Showing 90001 words to 93000 words out of 149166 words
tace "Wallahi Yan sanda zan kawo miki, sai kinyi nadamar ta6a Lafiyar jikin mu" aiko Nene ta tunzura tace "YanSanda? Naciii uwar Yan sanda, naci uwar hukumar jami'an tsaro dukkansu, Kinci uwarki idan baki dauko mun 'yan sanda ba, ke bari ma in k'ara laftar ku yanda zaki dauko mun su da hujja" ai ko Nene ta wawuro chazar ta, haba zo kuga relay tsakanin Miemee Saude da Aneesa, har suna tura junansu ko wannen su na rigerigen fita daga gidan Nene, a wannan karon ba Rafeeq ba hatta Zaid sai da ya dara.
Nene tace "kina iya fitowa me tsoro kamar farar kura" Simi simi Seebi ta fito daga dakin rungume da Ayman da ta ci kuka ya gaji, Rafeeq yayi k'okarin amsarta Ayman tak'i yarda sai dai Babanta ya amsheta ya sakata kan kafada, don yau taga tashin hankalin da bata taba ganin irinshi ba.
Zaid ya nisa yace "Wai me ya faru ne? Me ya kawo su Meema gidan nan?" Nene tayi charap kamar jira take ta shiga karanto ma Zaid abubuwan da suka faru tun bayan shigowar su Aneesa, ran Zaid ya 6aci matuk'a sai ya fi ganin laifin Rafeeq cikin 6acin rai yace da Rafeeq "why didnt you stop them da suka fara zagin Nene? Meyasa baka hana su ba? Kamar bazai amsa shi ba, sai dai ya daure yace "Saboda i know she'd handle them in her ways, which she did" ran Zaid ya 6aci zai sake magana Rafeeq yayi saurin cewa "Look Uncle i tried to warn them, i even told them to leave, but they didnt want to listen so i let them be, ko ba haka ba Neh-neh?" kamar ta san me ake cewa tace "Hakane Zaidu Bawan Allah" nan Zaid ya dai bata hak'uri ya ba Nasiba Hakuri, ya kalli Rafeeq ya galla mai harara shi kuwa ya dauke ido yayi kamar be ganshi ba, Nene tace "ka bar hararan shi, ai ni yau Dunkum ya burgeni, kasan shi ya mik'o min Chazar, kuma ya fassara min abunda suka ce" Rafeeq yayi dan guntun tsaki kamar ba shi ya gama daria dazun ba, Nene tace "Su dunkum ashe ana ganin hak'oran ka? Wato kai mugun abu ne abokinka ko? Sai kaga abun mugunta kake daria, ai da nasani da na shafda maka a gadon baya sai kayi darian da kyau" Zaid da Seebi sukayi daria shi kuma ya daure fuska.
Saude ta ja Majina tace "Sai na koya ma tsohuwar nan hankali, sai tayi nadamar abun da ta mana, sai zaman katsina ya gagareta, Wallahi sai ta yaba ma Aya zakinta" Meema na matsar k'walla tace "Wallahi Sis, in ke ba kiyi maganinsu ba ni sai nayi, wallahi zan iya kashe su da hannuna, duk tsanar da na ma tsohuwar nan, nafi tsanar Jikarta, na tsanesu, tsanar da ban ta6a ma kowa ba" Aneesa cikin kuka tace "Mommy, make them Suffer" Saude tayi darian mugunta tace "Ku zuba min ido" ta zaro wayarta ta lalubo Numbern tsohon Amininta *Mak'ale*.
