Showing 69001 words to 72000 words out of 149166 words

Chapter 24 - Ke alkhairi ce COMPLETE HAUSA NOVEL

BIEBIE   

22 Oct 2024

25735

waje ya sama mata Napep ta wuce Gida.

*Malali Kaduna*

Karfe Hudu saura minti 10 (3:50pm)Nasiba ta shigo Unguwar su,m, a Lokacin ana ta kiraye kirayen Sallahr Laasar, da ta hangi Gate din Gidan su taji wani sanyi ya ratsa ta, ta biya mai Napep kudin shi ta fada gidan, tun daga Gate take kwada Sallama.

Ummin da ta yi Rakiyya tace "Muryar wa na keji haka kamar Seebin Nene? Bata ankara ba taji an fado mata a jiki "laah itace ashe", ta rungume diyarta suna Daria, daga Katsinar? Ina Nenen? " tana chan ta k'i yarda ta biyo ni" tayi daria tace "ba ki gaida Mamin Ayman ba" tayi daria tace "sorry ban lura ba" Seebi ta juya ga inda matan da Ummi ta rako ke tsaye, ga Mamakin ta, matar ita take kallo, ta shagala da kallon ta, Nasiba ta tsurawa matar ido tana son tuno inda ta san fuskar, ta dai daure tace " Ina wuni? Shiru, Ummi ta dan dafa Mami tace "Mamin Ayman wannan diya tacw na ce miki tana karatu a Jamiar Katsina" Firgigi tayi kamar wanda aka tada daga bacci, tace "Allah Sarki" ta juya ga Seebi tace "Lafiya lau, kin dawo Lafiya?" "Alhamdulilah" ba ta jira sunce wani abu ba tace "barin koma gida kafin Ayman ta tashi" to a gaidata inji Ummi, suka juya cikin Gida, Mami ta tsaya bakin gate ta juyo tana kallon bayan Seebi, a ranta tace "Allah mai iko, meyasa nake ganinta kanar Rafee'ah?".

Murna gun Abbi da Anan ba a magana, kamar sun yi shekara basu ga juba ba, nan Nasiba ta dauki wayar Ummi ta kira Nene, har tayi Ringing ta gama bata dauka ba.

*WasheGari*
Tun da Safe Nasiba ta shirya Anan, ta raka shi har Makaranta, ta dawo gida ta ciro Garin Alkaman da Nene ta siyo musu ta tankade shi, Abbi ya fito daga daki, ya ganta sai aiki tankade takeyi, yayi Murmushi yace "Sarkin aiki, kin fa dawo kenan, to me za a mana yau?" tayi daria tace "Barka da fitowa Abbi, Alkubus zan mana" yace "Ahh kice yau zamu kwashi Gara" tayi daria, ta cigaba da aikinta, ko da Ummi ta fito tace zata sa mata hannu cewa tayi "Ummi ki bari, aiki na ne" haka ta zage ta kwaba Alkamar nan, ta yi hadin Alkubus, da kanta ta fita tayo cefane, tazo ta gyara kayan miya da kabewa ta yanka Alaiyahu, ta hada da kifin gwangwani, sai da Kwabin Alkamar ya tashi kafin ta zuba a madanbacci, nan da nan gida ya kaure da k'amshi, bayan ta gama ne ta zuzzuba a Cooler, Ummi tace "Ki saka ma Mamin Ayman, na san zataji dadin shi" Wannan matar da kika rako jiya? Tace "eh ita, tana da kirki, ba su dade da dawowa nan Unguwar ba, ta girmeni amma tana mutuntani" Allah sarki inji "Nasiba" Ummi tace "kiyi wanka ki mik'a mata, tunda Anan ya tafi Makaranta" Nasiba tace "toh".

