Showing 18001 words to 21000 words out of 184937 words
da wani gudan jininsa dan haka babu wanda zai ganeka sai wanda yay abun da kuma magoya bayansa dan haka inaso kasa ido sosai dan nasan su zasu iya ganoka amma bazasu taba nuna wata alama ba, suna da shiri akanka abdallah ka kiye!'
Adai-dai lokacin kuma suka karaso dan kareran get din da zai shiga da kai cikin ainahin estate din manyan masu gadi sojoji kusan biyarne akofar, kasancewar babu wanda baisan dady jafar ba yasa suka barsu suka shige kai tsaye zuwa get na biyu wanda daga shine kuma zakai ta ganin get-get na bangare bangare, batare da wani dogon bincikeba kai tsaye akabarsu suka shige bangaren Alhaji baba.
Alokaci daya abdallah yaji kansa yay wani irin mummunan sarawa da karfi tamkar ana buga masa guduma har sai da ya kai hannunsa ya dafe goshinsa, fahimtar hakanda dady yayi take yashiga karanto masa addu'a shima ahankali yake karanta innalillahi'wa'inna'ilaihiraji'un tare da allahumma ajirni fil musibati wa'aklifini khairan minha da la'ilaha'illa'anta subhanaka inni kuntu minazzalumin.kana ahankali sukayi sallama adai-dai lokacin da kofar ta zuge suka saka kai, yayin da sukaji wata kamilalliyar murya tana amsa musu,
Guri suka samu gaba dayansu akasa suka zube, saboda tsananin girmamawa ga tsohon dattijo mai tsananin mutumci da kamala.
Bayan sun gama gaisawa da dady ne, abdallah ya karayin kasa da kanshi kana ya gaishe da Alhaji baba, amsawa yayi cikin farin ciki da wani irin shauki na kauna da bege da lokaci daya ta saukarwa Alhaji baba.
Hannu ya mikawa abdallah yana cewa"zomana jikana abin alfaharina matso kaji dumin jikin kakanka!'abdallah bai kasance ragon namiji mai raunin zuciyaba amma ayau akuma gaban dattidon nan jiyake tamkar zai zubda hawayen tsananin tausayinsa da kuma kewarsa tare da zunzurutun kaunarsa hakanan yaji yana fargabar ranar da zai san cewa ya haifi bara gurbi acikin yayansa ya kuma hada iri da gubatacciyar zuria yana tsoron kar saboda bakin ciki ya hadiyi zuciya arasashi kowa ya huta.
Jin maganar Alhaji babane ya katseshi daga
dogon tunanin da ya fada yace" abdallah jikana kasaki jikinka kadauka cewa kana cikin gidanku kuma cikin ahlinkane, duk abinda zakayi kayishi kai tsaye amatsayinka na dan gidannan na kuma baka umarni duk wanda yay ba dai-dai ba acikin kannenka ka hukuntashi amatsayinka na babban yaya tunda yanzu babu wani babba saurayi da yay saura agaban mu duk suna da iyali!'ya karasa fada yana mai shafa kan abdallah.
Abdallah jinjina kai kawai yayi tare da kwantar da kanshi akafadar kakan nasa yana mai jin wata yar sangarta na shigarsa nakasan cewarsa tare da kakan nasa.
Cikin lokaci kankani babban holl dinsu da suke taruwa dan taro muhimmi ya cika makil, saboda sanarwar Alhaji baba na cewar duk wanda yake nan kusa har yan kaduna yana bukatar ganinsu cikin gaggawa,wadanda sukai nisa kamar na kano ko wata kasa haka akayi connecting dan suma su sami damar jin abinda ya hada taron.
Kowa ya nutsu yana sauraron bayanin Alhaji baba ta macrophon,kowa ya gamsu da abinda yasanar dasu har wasu suna cewa ai da ko awaya yasar musu ma ya wadatar.
Alhaji baba yayi gyaran murya kana yace"dalilina na cewa lallai sai kowa yazo shine inaso ku dauki abun da muhimmanci kuma kowa yasan cewa abdallah shima jika naneeee
(Waiyo ni fadima sauri nayi na zubawa mutanen dake dankare a holl din Ido ko zan samu nasarar riga su abdallah gano bara gurbin cikin zuriar Alhaji balarabe sai dai kash babu wanda ya nuna wani abu afuskarsa da zai sa na diga masa ayar tambaya,kai wadannan mutane ko suwaye akwai shu'umai)
Abdallah ya zubawa fuskoki da yawa ido ko shima zai fahimci wani sauyi daga wata fuska saboda jin furucin Alhaji baba, sai dai shi din ma babu abinda ya fuskanta.
