Showing 153001 words to 156000 words out of 184937 words
ba to zai kashe min Sayyid,hakan ta farune agaban matata shi yasa ita ma take min kallon wanda ya sadaukar da rayuwar ɗan ta akan wata buƙata,Hajja Habibu ya sakani acikin haɗarurruka da dama,ranar da naga gobara a ɗakin da Abubakar yake baƙaramin tashin hankali na shigaba dan atunanina Abubakar ɗin ne ya ƙone, sai kuma ƙonewar ɗakin nan tamkar shine tashin rayuwa ta,da baibayin da aka yiwa bakina da zuciyata duk ya kama gaban sa,wanda kuma tun daga ranar na saka idanu sosai akan duk wani motsi da Habibu zaiyi saboda ina son tona masa asiri,na rasa da wanda zan hada kai domin ya zamar min shaida,sai kawai Alhaji Rufa'i ya faɗo min dan haka na tare shi da maganar ban sha wuya ba ya fahimceni muka haɗa hannu,daga nan shi ya bani labarin su Abdallah da binciken da suke akan wanda ya ɗauke Abubakar, duk da nayi mamakin hakan sai dai kuma da nayi tunanin shifa jami'i ne sai na daina mamaki, A hankali muka cigaba da bibiyar Habibu har muka gano abinda yake shiryawa na sace Bintu na kuma gano Abubakar yana gurin su Abdallah,shine dalilin da yasa naje wajen Alhaji jafar dan yasanar dani inda su Abdallah suke, tunda na tabbatar a ranar Habibu zai sace"Bintu amma sai yaƙi bani haɗin kai daga ƙarshe ma ya fito ya nuna min zargin da yake min akan Abubakar,Ni kuma hakanne yasa na rabu dashi ba tare da na gaya masa shirin da Habibu yake ba,daga baya ne na tabbatar Habibu ya sace"Bintu kuma na bibiyi Abdallah nasan cewa zai kai masa Abubakar kamar yadda suka shirya,duk da nasan wata ƙil da akwai wani shiri da sukayi a ƙasa, amma hakan baisa nayi kasa a gwiwar isa wajen ba,duk da kema kin so ki ɗan bani matsala gurin tafiyata gurin!'ya tsaya da maganar shi daidai nan,yana ɗan ajiyar numfashi,alamun dai yaji daɗin fidda abinda ke cikin ranshi shekara da shekaru,Hajja dai jugum tayi tana al ajabin yadda ɗan ta ya yaudareta,domin duk mugun halinta taso ace yaran ta sun kasance na arziƙi ko zata iya cin albarkacin su ranar lahira,amma yanzu ma ai ga Mansur nan,wata zuciyar tace da ita"ai kuwa kin san barewa bazata yi gudu ɗanta yayi rarrafe ba,halin ki ne sak Habibu ya ɗebo sai kuma yace kauce ki ban guri,tashi tayi tana cewa Mansur dan Allah in dai na isa da kai kaje ka kwanta ka ɗan yi bacci kafin kiran sallah!'shima tashi yayi yana cewa shike nan Hajja amma dai yanzu bazanyi ba sai nayi salla tunda kinji har har n fara kiran farko,idan na kwanta zan iya makara dan haka sai nayi sallah!'daga haka ya fita daga falon zuciyarshi sawai ta rage mugun nauyin da tayi masa, sai dai kuma tunanin inda Hajja ta kai Abubakar yake wanda yana sane dashi azuciyar sa,kawai dai yayi shurune yaga abinda Hajja zata shirya akan fitowa dashi, yasan wata ƙila ta kaishi wani gidan daban dan akula da lafiyar sa kafin dawowar sa gida.
A ɓangaren Anty Nafisa kuwa, A cikin daren ta yiwa Hajiyarta waya tasanar da ita ta shirya tarbar ta tare da arzikin da zata zo mata dashi,Hajiya ladidi da ta haƙura ta saduda ganin babu hanyar samun arzikin gidan Alhaji Balarabe,tace"me kike nufi nafisa? maimakon ta bata amsa sai kawai ta sheƙe da wata irin dariyar farin ciki kana tace"Hajiyata labarin mai tsayi ne abin da yasa ma bazan ce gobe zaki ganni ba saboda ina so sai jibi zan fasa kukan mutuwar sa daga nan na haɗo kan dukiyata nayo gaba!'ita dai Hajiya ladidi jin Nafisan take kamar almara wace irin kukan mutuwa kuma zata fasa?kafin ta samu damar yiwa Nafisan tambayar afili tuni ta katse wayar tare da kasheta gaba ɗaya,takaddun da take ta haɗawa na kadarorin Abba Umar su taci gaba da haɗawa,wanda daƙikiyar ƙwaƙwalwar ta tabata tabbacin cewa na gaske ne,sai da ta gama haɗa su tsaf kana ta tashi ta koma ɗakinta tayi kwanciyar ta tana juyin farincikin samun sabuwar rayuwa..
