Showing 87001 words to 90000 words out of 184937 words

Chapter 30 - KUDURAR ALLAH COMPLETE BY FATIMA Y ADAM

21 Jul 2024

16899

tayi akusa da ita,kana cikin tausayin surukar ta ta tace"dan Allah Hajjo ki daina yawan damuwar nan bana so ciwon ki ya tashi kin ga dai yadda Alhaji Umar yake damuwa idan yaga halin da kike ciki,bayan shima ba cikakkiyar lafiya ce dashi ba, gamu nida ƴan biyu duk ba mason rasaki saboda ke kaɗai ce muke gani muji sanyi idan kika bari lalura taci ƙarfin ki tabbas zamu shiga damuwa!'wani wahalallan numfashi ta sauke kana cikin muryar da take cike da damuwa tace"Asma'u ina matukar ƙoƙarin da dauriya wajen danne abinda ke taso mun,babu yadda zanyi ne Asma'u ƴara biyu har da jika babu su babu labarin su,kema nasan dauriyar kikeyi amma ki sani Ni dake a kwai banbanci ke da ragowar ƙuruciya atare dake Ni kuma girma ya fara cim mani dole yanayi na danaki su banbanta,hannu tasa ta share hawayen da suke ta ambaliya kan fuskarta tare da cewa,kullum addu'a ta da fatana shine inga Laila da Sulaiman,fafi take nufi (afwan ban faɗi sunan fafi na asaliba sunan sa Sulaiman)ina son ganin su kafin na bar duniya!

Asma'u tace"Hajjo insha Allah burinki zai cika zasu dawo gida, kamar yadda suka tafi tare haka zasu dawo tare harma da jikallenki, ta ƙara sa maganar cikin san kautar mata da damuwarta.


Tunda ya fara sauraran recording ɗin da Samira tayi na tattaunawar su da Alhaji Sama'ila,ya rufe idanunsa yana mai ƙara tasbihi ga Ubangiji tare da gode masa da yashirya rayuwarsa ya ƙawata zuciyarsa da tsoron sa da kuma ƙauna ta masoyin da babu kamarsa Annabi Muhammad swa,jin maganar ta tsaya yasa a hankali ya buɗe idanunsa da suka sauya kala saboda ɓacin rai me tsanani da ya mamaye zuciyarsa,duban Safwan yayi tare da cewa ina so a yau din nan a kamomin Sayyid ku kaishi can gidan sirri ku ɓoyeshi,ina so ku kula da aikin ku bana buƙatar Kowa yaga lokacin da kuka ɗauke shi!' Safwan yayi salut ɗin sa tare da cewa angama Oga insha Allah baza asamu kuskure ba!'jin jina kan sa yayi tare da mai da dubansa kan Samira yace"Samira na gode da taimakon ki!'da sauri ta katse shi da cewa haba meye na godiya kar ka manta da wannan aiki na ne kuma saida na ɗauki alƙawari kafin na fara, dan haka ya zaman min dole na jajirce dan taimakon al umma!'na sani duk da haka kin cancanci lambar yabo aikinki yana kyau sosai!'godiya tayi masa kana sukayi sallama ya sallame su,shima daga nan ya kira Yahya su tafi dan yana son leƙawa asibiti.


Bintu tunanin ta hanyar da zata samu ta isar da saƙonta gurin Hajiya ladidi da Nafisa,ne hanyar da zata fara tarwatsa dangantakar su ko dan ta samu abin da takeso duk da tasan shiga tsakanin ɗa da uwa sai Allah, amma tanada yaƙinin Allah bazai kamata da haƙƙin su ba, tunda neman samun warware wani babban ƙulli take wanda zaiyi sanadin tar watsewar mutane da dama da kuma shiriyar wasu da dama, gashi bata san inda wayarta take ba tun ranar da aka kaita station, turo ƙofar ɗakin da akayi ne yasa ta dakatawa daga sintirin da takeyi tare da juyowa alokaci ɗaya tana kallon Anty Nafisa wadda ta shigo,ƙarasowa tayi gaban Bintu tare da miƙa mata wayar ta, Bintu kallon ta take cike da mamakin yadda akayi wayar taje hannunta ,kamar tasan tunanin da Bintu takeyi, tace"nima a wajen Hajiya Babba na karɓo lokacin na shiga gaida ta sai na tarar tana cewa Rahima tazo ta kawo Miki shine nace ta kawo zan baki nima nan nayo kinji dalili kuma nima rashin wayar taki ya dameni gashi babu halin na baki wata!'hannu tasa ta karɓa tare da cewa na gode nima yanzu tunanin wayar nake saboda ina buƙatar magana da Hajiyarki saboda...sai kuma tayi shiru da alamun kamar tayi suɓutar baki a zan cen nata, Anty Nafisa tace" ina jinki saboda me?shuru Bintu tayi tana ɗan kauce kauce alamun ta dai ya nuna rashin gaskiya,cikin da bar bar cewar zance tace"a'a babu ko mai fa wani saƙone da ban!'zuba mata ido Anty Nafisa tayi da alamun rashin yadda cikin idanun ta sai dai kuma ba tace komai ba amma yanayin ta ya nuna akwai Magana abakinta.