*************
K'arfe 9:30am ta fito don zuwa makaranta, lectures take dashi karfe 11:00am zata fita da wuri ne don ta samu Abun hawa ta isa da wuri, don tafiar kusan minti 45 ne, sauri takeyi bayan ta gama shirya Ayman tana bacci tace da Nene "Uncle Zaid zai zo ya dauke Ayman, zai kaita gidan Kakanin su Rafeeq (Baba TJ) ta musu yini, in kuma ta yarda ta kwana toh, Nene tace "to shikenan sai yazo kema Allah ya dawo dake Lafiya" har sunyi Sallama Nene tace ba zaki tsaya kici wani abun ba? tace "da naje Makaranta zan siya Panke, na fiso in isa da wuri" ta mata adduar tsari ta fita daga gidan.
Kamar daga sama taji horn dinshi ta waigo da sauri ta sakar mai murmushinta, shi kuma kamar ya ga wani kashi ya wani tubune fuska tare ds kawar da kai, bude k'ofa tayi ta shiga, "Hamma Rafeeq Good Morning" tsaki yayi yace "Fine" ya dauke kai, tunda suka hau hanya ba me ma danuwanshi magana, har suka iso makaranta, anan ne tace ya kaita ta bayan Science Theatre, kamar ba zai yi kwanan ba ya sha kwanar da k'arfi har tana bugewa da window, daidai Theatre suka tsaya, ba mutane a gurin, sai jefi jefi ake ganin tsiraran mutane. A ranta tace "Ya Illahi! Gani gareka" me makon ta fita sai ta gyara zamanta ta sa hannu cikin jakkarta ta ciro zoben da Mami ta bata, ta sa a yatsar ta na kusa da k'arami, ta gefen ido ya ke kallon duk abunda takeyi, ta wutsiyar ido ya k'are ma Zoben kallo, wani abu ya ji game da zoben, da sauri ya juyo gareta inda take wasa da yatsunta tana juya zoben a yatsar ta, Mukut! Ya hadiye miyau, ya kalli yatsan hannun shi yaga Irin Zoben ne, ya sake kallon na hannunta, sai da ta lura da ya tantance kafin ta bude k'ofar tace "Hamma sai anjima nagode" har ta sa kai zata fita ta tsinkayi muryanshi inda yayi guntun tsaki yace "Nace ba?" murmushi tayi kafin ta dakata tace "ya kace?"
Sai kuma yayi nadamar tsaidata to me zai ce mata? Zuciyar shi ta tunzura shi yace "Ina kika samo zoben hannunki? Anzo gurin tace " Auu wannan Zoben yatsa ta? A wonderful woman, with a beautiful heart gave it to me, kasan mene? Ta bani tarihin Zoben, wai her Beloved Son gave it to her ranar Zagayowan haihuwarta randa ta shiga shekaru 40, wai ashe musamman ya je Dubai ya sa akayi mishi Zobe guda biyu, ya kawo mata as her birthday gift, ya sa nashi ya sa mata nata yace da ita '"Mamina, this is my love for you, ya nuna mata na hannun shi yace this is the twin of your ring, even if we are far from eachother, this ring is linked to our Hearts"' Hamma na DonAllah basu burgeka ba? Ya dago ya kalleta, ta kasa gane yanayin da yake ciki, idanun nan sun kada sunyi Jazurrrr, ta firgita har ranta amma sai ta dake ta na karfafa ma kanta guiwa tace "Laaaahhh Hamma kalli Zoben hannunka, kamar nawa, duba ka gani, iri daya ne Wallahi, How is that even possible? A lokacin kuma a ranshi yace "She met Mami" tsigar jijiyoyin jikin shi suka tashi saboda tashin hankali" bata fasa magana ba tace kaima Zoben ka na da dan biyu? Akwai wanda ka ba Zoben ka? K'ila kaima Maminka ka ba" da k'arfi yace "Shutup" a tsorace ta kalleshi tace "Hamma na, are you okay? Did i said something wrong?" cike da nutsuwa yace "Get Out" Tsoro ya gama cikata, ba ta taba ganin ya fusata haka