Showing 42001 words to 45000 words out of 149166 words
yau din nan xaki fuskanci hukuma, Duk duniyancin Sauda yau ta rude, ta shiga rok'on hafiz da ya tsaya suyi magana, ba abunda yake zato bane, yace "baki da hankali, kina nufin banji me kuka ce bane? Ko ban fahimci abunda kuka ce bane? Ai duk abunda kuka fada is straight, ba sai na nema wani bayani ba, abu daya kadai zance miki, dole a zartar da hukunci kanki. "I wont let you keep hurting innocent souls, i wont let you keep hurting the people i love" ko ina na jikin Sauda rawa yake, tace "Hafiz Is not that you are saint or perfect, kar ka manta kai ka kawo ni matsayin da na ke a yanzu, da taimakon ka na shigo gidan nan, kuma kar ka manta da diyarka Aneesa, think wisely, tona ni barazana ce ga ruining reputation dinka, kuma if i go down, you go down with me as well". Hafiz yayi wani murmushi, yace "Sauda kenan, i dont care, ko me zai faru ya faru, ni nakawo ki gidan nan right? Kuma nine silan barin ki, its time i do good thing to the people who did alot for me, i dont care about the consequences, I am Ready, you cannot use me again". Yana kaiwa nan ya juya don barin dakin, Sauda da Meema a rude suka bishi a baya suna mai magiya amma fir ya k'i kula su, Parlorn Alhaji Habib ya shiga, Wayam ya gani, ya lek'a dakin nan ma baya nan, Sauda ta sauke numfashi, Hafiz ya wurga mata harara ya ciro wayar shi ya danna ma A.Habib Kira ringing daya ya dauka "Hello Hafiz" "naam Yaya, kuna ina, ni da na barku parlo kai da Zaid" yace "Eh wallahi, dama Zaid ne ya buk'aci muje Makarantan su Marigayi mu sanar dasu Rasuwarta" Hafiz yace "Okay, gani nan zan biyoku Umaru Musa din" Alhaji Habib yace "lafiya Hafiz?" Hafiz yace "sai dai nazo, yau ranar tonon Silili ne, there are things you need to know, yau ZAN FASA KWAI" dif ya kashe wayan, Sauda ta rude matuka, tana ma Hafiz magiya, we can fix this, feez-boy na tuba kar ka min haka" ai ko kallo bata ishe shi ba ya fice ya bar dakin.
Hannu ta daura a kai ta saka ihu, "Shikenan tawa ta sameni, karya ta ta kare asiri na ya tonu"
Meema cikin tashin hankali, don gani take idan asirin Yayarta ya tonu, bata ba auren Zaid gashi ita kuma har ga Allah ta sama ranta auren shi, cikin bacin rai tace "Haba sis, dont easily give up, akwai hanyar hana tsaida Hafiz, tunda yanzu fita zaiyi, kawai ki kira bad boys dinki kice su tareshi su gama mai aiki" Sauda cikin doki tace "kutt har na manta da wannan hanyar, hankalina ne baya jikina, bari nayi hanzarin kiran Mak'ale" da gudu ta fita tayi dakinta ta dailo numbern Mak'ale. Ringing biyu ya dauka "Hajjaju mutanen makka" ba ta tsaya sanya ba, tace "Mak'ale kana ina?" yace "gani ta wurin Fatima Shema Housing Estate" Hamdala tayi tace yauwa, wani aiki nake so ka min, ga Hafiz nan zuwa Umaru Musa University, so nake ka tareshi, ka kashe shi, i dont want him to make it to Umyuk" mak'ale yayi shiru yace "haba hajia, wannan aiki da safiyyan nan? Ba kya tsoron aka mamu? Gashi mu uku kadai ne, ba sauran mu" tace Mak'ale ka taimakeni, akwai matsala idan Hafiz ya isa Jamiar nan, zan baka Miliyan Guda" Shewa Mak'ale yayi yace angama "Hafiz Lema ya zama gawa" tace "yauwa Mak'ale, zaka gane shi ko?" yayi daria yace "baki da matsala, har kalar motar shi na sani" ya datse wayar Sauda ta sake Ajiyar Zuciya tana labarta Meema yanda sukayi da mak'ale.
