Showing 78001 words to 81000 words out of 149166 words

Chapter 27 - Ke alkhairi ce COMPLETE HAUSA NOVEL

BIEBIE   

22 Oct 2024

25732

ka min izinin ganinshi" Baba maigadi yace "Indai nine bakomai, yaro kana min kama da wata Aminiyata Aminene" Abbii yayi Daria yace "Ni ne Autan ta" Baba Maigadi yace "Haba biri yayi kama da mutum, kaind Mahaifin Nasiba ko? Ga kama nan wallah" daria yayi yace "barin ga Rafeeq" ya nuna mishi dakin Rafeeq da yatsa, kai tsaye Abii ya nufa dakin.

"Assalam Alaikum" be jira amsar shi ba ya shiga ciki, kwance ya ganshi yayi ruf da ciki, kafar shi ya dan ja, Zumbur Rafeeq ya tashi tsaye, yana mamakin Abbii, a ranshi yace wai "me mutumin nan ke nufi da shi?" Abbii ya kalli Rafeeq yace "Kasan cewa Nene Mahaifiya ta ce? Ita ta haifeni?, ko ya take i cannot replace her, She's my Mom ba zan lamunce wani ya mata rashin kirki ba, i cant watch anyone disrespect her, the words you used on her were harsh" shiru yayi, yana nazarin maganganun Abbii, tabbas be kyauta ba, the woman is soo annoying, sai dai ya dubi Girman Abbii yace "Kayi hakuri" Abbii yayi Murmushi yace "Bakomai" na maka Uzuri ai. Rafeeq ya kalleshi, Abbii ya cigaba da cewa "Kana jin zuciyar ka na maka nauyi, kana jin ka tsani duniya, wata sa'in ka kan so da ma ka mutu, kana gajia da rayuwa, kana cikin wani Bak'in duhu, Bacin rai da rashin Dangana ya hanaka neman Haske, abu yayi k'amari da har Addua baka iya yi don a ganinka baka da wata buk'ata da ya wuce a ce ka mutu, baka da wata ragowan Jin dadi a Duniya" be bari yace komai ba ya cigaba da cewa "Rafee'ah, mafi Soyuwar k'anwa a gareka, ka san wani hali take ciki a yanzu? Ba kasan tana bukatar adduar ka ba? Baka san ba abun da mamaci ya fi buk'ata da ya wuce addua ba? k'anwarka na bukatar Adduarka, in dai hakane, to for her sake, you have every reaaon to stay alive, you have to survive, you have to achieve your Goal in Life, you have to go back to your normal self, and one day get Married and your kids will pray for your Late Sister, You have to Fight that Demon in you for your sister" wasu manyan jijiyoyi suka ma Rafeeq tsaye a kai, so yake yayi kuka amma ya kasa, kukan yak'i fitowa, shi kanshi yasan cewa yayi sakaci, a hankali yace *"Help Me"* Alhamdulilah inji Abbii, yace "Help yourself first, How? ina so ka fara Sallah cikin Jami'i, kai Bawa ne dole ka rok'i Allah haka zaka yi da hannu ka gaya mishi bukantunka, Akwai wani ruwan adduoi da zaka mai dashi ruwan sha dinka, ba daci ba bauri ba komai, ruwa ne Kawai ka maidashi ruwan ka, sai abu na k'arshe akwai Wani Magani da zaka dinga Zuwa Gidan Nene Kana sha Yamma ko Dare, InshaAllah wannan zasu taimake ka" Rafeeq ya ja gwaron Numfashi, yace " I will do everything you said, amma i dont have to go to her Place, zan iya shan Maganin a nan ba sai naje gidan ta ba" Abbii yace "Ina so ka yarda dani, kayi yanda nace" dan guntun tsaki yayi yace "Najih" Abbii yace Your Medication Starts today, muje kasha maganin, sai ka taho da Jarkan Ruwan" be kulashi ba ya tashi ya fita, Abbii ya rufa mai baya.

