Showing 126001 words to 129000 words out of 149166 words

Chapter 43 - Ke alkhairi ce COMPLETE HAUSA NOVEL

BIEBIE   

22 Oct 2024

25728

ta rasu ta bar diya, kuma na san ba zata so diyarta ta sha wahalar Matar Uba ba kamar yanda kika ce, zata so ke ki kasance tare da ita, da Mijinta, Shawara ce"
Shiru tayi Alamun maganr Mahaifinta ya shigeta, Umma ma ta sake k'arfafa mata guiwa, Abba yace "Maza Autan mata, je ki kuyi magana kinji" cikin kunya ta tashi ta fita.
Zaune ta ganshi yana bin hotunan Parlorn da ido, nan ta samu ta k'are mai Kallo Tsaf, Haddade ne son kowa kin wanda ya rasa, ya hadu iya haduwa, komai na sa yayi, to meyasa zata ki'sa? A hankali ta k'arasa tare da Sallama, ya amsa tare da mikewa ya na wurga mata Murmushi, ya karaso kusa da ita, tana tsaye har suna jin hucin juna, yace "So??" cikin sanyi ta tace "You like smilling alot" Murmushin ya sake sakar mata yace "Dont i have reason to Smile? I'm with you afterall" Murmushin kunya takeyi, yace "So? Will you Marry me?" a hankali tace "Yes i'll Marry you" Murmushi suke sakar ma Juna, ji sukayi kamar sun shekara da haduwa, wani So da kaunar junansu ke shiga jinin jikinsu, wani Shaukin k'auna ke shigar Zaid, be taba jin wannan yanayin a tare dashi ba. Ta samu kwarin guiwan cewa "Mu zauna" suka zauna su ka tsura wa juna Ido, a hankali tace "Yaushe zan ga Ayman? Yace $whenever You are ready" tace "A shirye nake yanzu" yayi daria yace "yamma yayi, ki bari Gobe sai muje ko? Alright?" ta gyada kai cikin murna.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Zaid Matar da zaka aura nan da Sati Biyu fa?" cewar Abba, Zaid yace "Matar Rafeeq ce, Rafeeq zata aura" duk suka kalleshi suna neman karin bayani, Abba yace "Toh a katin daurin Auren da a ka kawo min sunanka ne a jiki" Zaid yace hakane, amma abun da ya faru shine ita yarinyar da Yaro na suna matukar son junan su, cikin rashin sani aka sa ranar da ni, Ko da Allah be kawo min Zainab ba, gaskia na fasa Auren yarinyar, don D'ana take so bani ba" Karaf Zainab tace "Kai fa? Kana sonta?" duk suka bita da ido, itama sai taji kunyar maganar da tayi, yace "Ina sonta, amma sai bayan haduwar mu dake na san cewa irin son da nake ma Rafeeq nake mata, ba irin So na Aure ba" wani dadi ya lullube ta, Abba yace "Toh yanzu ya kake so ayi?" yace "Abba, so nake in gabatar da Maganar ga Yayana, sai a hade Auren da na Rafeeq din nan da Sati Biyu" Abba yace "Wannan gaggawa haka?" Zaid yace Abba ba Gaggawa bane, saidai in kana da bukattar yin bincike a kaina, sai ayi abu a tsanake " Abba yace "Haba Zaid, bincike na me? Zaid ai kai ba bak'o bane, mun sanka mun san kai ko waye, ba sai anyi bincike ba, ba komai zamu shirya nan da Sati Biyun, zan kira kawunta in sanar dashi, Allah ya sa Alkhairi". Sosai Zaid yaji Dadi yace " Gobe InshaAllah zanje Katsinar don yi magana da Yayana da Magabacin mu" "Allah ya kaimu" inji su Umma, Cikin In ina Zainab tace "Abba nima ina so inje Katsinar don ganin Aymana" Abba yace "Toh uwar azarbabi, ba inda zakije, ki bari har ya kawo miki ita" "Abba Please kar ka hanani, kaga ban taba haduwa da ita ba, i cant wait till two weeks, Please Abbana" Abba yace " "Abba zuwan ta zai taimakeni gurin yi ma Yayana bayani, a yi hakuri a barta taje" Abba yace "I know she's safe with you, Allah ya kaimu goben ya kuma tsare Hanya" Zaid ya ji dadi sosai sukayi Sallama da niyyar Gobe zasu wuce Katsina.