Tuk'i yakeyi gaban shi na faduwa, ya sha round din Alkalem University ya dauki hanyar Institutions Road, ya na duba side mirror daidai FCE yaga kamar ana binshi, ko da ya duba mirror din sosai ya gane fuskan Mak'ale, shine ya fito daga dakin Maman su Rafeeq a ranar da suka ganta zindir. Nan jikin shi yayi sanyi, tabbas Sauda ce ta turo shi ya mishi wani mugun abu, gaban shi ya tsananta faduwa, ya taka giya ya k'ara gudun motar shi, suma su makale suka kara gudu, Hafiz ya tsorata matuk'a ya zaro wayar shi yayi dialing numbern Zaid "Hello Hafiz ka taho?" Hafiz yace "Zaid kazo ka taimake ni, akwai wasu masu bina" SubhanAllah a ina? Gamu nan mun kusa Batagarawa, sai fafatawa mukeyi, a guje Zaid ya fito daga office din da suke zaune shi da Alhaji Habib be tsaya mishi bayani ba ya fita, Alhaji Habib ya mik'e, yana kwalawa Zaid kira, Zaid be tsaya amsa shi ba. "Hafiz kana jina? "Eh zaid ina jinka" "yauwa i'm on my way" Zaid incase i dont make it-- Zaid yayi saurin katse shi Hafiz stop, i wont let anyone hurt you gani nan zuwa" "Zaid listen to me, ina so ku yafe min, And you cannot trust Sauda" kafin Zaid ya ce wani abu ji yake kiiiiiiii Alamun cin birkin mota, da karfi Zaid yace "Hafizzzzzz" sai ji yayi ance "kai fito daga motar nan" Zaid ya kara gudun da yakeyi har ya kai inda yayi parking motar shi.
Mak'ale suka ma Hafiz mugun bugu kafin suka tura shi motar su suka bar gurin.
_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg3⃣1⃣
A cikin mota suka lumama Hafiz Wuk'a, bude k'ofa sukayi suka wurgar dashi suka wuce, nan da nan mutane Suka taru kan Hafiz, Zaid ya fito daga Jamiar ya dinga kiran layin Hafiz har ya katse ba a dauka, nan ya ga taron jamaa daga gefe, kamar ya wuce sai Zuciyar shi ta kwadaita mai da ya tsaya, yayi parking motar yq kutsa cikin mutanen nan, ganin Hafiz yashe a k'asa jini ya sa shi karasawa da sauri, Yana kwala mai kira, Ya rungume Hafiz a jiki, sai tari yake tayi, murmushin Karfin Hali Hafiz ya sake da k'yar yace "Zaid, brother, ina neman yafiyar ku kai da Yaya akan duk wasu abubuwan da na muku, ku yafe min, ka ce ma Aunty Aisha ta yafe min itama, na san na mata laifi" Zaid kuka yakyi sosai, yana cewa "Stay Still Hafiz, i'll bring you to a hospital" Jamaa ku taimaka mana donAllah, Aiko bayin Allahn gurin Suka ciccibi Hafiz, suka kaishi motar Zaid, Zaid ya rokesu idan da wanda ya iya tuki ya jasu, wani dan makaranta ya ansa key din, shi da wani gaba, Zaid rungume da Hafix a Bayan mota, tarin Hafiz ya tsananta, kafin a kaishi asibiti ya amsa kiran Allah, Zaid ya fashe da wani irin Kuka, Gida ya bukaci su wuce, Alh Habib yai ta kiran Zaid a waya, da kyar Zaid ya dauka ya gaya mai halin da ake ciki, nan gaban Alhaji ya yanke ya fadi kasa Sumamme, don har Ranshi yake son Hafiz, DVC din UMYUK ya shiga rudani, da sauri ya dauko bottle water ya shafa ma Alhaji Habib, Attishawa yayi da k'arfi ya farfado, Sallalami ya farayi, yana kuka kamar mace.
