke faruwa ne? Na rasa ganewa, tun kafin in shigo katsina na dinga neman layin ki, be shiga, na shigo gida na ga alamun ba lafiya, don Hafiz na k'asa na kuka, na tambaye shi me ya faru ya kasa magana, ban bi takan kowa ba na hayo sama gunki, na iske wannan mugun kalamai da Rafeeq ke fada miki, ina zargin Rafeeq koya fara Shaye shaye"
Mami na kuka sosai tace "ko daya Zaid, Rafeeq na da hujjan yin hakan, kaji kaji abunda na sani" "inalillahi wa ina ilaihir rajiun" inji Zaid, Mami har tayi nadaman gaya ma zaid, a zatonta shima yarda zaiyi da zargin da ake mata na kawo kwarto cikin gida. Tace Zaid "Wallahi ban san komai game da hakan ba, ni dai kaji yanda na tashi na tsinci kaina" Zaid yace "yi shiru mami kar kiyi zunubi, na san halinki,Wallahi akwai wata k'ulalla, akwai wata a kasa, tabbas wannan wani irin tuggu ne aka shirya miki, to wa??" Mami tace "Allahu Aalam, Zaid ka saurareni da kyau, wannan boyayyen alamari ne da ba wanda yasani sai Allah, Habib ya sake ni, i wont be there to protect my children, whoever came for me is coming for my kids, is defintely coming to hunt my Childeren down, sunci nasara a kaina, Zaid kar su ci nasara a kan 'ya'ya na, Zaid i want u to protect them"
Zaid na kuka yace "Mami yaya ya yi saurin yanke hukunci, baya cikin hayyacin shi ne sanda ya sakeki, mu bari ya sauko, sai ayi magana nasan gaskia zata fito, ya maido ki dakin ki. Murmushin takaici tayi, tace " Zaid kenan, yanzu dai bawanan ba, Rafeeq yayi fushi sosai, fushin da be taba yin irin shi ba, ina tsoron kar zuciyya ta kai shi yin aikin da na sani, ina tsoron zuciyar Rafeeq, Zaid ka bishi donAllah, Ka kula min da d'a na" kamar wanda aka tsunkula ya tashi zumbur, don ya mance halin da ya ga Rafeeq dazun. Yace "Mami ki jirani i'll be back and everything is going to be Alright" a hankali tace "Go Zaid, Go" be sake magana ba ya fice da Sauri. Matakala bibbiyu, uku uku Zaid ya dinga hadawa ya sauka k'asa, sai dai ga mamakin shi Wangale yaga gate, ya duba gefe ya ga ba motar Rafeeq da yagani Parke a gefe hankalin shi ya daga, daidai nan sai ga Baba Maigadi ya shigo gidan da Cefane da Lettuce din da Sauda ta aike shi a hannu, Zaid yace "baba ina Rafeeq" Baba yace " Zaid yanzun nan na ga motar shi ta wuce fiyauu, na tsorata da yanda naga yana tuk'i, da alamu sauri yake" Hankalin Zaid ya tashi, ya na tafiya ya na magana yace "akwai matsala a gidan nan baba, matsala babba" Zaid ya fada motar sa ya bi bayan Rafeeq baba Maigadi ya mishi Allah ya kiyaye.
Zaid na fita itama ta hada kayan ta, kana ganinta kasan hankalin ta a tashe yake, duk ta dauki abubuwan buk'ata, ta sauko k'asa ta bude motar ta da ta siya da kudinta ta tura Akwatin ta, da sauri Baba Maigadi ya nufo gunta, "Hajia Lafia? Tafia zakiyi? Ince dai lafiya fuskar ki tayi Jaa, kuka kikeyi ne?" da kyar tace mishi "Baba, Habib ya sake ni" Salati maigadi ya saki, yau mun shiga uku, shi habibun ya sake ki?" me yayi zafi haka?" Murmushi tayi tace baba barin tafi, don Allah a kula da su Rafeeq, akwai wata Musiba da ta shigo gidan nan" Baba da ya fara kwallah yace InshaAllah, Allah shi yaye ya sa ku daidai ta da Alhaji ya maidoki dakin ki, don Wallahi ba shi kadai yayi rashi ba muma munyi". Tace nagode ta bude motar ta ta shige ta bar Haraban Gidan Habib Lema.
Gudun da Rafeeq keyi na tashin hankali ne, kamar zai buge mutane, Allah dai ya cigaba da kare shi, don be ganin gabanshi shi dai yasan tuk'i yake, ba tare da yasan inda ya dosa ba, Kiran Zaid ya shigo wayar sa, amma yanda sauran kiran suka shigo suka yanke haka wannan ma ya katse, Zaid ya damu matuk'a da kyar ya kira Maalesh ya ji in gidan su Rafeeq ya nufo Maalesh ya bashi tabbacin tun wurin 11 suka rabu. Zaid gudu yake yana duba hagu ko dama inda zai ga Rafeeq, kawai dai ya yanke hukuncin bin Hanyar Jamia ta wurin Ring road, speed ya k'ara, ba jimawa kadan Zaid ya hango motar Rafeeq daga chan nesa, gudu yake kamar dan tseran mota, hamdala Zaid yayi ya k'ara gudun motar shi, horn yake ta mai amma yak'i tsayawa, ta mudubin motar Rafeeq ya gane motar Uncle Z, shima ya kara gudun motar shi, Shima Zaid ya kara na shi, Gudun da sukeyi yafi kama da na masu race, ba me niyyan tsayawa, Burin Zaid ya tarar da Rafeeq, shi ko be da wani burin da ya wuce ya ta tafia har sai ya manta da wani damuwar shi.
