Showing 102001 words to 105000 words out of 149166 words
shiga mota ya bi bayan Rafeeq a guje.
A tare suka iso Kaduna, Maalesh ya kira Uncle Zaid yace "mai ya iso, gashi zai k'araso gidanshi" Uncle Zaid yace"Aa Mahmud bana gida, ina Gidan Maminku, kasan Malali ai? Yace "eh" "to in kazo ka kirani" yace "toh" ganin Rafeeq yayi hanyar Malali ya san cewa chan ya nufa ba tare da ya kira Uncle Zaid ba ya bi bayan Rafeeq har suka iso gidan Mami.
*******
A tare suka shiga gidan Mami tafito ta hadesu duka ta rungume, tana me murnar ganinsu duka, Ta ja hanayensu har parlo ta zauna, ta kallesu tace "Ayman na bacci kafin ku isheni da tambaya" murmushi sukayi a tare.
Zaid ya iso ya gaisa dasu ta hanyar musabaha, yace "ya akayi ka gane gidan Mahmud? Ya danyi shiru sai yace " na bishi a baya ne" Mami ta gabatar musu da abincin da ta dafa musu, nan Rafeeq yafara narkewa wai yayi tuk'i hannun shi na ciwo,sai dai ta bashi a baki, haka mami ta biye mai ta dinga bashi abincin a baki, Zaid da Maalesh sun saba ganin haka a gunsu kafin abubuwan su rinchabe, har suka gama.
Zaid ya kallesu duka yace "Ku saurareni, na son kuna mamakin dalilin da yasa nake nemanku ko? To lemme go straight to the point, ina lura da kalan kallon da kuke wurgar junanku dashi, ina sane da ba kwa magana, ina so ku sanar dani meye damuwar ku? Meye matsalar ku? Meye dalilin da ya sa abunda bakuyi shi a yarinta ba kuka fara shi da girmanku? Ina nufin meyasa kukayi dambe jiya? Ku bani amsa" Mahmud me ya hadaku? Maalesh ya kalli gefe yace bakomai Uncle Zee, ya juya ga Rafeeq ya tambayeshi, sha amsar kenan da ya bashi, ba yanda Zaid be yi ba don ya ji musababbin yin fadar su amma sunki bashi dama, sunki gaya mai komai. Mami tace "Ina ga tunda sunk'i magana ba sa son mu san meke tsakanin su ne, they chose to leave it to theirselves, nidai abu daya zance muku, you guys grew up together asif you're Siblings, dalilin ku Families din mu suka zama best of Friends more of relatives, and now kun dauko wasu halaiyar da ba naku ba? Bansan meya hadaku ba, bansan waye yafi gaskia a cikinku ba, but what ever it is, Fix it, kar in sake ji, kar in sake gani, idan na sake naji kun sake Dambe kai ko chachar baki ne zan sa6a muku sosai, kunsani ni ba bakuwar ku bace, i wknt take this, ina so ku shirya kanku right away". Ta tashi ta shige daki, Zaid ya zira key dinshi shima ya fita waje ya rage su biyu ne kachal a Parlorn.