Ahlin Alhaji balarabe sun karbi abdallah da hannu bibiyu, anan ya dinga ganin wata kauna akan fuskokinsu kansa ya daure matuka dan yakasa fuskantar gaskiyar kauna da akasinta, duk abu daya yake gani dauke a fuskokinsu, dady ane, ma da dady jafar yasan bai gamsu da zuwan abdallah ba, bai fahimci komai afuskarsa ba.
Ahaka taron ya watse kowa na kokarin ganin ya nunawa abdallah shi mai kaunarsa ne baka da zuci, Alhaji baba da kansa ya rakashi har bangaren inno ya sadashi da hadadden dakinsa kana yace" yayi wanka ga abinci nan ya dade da rigashi zuwa sannan ya kwanta ya huta.
Godiya abdallah yayi wa Alhaji baba,shi kuma ya juya ya fita yana mai tunasar dashi karya sake yi mai godiya. wadawa yayi bisa lumtsumeman gadon da yasamu wata iriyar shimfida ta alfarma da wani hadadden bedsheet,kansane yaji yana neman barewa gida biyu saboda yawan hayaniyar da yashaka yau shi tunda yake bai taba shiga hayaniya irin wannan ba dole dady yay ta bashi hakuri da tausarsa akan ya jure ashe yasan komai akan yawan hayaniyar gidan anya kuwa zai jura?
Tashi yay yana layi ya nufi bayi jikinsa duk babu kwari hutu kawai yake bukata yanzu dan wannan hayaniyar tasa duk san aikinsa yaji ba zai iya fita aiki gobe ba.
Tunda aka sauke ta atashar bulayi kawai take acikinta batasan ko Ina ba batasan kowa ba, batasan inda zata nufa ba, can kusa da wata mai abinci ta samu ta rabe sai baza manyan idanunta take taga ta inda Allah zai kawo mai agazamata, da dai taga zaman take ga yunwa na nukurkusarta kawai sai taciro naira dari biyu ta kara matsawa kusa da mai abincin tare da yi mata sallama!' alokaci daya kuma tana mika mata gudar dari biyu tace"abani abinci!matar mai abinci ta bi bintu da wani irin kallon yau naga India mai jin hausa,girgiza kanta matar tayi tana mai cewa' yi hakuri 'yan mata bamu da irin abincin ku anan sai dai kije restaurant' a canne suke yin kowane irin abinci!'ta karasa maganar da juyawa tana kallon mutanen da suka taru arumfar abincin nata, kallon bintu suke cike da farinciki yayin da wasu suke musun cewa ai amisha ce wasu kuwa suce ai pretty ce,
Bintu ta rasa inda zatasa kanta kawai sai tafashe da kuka!' saboda ita bata saba shiga cikin jama'a ba, balle wadannan da suke tai mata surutu aka, ganin haka yasa wani babban dan union ya sa wasu samari suka kori mutanen,
Matar nan mai abinci ta dubi bintu tace" yan mata Ina zakijene na ga kamar kin dade acikin tashar nan ko kin manta hanyane?da sauri bintu ta daga kanta!' matar tace"ayya to bari nasa yarinyata ta nuna miki hanya,juyawa tayi ta kalli budurwar dake tsaye agefanta tana saurarensu, tace" basira maza jeki ki nuna mata hanya ki saka ta a keke napep, ta fada masa sunan anguwar da zai kaita dan naga alama bakuwace batasan ko'inaba!'ta mikawa basira wata leda tana cewa" ga wannan sai ki bata idan zata iya cin abincin mu!'bintu cikin shagwababbiyar muryarta da ta riga ta sangarce agun baffa da fafi tace"na gode mama Allah ya saka miki da alkhari!' mai abinci cikin jin dadi tace"babu damuwa ki gaida gida Allah ya kiyaye!'ta amsa da amin tare da jin dadin karamcin da mama mai abinci tayi mata.