Kai tsaye ɗakin sa ta nufa,shiga tayi tare da ƴar sallama saman fatar bakinta,zaune ta ganshi kan sallaya da alama dai sallolin da baiyiba ya rama,wuceshi tayi ta shiga toilet ɗin itama,wanka tayi mai rai da lafiya wanda ta daɗe tana durzar fatarta,dan ji take kamar ta shekara ba tayi wankan ba,dan haka ta zage ta dirji fatar jikin ta da gashinta,har sai da fatar ta ta fara zafi ga jan da ta farayi abunka da farin mutum,alwala tayi ta ɗauro towel mai dan girma ta fito,wadrob ɗin sa ta bude wanda take da tabbacin ba zata rasa guntun kayanta anan ba,ilai kuwa ta samu wata doguwar rigar bacci mai santsi har da hijab dan haka ta ɗauka ta zura tare da saka ɗan turare kana ta zura hijab ɗin itama taje bayan shi ta tayar da sallar,saida sukayi sallar asuba kana suka koma biyan bashin baccin da suka ci...
Tun bakwai take zuba ido ko zataga daya daga cikin su yazo mata da maganar Abubakar,amma shuru take ji,gashi ta ƙagu taje tayi abinda yake gabanta,har daga baya ta yanke shawarar fara tafiya ta gabatar da babban ƙudurin ta,sai kuma ga sallamar Dady jafar a kofar falonta,duk da cewa ta riga ta shiryawa fuskantar kowanne daga cikin su amma sai da taji faduwar gaba,(Hajja kenan to ina batun kwanciyar hankali akan abinda babu Allah acikin sa)sauri tayi ta ƙara burkita yanayin ta tare da gaiyato tashin hankali kan fuskar ta,idanun ta kuwa ta shirya musu tun adaren jiya gasu nan sunyi jawur kamar gaske,zama yayi bayan ta amsa sallamarsa cikin wani irin yanayi da kukan da take ta san ƙirƙirowa kanta,Dady jafar yace"Hajja lafiya dai ko?cikin kukan da ta gama shirya zuwan sa tace"jafar ina fa lafiya,tun bayan dawowata gidan nan bayan rabuwar mu da Mansur yaran da na bawa ajiyar Abubakar da kuma likitan da na kai masa dan ya duba lafiyar sa,suka kirani suke sanar dani cewa Habibu ya tura abokan nan sa matsafa sun tafi da Abubakar ɗin!'ta ƙara sa maganar tana fyace hanci da haɓar zaninta,idanunta kuwa kai kace kukan tun daga ƙasan zuciyarta yake fitowa,da sauri Dady jafar ya mike cikin nuna mata tsananin tashin hankalin sa yace"innalillahi'wa'inna'ilaihi taji'un yasa hannu ya share zufar da ta tsatstsafo masa kana yace"shi kenan Hajja karki damu ai shi Habibun yana wajen su Abdallah dan haka zamu sa ya fito da Abubakar ko ta halin yaya fatana dai kar yasa sukasheshi!'Hajja ma mikewa tayi tana ɗan share hawayen fuskarta tare da cewa shikenan Jafaru amma kar wanda yasan da wannan maganar har sai mun sami nasarar kuɓutar da Abubakar daga hannun waɗan nan azzalumai!'yace"insha Allah Hajja karki damu komai zai tafi daidai!'daga haka sukayi sallama ya fita yana sakin wani ƙayataccen murmushi,yanzu ne ya kuma yadda da shu'umancin wannan mata,saboda shima yasan itace wannan matar me niƙaf tun ajiya Abdallah ya kirashi ya sanar dashi,ji yadda take yi tamkar wata ƴar wasan kwaikwayo,cikin ƙwarin gwiwa ya faɗa motar sa ya bar estate din ba tare da ya shiga ko ina ba.
Tana tabbatar da tafiyar sa,ta sheƙe da wata muguwar dariya,cikin jinjinawa kanta tace"saini Hajiya yagana mai buga gangar shaiɗan A bayan gida!'cikin takun ta na ƙaisa da alfahari ta shiga ɗakin ta,shiryawa tayi ta fito dan kaiwa ga inda zata cimma burinta.