ba, muryar shi ta sae ji cikin karaji ido rufe "I said get out" jiki na rawa ta dauki jakkanta ta bude k'ofa Zata fita sai kuma ta fasa, ta dawo ta kulle k'ofar, jin an kulle kofa ya sa shi bude ido a hankali, ganin ta zaune ya bashi Mamaki daure fuska yayi sosai yace "are you deaf? Dont you understand English again? Okay nace ki fita, ki fita ki Barmin Mota na Kai tsaye tace "bazan fita ba, you have to listen to what i am about to say to you, idan ka ga dama kayi aiki dashi idan ka ga dama ka watsar yabi ta bayan kunne, Rayuwa daya ce, you only get to live once, idan yau ka fadi ka mutu ka san makomar ka? Ni bansan kusancin ka da Ubangijin ka ba, amma yau ka mutu ina kyautata zaton kai dan wuta ne, saboda Me? Saboda kana Fushi da Mahaifiyar ka, baka neman Albarkar ta, kar ka manta akwai hakkinta akan ka, Fushi, duhu, emptiness, loneliness sun cika Zuciyar ka, kai kana tunanin kai ke da kanka, you can get to do whatever you like whenever you please with No Apology, kai komai kayi daidai ne 6acin rai ya hanaka facing reality, abu is very clear amma Zuciyarka ta mutu, ko ince ka kashe Zuciyar ka da kanka, alhali you are a good person with a beautiful heart, amma baka so ka ga hakan, you are forcing yourself to be mean, amma kasan Zuciyarka kai mutumin kirki ne, ga ka da tausayi, da kula, please realize that side of you, da tsawa ya katse ta cikin daga murya yace "Nooo, you think you know me? You know Nothing about me, nkw get out of the Damn Car" itama cikin muryar kuka take cewa "Nace maka ba inda zani, i am not done talking to you, if you dont want to realise your good side, then i'll make you realise them, lokacin da aka kai Nene Asibiti, mesa ka ke kula damu? Abinci safe rana da dare? Me sa kake kaini makaranta? Zuciyar ka me kyau ce amma ka danneta kai a dole ba ka damu da kowa ba, ko kuma ba wannan ba, ka tuna randa kace in fitar maka daga mota, randa zaka kawo ni Makaranta? Randa nake ta maka tsaki? Ka direni a tsakiyar daji? Na san ka tuna, ka tafi me ya dawo da kai? You could'nt leave me there because you care" da sauri yace "No i dont, i was only saving you from your Stupidity, kin tsaya tsakiyar titi kar mota ta bigeki, people would get hurt people like my Uncle Zaid and Maalesh" tace "koma dai meye you care about the people you love, ba dole sai ni ba, dama ai ni ba kowa bace, amma su ka damu da damuwar su, ka kasa barina sabida su, ka ga kuwa wannan shine abunda nake so ka fahimta, you have a beautiful heart" "ke i dont care about anyone, Uncle Zaid is all i care about and maybe Maalesh,i can sacrifice anything for them" ta mai wani kallo tace "really? To tell me, har yanzu me kakeyi da Zoben hannunka? Me kakeyi da danuwa Zoben da ka ba Maminka? Saboda kana sonta, akwai 6angaren zuciyarka da ke sonta, akwai 6angaren zuciyarka da ke son sake ganinta, fushi da bak'ar zucciya suke hanaka, Rafeeq na girgiza kai yace " Ki min Shiruuu please, Ya isheni Nasiba" da sauri ta kallo shi, a iya saninta da shi ko Seebi bata ta6a ji yace ba, amma yau ita yake kira da Naseeba? Ya ilahi, yaba ta tausayi ama dole ta ya gane abunda yake yi ba me kyau bane, tace "kaga matsalar ka ko? Baka son gaskia, da an fara gaya