Kusan mintuna 20 ba wanda yace ma wani k'ala, ba me niyyar magana, kamar daga sama Maalesh yaji maganar Rafeeq cikin sanyin yanayinsa, inda yake cewa "You asked me why? I will tell you why, Everything is because of Uncle Zaid, Saboda Uncle Zaid, i cannot love Naseebah, because of Uncle Zaid i cannot accept that i love her, because of Uncle Zaid i cannot let my feelings out. That is why Lesh, thats the reason". Maalesh yayi murmushi yace "nasani Feeq, amma kasani ban bar maka Seebi ba don ka bar ma Uncle Zaid ba, na bar maka ne saboda i want you to have her, na son kafini sonta, kafini bukkatar ta, kun dace da juna, AKWAI LOKACIN da zai zamana cewa Seebi ce farincikin ka, ko da yake itace farincikin ka. Idan har baka yi abunda ya kamata ba, wato ka sanar da ita abunda ke ranka, you'll leave me no choice But to compete with Uncle Zaid, don ni kai na bar ma wa, ba shi ba, because i love you, i want the best for you, you've suffered and gone through alot, now is your time to be Happy"
Wannan murmushin nan nashi na gefen baki dai yayi yace"Oh Maalesh, ashe kana so na har haka, okay listen closely, Uncle Zaid Mahaifina ne, shi ya rada min suna, duk wani wahalana Shine tun ina karami, har girma na, hakan ne yasa Babana yake min lak'abi da Ibn Zaid, Uncle Zaid na son duk wani farincikina, yana gudun bacin rai na, da wannan k'addarar ta fada a kaina, he's the only person that never thought of giving up on me, he stood by my side through my worse and rough times, he understands me better than anyone, he never judged me, he tolerated me, he took care of my Mom,he's done alot for All of us and Sacrificed alot. Ka gaya min Lesh, ya kamata in so abun da yake so? Ya kamata in yin butulci akan hallarcin da ya dade ya na min tun ina zanin goyo? Ya kamaceni da in so kaina har haka? Wallahi i can give my life up for him, i can Sacrifice my happiness for him, balle Naseebah" ya danyi guntun murmushi yace "Uncle Zaid ya fini sonta, ya fini kaunarta, ya fini buk'atar ta, ko don Ayman, da take buk'atar Uwa, i'm sure Naseebah zata kula da ita kamar diyarta" muryar shi na rawa ya danne ya koma zolayar yace "in banda abunka ni ai ban isa aure ba kasani ka girmeni fa yet you are just 25, i am jusy going to waste her time, shikuwa he's ready, kuma zai kula da ita fiye da yanda wani zai kula da ita" chan kuma ya koma magana dagaske "I love Uncle Zaid, i want the best for him, Lesh, help me do this please" Maalesh ya ja dogon numfashi ya sake, yace "Gaskia ne, Uncle Zaid ya chachanci fiye da haka, Alright, Uncle Zaid can have Seebin Nene" Murmushi Rafeeq yayi ya rungume Maalesh tare da fadin "Thank you, brother from another mother" su ka dinga bubbuga bayan juna. Rafeeq be ji wani darr din gaya Maalesh maganganun nan ba, don yasan Su hak'a su burne ne a gurin ne ba me jin zancen nan, He's sure Maalesh ba zai gaya ma kowa ba.
°°°°°∆∆∆°°°°°
Mami ta fito daga daki, ta gama jin zancensu, sun dan firgita ganin ta fito, ta zauna a tsakiyar su, tace "dama abunda ya hadaku kenan? Ta shafa sajen Rafeeq tace " I am proud of you R-Lema you are indeed your Father's Son, Ina Alfahari da kai, kasan cewa koda son Seebin Nene zai kasheka ba zan taba baka goyon ba, ba don komai ba sai don Zaid, Rafeeq gaya muku yanda Zaid yake a gurina bata Lokaci ne, amma zan baka tabbaci daya, banda Iyayena, Zaid ya fiye min kowa da komai a duniyar nan, Zaid ya sharen hawayena da kukana, Zaid ya tsaya dani lokacin da nake bukattar wani ya tsaya tare dani, I cannot ever repay him for what he's done to me, Rafeeq nafi son farinicikin Zaid akan naka, akan nakowa ma" ta daga hannayenta sama tace "Allah na gode maka da ka bani d'a mai hankali da tunani, Allah nagode maka da baka bari son zuciya ya rufe mai ido ba, ta riko hannunshi tace Thank you Feeq, nagode da baka tsaya competition da Kawun ka ba, You sacrificed Love for Family, remember thats what you do for your Family, ka zamto Fitila k'ona kanka ka haska wani ,ina Alfahari dakai Rafeeq Habib Lema" Allah ya muku Albarka duka, ta rungumesu tana hawayen farinciki.