Kwanan shi biyar be ganta ba, so da dama zai zo bakin k'ofar gidan yaga ko zai ga fitowar ta amma shiru, ya mata text kala 2 ba reply, wayarta in ya kira har ta gama ringing baya dauka, a rana sai ya jera tsaki fiye da dari, haka kawai yake jin kanshi wani wani iri, gashi Maalesh ba ya nan, haka kurum yaji he wants to see her, zumbur ya tashi daga kan gado, ya zura takalman shi, fita yayi daga gidan be dauki Mota ba, ya taka har k'ofar gidan Nene, mintin shi sha biyar tsaye gaban gidan, ya rasa yanda zaiyi, to wai ma ya ganta yace mata me? Tsaki yayi ya juya, zuciyar shi tace to ko lafia dai? Ko ciwon Nene ya tashi ne shisa ya daina ganin gilmawarta, ko a Unguwa sometimes ya kan ga wucewarta zuwa shago, dawowa yayi, ya tura k'ofar gidan, ya shiga Chan k'asan Mak'ogaro yayi Sallama, Nene na zaune tsakar gida tana gyaran wake ta amsa Sallamar tare da cewa Bismillah, kamar ya juya da ya ji muryar Nene, amma be san me ke tunzura shi ya shiga ba, cikin tafiar shi ya ida shiga gidan, Idon Nene a kan shi, a ranta tace "Yau su Dunkum ne a gidanmu" ba yabo ba fallasa tace k'araso ga wuri ka zauna, kan kujera ya zauna, chan taji yace "Sannu fa" kallon shi tayi tace "Ahh! Ai kai ke da Sannu me ciwon baki" be tanka ta ba, suka zauna jugum ita kuwa ta cigaba da tsintar waken ta, shi ko waige yake ta inda zai ga ta bullo, amma shiru, ko duniya zata nad'e ba zai iya tambayar Nene inda take ba" sun kusa minti 30 ba wanda yace ko 'kala, Nene ta yi Kamar bata san da kowa gun ba, sai 'yan wakokin ta takeyi masu kama da habaici (kuji min Nene kamar wata yarinya)haka ya k'araci zaman shi ya mike sai da yayi dan guntun tsaki kana yace "sai anjima" kamar jira take tace "mu jima da yawa" ya juya ya fita, ta bi bayanshi da gyatsine tace "Dunkum dangin Tsaka".

"Assalam Alaikum" ta fada cikin Siririyar muryar ta, Mami na zaune ta yi firgigit ta tashi don Nasiba ta gani tsaye gabanta da kwano a hannu wasu lokuttan tana rikidewa ta koma Rafee'ah, da Sauri ta amsa Kwanon Hannunta, ta rungumo tana shafa fuskar ta tana hawaye, Sandadar Nasiba tayi, ta kasa tabuka komai, chan Mami ta dawo hayyacin ta, da sauri ta ja baya tare da fadin "I'm so sorry, kina min kama da diyata, kiyi hakuri" Nasiba ta girgiza kai tace "lahh bakomai" ta jawo hannun ta ta zaunar da ita, suka gaisa, tace "Ummi ce tace ako miki" ta bude Coolern tana fadin me muka samu? Ahh Alkubus? Aikam Nagode sosai" ta dan ballo tasa a baki" gashi kuwa yayi dadi" Murmushi kawai Nasiba keyi, Ayman ta shigo parlon dauke da Doll babyn ta a hannu tana tafia dagwas dagwas, da alama tafiar batayi kwari ba, Nasiba ta tsura wa 'yar diyar ido, har Ayman ta tako kusa da Mami, Mami ta dagata sama, "Ayman baby na kin tashi? wa ya sauko dake daga kan gado? Yarinyar dai lafe wa tayi jikin Mami, Nasiba tace "Ayman sunan ta? tace "eh" Nasiba ta mik'a hannu tace "Zo nan Ayman" ga Mamakin Mami Ayman ta nufa gun Nasiba, Mami tace lahh kin ciri tuta, k'uiywa ne da ita, amma tazo gunki, ba ta yarda da kowa, ko gidanku mukaje bata yarda ta sauka k'asa zata mak'ale a jiki, daga ni sai Baban ta je daukan ta" Nasiba tayi murmushi tace "haka yara suke ai" Mami tace "to ya karatu? Wane Course kike?" tace "MicroBiology" "Allah sarki ajinki nawa?" tace "Aji na Daya" idon Mami ya kawo ruwa, Nasiba ta lura tace "Mamin Ayman lafiya?" Mami tace "you see, Diyata bata samu ta gama Makaranta ba, da ajinta biyu zata uku" Nasiba tace "Allah Sarki, Aure tayi ne?" Mami tayi murmushi ne ciwo, tace ta koma ga Mahalici, shekarar ta daya da rabi da Rasuwa" Nasiba ta rausayar da kai cike da tausayawa, tace "Allah Sarki Ubangiji Allah ya mata gafara, ya sa ta huta Amin" "Amin Nagode, shekarar ki nawa?" tace "19" tace "ita kuwa tana da Shekaru 20 ta riga mu gidan Gaskia, Shes just like you, ba wai kuna kama bane, aa, kawai ina ganinta a cikin ki, i see alot of her in you, shiyasa lokacin dana ganki i was so emotional, ki dinga sata a adduar ki kinji? Murmushi Nasiba tayi tace " InshaAllah, Ya Sunanta?" Murmushi Mami tayk tace "Sunanta Rafee'ah" zabura tayi ta zaro ido tace "Rafee'ah Habib Lema?" da sauri Mami ta gyada kai hadi da cewa "Eh itace, kinsan ta ne?".