WASHEGARI
KATSINA
(Sorrynku, ku cigaba da min uzuri, Same excuse din dai ne, zaa cigaba daga nan InshaAllah)

👧KE ALHERI CE🙇‍♀

     NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

CIGABAN5⃣9⃣

Gaba ki dayan su suna Zaune a Parlorn k'asa suna lunch, Ayman na kan cinyar Seebi ta na bata a baki, ba tare da ya kalleta ba yace "Dame dame zaki buk'ata a hidimar bikin?" a takaice tace "Nima bansani ba" ya tsagaita cin Abincin ya kallota kamar ba zaiyi magana ba chan yace "bangane baki sani ba, ba naji wannan friend dinki tace meye meye ba" Mami da Daddy da suke binsu da ido suka kalli juna suja bata baki, sun lura da Rafeeq yanzu abu kadan yake harzuk'a shi, Mami tace "Rafeeq, ai ba haka akeyi ba, ba da ita ya kamata kayi magana ba, ai ga Aneesa nan, ko kuma friends dinta zaka sama sai kuyi maganar komai" ya dan bata rai "Ni ba wurin wata da zanje, suna da Hayaniya gasu da damuwa, Bari zan ma Lesh magana, sai ya same su" Nene dai ta ta6e baki, ba ta son tanka musu, don yanzu zata sake layi shiyasa tayi shiru".
Sallama Zaid yayi a tare suka amsa, ya kusto kai yayi dining area inda yake jin surutan su da karan plates da chokula, Daddy yace "Zaid, kaine a tafe? Kai ba kajin sintiri a hanya ko? Ka dauki hanyar Katsina zuwa Kaduna kamar Tafiyar minti 30, kai ba ka gajiya ne? Kullum kana hanyar Katsina, shekaran jiya fa ka tafi" Nene tace "Yanzu dai ya iso Lafiya, ai shikenan, Mita na ne? ya ajiye Mata ai dole ya ke zuwa ganinta ko" Yak'e kawai Zaid yayi, Mami tace Sannu da Zuwa Zaid, Aneesa da Seebi sukace "Sannu da zuwa Uncle Zee" ya amsa cikin sakin Fuska, Rafeeq ya dago kai suna masu hada ido da juna, ya sakar mai da Murmushi Yace "Kazo Lafiya?" "Lafiya lau Boy" Mami tace "Oya Zauna ka kwashi Gara, nasan kana nan da yunwa" yace "Eh Mami, amma ba ni kadai bane, mu biyu ne" "kai da waye? Ka barshi waje? Haba je ka shigo dashi" Murmushi yayi ya fita, suka cigaba da cin abincin su, chan ko sai gasu sun shigo, Zaid a gaba, Zainab a baya tana tafe sum sum, sanye take ta Hadaddar Jallabiya, K'amshin turarenta ya sa su dagowa gabaki daya suka zuba mata ido, Zaid na zuwa ya sa Hannu ya dauki Ayman ya mik'a ma Zainab ita, Zainab ta amsheta ta rungumeta take taji hawaye sun fara bin kuncinta, abun mamaki Lamo Ayman tayi a jikin Zainab, bata yi mata k'uiwa ba, Sosai ta matse Ayman a jikinta tana jin so yarinyar har 6argonta.
Nene tace "Zaidu bawan Allah, wannan fa?" yayi Murmushi ya kalli Mami yace "Sister din Marigayiya Safiyya ce, shekaran jiya ta dawo daga Makaranta" Allah Sarki inji Mami da Alhaji Habib, Sannun ki da zuwa, kun sha hanya, ya su Mamarku? Ya kuma k'arfin hakuri? Allah ya ji k'anta ya rahamshe ta" Zainab ta amsa gaisuwar Mami, sannan ta Mata gaisuwar Rafee'ah, ta gaida Nene ds Alhaji Habib, Seebi da Aneesa suka gaidata, with a big smile on Rafeeq's face ya gaida Zainab, farat daya ta mishi, ko don ta na son Angel dinsa ne? Matashiya ce da ba zata wuce Shekaru daya da shi ba, 24 zuwa 25.