*KATSINA*
Dadi tamkar ya kasheta ganin ta gama hada So6o da Shinkafa da miyan Vegetables din ta da ruwan Asirin da ta amso, a ranta tace "Yau Alhaji sai yanda nayi dakai" ta gyara zaman dankwalinta dama taci kwalliyarta ta dauki tray tayi hanyar Parlorn Alhaji Habib dashi. Ta shiga da Sallama, Sandarewa tayi sakamakon ganin Nene da Alhaji Habib zaune a kan Carpet inda Nene ke k'ara zuba mishi danbun Tsakin masara da yaji Gyada da Zogale a ciki dama har, ya cinye plate guda wannan k'ari ne, parlorn sai k'amshin Danbu yakeyi Saude ta k'araso da masifa "me zan gani haka? Alhaji ga Abincinka nan na kawo maka fa?" yace "Saude karki damu, Nene ta min Danbu, ba zan iya tuna last dana ci dambu ba, wallahi yayi dadi, kema you should eat" ta kallesu kallon wulakanci, ta dai daure tace "ga Sobo nan kasha toh" bakinshi cike da dambu yana tauna ya na nuna mata wani jug din da ke gefe yace "ai Nene ta min Kunun Zak'i bakiji dadi ba, ko zaki sha" Waiyo takaici kamar ya kashe Saude, ji takeyi kamar ta runtuma Ihu, tsohuwa ta tsaneta kamar me, ji takeyi kamar ta kasheta, fuuu ta koma kitchen ta dire tray din tana huci kamar Zakanya.
*Kaduna*
Abii ya ji dadin ganin su Maalesh, ya kuma ji dadin ganin Chanji sosai gurin Rafeeq, Abi yace "Ko kunje gurinsu Nene? Suna lafiya ko?" subul da bakan Maalesh ne ya gaya mishi maganar gobara, Ummi da Abii suka sake salati, basu san da zancen ba, "ince dai ba abunda ya samesu? Ba su gaya min ba wallah, kuma yawancin kullum sai munyi waya," Rafeeq yace "Lafiyan su kalau, suna nan gidanmu, Daddy ne yace kar a gaya muku saboda kar a tashi hankalinku, kuma ai ya sa an fada gyaran gidan, so please kar ku tada hankulanku" Abbi ya jinjina kai, yace "to ku yaushe zaku koma Katsinan?" Maalesh yace sai mun kai Jibi ko Talata" "to shikenan in ba matsala ina so in biku don kwanciyar hankalina"
*Katsina*
Bata hak'ura ba, ta sake daura ma Mijinta abincin Dare da ruwan maganin nan, Tuwon Semovita ne miyan Kuka, bata taba mishi ba da hannunta sai dai ta sa ayi, amma da yake yanzu bukatar ta take so ta biya ta zage ta tuke tuwon nan sosai. Bayan Sallar Isha'i ta kwashi kayanta a tray ta nufi parlorn Mijinta, ranta fadi k'al don bata ga gilmawan Nene ba, don ma damar nan da ta samu duka ruwan magamin ta juye a cikin tuwo da miyan, ta shiga da Sallama. Damm kakeji alamun fashewar Tanagaran, Saude ce ta sake Tray din da ta dauko sakamakon ganin Nene da tayi zaune kan kujera Alhaji Habib kuma daga gefe ya na ta zak'ar danwake. Fuuuu ta tako gunsu idonta ya rufe ta shiga zazzago ma Nene masifa "Wai meye haka ne? Wai ba za ki daina dafa ma Mijina Abinci ba? Meyasa kike yin aikin da ba naki ba? Hakkina ne in kula da