_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

*Wannan Page din nakune Masoya _Nene Mamman(Nenen Seebi)_ Nene loves you all❤*

Pg4⃣3⃣

Nasiba ta fara sheshek'ar kuka ta nuna Mami da yatsa tace "kece Mamin Rafeeq?" da Sauri Mami tace "eh nice Nasiba, kin san Rafeeq ne?" Allahi Akbar da sauri Nasiba ta rungume Mami tana kukan farin ciki, Mami tarasa gane me Nasiba ke nufi da kukan da takeyi ne, daga bisani ta tsagaita kukan da takeyi, ta share hawayen ta, Mami ta tsura mata ido, tace "Nasiba me yasa ki kuka? Shin dama kinsan Rafeeq da Rafee'ah? Ki min magana ծiyata. Wani guntun tunani tayi ta girgiza kanta da sauri tace "aa ban sansu ba" ta mik'e da sauri tace "barin je gida Umminmu na Jirana" ba ta jira cewar Mami ba ta juya zata bar gun, da azama Mami ta rik'o hannun ta tace "Nasiba kar ki min haka, na san kina b'oye min wani abu, daga yanayin da kike a yanzu nasan kin san su, dukkansu, sanin da kika musu Sosai ne, ki fada min, Ya Rafeeq yake? Ba ta bari sun hada ido ba, murya na rawa tace " ni bansan su ba" haka kurum taji bata yarda da ita ba, akwai abin da ta ke 'boyo, ya zaayi da farko ta nuna ta sansu har ta na fada mata sunayensu yanzu kuma tace bata san su ba, ba zaiyiwu ba, yanda Nasiba takeyi ya nuna cewa tasan wani abu game da Rafeeq.

Ta kamo hannunta tace "Nasiba ke da Anan kadai ne gun Mahaifanku ko? Toh haka Rafeeq da Rafee'ah, na rasa Rafee'ah, K'addara ta rabani da Rafeeq, Ina sonsa sosai, ina so in san Halin da yake ciki, tun bayan tafian Uncle dinshi, bana samun Details yanda ya kamata, Misali Ummin ku ke cikin situation dina, zaki so ki ganta cikin matsanancin hali?" ta nuna zuciyar ta da hannu ta cigaba da cewa "You see dis heart of mine? Its Empty, you have no idea what i've been through, i mean what i am going through, i've Swallowed alot, ki taimakeni, Help a Helpless Mother please".

Nasiba ta isa gareta ta rungume ta, kuka takeyi sosai, ta dago ta share hawayen Mami, tace " Mami ki bar kuka, i will tell you everything i know about Rafeeq, da yanda na sanshi, Komai" jan Mami tayi har kan kujera, ta dauki Ayman ta sata a baya, da hijabin jikin ta ta goya ta, ta fara rirriga ta har ta koma bacci, ta kalli Mami tace "ina zaa kaita? Da hannu Mami ta nuna mata cikin daki, Nasiba ta kai Ayman daki, ta dawo ta zauna kusa da Mami.