Gida DVC ya kawo shi, a tsakar gida ya ga an shinfide gawar Hafiz, duk yan gidan na nan tsaye, ya tako har gaban gawan ya bude fuskar Hafiz, gashi nan fuskar tayi fayau, Waiyo Allah, zo ku ga kuka gun Alhaji Habib, Rafeeq na tsaye yana hawaye, mutuwar Rafeeah ta dawo mai sabo, ga Uncle Hafiz ya rasu, kwana Goma Tsakaninsu da Rafeeah, Zaid a zaune kusa da gawan yana kuka, Sauda da ke gefe sai ihu take tayi, Aneesa da ba wani sabawa sukayi dashi ba taji jikinta yayi sanyi, kuka take kamar ranta (Mahaifi ba wasa bane) Liman yace "ai sai a gaggauta a mishi sutura akai shi Makwancinsa" da taimakon Baba Tj da Yan Unguwa aka yi ma Hafiz wanka a Parlon Gidan, cikin Mintuna da basu wuce 50 ,ba aka kai Hafiz gidan shi na gaskia.
Alhaji Habib fa ya zare, ko Rasuwan Rafeeah be firgita shi kamar yanda na Hafiz ya gigita shi ba, duk ya bi ya fita daga hayyacin shi, Ya fara tambayan kanshi? Why are these happening to him? Da sauri yayi Istighfari da zuciyar shi ta tunasar dashi kar kayi sabo, kai musulmi ne.
Bayan Sati 1
Anyi Sadakar Bakwai din Hafiz, Zaid zaune da Habib da DPO din Police suna bincike, don ankai report cewa Kashe Hafiz akayi, Maganganun da sukayi da Hafiz ranar da ya rasu Suka dawo ma Alhaji Habib, Alhaji Habib da har yanzu be dawo normal ba yace "nifa da ya kirani, cemin yayi zai biyo Makarantar su Rafeeq, akwai Maganar da yake so ya gaya mana, har yana ikirarin Yau zai fasa kwai" Zaid yace "Jim kadan kuma ya kirani a tsorace yana neman taimako gurina wasu na binshi a baya, wasu da be san ko su waye ba, ina jinsu lokacin da suka umarce shi da ya fito daga motar" Officer yayi rubutu ya dago yace ko kun san shi da abokan gaba ko da wanda kuke zargi? Alhaji Habib yace "babu" Zaid ya tsaiya tunani, Hafiz yace mai he should'nt trust Sauda, to me tayi? Based on what? He's not sure, so ba zai zargeta ba, amma mesa Hafiz zaiyi warning dinshi? He has no clue". Officer ya musu Sallama ya tafi don fara gudanar da bincike. Zaid kuwa ya kudurta a zai fara binciken shi shi kadai, zai kuma fara da Sauda.
Bayan Sati 2
Zaid ya kalli nephew dinshi yace "Rafeeq, saura kwanaki biyar ku fara final exams dinku, Shin Rafeeq ba zaka ma kanka fada ba? Shi ba zaka fara karatu ba, ina da labarin ko lectures baka zuwa, duk tests din da akayi bakayi ko daya ba,ina so kayi karatu ka fita da first class, for how long do u want to live in the past? Its time you move on, please start studying" shiru ya mai be tanka shi ba, Zaid yace "Feeq, kana fa jina" kamar ba zai tanka ba yace "I dont want to, i am not ready" Zaid ya dan sassauta murya yace "Haba Feeq, ka kwantar da hankalin ka ka koma makaranta, kana da hope, kana da what it takes to acheive your dreams in life, please Rafeeq buckle up" Zaid fa ya kai Rafeeq bango, cikin daga murya Rafeeq yace" bana son acheiving komai, my life is already ruined long time ago, i dont have any hope, i dont want to live anymore, Rafeeah should be here, i supposed to die, i dont wanna live, i want to die, meyasa da ta sake ziyartar Family din nan ta dauki uncle Hafiz? Mesa ba ta daukeni ba, ni ke son mutuwa, mesa da Thugs suka zo kisa suka kashe uncle Hafiz? Ni ya kamata su kashe ba shi ba, i wish Akwai wanda zai kasheni, or i wish i could end my life" Zaid ya kashe Rafeeq da Mari, ya nuna shi da yatsa "I didnt raise you as my child to be a non-believer, Kai Musulmi ne, You act like one, not one who fight with his Destiny, you are Rafeeq Habib Lema, kuma Dole ka rungumi kaddararka, Makaranta kuwa sai kayi shi, i've waited for this for so long" Rafeeq ya k'ek'eshe ido yace "Wallahi bazan yi karatu ba, i dont want to study, i dont want to, idan kuma ka matsa mun Zan shiga duniya, you will never ever see me again" Zaid ya tsorata, yayi saurin Rungume shi, yana kuka, "aa, Rafeeq be kai ga haka ba, na bar maganan ba zan matsa maka ba, please dont leave me i cant live without you" Jikin Rafeeq yayi sanyi ganin Uncle Zaid na hawaye a kanshi, wani irin so Uncle Zaid ke mishi, ya dan dago ya share mai hawaye.