Wayar sa ce ta tasheshi daga nannauyan baccin da ya kwashe su,kamar ba zai daga ba,sai kuma ya daga ganin Safwan ne akan layi,baiyi magana ba,sai daga can ɓangaren ne Safwan yace"sorry sir Abune ya taso na gaggawa,dama wannan Abigirl ɗin ce ta farka!'cikin sauri Abdallah ya ɗan zame Bintu daga jikin sa tare da miƙewa zaune,yace"Safwan kuyi mata duk abinda ya kamata kar kubarta cikin mummunan yanayin da zata kasa amsamin ɗinbin tambayoyin da nake son yi mata!'cikin girmamawa Safwan ya amsa kana suka katse wayar.
Cikin kanƙanin lokaci ta isa gidan saboda uban gudun da take sheƙawa,kai wannan tsohuwa akwai ƙarfin hali,ko da ike matan Alhaji Baba suna da matukar kyanjikin da bazaka iya tan-tance shekarunsu kai tsaye ba,shi yasa Hajja take jin kanta har yanzu da sauran ƙuruciyar ta,tana shiga suka shiga miƙa mata gaisuwa,yadda take amsawa ma kaɗai ya isa ya baka tabbacin yadda ta dauki KANTA,kujera aka dasa mata gaban Dady Abubakar wanda yake zaune hankali kwance,kai bakace saceshi akayi ba, murmushi tayi kana tace"da kyau yarona,da ganin alamu dai zaka iya bani haɗin kai cikin sauki ba tare da ka wahalar da hajjan ka ba!"ta faɗa tana wani shu umin murmushi,shima murmushin yayi tare da cewa,Hajja kar ki manta fa Ni ɗan ki ne ko nayi gaddama wa Habibu aike bazanyi miki ba,dan haka tambayeni duk abinda kekeson tambayata!'dariya tayi wadda ke cike da farin ciki kana tace"yauwa my son, shi yasa tun farko ka shiga raina ban taɓa kuma tunanin cutar da kaiba,inda dimon ɗin nan yake kawai nakeso ka faɗa min sai na mayadda dakai gida gaban iyayenka da ƴaƴan ka!'wata irin dariya ya sheƙe da ita, sai da yayi mai isarsa kana cikin muryar sa ta ainahi yace"kai wannan tsoho akwai shashasha!'sororo sukayi gaba ɗaya suna kallonsa cike da ɗin bin mamakin yadda akayi muryarsa ta canja lokaci guda,kafin ta gama fita daga mamakin da ya sakata ya kuma jefa ta cikin wani irin firgici da tashin hankali,sakamakon yaye fuskarsa da yayi,yacire fuskar ABUBAKAR da aka saka masa,fuskarsa ta cikakken bayerabe ta bayyana.
Wata irin zabura Hajjah tayi tare da dafe ƙirjinta da yake wani irin bugu,cikin rawar hannu da na baki ta shiga nunashi da yatsa,yayin da bakinta ya kasa furta abinda take son furtawa,da ƙyar ta iya fuzgo maganar tace"kai kaiwaye? ID ɗin shi ya curo ya nuna mata yana mai ɗage mata gira,yace"wannan duk lissafin yaro mai ƙwazone, Abdallah yayi nisa babu mai iya taradda dashi,tunanin sa yana tafiya daidai kuma aikin sa na tafiya daidai da abinda yazo tunanin shi,ku da kuna nufin a jakar kwaƙwalwar ku ke da ɗanki Abdallah zai dauko mahaifin sa ya kuma mayar da shi inda ya kubuta da ƙyar? girgiza kanshi yayi yana wata dariyar tura haushi,Hajja kuwa tsugunawa tayi tare da dafe kanta ta rasa abinda yake mata daɗi, wannan shine taga samu taga rashi,yanzu ya zatayi ke nan,kashe mutumin nan zatayi ko zata rabu dashi ne in yaso ta rokeshi ya rufa mata asiri ta hada masa da manyan kuɗaɗen da zai jima yana amfanarsu?kai anya kuwa hakan zata yuwu?Gara kawai tasa sukashe shi hakan shine zai zama rufin asirinta,to amma ya zatayi da ƙaryar data zubawa Jafar?meye manufar sa da bai gaya mata cewa ba ABUBAKAR ne suka zo dashi ba?tunawa da wannan yasa takuma shiga tashin hankali,sosai ƙirjinta ke bugawa tamkar wanda ake kiɗan ganga acikin sa,miƙewa tayi tare da yanke shawarar kawai ta cigaba da rike mutumin nan anan har sai ta tabbatar da cewa ba ganota Dady jafar yayi ba da har ya ɓoye mata,abinda suka aikata akan Abubakar,fita tayi tana cewa ku ci gaba da riƙe shi anan,koda ta zauna cikin motar ma kasa ja tayi jikin ta duk yayi sanyi,amma gaskiya yaron nan ya shammace ta da yawa,ko ina Abubakar ɗin yake oho?ita yanzu da zata samu tasan inda dimon ɗin nan yake ai da komai ma zata iya ɗauka,A hankali take jan motar tunani fal cikin ƙwaƙwalwar ta...