"A Makaranta na fara ganinshi, shi da abokin shi Maalesh, ina tare da k'awayena muna neman abun hawan da zai maida mu Cikin Gari.............................................." tsaf ta kwashe komai da ya wakana tsakanin ta da Uncle Zaid da Rafeeq ta gaya mata daga ranar da ta fara ganin su har zuwa rana irin ta yau. Abu daya ta boye mata, Mafarkan da takeyi da Rafee'ah, bata gaya mata tana mafarki da Rafee'ah ba.

Mami tayi Murmushi tace "Its a Small World afterall, So kakar kice Nenen da Zaid ke ban labari? Wacce ta bashi kuka da daddawa?" kai Seebi ta daga, ta riko hannunta tana murzawa tace "Labarin da Maigadin Lema ya baki, dukda ba ki gaya min me yace miki ba, kin yarda zan iya aikata abun da ake zargina dashi?" Murmushi Nasiba tayi tace " Bansani ba, and i wont Judge you, but i know a responsible Mother wont do that at her Matrimonial Home" Murmushi Mami tayi tana jin son Nasiba har ranta, irin son da take ma Rafee'ah tace "kinsan lokacin da na fara ganinki, naji ina sonki, like i told you I see Rafee'ah in you, Nasiba shin zaki zama diyata? We'll you make me feel like a Mother again? Kuka Nasiba ta fashe dashi, ta rungume Mami ta na daga mata kai, tace "Mami nah, you are my Second Mom" kukan farin ciki Mami ta fara yi "Seebi na, ina sonki kinji?" nima ina sonki Mamina". Daria sukayi duka.

Nasiba tace "Ayman fa? Kin sake aure ne? Mami tayi murmushi tace "anya zan sake Aure kuwa? Bana tunanin zan so wani ծa namiji baya ga Daddyn su Rafee'ah" da sauri tace "Aa Mamina kar kice haka, ba me cire rai daga rahamar Allah, kar kiyi Mamaki zaki koma dakin ki, abu ne fa na Allah, bana so kina cewa haka kinji Mami na" Murmushi Mami tayi ta k'ara jin son Nasiba a ranta, tace "Rafee'ah-Aymana taci sunan Marigayiya Rafee'ah, Ayman diyar Zaid ce, be taba gaya miki yana da ծiya ba? tace "aa be fada min ba" Mami tace "Matar shi ta rasu Shekarar da ta wuce, bayan suna ta Rasu" cike da tausayawa tace "Allah Sarki, Allah ya gafarta mata, ya sa taci Albarkar Haihuwa, ita kuma Allah ya rayata" "Ameen Ameen" Mami tace "to kodai Yak'i gaya miki yana da d'iya ne don kar kice ya miki tsufa, ba kya son tsoho? Cike da kunya da jin nauyi tace "Lahhh Mami" tayi saurin boye fuskarta jikin Mami don taji maganar wani iri, ita kuwa Mami sai dariya take mata.

*Katsina*
"Shin Sallama ake ko fito? (whistle) inji Nene, daga bangaren shi ya buga tsaki da yaji muryan Nene, ji yayi kamar ya koma, don dai zuciyar shi na tunzura shi yazo ya ga Seebi da ya juya wlh, don Wulakanci ya daddage yayi Sallama amma sai tace yana whisir? Wannan tsohuwar na da damuwa, be bi ta kanta ba ya sake Sallama cikiciki, tace "Shin, an amsa maka ka shigo mana" tsaki yayi ya nufa cikin gidan, sanye yake da 3quarter, Nene na ganinshi ta chanza fuska tace "Touuu, nidai ince, nasan za'a rina naji sallama kamar fito, ashe su dunkum ne dangin tsaka" Ya kalleta sosai yayi kamar be jita ba, tace "ka tsareni da ido, to ai sai ka zauna ga tayani gulma nan" ya tsaya yana mata kallon rashin fahimta ta nuna mai kujera tace cewa nayi ga kujera ka zauna, guntun tsaki yayi ya zauna, yana kallon saitin dakin su, yana jiran yaga fitowar Seebi, Nene ta zauna kan tabarma kusan minti 15 be ce komai ba, da taga shirun yayi yawa ta daure tace "ina Malush?" shiru be amsata ba, a ranta tace ko dai be ji ni bane? Ta bude murya ta sake cewa "Nace ina Malush?" shiru ya mata, Nene ta bude baki cike da mamaki tana kallon shi, chan k'asa taji yace "Yana Kano" Lallai kawai tace tana jinjina kai. Shiru ya sake giftawa har fiye da na dazun, kusan minti 20.