Tun kan ma su fita daga cikin tashar suka samu mai napep,basira ta dubi bintu tace" wace anguwa za'akaiki? bintu shiru tayi tana son ta tuna sunan anguwar da fafi ya gaya mata amma ikon Allah shaf ta manta,mai keke yace"Ina gafa wannan hausarce tayi mata nauyi bari na lissafo mata sunan anguwanni ko zataji ta fada!'kafun ma basira ta tanka masa ya shiga lissafo manyan anguwannin masu kudi da fada aji, bintu tanajinsa har yanzu bai fadi makamanciyar sunan anguwar da zataje ba .gajiyar da tayine yasa yana cewa'mai tama sule tace"muje nan zani!'me napep yace au wai dama kinajin hausa kan uba alkur an ban zaci ta'iya hausaba kudurar Allah kenan!'basira tace da Allah mazarkwaila sarkin zaki wuce kuje ka kaita ka'ishi mutane da surutu kamar ba gobe!'dariya yayi kawai dan yasan gaskiya ta fada, mikawa bintu ledar take away tayi gami dayiwa junansu sallama,mai napep yaja suka wuce.
Hajiya anzo mai tama a'ina zaki sauka?ahankali bintu take bin anguwar da kallo,tare da manya-nanyan gidajen da sukayi mata kawanya,tunani take idan ta sauka to Ina zata nufa?wa tasani acikin wannan haddadiyar anguwa ?amma abin da tasanine dole ta sauka tunda itane ta zabi akawota nan din, dan haka tace da mai napep ya sauketa,burki yaja akofar wani haddaden gida yana mai cewa" hajiya kudinki naira dari uku!' batare da tace"komai ba ta mika masa dari biyun dazu da mai abinci bata karba ba,yana amsa ya figi napep dinsa ya kara gaba.
Tsuru tayi agefan gidan da ya ajiyeta tare da zabga uban tagumi,ji tayi cikinta yana wani kuuu sai alokacin ta tuna da yunwar dake dankare acikinta, gabas ta kalla kudu da arewa bata ga kowa ba dan haka a nutse ta juya baya taci abincinta, duk da bata wani ci mai yawaba cikinta ya riga ya cushe.zama ta cigaba dayi awajen ga tsoro da ya cika ta, fanfo ta hango daga dan nesa da ita da sauri ta karasa gun ta bude fanfon aiko ruwa ya zubo shaaa, cikin azama ta kafa kai tasha tayi nak, kana ta daura alwala ta dawo inda take, ta shimfida dan kwalin kanta tayi sallolin da ake binta kana ta dora da na filfilu, tana nan dai azaune har aka kira sallar magriba sai alokacin ta fara ganin mutane suna fitowa masallaci, wasu kuma sun dawo daga aiki, sai kuma taji hankalinta ya dan kwanta da taga jama'a musulmai suna hada-hadar shiga masallaci.
Sai da akayi sallar isha dayawan jama'a suka dinga fitowa daga masallacin,motace ta dallareta yayin da aka bude wawakekiyar kofar get din gidan da take rabe ajikinsa, cikin sauri ta mike saboda yadda idanunta suka mutu saboda hasken fitilar,
Bayan motar ta shige ne aka maida kofar aka rufe, sai kuma tsoro ya kamata, bintu sarkin kuka, take ta fara sana ar tata,sake bude kofar taga anyi da sauri ta zabura ganin wata girkakkiyar mata ta fito daga cikin gidan kai tsaye ta nufeta,bintu na ganin haka ta karawa kukanta sauti dan kuwa bintu matsoraciyace ta sosai, matar na zuwa ta jawo hannun bintu suka shiga cikin gidan, d'an da katawa matar tayi kana ta dubi bintu fuskarta babu yabo ba fallasa tace" kimin shiru ba wani abu zan miki ba mai gadine yasanar dani ya ganki ta CCTV tun dazu kina zaune banyi ma niyar kula kiba saida mai gidana ya dawo ya kuma yi min maganarki yace inzo na shigo dakeee...
Tofa yanzu aka fara wasan
Wai hannun wa bintu ta fadane? Shin zata samu nasarar shiga estate?idan ta shiga wace irin rayuwa take agidan ?a wane matsayin zata shiga?
Shin ya rayuwar abdallah zata kasance acikin ahlinsa? Anya kuwa abdallah zai iya zama cikin hayaniyar ahlinsa ko zai fece? Da gaske zai iya zabar abokiyar rayuwa acikin jikokin Alhaji baba? Wai kuwa Ina labarin dije?meye shirinsu Alhaji hashir ne da suke neman inda aka boye Alhaji abubakar? Ina hajiya zulaiha ta shige shin itama Bata gane gudan jinintaba abdallah?meye hakikanin zuciyar alhaji mansur ?akwai tambayoyin da bamuzo gabar yinsuba, ku biyoni Dan jin tarin amsoahinku.......
