Showing 72001 words to 75000 words out of 184937 words

Chapter 25 - KUDURAR ALLAH COMPLETE BY FATIMA Y ADAM

21 Jul 2024

16864

da buwayar sa.


Wani irin farin ciki Alhaji Baba yake ciki dashi kansa bai san adadin sa ba, Abba Umar kuwa bayan farin cikin da ya tsinci kansa aciki hakanan sai tsohon mikin sa ya kuma tashi, can dakin mahaifiyar sa ya nufa ya sauke mata damuwar sa kamar yadda yasaba,ita kuma ta tarbe shi da tsantsan soyayya da tausayi wanda yake tsakanin uwa da ɗanta,duk da cewa itama tana cikin wani irin hali na damuwa da kewar gudan jininta da kuma farin cikin wannan Aure ji take kamar ta taka rawa saboda tsananin farin ciki,tana shafa kansa tana murmushi mai ɗauke da kishiyoyin ma'anoni, cikin taushin lafazi take cewa, Allah Ubangiji yasa Auren nan yazama sanadin wani haske da zai baiyana nan ba da jimawa ba cikin wannan ahlin, Allah Ubangiji yasa wannan Aure daka ɗaura ya zama sanadin kawo farin ciki A rayuwarka data ahlinka, Allah Ubangiji yasa wannan Aure yazama shine sanadiyyar ruguza duk wani ƙulli da aka ƙullashi acikin gidan nan!'da Amin Amin yake ta amsawa yanajin wani farin ciki da tun faruwar al'amarin bai kuma samun makamancin sa ba,(to nima dai ina yi muku fata da addu'ar ɗorewar farin ciki da kuma bayyanar gaskiya mu kuma Allah ya kawo mana ƙarshen masifun da suka addabi kasarmu ya kawo mana kuma farin ciki A cikin al'ummar mu yatabbatar mana da shugabanni masu adalci Amin Ya Allah)

Tofa FANS Taufiƙa sai ku zama cikin shirin abinda zai faru idan taji wannan labarin

Ko ya Abdallah da Bintu zasu ji idan suka sami labari? yaya Bintu kuwa zata karɓi aikin da Anty Nafisa ta bata?to wai ya zaman Aure zai kasance tsakanin waɗan nan taurari?Samira kuwa zata sami nasara akan Alhaji Sama'ila?kai dama sauran manyan tambayoyin da suke ƙulle acikin wannan rikitaccen labarin wanda da sannu zan warware muku zare da abawa dan haka sai ku shirya ku kuma kimtsa yan zu akasoma.

Fatima y Adam✍🏽
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 31 ```


A wannan rana zuciyoyi da yawa sun baƙanta wasu kaɗan daga ciki kuma sun faranta,taɓan garen,inno dai har yanzu zuciyar ta tana cikin zulumi da wasi wasi zuwa yanzu ta fara hararo tabbas A kwai wata maƙarƙashiya cikin al'amuran Bintu, da akwai wani ɓoyayyen sirri wanda bakowane yasan da shiba domin idan ba haka ba meye ruwan ahlin ALHAJI BALARABE da rayuwarta? meye yasa ake binta da sharri da makirci haka alhalin babu hurumin ta cikin mugayen al'amuran gidan, tabbas da A kwai wani ɓoyayyen sirri wanda insha Allah ita kuma sai ta binciko shi tare da taimakon Allah, amma bazata zuba idanu alalata rayuwar marainiyar Allah ba,tayi farin ciki da wannan Aure amma ta wani ɓangaren tana jin wata irin fargaba tanaji kamar wani abu zai iya samun Bintu ta rasa me mutanen gidan nan suke nema haka da kowa idansa ya rufe da salon mugunta da makirci na rashin imani idan ba rashin imani ba kamar Bintu za'a ɗorawa alhakin kisa har kuma a rufeta,ga kuma Abdallah da ba dan Allah yasa da sauran shan ruwan sa ba da yanzu batun wani ake bana saba, kai Allah ya kare mu daga sharrin zuciya ya tsare imanin mu.