mijina, cinsa da shansa sun rataya a wuyana, ki tsaya a matsayinki na Alfarma da aka muku na wurin zama, zak'ewarki ta fara wuce gona da iri" Alhaji Habib yace "haba Saude, ina laifin wanda ke kula da naka? Menene laifi don Nene ta bani Abinci?, kin tsaya kina mata rashin kunya, kar ki manta bake ba ko ni ta isa ta haifa please ki kula" Saude ta shiga tafa hannayenta "Wonders shall never end, Alhaji you are making me feel like i am sharing You with this Old thing" chan kuma ta saki daria tace "Ehwo, kar dai son shi kike? In sonshi kike kuyi aure mana a raba mana kwana kowa ta san matsayinta, don naga shishigewar ta yi yawa" sai a sannan Nene tayi magana tace "Yaro Man kaza, Saude kenan, ai ke baki isa in hada miji da ke ba, da kinzo lokacin da nike Aminene Mamman da bakiyi kuskuren yin zancen nan ba, kuma da yanzu misali zance zan auri Mijinki Wallahi ko iskar da ya debo ki ba zai kalla ba, ba zaki iya Kishi da ni ba, don indai bariki ne baki sam hanyarta ba, ni na biya Allo na, kuma na wanke shi, ki kula ki san kallar maganganun da zaki man" ta na kaiwa nan ta wucewarta don in ta tsaya tana iya kaima Saude Hannu, kuma ba zataji dadi na idan Alhaji Habib ya bar ganin kimarta. Ran Daddy bace yace "Saude are you out of your senses? Meya shiga k'wak'walwarki da har kika iya yin maganar nan, You are unbelievable" ya buga tsaki ya wuce daki shima, ita kuma Saude ta durkusa ta rushe da wani irin uban kuka.
7:14am
Tunanin ta ta Ina zata fara shiga dakin Daddy har ta soma bincikar dakin bata tare da an ganta ba? Dabara ta fado mata ta mik'e ra shiga parlorn Daddy da Sallama ta ganshi Zaune da Nene suna Karin kumallo, k'osai ne da koko, Seebi na mamakin Nene yanda tayi katokato tayi kanekane tayi kakagida da kula da Abincin Alhaji Habib kamar itace matar shi, ta girgiza kai ta gaidasu, ya amsa mata cikin sakin Fuska, tace "Daddy ina fatar kana jin dadin Weekends dinnan" yace "Sosai ma, Nenenki tana cika da Abinci, baki ga har na fara tumbi ba" Nene ta chafe ai ni nan da ka ganni, ba daga baya ba na iya kula da mutane" Seebi ta kawar da Zancen kafin Nene ta 6allo musu ruwa tace "Daddy grant me the priviledge to make your room for you,i've been doing nothing ever since our stay, please dont say no" Nene tace "Uban me kike cewa? Ta danyi yak'e tace cewa nayi ya bani dama in gyara mai daki tunda yau Lahadi ba abunda nakeyi" Nene ta yashe hak'ora tace kinyi tunani" yayi murmushi jin dadi yana ganin Nasiba kamar Rafee'ah, yace "Seebi, you are my Daughter, like Rafeeq, kina da damar shiga inda ranki yakeso da sanda kikeso a gidan nan, balle dakin Daddynki, ki shiga ki gyara mun kinji?" Nasiba tayi murmushi ta shiga tana godia ga rabbi.