_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

     NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

This Page is for you Mrs Ruff Baby Aisha(Maman Irfaan) ILY❤

Pg4⃣6⃣

Abbii ya shiga gidan, Rafeeq na biye dashi a baya, Nene ta kallesu zatayi magana Abii ya mata nuni da tayi shiru. Ya kalli Nasiba yace "Seebi kina iya dauko Jarkan ruwan nan? Ta daga kai, ba ta jira cewar Abii ba ta shige daki ta kinkinmo jarkan Ruwan, da kanshi ya dauko Kofi ya bulbulo ya Mik'a ma Rafeeq Cup din, yamutse fuska yayi ya kurba, jin da yayi ba taste, ya sashi kafa kofin ya shanye ruwan ciki tass. Ya shiga cikin Dakin, ya dawo da Robar magani na hadin mai da zuma, Ya nuna ma Rafeeq yace wannan shine dayan Maganin, shine wanda nake gaya maka za ka dinga sha so daya a rana, kuma shine zaka dinga zuwa wurin Nene ka dinga sha, Cokali daya ne, ba zaka ji dadin shi ba, amma daurewa zakayi ka sha" kai kawai Rafeeq ya daga, Spoon Nasiba ta mik'o ma Abbi, ya tsiyaya maganin cike yayi bakin Rafeeq dashi, Rafeeq ya bude baki Abbii ya juye mai, wani iri taste mara dadi yaji, tuni yayi yunkurin zubdo shi, amma Abbii ya sa shi dole ya hadiye, ya sake bulbulo mai ruwa Rafeeq ya shashe bakinshi, Abbi yace "Sannu, daurewa zaka dinga yi, kasan magani ba dadi, Allah dai yasa a dace "Zan tafi" inji Rafeeq, Abbii yace "To ka tafi da jarkan ruwan" Rafeeq ya kalli Jarkan ya ga bazai iya dauka ba har gida, yace "Zan dawo in dauka" Abbi yace ai ba da duka zaka tafi ba, diba maka zaayi, idan ka shanye sai ka ka'ara kawowa a dura maka, ko robobin da kake shan Ruwa, dazun naga kusan guda nawa a Dakinka, yanzu ke Nasiba ki samo roba ki zuba mai, gobe sai ya kawo Robobin da za a dura mishi a ciki, sai ma ya sa a fridge in yana bukatar mai sanyi", "sai kuma chan gida ka basu su dinga maka abinci da ruwan" ganin yanda ya chanza fuska ne yasa Abbi fahimtar be cin abincin gidan, kuma ya tuna Nasiba tace siyan abinci yakeyi, sai yace "ko su nan zasu dinga dafa maka abinci? In dai ka samu lokaci ka dinga lek'owa kaji ko?" kai kawai ya daga. Nasiba ta dura mai, kamar jira yake tana bashi ya juya, har ya kusa fita ya juyi ya kalli Nenen da tsura mai ido, ya danyi guntun tsaki yace ma Abbi "kace mata ba ruwan ta da ni, magani kawai zata dinga bani" Murmushi kawai Abbi ya mai alamun Yaji, Nene zata yi magana Nasiba tayi saurin toshe mata baki, duk sukayi daria.
"Nene nasan ba zai jure shan maganin nan ba in yana wurinshi, shiyasa nace zan bar maganin a gunki, yanda zai dinga zuwa yana sha a gabanki ya hadiye, amma DonAllah kar ki biye mishi kuyi ta sa'in sa" Nene ya ta6e baki tace "najih" Abbii yace "Nikam Seebi Rafeeq baya miki kama da wata?" Murmushi Nasiba tayi tace "Mamin Ayman" Abbi ya gyara zama yace "ya akayi kikasan ita ke raina?" tace "saboda da ita su ke kama, Mamin shi ce" Abbi yace "bangane ba" tace "Maman shi ce Mahaifiya" "Allahu Akbar biri yayi kama da mutum" inji Abbi nan Nasiba ta shiga basu labarin yanda sukayi da Mami, duk suka tausaya mata.