Ita kuwa Hajjah ƴar duk inda ta daɗi sha ce,bata zauna da Bintu ba bare tace" ga abinda zata iya aikatawa da wanda baza ta iya ba,kawai dai ita tana tsakiya babu ruwanta da duk wani al'amarin da yake gudana A cikin ESTATE ɗin ita abin da ya dameta shine damuwar ta, ba ruwanta da shiga shirgin da ba nata ba ko ba asata cikin saba,amma tana da zafi idan kataɓota,kuma bata fiye ɗaukar matsalar wani matsayin tata ba,amma idan ka zauna da ita tana da fara'a dan zan iya cewa duk cikin matan Alhaji Baba ta fisu sakin fuska da wasa da jikoki shiyasa dayawa jikokin nasu sun fiyi mata wasa akan su Hajiya Babba da Inno,kuma tun yaran gidan suna ƙanana idan sukayi laifi itace mai hukunci,shi yasa ta wani ɓangaren suke bala in tsiron Hajjah,dan haka yanzu ma tuni ita ta manta da batun Bintun sai da taji sanarwar Auren ne take cewa to shi Abdallah yaji sauƙine? Jabir da shi ya kawo mata tsegumin ya bata amsa da yaji sauƙi,daga haka bata ƙa ɗaga zancen ba sai fatan Alkhairi da tayiwa Auren.




Ita kuwa Hauwa'u dama tuni tasawa zuciyarta dan gana, dan taga yanzu faɗan yafi ƙarfin ta na manyane sai dai ta koma gefe ta taya Taufiƙa yaƙin tunda ita taga zata iya amma zata bada gudummawa wajen ƙuntatawa rayuwar Bintu ita yanzu tuni ta haƙura ta amshi soyayyar Nabil da ya daɗe yana mata naci, ya fiye mata kwanciyar hankali akan taje inda ba asan da ita ba balle akai ga batun so.



Hajiya zulaiha ta kai ta kawo yafi sau goma gaba ɗaya kanta ya ɗaure da wannan al'amarin,ta zurfafa tunani sosai akan Bintu kuma tabi duk wasu hanyoyi dan ganin ko zata kama Bintu da wani laifi amma bata gani ba, tabbas yarinyar nan ta shiga komar magauta akwai ayar tambaya fa meyasa suke bibiyar ta kamar yadda suke bibiyar duk wanda ya kasan ce ahlin ALHAJI BALARABE wanda yake da masaniya akan ɓoyayyen sirrin nan?gaskiya abin nan da matuƙar ɗaure kai ita yanzu sanadin wannan muguwar rayuwar da ake yi A cikin ESTATE ɗin nan yasa duk ta hana ragowar ƴaƴanta zaman cikin gidan ko wanne ya lula wata ƙasa shida iyalan sa Rahimace kawai ta rage mata a gabanta,anya kuwa da wanda aka cutar a cikin ahlin nan sama da ita, ansa ta rabu da yaranta wanda suke sune sanyin idaniyarta abin alfahari agareta duk saboda kar acutar mata dasu ko arabata dasu kamar yadda aka rabata da hasken zuciyarta da kuma mijinta abin alfarinta me share mata hawaye a koda yaushe da yawan lallashin ta,wani irin kuka ne ya kufce mata mai azabar raɗaɗi,me cike da kewa ta rashin masoya guda biyu.