FATIMAH Y ADAM✍🏽
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page 56 ```
Yana gama waya da Safwan ya tashi ya faɗa toilet,wanka yayi ya shirya tsaf,kana yazo ya tsaya akan Bintu da har yanzu take ta shaƙar baccin ta hankali kwance,a hankali ya sunkuya ya kai bakinsa kan ɗan ƙaramin bakinta ya sumbata,wanda hakan ya farkar da ita, zuba masa ido tayi kana kuma ta ɗan tura baki tare da cewa nifa bacci nake ka tasheni!'ɗage mata gira yayi,ba tare da yace"mata komai ba yaja hannunta ya miƙar da ita tsaye, sannan a hankali ya kuma janta har zuwa cikin toilet duk bata ce mashi komai ba,sai da taga yana ƙoƙarin cire mata kaya,kana tayi saurin riƙe hannun damansa cikin tura baki tace"wai mi zakayi ne? cikin haɗe fuska yace"wanka zanyi miki!'zaro manyan idanunta dake matuƙar burgeshi tayi,kana cikin san ya tausaya mata,tace"dan Allah kabari zanyi da kaina!'ba tare da ya tanka mata ba,ya rabu da ita tare da ficewa daga toilet ɗin,wata doguwar ajiyar zuciya ta sauke kana tashiga tsaftace kanta.
Bata sameshi a dakin ba sai kayanta da ta tarar har da mayafi da alamu dai yanzun ma fita yakeso suyi,a nutse ta shirya duk da yunwar dake sakaɗar ƴan hanjinta,tsaf ta fito da ita cikin doguwar rigar atamfa mai kalar kore da baƙi, sai hakan ya kuma haska kyawunta da ƙuruciyar ta suka kuma bayyana,takalmin ta ta zura bayan ta feshe jikinta da sassanyan turarukan sa,fita tayi cikin wani irin taku tamkar wata ɗawisu.
Zuba mata ido yayi yayin da yake zaune bisa kujerar dinning table,shigarta,da nutsatstsiyar kwalliyarta da babu hayaniya, ƙamshinta da yanayin takunta shi ya fi tafiya dashi,A hankali ya lumshe idanunsa tare da kwantar da kansa jikin kujerar,jinta dafdashi yasa shi ƙara buɗe idanun yana binta da wani irin kallo wanda ita kuma yake karya duk wata laka dake jikin ta,zama tayi tana bin jerin kwanayen abin karin dake kan table ɗin da kallo,zatayi magana ya rigata da cewa,inno da Hajiya Babba ne suka aiko dashi!'ya faɗa idanunsa na kanta bai ko rissuna su wajen kallon nata,ƙasa tayi da kanta tana jan yatsunta,ita kam ta rasa wannan kallon ko na magani da meyene?katse mata zancan zuci yayi da cewa,ki zuba mana ina saurine!'tashi tayi ta fara saven ɗin sa kana ta zuba itama,yunwa take ji dan haka ba ta tsaya nawa ba ta zage ta cika cikinta,shi dama Abdallah ba baya bane wajen bawa ciki haƙƙin sa,sai da suka gama kana suka fita falon inno,azaune suka sameta ita da taufiƙa wanda rabon da Bintu ta ganta har ta manta, Abdallah kuwa baima shaida ta ba,amma ita idanun ta tamkar zasu faɗo wajen kallon sa,har sai da Bintu ta samu kanta da zabga mata harara,gaishe da inno yayi,ya na gyara zaman agogon hannun sa, Bintu kuwa zuwa tayi jikin innon ta kwanta tana zuba mata shagwaɓa,inno tace"nikam zaki ƙarasani ne? jikina ba irin na mijinki bane mai ƙwari!'ta faɗa cikin dariyar farin cikin ganin su cikin walwala,tura baki Bintu tayi ba tare da tace" komai ba sai idanun ta dake kan Abdallah da take ganin kamar yana kallon Taufiƙa,kawai ji tayi idanunta sun kawo ruwa wanda kuma bata san dalilin hakan ba,Muryar Taufiƙa ta tsinkayo tana gaida Abdallah, ai ko da sauri ta kuma maida hankalinta kansa dan taga yadda zai karbi gaisuwar,amsawa yayi yana ƙoƙarin ɗora waya A kunnen sa,duk da taga yadda yayi amma hakan baisa taji nutsuwaba,juyowa yayi yace"da inno zamu fita amma bazamu jima ba!'inno ba ta tsaya tuhumar inda zasu ba,tayi musu fatan nasara,tashi Bintu tayi ta bi bayansa tana jin kamar ta tsinkawa Taufiƙa mari,Wanda ita kuma Taufiƙan fiye da haka take ji akan Bintun,duk sanda zata ga Abdallah to kuwa sai taji ana ƙara iza wutar san sa a zuciyarta,dan ma bata nan kwana biyu ita da Siddiqa da tasan abin sai yafi haka yawa azuciyar ta.