Mami tace "Zauna kinji Zainab mu ci Abinci" Zaid ya Ja kujerar baya ta zauna shima ya zauna don cin Abinci.
Bayan sun gama cin Abinci suka hadu a Parlor, Ayman har tayi bacci jikin Zainab, Zaid ya kalli Alhaji Habib da Mami, yace "Erhm,Yaya, Mami, dama na kawo Zainab ne don taga Ayman da kuma in sheda muku cewa zan aure ta, ba wai don tana k'anwar Safiyya ba, aa saboda dai ina sonta" Rafeeq ya zaro ido yana mamakin furucin da Uncle Zee keyi, Mami ta dan razana a ganinta kamar cin fuska ne ga Nasiba, ace tun Kafin Aurenta har an fara maganar yi mata Kishiya Mami ta k'irkiro Murmushi, Daddy ya yi ta maza yace "Zaid, ina ganin ai kamar its too early, ya kamata ku k'ara fahimtar junanku, da ka bar wannan maganar an cigaba da Maganar ka da Nasiba, nan gaba sai ayi maganar Zainab din tunda ka nuna kana sonta, mu kuma abun da kake so zamu maka" Gaban Zainab ya yanke ya fadi, kar mutanen suk'i amincewa da ita, gashi ta bari Son Zaid ya mata Kamu ba na wasa ba, har ta fara tausayin kanta. Jin muryar shi tayi yace "Aa Yaya, zan aureta in the next two weeks, ba zan iya bari har mu kai wani lokaci ba tare da juna ba". "Kai Zaidu Bawan Allah kalle ni nan, ni tsarar kace? Ko don kaga ina daga maka k'afa shiyasa kake son Takani? Seebi ta maka kama da wacce zaka Wulakanta? Kai ka samu farar mace ko? Dangin larabawa zaka ma Seebina Wulakanci? In banda Wulakanci ya zaka fara maganar Auren wata tun kafin ka aureta? Don cin fuska kace rana daya zaa daura? To wallahi ka fita idona in rufe, ban ta6a watse maka karama ba, banso in fara yau, ina ganin girmanka, ka ja dan gemunka kayi fatali da wannan magana ta auren wata" Seebi ta dago cikin nauyin baki tace "kiyi hakuri Nene, ba komai Wallahi, bakomai don ya aure mu Lokaci guda, Uncle Zaid Allah ya sa Alheri" "ke dallah rufe min baki, me kika sani, banza samna kawai, in banda banza wa ke bada goyon baya a mata Kishiya? Bazan hanashi Aure ba, amma saidai ya zabi daya, Saidai a fara daura Aurenku in kin haihu yana iya Auren" Nene ta karashe ta na me hararar Zainab da ta gama tsorata da Nene, Mami tace "Kiyi hakuri Nene, da Nasiba aka fara Sa Rana, da ita zaa fara daure Auren"