Bintu ta kawar da wancan zan cen da cewa Anty Nafisa a kwai wani abu sabone? cikin wani yanayi Anty Nafisa tace"Bintu ai ko da yaushe gidan nan baya rabo da sabon labari wanda yake ƙunshe da sabuwar manaƙisa,na san da cewa burina ya sha ban ban da sauran burukan da ke zuciyoyin gidan nan,dan haka Ni bani da damuwa da sanin abinda suke hari burina kawai shine buri, tunda bani da kishiya ta wajen tarayya da abinda nake so to duk me sauƙine,shi yasa kikaga ban cika azarɓaɓi cikin aikina ba,dan nasan burina zai cika,to amma kuma yanzu wannan tunanin ya rushe saboda abinda na gano wanda Gara ace ina da masu tarayya akan dukiyar mijina, Bintu ta ɗan numfasa kana tace"yanzu me kike so dani ina cewa Ni aikina sai nan da watannin da kika ƙaiyadewa cikin ki zan fara? Anty Nafisa tace"hakane,amma akwai abinda yake son shigowa cikin burina shi yasa nake ganin gwara tun kafin cikin yayi ƙwari mu yi abinda ya dace kawai zaki aiwatar da aikinki acikin wannan lokacin!'duk da cewa Bintu ta girgiza da jin sauyin ra ayi daga Anty Nafisa amma sai ta dake ta nuna jarumta akaron ta na farko,dan haka cikin ƙwarin gwiwa tace"to amma kina ganin hakan ba zai zo da wata matsalaba,kuma meye abinda yake shirin kawo miki Barazana cikin burinki?wani irin kallon anya na gaya miki tayiwa Bintu, kana kuma tace"ina ganin babu wata matsala da zamu fuskan ta ki daina wannan tunanin fatan nasara ko da yaushe nakewa kaina ba faɗuwa ba,san nan kuma babu buƙatar kiji dalilin da yasa nake son janyo aikin nan kusa,kawai kiyi abin da nasaka ki ba wai tambayar abinda bai zama hurumin ki ba, wannan sirrinane da idan ba Hajiyata ba babu wanda yasani a duniya!'da sauri Bintu tace"shike nan na gamsu da bayananki amma nima ina da shawarar da zan baki!' Anty Nafisa tace"ina sauraran ki bamu da lokaci me yawa!'Bintu ta ɗan yi ƙasa da murya tare da cewa me zai hana ki fara ɗaukar matakin karɓar duk wasu manyan kadarorin mijinki cikin dabara kisa duk ya saka miki hannu su zama mallakin ki kafin mu kai ga sheshi"zubawa Bintu ido tayi cikin zurfafa tunani da mamakin manufar Bintu a kan wannan shawara,cike da mamakin tace"Bintu meye manufarki ta can ja min tunani?ɗan waige Bintu tayi tare da ƙara tabbatar da babu wanda yake musu laɓe, kana ta kuma yin ƙasa da muryar ta tace"manufata saboda koda idan ya mutu ƴan uwansa zasu iya handame dukiyar ke kuma wata ƙil dun haƙilon da kikayi akan dukiyar ya tashi Aban za saboda na fahimci gidan nan kowa haɗamammene basu da godiyar Allah duk irin tarin dukiyar da mahaifin su yake da ita amma kullum burin su shine ta yaya zasu ƙara arziki,ina ganin idan kika tsaya kallon ruwa tabbas kwaɗo zai iya yimiki ƙafa!'ta ƙara sa maganar tanayiwa Anty Nafisa wani kallo tare da fatan karɓuwar shawararta batare da tayi dogon na zari ba,ai kuwa cikin wani irin mamakin yadda akayi Bintu tayi wannan dogon tsinkaye,Anty Nafisa ta rugumota tare da cewa U are very smart, Bintu kina da fikira tabbas shigowar ki gidan nan ba ƙaramin cigaba da nasara zai kawowa rayuwata ba,na amince da sha wararki sai dai kuma a inda gizo ke saƙar yadda za ayi yasaka min hannun tunda mijina ba shanyayye bane atsaye yake da ƙafafun sa!'Bintu tace" masha Allah anzo gurin Nafisa kinga ta kanki tunda kika yadda dani sai na kawo ƙarshen makircin ku,taɓa tan da Anty Nafisa tayi yasa tayi firgigigit, Anty Nafisa tace"ya kikayi shiru?a hankali Bintu ta sauke doguwar ajiyar zuciya kana tace"mafita nake nemo miki!' cikin zaƙuwa Nafisa tace mecece mafitar? Bintu tace"mafitar itace in dai har kin yadda dani kuma kin gansu ba dan kuɗi zanyi miki aiki ba sai dai taimakon rayuwata da rayuwar waɗan da suke jirana dan taimakon ta su rayuwar, shine ina so ki dinga bi a sannu a hankali kina sace kadarorinsa, Ni kuma ki dinga bani zansa ka ayi fake ɗin takardun saiki maida masa fake ɗin ke kuma ki riƙe original ɗin!'ɗan jim Nafisa tayi daga bisani kuma taja wani dogon numfashi kana tace"kina da hanyar yin hakan yadda baza aganomu ba?da babu ai bazan kawo wannan shawarar ba!' ta faɗa tana ɗan goge fukarta, Anty Nafisa tace"ba dai Ni zaki bawa original ɗin ba idan akayi fake ɗin?tace"haba Anty Nafisa kamar bakya gane yaren da nake miki, ke zan bawa mana kinga idan ko mai ya faru koda sun so cutarki ke tuni kinyi maganin su,guduwa zakiyi abinki baruwan ki da tuhuma dama Ni ba asan meke tsakanin mu ba ina ga wannan hanyar itace mafi sauƙi wajen karya ƙwaɗayayyu!'Anty Nafisa tace"tabbas Maganar ki haka take bazan yi ƙasa a gwiwa ba tun daga yanzu zan fara nema da lalube tunda baya ƙasar!'juyawa tayi cikin sauri tana cewa Bintu bazaki ƙara ganina ba sai da wasu daga cikin kadarorin mijina!'daga haka ta fita daga ɗakin.