maka gaskia sai ka tsaida mutum, ita gaskia kwara daya ce kuma daci gareta, Listen now, i am going to make this Straight to you, Incase you dont know, Aljannar namiji yana k'asan tafin Mahaifiyar shi, sai ya bita zai samu shiga, sai da Manzon Allah ya kira Uwa so uku kafin ya kira Uba so daya, ko kasan duk wanda ya sa Mahaifiyar sa kuka be ganin daidai? Ka san iyakar hawayen da tayi a kanka? Kasan zunuban da kake kwasa a ranar da tuna da kai ta zubda hawaye? Ya Illahi! i dont have to lecture you on this, kai kasan wannan abun amma fushi ya hanaka ganin hakan, ka ta6a tambayan kanka? Shin yanda nake ma Iyayena musamman Mahaifiya ta ina kyauta wa? Duk abunda ta mun tun ina cikin ciki har girmana ta chanchanci abubuwan da nake mata, kai ko me tayi, She's still your Mother, ko kisan kai tayi, she'll remain your mother, balle something you are not sure of, something no one is sure of, You didnt bother to find the truth, kai an maka laifi, ba wanda ya kuma isa ya ce kayi, ask yourself if this is the way you want your children to treat you when they're grown. Don abun da kayi shi zaai maka wallahi, fiye da ma wanda kayi, dole a maka, If you're not measuring up, it's not too late. You can make a change this very day. Uwa ta fi karfin wasa Wallahi, ka tashi ka fusknaci matsalar ka tun kan dare ya maka, tun kan ka wayi gari ace ba kai ko ita a duniya, Only then zaka higa damuwan da yafi wannan matsi i've said my peace" ta na kuka ta ciro paper da biro tayo rubutu, ta ajiye mai a cinya, tace "gashi this is her address, bance kaje ba, you decide what to do with it, ina so kayi tunani, ka tuna Who is your mother" ta share hawayenta ta bude motar ta fita tabar Rafeeq zaune kamar gunki.
Hannu ya sa a kai ya damk'i gashin kanshi, Jijiyar kanshi kamar ta fito, Nan ya soma tunanin halin da ya iske Mami a ciki, sai ya tuno ծaծծaծan lokuttan da sukayi da Mami Daddy and Rafee'ah ad a Family, Ya tuna wacece Mami, abunda be taba yi ba, kanshi ya hau sarawa, ya kusa Minti 30 bayan fitar Nasiba yana hawaye, hawayen da ya rasa na meye, ya kunna motar shi ya fita a guje kamar be shirin tashi Sama" Nasiba ta fito daga maboyarta tace "Allah ka sa yaji, Allah ya tsareka R- Lema".
_Malali Kaduna_
Shigowar ta kenan daga Gidan Ummin Anan, ta mik'a musu Coolern Danwake, don yau Danwake tayi, ta kalli agogo taga k'arfe 3:16, tace kaii bari inyi bacci kafin laasar tayi, kan kujera ta dan kishingiծa ji tayi motsin mutum tana dan kallo kofar ta ga Mutun tsaye, jiki na 6ari ta mik'e tsaye, ta kasa yarda da abun da idonta yake gane mata, baki na rawa ta nuna shi da yatsa tace " Rafeeeeeeq" A hankali yace "Mamiiiii" Da sauri ta runtse ido daidia digar hawayenta tana adduar kar ta farka da wannan mafarkin da takeyi, yau Rafeeq ne ke kiranta da Mami? Ba zata so ta ta6a tashi daga barcin nan ba, takowa yayi kusa da ita ya sa hannu ya share mata hawayen da ke zuba a idonta, jin an tabata yasa ta gane ba nafarki bane, a hankali ta bude idon ta fes kan fuskar shi da ta koma ja, girgiza mata kai yayi, da sauri ta rungumeshi tana kuka, "Rafeeq, Rafeeq my Child, Rafeeq ka yafe mini, Rafeeq na hallaka rayuwar ka, Rafeeq ka yafe mini DonAllah" shima kukan yakeyi