Wurgi takeyi da duk abinda yazo hannun ta, Siddiqa da Farida ne suke ƙoƙarin kamata duk tabi ta jiwa kanta ciwo saboda gilasan da ta fasa kuka take tare da wani irin ihu na tsan tsan baƙin ciki da takaici,da suka kasa tsaida ita sai suka ruga suka kira inno, inno tayi matuƙar mamakin wannan haukan na Taufiƙa,cikin muryar da take ɗauke da tsantsar baƙin ciki tace"Taufiƙa Ni dai wannan halin naku na ɓaƙin hali da shegiyar baƙar zuciya ba acikin zuriyata kuka sameshi ba,dan duk cikin yarana mata shida cas ban haifi me baƙar zuciya da mugunta ba sai dai acan dangin ubanku kuka kwaso wannan mugun halin, tur wallahi Taufiƙa kinji kunyar rayuwarki da babbar asarar da idan baki gyara halinki ba rayuwarki bazatayi kyau ba,kuma har abada ke da Abdallah dan ya riga yayi miki nisa wutsiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa,baku dace ba ko ta wanne ɓangare, Bintun dai da kika tsana da ita ya dace Allah baya jarabtar kamilin mutum kamar Abdallah da Auren mace irinki, kina zaune a gidan nan zakiyi kallon yadda ake zaman Aure mai cike da mutunta juna kina zaune a gidan nan zakiga yadda Abdallah zai maida Bintu sarauniyar mata kina zaune a gidan nan zaki kalli soyayyar da baki taɓa ji ko gani ba arayuwarki, kina zaune a gidan nan zakiga yadda Abdallah zai durƙusa ya juya baya Bintu ta hau ya goyeta ya sa majanyi ya ɗaure kuma kina zaune zakiga yadda yarinyar da kika ƙasƙantar zata juya mijin da kikaso kike gani ya wuce ajinta, kina zaune kuma zakiga yadda Bintu za tayi taƙama da estate din nan kamar yadda kike mata borin tsiya,haka kuma kina zaune Bintu zata riƙe arzikin da baki taɓa mafarkin samun sa ba arayuwar ki, Taufiƙa Ni na gaya miki wannan wataran ko babu raina sai kin tuna da wannan kalaman nawa saboda da ikon rabbil izzati duk abinda nazana miki sai sun tabbata A kan rayuwar Bintu saboda ita ɗin kamar waliyiya take saboda wankakkiyar zuciya bata nufin kowa da sharri sai Alkhairi, wannan alkairin shine zai bibiyi rayuwarta da dukkanin zuriyarta insha Allah!'daga haka ta fita daga ɗakin cikin farin ciki saboda ji take ta fato Taufiƙa a kan yadda ta daɗe aranta, ta wanke takaicinta na tun ranar da suka dawo gidan akan abinda sukewa Bintu gashi tana jin abinda ta faɗa tamkar sun riga sun tabbata akan bintun duk da tasan a kwai ƙalubale cikin rayuwar ta to amma tayi yaƙinin cewa da sannu wannan lokacin zaizo.


Sayyid ma yashiga halin ɗimauta da jin wannan al'amari, saboda akwai shirin da yasoyi kafin faruwar lamarin to amma dai ko yanzun ma babu abinda zai dakatar dashi daga aikin da aka saka shi duk da bai san wanda yayi wa Bintu wannan test ɗin ba amma dole zai bincika ya nemo wanda ta haɗa kai dashi ko wanda yasa ta aikin dan yanzu aikin da aka bashi kenan kuma da sannu zai zamu nasarar aiwatar da abinda yake aikin sane, dan ya ɗau alwashin ba zai bawa waɗan da suka sakashi aikin Nan kunya ba.