Yana kula da yadda Bintun ke ta faman cin magani,saboda duk wani motsinta akan idanun sa ne,shi dai bai ma gane Taufiƙa ba bare ya gane dalilin hararar da Bintu ke antaya mata,shiga mota sukayi duk da yaso yashiga ɓangaren Hajiya Babba da Alhaji Baba Amma hakan bai samu ba sakamakon saurin da yakeyi,Bintu na ƙoƙarin shiga suka haɗa idanu da Anty Nafisa,ɗauke kai tayi tare da rufe ƙofar,tana mai ci gaba da kallon Anty Nafisa ta cikin baƙin glace ɗin window motar,sosai ta hango tashin hankali kwance kan fuskarta da kuma asalin mamakin da ya rufeta wanda Bintu bata san na meye ba,ji tayi ya jiyo da kanta saitin sa,cikin al'adar sa ta dage gira yace"Ni zaki kalla ba itaba!' so tayi ta harareshi saboda haushin sa da tasamu kanta da ji,amma sai taji baza ta iyaba hakan ne yasa ta juya hararar zuwa wani irin kallo na musamman da bata san ta iyashi ba,kuma batasan halin da yasaka wanda aka yiwa kallon ba,kawai dai taga ya koma ya kwanta sosai yana ɗan lum-lumshe idanunsa tamkar wanda yake shirin komawa bacci,A hankali ta tsinkayi Muryar shi yana cewa,me haka Bint?me nayi Makine?ita zaton ta fushin da takeyi yake tambaya,dan haka sai ta kuma tura ƙaramin bakinta tana magana ƙasa ƙasa,ba waccen Taufiƙan ce take ta kallon ka ba!'sam Bint bata fahimci komai akan abinda tayiba hasalima bata san manufar yin hakan ba,buɗe ido yayi sosai yana kallon fuskarta dake a kwaɓe da alama dai har yanzu da haushin abun atare da ita,dogon hannun sa yasa ya jawota jikinsa gaba ɗaya,ya kuma haɗa fuskarshi da tata,ba tare da yace"da ita komaiba,sai numfashinsa da yake saukar mata kan fuskarta,kwantar da kanta tayi sosai tana jin abinda ya tsaya mata na sauka A hankali,sai kuma ta shiga fitar da numfashi mai ɗauke da manufar samun nutsuwa.
Hajiya zulaiha dake tsaye itama ta lumshe idanun ta tare da cewa,insha Allah ka kusa dawowa gareni,inajin haka ajikina,tun sanda na fara ganin Abdallah nake jin wani abu game dashi wanda nake fata ya zama gaskiya!'Rahima dake bayanta tace"Ammi kamar me?kuma dama baki taɓa haɗuwa da Yah Abdallah ba tun tsawon zaman shi agidan?Hajiya zulaihat tace"ban taɓa haɗuwa dashiba ban taɓa ganin sa ba,sai a daren jiya da suka dawo akan idanuna!'Rahima tace"wallahi Ammi nima inajin kwatan kwacin abin da kike ji,to komeye dalilin hakan?kama hannun ta tayi suka shige falon tana cewa,Rahima Allah ne masani shi kaɗai yasan abinda ke ɓoye,sai dai muyi fatan duk abinda zai biyo baya ya zama Alkhairi!'..
Cikin wani irin tashin hankali da sauri mai haɗe da gudu ta koma ɓangaren ta, cikin karkarwar jiki ta zaro wayarta daga jaka har tana neman faduwa,wajen kira ta shiga ta nemo nomber da zata kira,wayar sai ƙoƙarin faɗuwa take saboda yadda jikin ta ke rawa,da ƙyar ta