"Oh Allah make it easy for me, Allah ka taimakeni ka nuna min abunda nake nema, ta shafa adduarta" nan ta fara da kewaye ta wanke toilet din tas, bayan ta duba duk lungu da sak'on Kewayen bata ga Komai ba, ta dawo daki, bata tsammani za a saka Wani abu a cikin Wardrobe, nan ta hau neme neme daga nan daga chan jawo nan, jawo chan, wayam, har ta fara gajia ta shiga gyaran Gado, haka kurum hancinta ya jiye mata wani wari, ta shiga shinshine shine, tayi Imani warin nan daga k'ark'ashin Gado yake, da k'yar ta samu ta daga katifar gadon me nauyin tsiya, gabanta ya fadi da ta hangi wani yar k'aramar tukunyar k'asa da aka daure da wasu zare, jikinta ya hau rawa, ya zatayi yanzu? Nan ta shiga karanto adduar da ta shigo bakinta tana k'arafafa ma kanta guiwa is now or never, Dole tayi jihadin dauko ko menene, nan ta samu wani kwarin guiwa tayi bismillah ta dauko tukunyar nan,da k'yar ta samu ta maida katifar tayi laying dinshi duk hankalinta baya jikinta, tayi saurin saka tukunyar a dustbin din dakin ta fita, har yanzu suna Zaune inda ta bar su, baki na rawa tace barin je in dauko zubar da bolan nan sai in kunno turaren kamshi, Daddy yahi murmushi yace "Bless you My Child" Kallo daya Nene ta mata ta san bata cikin hayaccinta batayi yunkurin binta ba, Hijab tayi sauri ta saka ta fita daga cikin gidan, jiki na rawagudu gudu sauri sauri ta bar gidan, ko lura da Baba maigadi batayi ba, ta samu Keke Napep. Da k'yar ta lalubo magana "Arriyadh Islamic Medicine zanje" yace "ki shigo" suka hau titi jikinta be bar rawa ba, cikin ikon Allah isarta tayi daidai da zuwan Mallam Usman, ya kalleta yace "Nasiba lafiya naganki da sassafen nan? Ince dai Rafeeq lafiyar shi lau?" bata iya bashi amsa ba sai dai ta mik'a mai dustbin din hannun ta, yana lek'awa ya shaidi Tukunyar nan ta tsafi ne, ya kalleta yace "ki kwantar da hankalinki Nasiba, you are safe, no harm may come to you here" Ajiyar Zuciya ta sake me k'arfi, mai gadi ya bude musu Asibitin suka k'arasa tare, wani daki ya shiga bayan ya umurce Seebi data tsaya waje, Mallam yayi 'yan adduoin shi tare da sakin wannan tukunyar kasa, nan take tukunyar ta fashe, wani ruwa me doyi tare da wasu kadangaru suka gani guda bakwai, kandangarun masu rai, k'okarin guduwa sukeyi Mallam ya shiga Karatun kurani mai girma, amma idan yayi nan sai wasu suyi chan a guje, be so su bar dakin, don in suka bar dakin akwai Matsala, Tun Mallam na fafatawa da kadangarun nan har ya fara gajia, ya dan bude murya yace "Mallam Salis dauko mun recorder din nan ka kunno ta ku ku're volume" jiki na rawa Mallam Salisu ya nufi office din, ganin kamar zai bata lokacine mallam ya vigaba da karanto Amanar Rasulu, Wani k'arfin guiwan da bata taba ji ba yazo mata lokaci daya, bata san lokacin da ta bude dakin da Mallam Usman ke ciki ba ta shiga tana karanta Ayatul kursiyy da karfi, tana kaiwa k'arshe ta bi Mallam da karatun Suratul Jinn suka hada baki wurin karatun nan, cikin ikon Allah K'adangarun nan suka fara wani irin ihu, chan suka fara fashewa sai kuma suka fara ci da wuta, Mallam da Seebi basu bar karatu ba, har sai da suka k'one kurmus ko toka ba'a gani.
Daidai lokacin da Alhaji Habib yaji kanshi ya mai nauyi ya mike tsaye tare da rik'e kai, Ya fara ganin Nenen bibbiyu, dakin na juya mai, abubuwan da ya mance su yake tunanowa chan kuma ya zube k'asa, kuma sai ya tashi a zabure Dda k'arfi yace "AISHATU".
_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
Pg5⃣5⃣
Nene tace "Alhaji Lafia? wacece Aishatu?" Alhaji Habib ya k'ura wa Nene ido kamar me son tunano wani abu, cikin sanyi yace "Ina zuwa Nene" ya zura takalman shi, ya wawuro