Acan cikin copy kuma Samira ce tare da Alhaji Sama'ila zaune bisa kujerun ƙarfe sai ƴan kayan lashe lashe agabansu,Alhaji Sama'ila ne ya dubi Samira cikin zaƙuwa da san jin abinda zatace masa yace"Samira inajinki jiya da tunanin maganar da zamuyi nayi bacci!'murmushi tayi kana tace"abinda zan gaya maka wani Abune da ya shafi rayuwata wanda kuma naga ka can canta da nasanar dakai saboda yadda da zaman amana!'jinjina kansa yayi cike da gamsuwa da jin daɗin lafazinta,ta cigaba da cewa,shiyasa na shirya gaya maka duk wani sirrina wanda zaka iya zuwa kaji shi a wani baki na da ban, kuma hakan zai iya kawo mana saɓani cikin kyakykyawar mu'amalar mu!' katse ta yayi da cewa duk naji wannan na kuma fahimta ki sanar dani abinda yake faruwa kai tsaye karki samu damuwa!'ƙasa tayi da kanta kana cikin taushin murya tace"Ni dai na kasan ce ƴar babban gida kuma wadda take da tarin dangi da ƴan uba saboda mahaifinmu yana da tarin mata,shiyasa ya tara ƴaƴa da yawa,haka kuma yana da tarin dukiya wadda har ta zama abar kwatance cikin jama"a,amma abin mamakin sam mahaifinmu baya mora mana da ko biyar daga cikin arzikin sa kowa sai dai ya nema da kansa, matan mu da mazan mu hakan ne yasa har so muke muga mahaifin mu ya faɗi ya mutu,ganin abubuwan suna daɗa yawa sai kawai mukayi shawara a junan mu na me zai sa mu kasheshi tunda yaƙi mutuwa, wannan shawarar duk munyi amanna da ita amma iya mu waɗanda suke da buƙatar hakan,dan haka muka shirya da wasu ƴan daba mukayi ciniki dasu suka shiga har gida suka soka masa wuƙa, wannan shine sanadin mutuwar mahaifinmu kuma mun sami abin da muke nema na dukiya da kadarori!'sauke numfashi tayi tana dauke kanta ƙasa cikin sanyin murya tace" masa wannan labarinne bana so kazo kaji daga baya ka tsaneni shiyasa naga gara na faɗa maka da bakina saboda ka fahimceni!'shiru gurin ya ɗauka na wasu daƙiƙai daga bisani Alhaji Sama'ila ya gyara zamansa tare da goge zufar da ta ɗan taru saman goshinsa kana yace" Samira yanzu nadamar abinda kika aikata kike kome?shiru ta ɗan yi kana kuma tace"bazan yaudareka ba Alhaji Sama'ila sam bana nadamar abinda na aikata koda zuwa za ayi A tafi dani akan laifin kisan mahaifina!'ta ƙara sa maganar cikin nuna taurin zuciya, murmushi yayi tare da cewa gaskiya Samira kin burgeni wannan abin da kikayi shine ya nunamin zaki iya zama dani kuma zamu gudu tare mu tsira tare, tabbas zan iya saka ki cikin tafiyar mu,dan haka nima zan gaya miki kaɗan daga cikin aikin da mukeyi a yanzu amma ba yanzu ba sai mun sake zama!' tace"amma ko na jiya ne ka sanar dani saboda hankalina ya tashi sosai!'yace" kar ki damu ba komai bane wannan muna kan war ware matsalar tace" duk da haka dai yakamata ka faɗa koda taimakon da zan iya yi maka!'ɗan jim yayi kana yace"hakane,bata labarin abinda ya faru da Bintu da Abdallah yayi tare da yi mata bayanin abinda suke nema ya dai yi mata bayanin komai ataƙaice ya kuma ce zai sakata cikin tafiyar tasu,cikin farin ciki tace"amma da kasan da wannan business ɗin baka taɓa tallata min ba, Alhaji Sama'ila ya ƙyalƙyale da dariya cikin dariyar yake cewa to ai gashi yanzu na tallata miki har ma na siyar miki da ita!' itama dariyar tayi kana kuma ta ɗan maida fuskarta serios tace"kuma ku bakwa tunanin wani ko wata da zai iya sakata yin hakan?girgiza kansa yayi tare da cewa, gaskiya bama tunanin kowa,dan A binciken da muke kanyi kenan!'ta wacce hanya kake gani zanbi dan taimaka muku? yace" zamuyi maganar da sauran team ɗina idan ta kama ma ayi mitin ɗin dake duk zan sanar miki!'murmushi tayi tare da saurin danna sevin a recording ɗin da tasaka kana ta miƙe tace"to shike nan dear Ina nan inajiranka ni zan wuce gida!'muje nima ai wucewar zanyi!'daga nan suka taka har zuwa bakin motar Samiran, ya buɗe mata ta shiga suka kuma yin sallama kana ta ja motar sai da yaga fitar ta kana shima ya shiga tasa ya bar gurin.



Sai da yagama sauraren recording ɗin kana ya ɗan yi wani muskilin murmushi,karkuso kuga fuskar Abdallah da murmushi saboda matuƙar kyan da yayi masa kumatunsa saida ya loɓa irin na Bintu,cikin daddaɗar Muryar sa yace"na gode Samira kinyi ƙoƙari sosai ina fatan mana nasara cikin dukkanin aiyukan mu dana yanzu dana gaba!'amin ya hayyu ya ƙaiyumu,ta faɗa tana ƙoƙarin ta shi sallama tayi masa,bayan fitarta ya ɗan jingina bayansa da makarin kujerar tare da lumshe shanyayyun idanun sa,ko ya waccen rigimammiyar take ciki? tun ɗazu ya bada take away a ka kai mata ko taci ta haƙura da kukan oho mata rigimammiya kawai, tsadadden agogon dake ɗaure a hannun sa ya kalla ƙarfe uku da arba'in miƙewa yayi ya kwashi tarkacen sa kana ya fita, masallaci suka fara shiga sukayi sallah daga nan suka nufi gidan sa na area 1.