A karo na uku (3) ya sake jin K'arar waya, tun dazun wayar ke ringing tana katsewa, k'arar wayar na damunshi, kuma shi yak'i tashi ya tafi, dan guntun tsaki yayi ya kalle ta yace " Wai ba karar Waya nakeji ba?" Nene ta hau salati, tace "kai don Manzon Allah? Wai wayace? Yo tun Shekaran jiya nake jin irin k'arar nan banyi zaton waya bace, wai ashe wayar Nasiba ce" be dai ce da ita komai ba har wayar ta sake ruri, cigaba da surutu tayi tana bashi labarin yanda takejin k'arar wayar kullum, ta ma mance rashin jituwar su, yace "ai sai kije ki dauko ga wayar chan an sake kira" da gudu ta ruga daki, amma kafin taje ya katse, kan Wardrobe ta ciro wayar, tun randa Nasiba ta bata wayan ta aje a sama ba ta sake bi ta kan shi ba, ta fito da wayar a hannu ta mika ma Rafeeq "kaga dunkum, duba min kagani waye? Kamar bazai amsa ba, sai da ya gama kallon wayar a hannunta kafin ya amsa, ya jujjuya wayar a hannun shi, a ranshi yace "Tecno, sai k'arar tsiya" ya bude wayar, 34 Missed Calls ya gani, accordingly ya duba Missed Calls din, Abbina Uncle Zaid, Ummina, Ya-Maalesh Miemee, Usheey, Hamma na, a ranshi yace Hamman ta? Messages ya duba, Daga na Uncle Zaid, sai na Maalesh sai wanda ya mata, a sama yaji muryan Nene, inda take cewa "Shin zaka gaya min wanda ya kira ko sai ka gama latse latsen wayan, ko no engilish? Guntun tsaki yayi, da kyar yace "wai Abbi" tace "Mahammadu ne, baban Nasiba latso min shi" a ranshi yace wa ya tambaye ki? Ya mata dialing numbern, ringing daya suka dauka, cike da doki tace "Halo, Mahammadu ya kuke? Yanda Nene ke waya zar takaici, kamar bakauyiya, hakan yasa shi mikewa don tafia, ya kalleta yanda take daria, a hankali yace "kina da matsala" karaf kan kunnen Nene, tace "da wa kake? Ni ke da matsala? Matsalar ubanka?" be tsaya bi ta kanta ba ya fice daga gidan, ta bi bayanshi har zaure, "tsaya mana, rasa kunya beran kitchen, da ba don ina kunyar Zaidu bawan Allah ba yau da sai na maka mugun duka, in maka lagalaga, in kuma kai ka Asibiti, yanda kayi jiyyata nima inyi jiyarka dan banten uba" kwatakwata ta manta da wayar da takeyi. Su har sun gaji da Magana sun kashe. Ta dawo ciki tana mita, ta kafa waya a kunne, Hello, daidai nan Seebi ta sake kira da wayar Abbi, a firgice Nene ta cire wayar daga kunne don k'arar ya cika mata kunne, ta latsa wayar ta kafa a kunne, tace "hallo Mahammadu" Seebi tace "Nene na nice" cikin masifa Nene tace "to dan kece sai ki dod'en kunne da kira?" Nasiba ba ta damu ba tace "ke da wa kike fada, naji kina ma wani masifa?" nene tayi tsaki tace "ni da wannan dunkum dangin tsakan mana, wai ni zai kalla yace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login