Washegari Zaid ya je Umaru Musa Yaradua University, Maalesh ya mai jagora gurin HOD dinsu, Zaid ya gaya musu matsalar Rafeeq, yana so a bashi shawara, Level Coordinator na su Rafeeq yace "Inaga yayi deferring semester din, har sai ya dawo normal, so that it wont affect his CGPA" HOD yace "Gaskia, ne, Yayi Deferring Semester din wato zai Jiginar da Semester din, ba wai yayi spilling bane, only disadvantage din shine, Mates dinshi zasuyi Graduating shikuma zai dawo" Zaid yace is better ai hakan, InshaAllah zuwa next year din zai dawo normal self dinshi sai ya zo ya cigaba daga inda ya tsaya" nan suka tsaida Magana.
Zaid ya samu Yayan shi ya mai bayanin komai, Yayan yayi naam da hakan, yace to kai Zaid meye plans dinka kan danka? Ina tsoron Zuciyar Rafeeq tunda har ya iya ikirarin shiga dunia, kar abokanan shi suyi influencing dinshi, su koya mai wasu halayar" Zaid yace " nayi tunanin haka, shisa nace za mu danje hutu da shi, zan dauke shi muje Embassy muyi purchasing Visa" Alhaji Habib yace "hakan yayi, K'ila ya dan washe ya dawo daidai". Zaid ya sanar da Rafeeq zasuje dan hutu a kasar waje, ya fadi any country of his choice, Rafeeq beyi wani murna ba don shi a ganinshi be kamata ace yana jin dadi ba, be ce komai ba, Zaid yace ko muje Dubai, ko London, ko Saudi? Rafeeq dai be ce komai ba.
Zaid dai ya yanke hukuncin zuwa Paris Bayan sunje sunyi Umra, ya gama musu komai, ya dauko Hutun Wata 3 a Gurin Aiki, suka wuce Saudi Arabia da, sai da sukayi kwana 7 kafin suka wuce Paris.
Watan su Biyu a Paris daga shi sai Zaid a daki daya a Gado daya, Yanzu Ba yabo ba Fallasa, kadaran-kadahan dai, da kyar ya ke bin Zaid gurin bude ido, Zaid be da wani burin da ya wuce ya ga ya kyautata ma Rafeeq,hakan ya sa Rafeeq ya sa Zaid a zuciyar shi sosai, yaji duk duniya be da wanda yake so sama da Zaid, ya sama mishi gurbi a ranshi, shima ya kudurta a ranshi InshaAllah zaiyi k'okarin kyautata ma Rafeeq.Haka suka dawo Nigeria.
Nigeria ta na nan yanda suka barta, ba wani cigaba game da binciken Hafiz, ba wani leads, Alhaji Habib yace a barsu Allah e Zai isar musu, Mayya kuwa Wato Meema, son Zaid kamar ya kasheta, ba gun bokan da bataje ba ya karkato da hankalin Zaid gareta amma a banza, da taga ba sarki sai Allah sai ta fara chusa kanta gunshi, tana nuna maitar ta fili, tuni Zaid ya dagota, amma shi ya datse ma kanshi, shi Mijin Mace daya ce wato Safiyya. Zaid ya kasance mai taka tsantsan da Sauda, duk da be ga wani alamun Sauda na da wani hali ba, amma be cin abincinta be kwana gidan, dadin shi daya ba ruwan Rafeeq da cikin Gidan, shisa yake siyo mishi abubuwan bukata na kayan kwali da gwangwani.