Lokacin da aka kawo mata take away ɗin tuni ta daɗe da tashi tayi wanka ta mayar da kayanta, dan haka ana kawo mata ci tayi ta ƙoshi,daga nan kuma sai duk tsoro ya rufeta ta kalli ko ina taga ita ka ɗai ce,sai tsoron ya kuma kamata tuni ta fara ruwan hawaye daga ƙarshe ma ta saki kukan gaba ɗaya,da taji motsi sai ta zabura acikin wannan halin ya shigo ya sameta wanda ita saboda rigima ba tasan yashigo ba kukan ta kawai takeyi tamkar wanda yake mata daɗi,ɗan tsayawa yayi yana dubanta wai ita kuka baya mata wahala ko yanzu me akayi mata kuma oho? ɗan tsaki yayi wanda shi ya ankarar da ita, da gudu ta miƙe zata gudu yayi saurin sa mata doguwar ƙafarsa aiko tuntuɓe taci ta zube ƙasa tana riƙe ƙafar cikin tura baki tace"to Ni me nayi maka kuma naga dai kai kabani tsoro!'harara ya zuba mata batare da yace"mata komai ba ya wuce dan shiga ɗaki, da gudu ta tashi tabi bayan sa,ɗan juyowa yayi yayi mata kallon ki kiyayeni ɗan marairaice wa tayi tare da cewa Wallahi Oga Abdallah tsoro nakeji!'ki shirya zamu koma gida da sauri tace"nan ba agida muke ba wane gidan kuma zamuje? ESTATE ya faɗa tare da cigaba da tafiya,tunda ya faɗi kalmar estate jikinta yayi sanyi zuba masa ido tayi har ya shige ɗakin sa, A hankali takoma ta shiga ɗakin da take ta ɗauko mayafin abayar jikinta, falon ta dawo ta zauna tare da zuba ta gumi anya kuwa zata iya ci gaba da rayuwa a cikin wannan ahlin? anya zata iya cigaba da zama ana ƙulla mata sharrin kisa?idan kuma basu karɓe ta bafa? inno fa ga Hajiya Babba itama tasan duk sun tsaneta yanzu kallon makashiya suke mata, ta tuna lokacin da ƴan sanda suka tafi da ita babu wanda yayi yunƙurin ceton ta babu wanda ya nuna alamun ya yadda da abinda ta faɗa,ya zatayi ta iya zama da inno cikin halin tsana da ƙyama? tabbas a wannan lokaci baza iya duban idon inno da Alhaji Baba ba, ga kuma Hajiya Babba matar da tabata yadda a rayuwa, kallon ƙofar ɗakin da yashiga tayi haka kuma zuciyar ta na cigaba da tunzura ta akan ta tashi ta gudu tun kafin ya fito ya mayar da ita cikin wannan gida mai kama da ramin macizai a wajen ta, cikin sanɗa ta miƙe batare da ta yadda tayi wani motsi mai ƙarfi ba, da sauri ta gangara ƙasa cikin Sa'a ta samu ƙofar falon babu security cikin hanzari ta fita, dai dai lokacin kuma mai gadin ya zaga baya, dalilin kenan da tasamu damar fita batare da kowa ya lura da ita ba.


Cikin hanzari ya fito falon ganin bata nan sai ya ɗan ƙonƙosa ƙofar ɗakin nata jin shurun da yayi yasa ya shiga yana mai tunanin yanzu haka kuka take tunda ba gajiya take dashi ba idan tanayi har wata jiniya take masa da ado dan ya kuma yin daɗi,zubawa ɗakin ido yayi tare da ɗan kasa kunnensa ko zai ji motsi a banɗaki sai dai har kusan mintuna biyu baiji motsin komai ba, takawa yayi A hankali ya isa bakin toilet ɗin saida ya ɗan kasa kunnensa kana ya tura ƙofar,ga mamakinsa bata cikin toilet ɗin,da sauri ya fita tare da sauka babban falon ya shiga dubawa ko wane ɗauki daidaita duba kiching da sauran guraren dake cikin falon amma duk neman sa baiji koda motsinta tsorone yafara kama shi karfa a shigo har cikin gidan nan a sace yarinyar nan,a hankali ya fara kiran sunanta tun yana faɗa a hankali har ya koma ɗaga muryar sa amma shiru a yadda ya lurama babu kowa cikin gidan fita yayi can wajen get,sojan me gadin ya shiga ƙwalawa kira kamar zai dake shi,da sauri ya ƙara so inda yake jiki na rawa gani ranka shi daɗe!' cikin fusata Abdallah yace"wa kagani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login