Wani irin tsalle tayi tare da faɗawa saman gadonta ta rungume fulo tana sakin wani murmushi me cike da samun ƙarfin gwiwa da kuma hangen nasara wadda take tun karo su nan ba da daɗewa ba Anty Nafisa kin gama zuwa hannu watan cin ubanki da faɗuwarki yayi wannan farin cikin da takeji kamata yayi acce da me taya ta,babu wanda ya daɗi mata sai ogan ta shi yakamata ya ji wannan sarasa da suka samu ita kanta tayi mamakin yadda wannan tunani yazo mata lokaci ɗaya tare da tsara yadda zata tafiyar da komai cikin kwanciyar hankali da nasara.

Duk mintuna sai ta duba agogon dake manne jikin bangon kiching ɗin Allah Allah takeyi ya dawo ta zaƙu ta sanar dashi wannan labari, ɗan tura baki tayi cikin karaya take cewa yanzu haka ma ya gwaleni ko yaƙi nuna farin cikin sa kuma ba lallai ya yaba min ba,bazan ma faɗa maka ba na fasa!'ta ƙare maganar tare da murguɗa ɗan ƙaramin bakinta.


Kamar yadda ya saba saida ya tsaya ya gabatar da sallar magriba da isha kana ya nufo cikin gidan,kai tsaye part ɗin sa ya shige bayan yayiwa inno sannu da gida.