*****************
Yau ne tafiyar Abbi, ya shirya kayanshi sun fito domin rakashi tasha, sai ga Rafeeq ya fito daga motarshi da Robobi cikr da Leda, ya kalle su one by one, kafin yace "Barka da Safiyya" amsa wa sukayi, binsu yayi da ido kafin yace "Ruwan zaa bani" Abbii yace "to ke Nasiba kije ki dura mai ruwan, Nene kuma kiyi zamanki ba sai kinyi wani rakiya ba" tace "ai wallahi sai na raka ka" Seebi tayi fuskar tausayi tace "Hamma Rafeeq bari mu raka Abbii tasha, idan mun dawo sai in dura maka" Rafeew be ce komai ba Abbi yace "Aa, je ki dura mai, muna jiranki" nan Rafeeq ya gane cewa yau Abbi zai koma Kaduna, ya kalli Abbi cike da nutsuwa, dan zaman da sukayi tsakanin Jiya da Yau yaji zuciarshi ta kwanta da shi, be son ya tafi, ina ma ace ya k'ara kwanaki, yanzu da be zo ba tafiya zaiyi without saying goodbye? a hankali ya kalli Rafeeah da ke jiran ya miko mata ledar robobin, yace "Wait, we'll all go" Abbii yace "aa Rafeeq, ka tsaya kayi uzurin ka" Rafeeq be jira cewar Abbi ba ya taka har gabanshi ya amshi jakkar hannun shi, ya wuce motar shi ya bude ya saka a booth, hakan ne yasa Abbii Murmushi ya nufa motar ya zauna gaban mota, su Nene da Nasiba cikin murna suka shiga bayan mota, Rafeeq ya ja motar yayi Tashar KTSA. Ba me maganar har suka iso Tashar, har cikin tsar Rafeeq ya shiga da motar sa, bayan da Abbi beyi ba da a sauke shi nan su juya, amma yak'i, jin ana Fadin Kaduna Kaduna ya sa Rafeeq parking ya nufa Motar, da Sauri Abbi ya fita ya bi bayanshi, Rafeeq gaban kwandaster (conductor) yace mai "Nawa?" karen mota yace "1500" Cikin Aljihu Ya sa Hannun shi, ya zaro 2k Abbii yayi saurin rik'e hannun Rafeeq, Rafeeq ya kar6e hannun shi cikin nutsuwa tare da girgixa ma Abbi kai ya mik'a ma Kwanduster din, kamar jiran zuwan Abbi ake, Motar su ta tashi, bayan sun bishi da adduoin sauka Lafiya, suka koma Mota. Rafeeq ya ja ya bar tasha.
***********
Da dare ya nufa Gidan Nene amsan Magani, Sallama yayi ya shiga, Nene ke zaune tana jin radio, Nasiba na gefe tana duba Wani Littafi, tace "Hamma na sannu da zuwa" Kallon Nene yayi instead ya amsa gaisuwar Seebi yace "Sannu Fa" Nene da yak'en da ya fi kama da kuka tace "Ahh kai ke da Sannu" be kulata ba ta tashi dauko Magani don ta zan silar zuwan kenan, Ganin haka Nasiba ta matsa kusa dashi tace "Hamma ka ci abinci?" kamar ba zai amsa ba yace "i am not hungry" ta marairaice tace "DonAllah in dafa maka ko Indomie ce?" shiru yayi kamar be ji ta ba, har ta cire rai zai amsata ta mike don komawa mazaunin ta, cikiciki taji yace "Ki dafa min" Da sauri ta juyi da murmushi dauke kan fuskar ta, daure wa yayi kamar ba shi yayi maganar ba, da sauri ta zura Hijab ta bude jakkar School dinta, yana kallonta, sai da tayi hanyaf fita ta tsinkayi muryar shi yace "Ina zaki" tace "Shagon Ummu Sudais zanje in siyo Indomie din" (GWS Ummu Sudais ILY). Guntun tsaki yayi ya mik'e ya zura takalman shi ya fita daidai ita yace "Ki barshi" tace "Hamma-" katse ta yayi ta hanyar daga hannu yace nace "ki barshi ko? Koma ciki" ba musu ta dawo ciki amma ranta ya baci, to meye abun daga murya? Nene ta fito da Goran Maganin a hannunta tace "Ina Dunkum din?" Seebi ta ta6e baki tace "ya tafi" Nene ta daga murya tace "Kika barshi ya fita?" Seebi cike da takaici tace "rike shi zanyi ince ya dawo? Nene tace "ke tamabyar ki nayi bace miki nayi ki zagar min uwa ba" Seebi dai ba ta sake magana ba ta shige Daki.