Zaid ya dafe kai yace "Nene wallah ban isa in Wulakanta Nasiba ba, ya zaayi in Wulakanta ta? Ina mata tanadi ne, tanadin da zata fi kowa Farinciki da faruwar shi, ina so taji dadi har karshen rayuwarta, na sa ma mata wanda zai so ta ya kula da ita fiye da ni, na gano wanda ya fi ni sonta, na kuma gano ina ma Nasiba So irin na Uba da Diya ne" Seebi da Rafeeq suka tsura ma Uncle Zaid ido, Rafeeq fargaba ce, fargaban wanda Uncle dinshi ya samo ma Nasiba, Nene tace "Zaid me kake nufi ne na kasa gane komai, meyasa kake maganar Wani bayan ga ka?" a takaice yace "Saboda ba ni zan aureta ba" duk suka ware ido "Rafeeq zai aureta, Ya fi ni sonta, ya fi ni k'aunar ta, kuma zai kula miki da ita fiye da zatonki" Nene ta murtuk'e fuska tace "Waye Rafeeq?" Zaid yayi Murmushi yace "Dunkum Naki" Nene ta dafe kirji tace "Allah ya tsari Kakata Laminde, Dunkum din zan baiwa Nasiba, koo a mafarki" kan Rafeeq a k'asa, ya shiga duniyar tunani, son Uncle Zaid na ratsa shi, Uncle Zaid ba zai ta6a hutawa ba sai ya mallaka mishi Seebi, da me zai saka ma bawan Allahn nan?.
Ai Nene in gaya miki, Dunkum dinki na son Seebi yanda baki tunani, kuma nagane ta na sonshi, shiyasa zan aura musu junan su, kuma kinsan kin fi son farincikinta fiye da na kowa ko? to Rafeeq ne farincikin ta, kar ma ki shiga tsakani don tun Asali Seebi bata taba so na ba, tana dai ganin girma na ne shiyasa ta amince da Aurena, in kin musa gata ki tambaye ta" Nene ta kalli Seebi, tace "Ke Seebi wai haka? Wai dunkum kike so" Nasiba ta daburce ta fara girgiza kai alamun aa,bata san yanda aka gane cewa tana son Hamma Rafeeq ba" Nene tace "magana zakiyi ki na gyada kai kamar k'adangaruwa" Nan ta k'ara rudewa, "E- aa, aa bana so" Nene ta ta6e baki, tace "Ja'ira, ba ta iya k'arya ba, duk yanda tayi k'arya sai ka dagota, Aishatu son shi takeyi Wallahi, amma kin bada ni wallahi, ki rasa wa zaki so sai Dunkum? Dunkum fa Seebin Nene, yo ni ko a k'afa aka daura min Dunkum ai sai na kwance" Rafeeq ya dago kai ya kalli Nene, suka galla wa juna harara.
Zaid yayi murmushi yace to Alhamdulilah yanzu dai Tare zaa daura Aurenmu, sai A fara Shirye shirye, Daddy yace "Zaid think of what you are doing, ya zaayi Rafeeq yayi aure yanzu? He will only hurt her with his attitudes, dont do this" Zaid ya kallo yayan shi yace "Yaya, this is my descison, Rafeeq is My Son, and i can get him Married whenever i want" Alhaji Habib ya ja baki yayi shiru, Mami ta dan ji wani Sanyi a ranta da abu yazo da sauki da haka, dama bawai ba ta son Rafeeq da Seebi bane, aa tana dai Son saka ma Zaid hallacin da ya mata. Zaid ya ma Mami ido, Mami tace "Zainab tashi mu shiga ciki ko? I know you must be tired" Zainab tayi Murmushi Ta mik'e Aneesa ta karbi Ayman da ke bacci a hannunta ta hau da ita sama din kwantar da ita, Daddy ya bi bayan Mami, Zaid ya Mik'e yace "bari naje na dan watsa ruwa donAllah Nene ki dan kwada min Zogale yanzu" Nene ta galla mai harara Zaid ya fice yana daria.