Baƙaramin mamaki yayi ba ganinta a falon nasa amma sai ya basar yayi kamar bai ganta ba,ɗan harara ta watsa masa ƙasa ƙasa tana aiyana wa aranta dama tasan wulaƙanci zata sha gashi tun daga yanzu ta fara gani,ita sam bata ga wani abun faɗa da haƙilo da Taufiƙa takeyi kan wannan muskilin ba,wanda magana ma sai ya gadama zaiyita,ji tayi yana cewa idan kin gama bani saƙon hararar sai ki tashi ki tafi ko!'cikin dawowa hayyacinta tace"Ni ban harare kaba sannu da zuwa fa nake maka amma kace na harareka!'cigaba yayi da takun sa cikin nutsuwa batare da ya tanka mata ba ya dai san wannan zaman a kwai dalilin sa,shigewa yayi ɗakinsa ita kuma Bintu ta cigaba da zaman jiran sa, duk da tace ya bata haushi ta fasa faɗa masa cigaban da suka samu,(to Hajiya Bintu bari nima najira naga ya zata kaya muku keda jarumin naki wanda kika kira da miskili duk da naga kamar ke ba yayi miki miskilan cin)


Yadda ya tafi ya barta haka ya dawo ya sameta,nan ɗin ma bai kula ta ba ya wuce kan dinning table dan bawa ciki hakkin sa,sai da ya gama tsaf kana ya taso ya dawo cikin falon,zama yayi kan hamshaƙiyar kujerar sa tare da ɗora ƙafafunsa kan ƙaramin Centre table ɗin dake gaban kujerar,rimot ya ɗauka ya kunna tafkekiyar placsiman da ta mamaye rabin bangon,Bintu dai kallo take binsa dashi ƙasa ƙasa haka nan taji ya mata kyau shigar da yayi ta wata Jessi da ƙaramin gajeren wando iya gwiwa ya burge ta ga wani sihir taccen ƙamshi da ya mamaye wajen tun fitowar sa yayi wani fresh dashi fatar sa sai wani glowing take,cikin ƙasai tacciyar muryarsa yace"ya dai kallon fa?wata irin kunya ce ta kamata kai wannan mutum kwai ƙwaƙƙwafi duk yadda tayi takatsan tsan wajen kallon sa amma sai da ya ganota,tashi tayi zata fita daga falon, ta kuma tsinkayar muryar sa yana cewa karki sake ki fita daga falon nan idan ba haka ba kin san karon mu dake ba zai kyau ba!'dawowa tayi tare da zama inda ta tashi,nuna mata gefan sa yayi ba tare da yayi magana ba,babu yadda ta iya dake yanzu ta fara gane yaran sa na magana da nuni ko da gira ko da ido,

Rarrafawa tayi amma bata zauna kan kujerar ba sai ta zauna ƙasa jikin kujerar da yake zaune,cikin huskey voice ɗin sa yace"me kike son sanar dani?kawar da kanta gefe tayi tare da sa hannu ta rufe bakinta kamar ance mata zaiyi magana shi ɗaya batare da izinin ta ba,kawar da kanshi yayi daga kanta ya kuma cewa ina jinki,still dai batayi magana ba,kawai gani tayi ya miƙe tare da shigewa daki,binsa tayi da harara kana a fili tace"nima na zama miskilar ramawa zanyi kaji idan da daɗi idan akaiwa mutum magana yaƙi bada response dan haka bazan faɗa ba!'batasan fitowar sa ba sai kawai ganin sa tayi akanta yana ƙoƙarin haɗa allura,da sauri ta miƙe tare da neman hanyar guduwa amma kafin tayi wani yunƙuri ya cafko hannun ta cikin sanyin kuka tace"to Ni nace maka ban da lafiya ne kuma ba sai mutum bai da lafiya ake masa allura ba?cikin ɓoye murmushin da yake son kufce masa yace"ai naga kamar ciwon baki kike shi yasa zan miki allura sai bakin ya buɗe sosai!'cikin kiciniyar kwatar kanta tace"Ni wallahi lafiyana ƙalau ban son allura dan Allah kayi haƙuri kaji!'ta ƙarasa maganar cikin rarrashi kamar tana lallaɓa yaron goye,noƙe kafaɗa yayi tare da ƙara haɗa fuska yana mata nuni dole fa sai yayi mata allurar nan,tana ganin haka kawai sai ta shige jikin sa tare da cumimiye shi dan kar ma yasa mu damar ɗaga hannun sa danyi mata allurar.......