Chan sai ga Rafeeq ya shigo da Carton din Indomie da crates din k'wai guda biyu, Nasiba na ganin shi tayi saurin tashi ta tarye shi don ta ga yanda yake tafia kamar zai kife, tace "Hamma you dont have to do that" hararar ta yayi yace "jeki dafa min, i am hungry" wani dadi taji ya lullube ta da sauri ta aje kwalin gaban Nene, Nene ta kalli Rafeeq tace "Sannu fa" wani murmushi ya kubce mai, wai shi take koyo, wannan tsohuwar is full of wonders.
_Bayan Minti 15_
Gaban shi ta dire Indomie din da aka dafa da ruwan Magani da fried Egg, kamshin ya cika mai hanci, tuni ya fara Salivating, Ba wasa ya hau cin indomie din yana jin dadi, Nene ta ta6e baki tace "kadifiri, a gama jin dadi a zo a kur6i magani" ai ko yana gama sha, ta zuba magani a cikin spoon tace "Kar6i" warin maganin ya daki hancin shi, ga shi ya ci k'wai haka kurum yaji amai ya taso mai, ya fara k'ak'arin amai, ganin yamutse yamutsen fuskan da yakeyi sai tayi zaton iyarshege ne, da sauri ta toshe hancin shi, kafin ya ankara ta mai dure, ta juye maganin a bakinshi, ta sa gudan hannubta ta damk'e bakin Rafeeq, gashi be nunfashi, be da zabin da ya wuce ya hadiye maganin, sai da yayi sakwan 15 kafin Nene ta sake shi, Nasiba ta kasa ce ma Nene komai don tasan yau akwai dirama, da gudu ta bulbulo mai ruwan Maganin shi ta mik'a ma Rafeeq, ba sanya ya kafa kai ya shanye ruwan, ya juyo ya na ma Nene wani irin kallo. Kunnenta ta kama da hannu biyu tace "Sori Gaye" Sosai ta bashi daria, kauda kai yayi lokaci daya ya murtuk'e fuska, chan kuma yace "kina da hayaniya, ki dinga yin abu a hankali" Nasiba ta bude baki, a zatonta Nene zata balbale shi da masifa, sai ta bata mamaki da cewa "Naji Dan gaye na, ga Farar ka tun rannan na ajiye maka" ta ciro Farar a gefen Tabarma da yake dare ne ba wanda ya lura dashi. Murmushi Rafeeq yayi wanda ya sa fuskar shi kyau Sosai ya sa hannu ya amsa tare da kallon Nene, Nene ta san me zai ce, a tare sukace "Sannu Fa" Nene da Nasiba suka sa daria, shi dai Murmushi kawai yayi. Nasiba tace a ranta "Finally these two are getting along. Lallai magani ya fara aiki so soon"
***********
Bayan Kwanaki Goma(10days later)

(Kuyi hakuri da page din nan, girman Alkawari ya sa nayi typing page din, Zan dasa daga nan gobe InshaAllah👻)

👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

     NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

This page is for you my Everlasting Babe Miemee 👄Bee❣and My Coach Lubie Maitafsir❣ Aunty Sis and I love you two to the moon and back #1love.