sosai, kukan da be taba irin shi ba, yace "Mami meyasa? Mami Why? Why? Why?, Mami meyasa zakiyi haka?" ta dago da sauri tace "Wallahi bansani ba, bansani ba Rafeeq, ni nasan banda mafita, Allah kadai ne gatana shi kadai yasan me ya faru a wannan ranar, amma Wallahi bansan komai da ya faru a ranar ba i totally have no idea, please believe me my son" Zuciyar shi ta tambayeshi Wai kai dama tun farko meyasa ka yarda da Mamin ka zata iya aikata abu makamancin hakan, ita da kullum take maku Nasiha kan ku nissanci Zina, wata Zuciyar tace da idonka ka ganta" da sauri ya kawar da tunanin nan, ya sake rungume ta, yace "it doesnt matter anymore, ba zaki iya aikata hakan ba, i was blind to see, we all were blind to see the good in you, but not anymore, I swear on my Dead Sister whoever did this to you will pay" tace "Aa Rafeeq kadaina irin rantsuwar nan, be da amfani, ba kyau, kuma dont let anger have control over you, calm down" Yayi ajiyar Zuciya yace "Mami, whatever i said to you in the past, please forgive me, i dont mean any of it, i was stupid to forget who You are, someone said in har kina fushi dani ba zan taba ganin daidai ba ki yafe min" "Shhhh my baby, ba ka min komai ba, I got you, i always do" ta jawo hannun shi ta zaunar dashi ta dinga shafa hannun shi tana murmushi tana ganin komai kamar mafarki, tace "kasan me na dafa? Ya girgiza kai, tace "Danwake" yaui dariya yace kina son danwake har yanzu? Tace "kai ka koya min danwake" ya tashi yace barin zubo mana ko? Ya shiva kitchen ita kuwa ta dubi gabas tayi sujjada (Sujjudush Shukur) tana me godia ga Allah da ya dawo da danta gareta, saura Baban shi da take adduar Allah ya sa shima ya fuskanci gaskia, Rafeeq ya zubo musu Danwaken ya kawo parlor ya ajiye a kan Carpet, ya rik'o hannun Mami ya zaunar da ita a k'asa ya koma ya dibo mai da yaji a kwano yazo ya zauna, haka suka fara ci yana sa mata a baki tana sa mai a baki, hawayen farinciki sukeyi duka, har dai Rafeeq ya koma lallashin Mamin shi har suka gama, ya kwashe kayan ya shiga daki yayi alwala yayi Azahar ya ja su Jam'i sukayi laasar, nan suka hau labarin duniya.
"Allah sarki Nasiba, Nasiba Alheri Ce Rafeeq, Nasiba Alheri ce a garemu duka, ko ba ka fada ba nasan ita ce Silar zuwan ka Kaduna" murmushi kawai Yayi yace "Mami ke ina kika santa? tace "tashi muje gidansu yanzu" yace "aa i want to spend more time with you" tace ba nisa makota ne yanzu zamu dawo, suka nufa Gidansu Nasiba, Daidai shigowar Abbi, Rafeeq na ganinshi yaje ya rungume shi, Abbi ya bubbuga bayanshi, ya ji dadin ganin Rafeeq haka, Lallai in ciwo cuta ce to tabbas addua Magani ce, yace "Jiki yayi kyau Rafeeq, Allah ya sa a dace yayi murmushi" "ina Mutuniyar taka? Nenen ka?" guntun tsaki yayi chan kuma yayi murmushi ya kwashe labarin abun da ya faru jiya ya basu, Dukkansu dariya suke tayi, Abbi ya girgiza kai yace "nace ma Nenen ta daina biyewa yara ta ki ji, ita jinta takeyi kamar yar shekara 15" suka sa daria. Anan yazo ya hau kan Rafeeq, Rafeeq ya daure fuska beson yara, amma ganin idon Abbii da Ummi a kanshi ya sa shi yin yak'en dole, Anan na matukar kama da Nasiba, yace ka san Adda Seebin Nene? Kai kawai Rafeeq ya gyada, to ka tafi dani