More Comments
More typing

Fatima y Adam✍🏽
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 36 ```


Zuba mata ido yayi yana kallon yadda take ta tura fuskarta cikin ƙirjin sa,cikin san ganin yanayin nan nata na tsoro ya shiga laluben inda zai soka mata allurar, jin haka yasa ta ɗago da sauri idanun nan duk sunyi waje yanayin nata gwanin sha'awa tace"plzzzz!' yayin da taja harafin ƙarshen da tsayi tana wani irin ƙifta ido wanda hakan yasa Abdallah shagala da kallon fuskar tata tare da ƙurawa tausasan lip ɗinta idanu,tura bakin ta tayi tare da kici-kicin ƙwatar kanta,wanda hakan yayi saurin ankarar dashi,cikin wani irin yanayin dayake ratsa duk wata kafa ta jikin sa tare da magudanar jini da ɓargonsa,ya zame ya zauna cikin kujerar tare da ita ajikin sa, cikin sanyin jiki yace"to zaki gaya min ko sai nayi allurar? da sauri ta kaɗa kanta kamar wata ƙadangaruwa, yace"ok bakin baiyi sauƙin ba kenan ya faɗa yana mai san kwace hannun sa da ta riƙe ka tau mau,cikin yanayin ta na shagwaɓa tace"Allah zan faɗa maka amma karkayi min allura na tuba bazan sake ba!'ta ƙarasa faɗa tana wani langaɓe kanta akan kafaɗarsa,yace"oya ina sauraren ki!' to ka cikani mana saina faɗa maka,da idanunsa yayi mata nuni da hannun sa da tariƙe da yadda take zaune akan sa tamkar wani kujera,da sauri ta sake shi tare da zamewa daga jikin sa ta zauna a ƙasa tana gun gunin yadda yake sata tana Hayewa jikinsa,


Taɓe bakin sa yayi gami da gyara zaman sa yana fuskantar ta sosai kana yace" oya Tell me!' A hankali Bintu ta shiga bashi labarin yadda sukayi da Anty Nafisa bata tsayaba har sai da taxo ƙarshe,kana ta ɗago kanta dan ta kalli yanayin sa,ganin ya wani turɓune fuskane yasa Bintu cikin fargaban Allah yasa dai ba kwaɓa tayi ba garin san gyara,ganin yanayin ta ne yasa ya ɗan saki fuskarsa tare da ɗaga hannun sa ya dunƙule su kana yayi mata alamun jin jina,kawar da kanta tayi alamar dai bata gamsu ba, Cikin taushin muryarsa yace"kinyi ƙoƙari sosai,kuma duk yakar Dar da ta baki, ki dinga sauri wajen bani Ni kuma zansa A shirya mata ta kaddun bogi masu kyau sai kuma nasa ayi wanda bai kai na wajenta kyau ba A matsayin sune fake ɗin,sai na haɗa na baki ke kuma sai ki bata daga nan zamu dinga ajiye original ɗin a wajen mu har muga abinda Allah zaiyi,jin jina kanta tayi cike da gamsuwa,kana tace" kuma bazata gane bamu bata original ɗin ba,yace"insha Allah bazata gane ba Allah zai bamu na sara akanta zai rufe mata idanunta ba zai bata ikon ankara da abin da muka shirya mata ba har sai dubunta ta cika!'Allah yasa taimakemu ta faɗa tare da cewa, bacci nakeji!'kai tsaye ya nuna mata hanyar bedroom ɗinsa,kallon sa ta tsaya tanayi wato dai yauma aɗakinsa zata kwana kenan? ganin ya miƙe tare da nufar ɗakin sa ya sa itama ta tashi da sauri tare da nufar hanyar fita daga falon,bai ce mata komai ba yayi shigewar sa.


A hankali ta buɗe ƙofar tare da saka kanta tana ɗan leƙawa, ganin gurin shiru ga duk fitilun falon innon a kashe suke baka iya ganin ko tafin hannun ka,tsorone ya kamata ji tayi kamar an taɓata,hakan yasa ta juya da gudu ta koma cikin falon Abdallah,wanda ba ita ta tsaya ba sai a tsakiyar gadon sa tana mai da numfashin gudun da ci, Abdallah dake tsaye gaban madubi yana fesa turare ya ɗan kalleta tare cewa Aran sa zabuwa kawai ko mai na tsorone da kuka a wajen ta,lulluɓe jikinta tayi gaba ɗaya amma fa ita tunanin ta ya za ayi ta iya bacci batayi wanka tasa kayan bacci ba gaskiya da sake hakan bazai yiwu ba agurinta, ganin yadda take ta juyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login