Zaid ya taka motar nan da karfi, har Allah ya bashi ikon shan gaban motar Rafeeq, Ran Rafeeq ya baci, niyyan shi ya cigaba da tuk'in har ya buge motar Zaid, amma zuciyar shi ba zai bari ba, Uncle Zaid ne fa a motar, mutumin da yake so sosai, ba zai so ya buge shi ba, be da wani zabin da ya wuce ya tsaya da motar sa.
"Aishatu lafiya? Kinzo kin tasamu gaba kina ta kuka, wani abun ne ya faru?" Baba Tijjani ne mahaifin Mamin su Rafeeq ne ke mata tambayar nan, duk ya tsufa sosai, mamar tace "haba mama na, idan wani abu ya faru ki gaya mana, ba wai ki tasamu da kuka ba" da k'yar ta tsagaita kukan ta ta labarta musu iyakar abun da tasani, Sallalami da Salati suka fara, mamarta harda kuka, Baba Tijjani yayi shiru yana nazari, chan yace Aishatu, na san wa na haifa, na yarda dake, ban haife ki don ki zama ma zinaciya ba, da mijin ki da 'yaranki, tabbas idan aka duba wannan lamari zaa ga shiri ne a dunkule sai mai hankali zai gane" Mamar Mami tace "amma shi kuma habib harda Saki? Baba Tj yace "sharri ne dai don a hadata da mijinta, ni ban ga laifin Habib ba, don ko ya samu duk wani evidence da ya ke bukata, ko wani namiji haka zaiyi, amma ina da tabbacin da Habib ya kwantar da hankalin shi ya duba lamarin nan zai gano gaskia, tashi ki shiga daki Allah shi zai saka miki" tace baba ina so in bar gidan nan, don na san Zaid ba zai taba bari na a nan ba, duk yanda zaiyi sai ya maida ni gidan Yayan shi, bana son hakan ya faru na fiso Habib ya gano gaskia da kanshi kuma ina bukatar lokaci da zan huta in yi idda na, ina neman izinin ka na barin garin" "Aa Aishatu, ba zan bari kiyi zaman kanki ba" Mama tace "ta je Malumfashi gurin Inna mana" Baba Tijjani yace "kina iya zama malumfashi gun kanwara mamarki?" tace "Eh Baba, idan ka min izini yanzun zan tafi" yayi shiru yace "Allah ya kiyaye hanya, Allah ya tsare ki kula da kanki".
Ganin Rafeew be da niyyar fitowa daga motar shi ne ya sa Zaid fita da sauri ya nufe shi, har ya tako gaban motar Rafeeq, ya bude gaban motar, ya sa hannu ya fito da Rafeeq, ya kalle shi, shima ya tsorata da yanayin Rafeeq, fuskar nan ta yi ja, idanuwan nan sun kada sunyi jazir, ga digon hawaye ko k'wallah, jijiyoyin kanshi sun mik'e. Zaid ya tausaya ma Rafeeq sosai yace "Rafeeq" Ko kallon shi Rafeeq beyi ba, Zaid ya kara cewa "Rafeeq kayi hakuri, kayi kuka, cry it all out, kar ka barshi a ranka, pour your heart out, i know this is hard for you, let it flow Rafeeq, let it flow"
Da sauri ya rungume Zaid sosai, sai a sannan ya samu Hawaye suka fito daga idanuwan shi, sai a sannan ya fara kuka a hankali yace "Uncle Zaid, Help me"
_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE 🙇?