Pg4⃣7⃣

"Oh shit! sorry Angel i didnt mean to shout at you" duk yayi wani iri kamar me shirin kuka, 6are baki ta sake yi, kamar ana k'wak'ule mata idanuwa, kuka Rafeeq ya fashe dashi sosai, be son kukan Ayman, yana waigawa ya ga Uncle Zaid ya idar da Sallah ya tsaya yana kallon su kamar TV, ganin Rafeeq na kuka ya sa Zaid daria, da sauri Rafeeq yayo kan Zaid kamar zai kife shi da duka don takaici, yana kallon su amma ya k'i cewa komai, "Uncle please make her keep quite" a tak'aice Zaid yace "No, i didnt make her cry, you make her calm" Cikin marairaicewa Rafeeq yace "pleaseee" Zaid ya ksrbeta, tana ganin shi tayi lamo tana ajiyar zuciya, Zaid yace "ka duba bayan Seat akwai Basket dinta ka kawo min, she must be hungry" da gudu Rafeeq ya fita waje duk ya bi ya rude, Zaid ya bishi da ido ya na Murmushi, chan sai gashi ya dawo da Basket din Abincin Ayman-Rafee'ah, Zaid ya ce bude flask din ka zuba ruwan zafi a bowl din ciki, Sai da ya dauraye Dan kwanon kafin ya bude flask din, Zafi rau kamar yanzu aka zuba a ciki, tun Ruwan Zafin da Mami ta sa musu a flask ne da safe, har yanzu be huce ba, nan Zaid yayi guiding Rafeeq ya dama mata Baby food din, Zaid ya lasa yaji yayi daidai ya shiga bata a baki kamar yanda ya ga Mami nayi, ta dinga sha har tayi gyatsa, Zaid yace "kwaso kayan booth din gaba ki daya, banda Trollys din, akwai dan kit daga gefe kayan wankan ta na ciki" haka Rafeeq yaje ya dauko, suka tu6eta a tare, tayi kashi a pampers dinta, Rafeeq ya rintse ido tare da kawar da kai gefe ya mata tsarki, hannun kamar zai yaddashi, Zaid ya dinga musu daria, a tare suka mata wanka da ta juya ta hada ido da Rafeeq sai tayi kamar zatayi kuka(😩) Da sauri Zaid "zaice yi shiru babyn hammanta" sai tayi shiru ta fasa kukan, haka suka gama mata wanka duk sun jik'e kayansu kamar sunyi wasan ruwa, kusan Minti 30 suna shiryata kafin Zaid ya hadata da chocholate daTeddy bear, Daga Rafeeq har Zaid suka zube kan Gado yaraf a gajiye, suna maida numfashi kamar wanda suka shekara suna aiki, Rafeeq cikin gajiya yace "You should get married, only to someone who will take good care of her" Zaid shima yana maida numfashi, be ta6a wahalan Ayman ba kamar haka, lallai Mami na k'ok'ari, shima a gajiyen yace "Yes, you are right, i'll get married soon" suka kalli juna suka sa dariya. Jin horn din Motar Alhaji Habib yasa Zaid mik'ewa, yace "Yaya ya dawo" Rafeeq be ce komai ba, Zaid ya mai nuni da Wata Leda yace "ga tsaraban ka chan" murmushi kawai yayi ya bude ya ciro kwalin Turare, da agogo, da links na kaya, da pack din Vest, sai takalmi. Murmushi Rafeeq yayi yace "You are the best".

"Babyn hamman ta zo muje mu gaida Yaya" Zaid ya kalli Rafeeq yace "ko kuka takeyi akace yi shiru babyn hammanta zakaji tayi shiru, she has no idea who the hamma is, yau ta ganshi tana mai RM" murmushi kawai yayi yace "A sannu zata san waye Hamman ta" Rafeeq ya mike ya nufeta yace" zo muje gun Hamma" ga mamakin shi ta mika mai hannu shi kuwa ya sa6e ta, suka fita, Zaid ya dauki ledar Tsaraban da ya ma 'yan cikin gida.

Shekara kusan daya da wani abu rabon da ya taka koda k'ofar parlorn cikin gidan, tana hannunshi ya dinga bin parlorn da ido, yana nan yanda yake, a hankali ya shiga tunano bak'in abun da ya faru, tun daga Randa yaga Mamin shi da wani a daki zuwa ranar rasuwar Rafee'ah, dalilan da ya ke hanashi tunkarar dakin kenan, ya juya zai koma, Zaid yayi saurin girgiza kai yace "mu shiga" ba musu ya bi bayanshi suka hau Sama har Parlorn Daddy. Daddy na ganin su ya mik'e tsaye, bawai mamakin dawowan Uncle Zaid yakeyi ba, aa Mamakin ganin Rafeeq yakeyi a cikin gidan a Saman shi, hawaye suke shirin bullo wa yayi saurin tare su, ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login