Comment.......
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
Wannan page din kacokan na sa daukar dashi ga yan fans din KUDURAR ALLAH ina matukar godiya gareku Allah ya bar kauna love u lodi-lodi..,..
```Page 11 ```
Tunda ya kwanta bashi ya farka ba sai da yaji kiran sallar asuba acikin kunnensa, ahankali ya bude manyan idanunsa dasuka koma wata kala mai matukar kyau da burgewa saboda baccin da bai isheshi ba, cikin yar kasala ya mike daga kan lallausan gadon nasa ya nufi hanyar toilet dan dauro alwala, yana fitowa yaji ana taba nock din dakin, ahankali ya karasa jikin kofar yana mamakin kowaye acikin wannan lokaci, ga tsananin mamakinsa Alhaji baba ya gani tsaye yana doka masa nutsatstsan murmushi wanda yake gauraye da wata irin mashahuriyar kauna,cikin tsananin kulawa yace" abdallah jikana fito mutafi masallaci ba nisa bane acikin estate dinnan yake dannasan haryanzu akwai gajiya atare dakai!'jinjina kai kawai abdallah yayi tare da kama hannun Alhaji baba yana cewa na fito, ai da kasani baka zo har nan ka wahalal da kanka ba sai mu hadu amasallacin!'Alhaji baba ya gyada kansa ayayin da suke jerawa yace" abdallah daka yanzu duk sanda kaga banzo na ta da kai mun tafi sallar asuba ba to ka kaddara aranka ba lafiya ba, dan tun daga yau na wajibtawa kaina, sai dai kuma idan baka nan ko na mutu ko kuma kayi aure kayi nesa dani!'adai-dai lokacin sukazo kofar masallacin dan haka zancen nasu ya yanke.
Ko da aka idar da sallah sun jima aciki suna karatun alkur'ani Alhaji baba ba karamin dadi yajiba da yasamu abdallah yadda yake tsammata, wato mai tsananin ilmin addini da kuma aiki dashi,saida gari ya danyi haske kana suka fito Alhaji baba har kofar dakinshi ya kuma rakashi kana ya dubeshi cike da kauna, yace"abdallah kaje ka kwanta za'akawo maka kayan karinka idan katashi nasan yanzu kana bukatar hutu!' ahankali abdallah yace"na gode!' alhaji baba bai saurareshi ba ya wuce dan komawa bangarensa.
Lumshe manyan idanunsa yayi wanda suke cike da zara-zaran eyelashes,yana mai jin kansa awata duniya ta daban, gashi dai acikin yan uwansa kuma mahaifarsa amma bayajin farinciki da walwala atare dashi, abu daya yaji tun shigowarshi gidan shine kauna da tausayin Alhaji baba sai kewa ta mahaifansa da ta lulllubeshi,yana jin kewar mahaifiyarshi saidai bazai iya haduwa da ita ba ahalin yanzu domin bazai iya jurar ganinta batare da ya nuna tsananin kewarta da dokinta agareshi ba,ko ita ma ta mantashi?ko tana tunanin sa ahalin yanzu?kwanciya yayi asaman gadonsa yana mai shafo tattausar sumar kansa da tai matukar kayatuwa wadda tai dai-dai da dan siririn sajen da ya kawata fuskarsa ma'abociyar kwarjini da haiba, rufe idanunsa yay yana mai kokarin gayyato bacci ko yasamu kansa ya daina masa ciwo.
Kaiwa take tana komowa kamar mai safa da marwa, can dai kuma ta zauna,tana mai cije bakinta ta rasa ma wani irin tunani zatayi karfa garin sanyin jiki tabari abubuwa su cakude mata, kai Ina ai haka ma baza ta taba faruwa ba,duk yakin da nakeyi shekara da shekaru amma ace lokaci daya wasu banzaye suzo sucini da yaki ina bazan taba barin haka ta faruba, sai na ga abinda ya turewa buzu nadi!' takarasa fada tana fitar da wani irin zazzafan huci.