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
*Assalamu Alaikum*
_Da farko zan fara da nuna godiata da jin dadin yadda kuke biye dani a cikin_ _littafina na *KE ALHERI CE*_
_Nagode sosai Allah ya saka maku da alkhairi yabarmu tare._
_Kamar yarda korefe korefe sukayi yawa akan page 23 na littafina masu yi a grps da masu biyoni prvt duk ina son inyi clearing mind dinku daga abinda kuke ganin na aikata da wasunku suka daukeshi daidai da kuma wadanda suka dauke shi ba daidai ba. (Yin daidai sai ubangijinmu cos_ _dukkanmu tara muke bamu cika goma ba_)
_Kamar yadda kuka sani duk wadda tabi littafina daga page one zuwa yanzu tasan inda littafina ya dosa.. Kamar yarda kuka karanta kuka gani there is darkness in *Rafeeq's* life wanda yake saka shi yin duk wani abu da wasu dabiu da ba halinshi bane a da, wanda har na gangaro zuwa page 24 inda kowa ya gane dalilin shigar *Rafeeq* wannan yanayin da yake na yanzu._
_Kaidi irin na mata( *Wanda ko shaidan tsoronsu yake*) ya kuma hadu da kaidi na kishiya mara imani babu abinda baya janyowa.. abinda ya faru da Mami is well planned by Saude so ko sirikinta ne zai iya ganinta a yanayin data samu kanta_ _balle kuma dan cikinta sbd dama burinta ta kafa shaida mai kyau ta ido sbd idan dunia zata taru tana gaya ma *Rafeeq* abinda_ _mahaifiyarshi tayi bazai taba yarda ba kamar yarda uncle Zaid da iyayenta basu yarda ba..Saude tayi hakan ne dama don su gani da idonsu su zama shaidar kansu,wanda hakan ya tabi zuciyar Rafeeq har ya_ _haddasa mai duhu da bakin cikin da yake kwana yana tashi dashi kullu yaumun.._ _haka kuma rayuwarshi ta watse ta tarwatse sbd abinda ya gani da idonshi._
*_Kowacce tayi addua Allah ya rabata da muguwar kishiya sbd babu abinda basu iya aikatawa tunda babu Allah a cikin al ammuransu._*
_Allah yasa muna fahimta da amfana da darussan rayuwa dake ciki_
*Biebie* luv u loads💖❣💕
Pg2⃣6⃣
Kuka yakeyi kamar karamin yaro harda majina, Uncle Zaid beyi yunkurin hanashi ba, sai da yayi ma ishi kafin ya tsagaita da kukan. Uncle Zaid ya kira Maalesh yace yazo ya iske shi ring road yana jiran shi, kar yazo da mota, baa fi 15mins ba sai gashi, a rude Maalesh ya fito don be san meke faruwa ba yace "guy howfa? Kallo isasshe Rafeeq be ma Maalesh ba, Zaid ya mai alama da yayi shiru. Key din motar shi ya ba Maalesh, ba tare da ya tambayi me zaiyi da key din ba ya shige motar Uncle Zaid, shikuma zaid ya tura Rafeeq cikin motar sa, Zaid ya zauna a mazaunin driver ya ja motar ba me cema danuwan sa k'ala, jefi jefi Rafeeq yake sauke ajiyar zuciya, hanyar gida suka dauka, a hankali Rafeeq yace "please dont take me home" ba musu Zaid ya chanza hanya ya nufa gidan su Maalesh, daidai gidan su Maalesh Zaid ya tsaya yin horn, Rafeeq be jira maigadi yazo ya bude gidan ba ya fita daga motar ya shige Gidansu Maalesh ya nufi side dinshi.
Zaid ya girgiza kai ya fito, Maalesh ma ya fito, yace Uncle Zaid me ya faru da Rafeeq ne? Ban taba ganninshi haka ba, da kyar Zaid yace "he is broken" ya sake bashi key din motar shi, yace "je ka kai motar Rafeeq gida ka dawo yanzu" Akwai mutane cikin gidan?" Maalesh yace "aa Mummy taje kaduna, ba kowa" yace key din dakin ka fa? Maalesh yace "akwai daya gun Rafeeq, amma ga wannan incase ya barshi gida" Zaid ya amsa ya nufa cikin Tangamemen Gidan su Maalesh.
Be ga Rafeeq ba a kofar dakin, hakan ne ya bashi tabbacin Rafeeq na ciki, ya murda kofa yaji ta rufe, key din da Maalesh ya bashi ya zaro ya bude kofar, tare da shiga da Sallama, chan kusurwa ya ga Rafeeq kwance, be kula shi ba ya shiga toilet yayi Alwala kasancewar lokacin Sallah yayi.
Bayan ya idar da Sallah ya zauna kusa da Rafeeq ya janyo hannun shi ya hade da nashi, yace Rafeeq ka saurareni, "Mamin ka ba tayi- da sauri yace kar kayi shaidar zir Uncle Zaid, ni nasan abin da nagani, naga zahiri ba labari aka ban ba" Zaid yace najih Rafeeq, kaga zahiri ba labari aka baka ba, amma shin kagan su suna aikata Zina? Mahaifiyar ka ba ta chanchanci haka daga gareka ba, kar ka mance irin So da K'auna da take maka, Rafe--" Uncle Zaid ya isheni, Wallahi zan bar maka gidan nan, idan kana min maganar ta kana sawa ina k'ara tsanar ta" jimm Zaid yayi, sai ya yi shiru don baiwa Rafeeq Lokaci, ya mik'e yace "bari inje in dawo".
Isketa yayi kitchen tana kokarin dafa ma Alhaji Habib Ruwan Zafi, Hafiz yace " Sauda, na san kina da hannu akan abun da ya faru da Aishatu, komai shirin kine ke ki ka k'ulla mata wannan sharrin." tayi wulwul da ido, tace haba Hafiz, me kake cewa? Rashin imani na be kai nan ba, muna zaman lafia da ita me zai sa in neme ta da sharri, ni bansan me ka mayar dani ba, yace "Sauda na san halinki sosai, wallahi nayi bincike nagano gaskia, to zan tona