Baka jin komai sai k'aran Ac din da ke Parlorn, kamar ba wasu hallittu a ciki, tana nan durkushe a k'asa, shima daga dayan gefen yana durkushe a k'asa, Nene ta kalli wannan ta kalli wannan, da ta ga zaman bana k'arewa bane sai ta tashi ta fita, to hakan ma bayan fitar ta, sai da suka fi 15mins, ba wanda ya tanka ma danuwansa, Seebi sai wasa take tayi da 'yan yatsunta, shi ko tarrarabin yanda zai fara mata magana yakeyi, sai ya bude baki zai yi magana sai ya kasa, kirrr yaji wayanshi alamun shigowar message daga Uncle Zaid, ya bude message din *"Drop the Ego, Pride and Whatsoever, Tell her how much she mean to you, Tell her how much you love her"* Rafeeq ya karanta message din yayi dan guntun tsaki, shifa abunda ke bashi wahala kenan bayani da baki, ta ya zai fara mata wasu surutai, ya sake sakin tsakin. Bayan nan ma wani mintuna goma suka k'ara shudewa, Nasiba ta aiyana a ranta ba zai mata magana ba, Uncle Zaid yayi kuskure da yace Feeq na sonta, ta mik'e tsaye tayi hanyar Sama, be an kara ba sai ganinta yayi zata fara taka bene, guntun tsaki yayi yayi saurin shan gabanta, ya zuba mata daradaran idanuwanshi cikin nata, da sauri ta runtse ido, wani kallo yake binta dashi, yana k'are mata kallo, nishadi na shigar shi, cikin kasan mak'oshinsa a hankali ya furta "Naseeebahh" a hankali ta soma bude idonta ta sauke su fes a kansa, ba zata iya jure kallon shi ha ta kawar da kai gefe, toh anzo gurin, besan me zai ce mata ba, sun kusa minti bakwai a tsaye ya rasa ta inda zai fara magana, sai ya bude baki zai ce wani abu sai ya kasa, da ta gaji da tsayuwa tace "Hamma zan hau sama, ka dan matsa daga hanya" Rufe idonsa yayi ya fara zubo zance kamar Radio, shi kansa be san me yake fada ba ga abunda yace "Nikam Soyayyah bata cikin kaya, love was Really not my thingy, I was a real time Player, banda burin Love, because a gani na bacin lokaci ne, I had more than a Hundred Girlfriends, banda Damuwa ko kadan, all i do is Eat, Pray, Sleep, Dump a girl, Repeat... Why? Because i am Rafeeq Freaking Lema. A rana daya mata fiye da goma za su kawo min kansu su bani kansu tun kafin na shiga Jami'a, amma sai Allah yayi ni ba mazinaci bane, Allah ya jarabbeni da k'addarori da dama, na shiga halin Bakin Duhu ta yanda na cire rai daga rahamar Allah, duk da haka abun baya damuna, i enjoyed myself being the IDGAF (ban damu da kowa ba, lols) about anybody, not even my Dad, the only humanity left in me was the love of My Uncle Zaid, Ibada ma a lokacin zan yi ta, amma ba kamar yanda ya kamata ba, Sallah ma sai na ga damar yinta nakeyi, na shiga Halaka fa ba tare da na nuna damuwa ta a hakan ba, Rana daya Allah ya jefo ki cikin rayuwata dalilin Sanadi, Sanadin Alkhairi, Naseebah, tun farkon haduwar mu dake na san Akwai Dalilin da ya sa ki ka shigo rayuwata, tun farkon haduwar mu na fara ganin haske a rayuwata, Damuwar wani ba damuwata bane ba, amma damuwarki damuwata ce, na fara damuwa da lamarinki, duk yanda na so in k'untata miki, ina kasawa, theres Something about you that i just dont know how to put it, amma All i know is KE ALHERI CE, you are a Blessing, you and your Entire Family, and let me say Something that i've never said to you in a Nice way, THANK YOU, Thank You Naseebah Muhammad".
Zatayi magana ya katse ta hanyat cewa "Shhh, ban gama ba, thats a short story, And this, i dont know how to put this, i am not good in expressing myself, from What i noticed, Baki da Damuwa, baki da Hayaniya, Baki da matsala ko kadan, Unlike your Neh-neh" Murmushi mai sauti tayi, ya sausauta murya cikin murya me kama da Rad'a yace "Ina Sonki Seebin Nene, Ina Sonki Sosai" wasu zafafan hawaye taji sun fara sauko mata, Hawayen Farin ciki, rudewa yayi ganin tana fitar da hawaye, guntun tsaki yayi ya ciro Handky daga cikin Aljihun shi, "Lord of Mercy! Fine! Ba kya sona shiyasa kike kuka, ki share hawayen ki, kiyi hak'uri, I know what to do, Zan bar garin kafin daurin Auren, don nasan Uncle Zee ba zai taba saurarena ba idan nace na bazan aureki ba, kinga idan bana nan ba zaa daura auren ba" a ranta tace "What is his Problem? Why is he acting so stupid?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login