Majalisar da take kasancewa afalon inno ce yau take ta tafka mahawara kowa da a bokin yinsa kasancewar bikin da yake ta da da matsowa dan yau sauran kwana goma afara shagalin bikin,shiyasa idan suka zauna basu da wani zance idan ba na yadda bikin zai kasance ba, amare hudu angwaye hudu sai dai dake da akwai zumunci tsakanin iyayen amaren da angwayen yasa komai za ayishi ahade dan haka suke cewa' bikin mutum takwas za'ayi 'acikin estate din na Alhaji balarabe,
Khadija da haulat yayan nana karama wadda suke kira da hajiya mama sai kuma yarinyar aunty hafsa, ita kuma suna mata lakani da maman maiduguri, ita kuma zata aurar da rukayya babbar yarta, yayan maman maiduguri gaba daya su hudun suna nan cikin estate kamar yadda duk dan da aka haifa ba daga cikin estate ba to sai yay kaura ya dawo cikin yan uwansa, shiyasa yaran gidan gaba daya suka taso awaje guda, sai Abdurrahim d'aga hajiya zulaiha yayan rahima, suna matukar ji da bikin nan kasancewar sun kwana biyu ba'ayi biki a estate din ba.
Hayaniya suke sosai sun cika falon da shegen musu, mazansu da mata kowa so yake asaurari zancensa dan haka hayaniyar tayi yawa har hawa kai takeyi, hatta inno da bata cika damuwa da harkokin hayaniyar suba yau sai da taji sun dameta,
Ahankali yake bude shanyayyun idanunsa da har yanzu suke cike taf da bacci dan ko karyawa har yanzu baiyi ba tun da suka dawo daga masallaci da Alhaji baba wani bacci mai cike da mafarkai kala-kala yay awan gaba dashi, shine bai farka ba sai yanzu da wata iriyar gigitacciyar hayaniya mai fasa kwanyar kai ta farkar dashi, hannu yasa ya dafe saman goshinsa yana jin hayaniyar har tsakiyar kokon kansa,mikewa yayi ya nufi tailed, wanka yayi kusan minti arba'i kana ya fito yana sanye da rigar wanka sai karamin towel ahannu yana tsane kanshi,.cikin mintuna talatin yagama shirinsa tsaf cikin shigar kananun kaya wanda sukabi zubin jikinshi da kyakykyawar kirarshi ta sadaukan maza, yayi matukar kyau na ban mamaki tamkar ka daukeshi ka gudu, ya feshe jikinsa da manyan hadaddun turarukansa masu kamshi, falonsa ya fita, inda ya kara jin sautin hayaniyar tamkar afalon akeyi, runtse idanunsa yayi yana mai jin wani irin zafi aranshi tare da takaici,gashi ba gwanin magaba ballentana yace zai musu magana,Amma tunda hakane abun lallai yaran nan zasuci kaniyarsu tunda ba yadda zaiyi, zaman gurin dole ya kamashi dolene ya dauki mataki idan ba haka ba babu shakka yaran nan zasu kasheshi da wannan kadadinnasu mara tushe da ma'ana,dan bai dauki hakan ako mai ba sai tsabar rashin tarbiya.
Kadan ya tattaba kayan karin da aka kawo masa, shima tea kawai ya sha, sakamakon rashin sanin daka Ina abincin suke, tashi yayi ya nufi hanyar fita babban falon cikin takunshi mai cike da nutsuwa da wata irin ta kama, kai kace sarkine amma shi bai san duk yana wannan ba, dan haka halittarshi take,
Wani irin sassanyan kamshine ya farayiwa kofofin hancinsu sallama kana ginshirarren takunsa mai cike da nutsuwa sai kuma kwarjininshi da ilhama wanda rabbi ya bashi sai kuma kyakykyawar fuskarshi mai cike da haiba, kai bazakace ya taba sanin yadda ake murmushi ba,
Tsit kakeji falon yayi ai tuni kallo ya koma sama ,mai sakin baki nayi mai zaro Ido nayi kan uban nan Allah mai kudura da irada tsarki ya tabbatar ga ubangijn da ya halicci wannan kyakykyawar surar cewar hauwa'u kenan da takasa kawadda da idanunta akan abdallah da yasamu wata kujera can nesa dasu ya zauna, zaman nasa ma kansa abin kallone, dukkanin su suka hadiye wani kakkauran miyau da ya daskare akan harshinansu,najib ne yay karfin halin cewa