Zaid ya koma bakin aikinshi, Mami ta rok'i Zaid da ya nema mata dan karamin Gida, ba zaiyiwu ta cigaba da Zama a cikin shi ba, da iyalan shi, wata rana zaa gaji da ita, duk yanda Zaid yaso tankwara ta ya kasa, be da wani choice da ya wuce nema mata Gida a Malali, tayi Parking ta koma chan, tana me kewan Safiyya da ta sha kuka ranar rabuwar su.
Bayan wata 1
Su Maalesh sunyi Graduating, suna ma jiran ayi posting dinsu Service (Bautar kasa).
Rafeeq ya kira Zaid a waya, Zaid yayi mamakin ganin kiran wayan shi, da sauri ya amsa, kamar ba zaiyi magana ba Rafeeq yace "an fara registeration, nayi, idan anzo 2nd Semester zan koma Makaranta" dadi kamar ya kashe Zaid, ya dinga shima Rafeeq Albarka, yasan yayi hakan ne don shi, don ya sa shi jin dadi, kuma ya sa shi din".
A yau Asabar Safiyya Matar Zaid ta haifi diyarta Mace kyakyawa Kamar Rafee'ah, Jini ba wasa ba, Murna gun Zaid kamar ya rungume Iska, Ranar Suna aka radawa diya Suna Rafee'ah, yan Katsina sunzo suna, Sanin zasu zo ya sa Mami tak'i Zuwa sunar tayi zaman ta Gidanta, Rafeeq ma ya zo, ya dauki diya ya rungume yaji sinta har cikin jinin jikinshi, dadi biyu, Ga ta jinin mafi soyuwar Halitta Uncle Zaid, ga ta da Sunar Rafee'ah.
Bayan Yan suna sun watse Safiyya jini ya barke wa Safiyya, ta fara tsinkau tsinkau,Zaid ya tsorata matuka ya danna kiran Aunty Aisha, suka dunguma suka kaita Asibiti, Nan dai Safiyya tace ga garin ku nan. Inalillahi wa ina ilaihir rajiun. Bayyana Rudun da Zaid ya shiga bata baki ne, kowa ya ji mutuwar Matar Zaid Safiyya, sai dai mu roki Allah ya sa Aljanna ce makomarta.
Zaid ya Zare kamar zautattace, don yana kaunar Matarshi fiye da tunani, yana tausayin su shi da diyar shi Rafee'ah-Ayman, Rafeeq da Baban shi da Maalesh sunzo janaizar, sun sauka masauki, Meema ji take yau Sallah a gunta don ba karamin farinciki mutuwar matar Zaid tayi ba.
Kwana 3suka tafi, banda Rafeeq da yace shi zai tsaya da Zaid don yasan yana bukatar shi, kamar Lokacin suna, Mami bata bari sun ganta ba, sai Bayan da suka tafi ta dawo gidan Zaid tana kula da diyar shi.
Rafeeq ya fito daga mota ya shiga gidan Uncle Zaid, Kai tsaye yayi Parlor, Tsaye ya ga Fuskar da ba zai taba mancewa ba, Fuskar Mahaifiyar shi, tsaye take rungume da jaririya, Jikin Rafeeq ya hau kyarma, idon shi ya rufe da sauri ya je ya fizge Rafeeah-Ayman, daga hannun ta, ya rungume ta, Zaid ya mik'e da sauri yace "Rafeeq" yace "me wannan Matar takeyi a gidan nan? Har ta ke taba min k'anwa? Zaid ya sausauta murya yace "Shes been here for a while" Rafeeq cikin bacin rai yace "and you never bothered to tell me? Zaid yace" coz u never