Showing 6001 words to 9000 words out of 184937 words

Chapter 3 - KUDURAR ALLAH COMPLETE BY FATIMA Y ADAM

21 Jul 2024

16849

hudu maza biyu mata biyu

Shi kuwa umar hjy zainab
(inno) itace" ta hadashi da ' yar' aminiyarta hjy ladidi me suna nafisa,

Hjy ladidi ' yar' salin garin minnace, aurene ya, kinki mota ya kawota garin abj
da yarta guda daya tilo nafisa ba sai nace muku nafisa ' yar gata bace ku kanku zaku fada, kasan
cewa kowa yasan yadda d'a guda daya yake agun iyayensa to irin wan nan son akewa nafisa agidansu,
""itaka kadaice'acikin suru kan alhj balarabe bata taba haihuwa ba ko batan wata kuwa,

Yakamata musan meye halaiyar alhj balarabe,

Alhj balarabe mutum ne me tsananin addini da ku ma amfani dashi yana da
tausayi da hakuri haka kuma ya' iya mu' amala da mutane yana da san kyautatawa' al 'umma, ya gina makarantu da masallatai babu adadi, ga asibitocin da ya gina dan kawai tallafawa marasa karfi da Kuma marayu,
wannan dalilin ne talaka
wa su kaso ya tsaya musu
amatsayin gomnan jiha
amma sai yaki fur, acewa
rsa" bazai taba iya shiga abinda zaisa yasa 'bawa mahaliccinsa ba,
da wannan' hujjar tasa suka hakura badan sun so ba,

Alhj balarabe baisan
wace irin waina ake toyawa a,cikin estate dinsa ba,zuciyarsa daya yake kallan kowa baya kuma
tunanin ana aikata wani
mummnan ta adi,

Yana can hadadden ban
garensa shi da matansa
dattijan da jin dadi da da ula suka boye tsufansu,

Inaso makaranta kuyiwa labarin KUDURAR ALLAH
kyaykywar fahimta, shine dalilin da yasa na fayya- ce muku sunayen ' ya'yan alhj balarabe da kuma wadànda suka rabeshi,

Hali,dabi'a da Kuma manufa duk suna cikin labarin,


CIGABAN LABARI

...…..Estate.....

Wani kimtsetstsen falo ne me matukatukar gir
ma da kyau wanda yaji kayan more rayuwa da dima- diman kujeru masu
tsananin kyau da burge-
wa,babu wasu yawan tar-
kace acikinsa bayan sai-
tun kujeru kala biyu sai kuma run dumemiyar placzima tv,

Wani sanyayyen kamshin
turaren wutane tare dana
air freshener, wanda suka hadu suka bawa falon wani ni'imtaccen kamshi me san yaya zuci
ya,

Saidai duk wannan ni'ima hakan bai hana damuwar
hjy zulaihat kassara ruhin
ta ba,
""cikin tsananin damuwar dake cin zuciyarta tasa hannunta ta dafe saman
kanta dake barazanar barin gan-gar jikinta sabi da tsananin sarawar da yakemata,

Rahima dake tsaye akarshen matakalar da zata sadaka da falon ta
bangaren hagu,yayinda hjy zulaihat ke ta bangaren gabas akan 'kawatattaun kujerun dining table din da ya ma
maye gurin,ayanzu kanta a,kife yake dan haka batasan rahima ta zoba,
sai kawai ji tayi andafa kafadarta, cikin tsananin
tsoro da firgita!' ta dago kanta, ganin rahima ce yasa ta saki wata 'kak'kar
far ajiyar zuciya, kana' ta
yi saurin goge hawayen da suka 'bata kyakykya-
war fuskarta tare da 'kirkiro murmushi akan fuskarta.

Hannun rahima ta kamo tare da kokarin boye damuwarta, tace" rahima
'yanmatan Abbie ba ki koma bacci ba?
rahima da tacika da tausayin ' ammin tata,
tace" ammina yaza'ai na
iya bacci bayan kina nan
cikin wani'mugun yanayi
da tsananin damuwar da
take neman hargitsa farin cikina,
"taci gaba dacewa" ammi tun ban mallaki hankalin
kainaba nake ganinki cikin wannan damuwar,
kuma duk sanda natam
bayeki saikice mun bahurumina bane, ammi
meyasa? ta fada cikin zubar da wasu zafafan hawaye,

""Cikin nutsuwa irin ta mata masu tsananin hakuri ammi tace"rahima
kinutsu kidena wannan ihun haka!dan wani zai' iya shigowa ya Kuma fuskanci halin da muke
ciki,hakan Kuma bakara
min hatsarine agaremu ba dagani harke!
wannan damuwar da kike
gani' atare dani sirrin rayuwata ce"kuma jinsa ga wani fansane garayuwata da kuma rayuwar wasu,dan haka inaso kikama kanki da
dakyau ki adana wadàn nan shir mammun tambayiyin'naki!takarasa maganar da wani irin hada rai dan karma rahima tasamu damar
ragargazo mata wasu tambayiyin,

Sai dai duk da hakan bata tsira ba,dan tana dasa aya,rahima ta dora
da abinda yake cikin' zuciyarta tace" to ammi
meyasa bazaki fadawa Koda 'ya'yan cikin ki bane?
idan, ni kina ganin nayi kan-kanta da jin damuwa
ko kuma sirrinki!kai tsaye ammi tace mata" saboda
ban yarda da kowaba, ban' amince da kowaba,
ban yarda, da amanar kowaba, haka kuma ban
yarda da gaskiyar kowaba, da sauri rahima
taca" ammi harda mu 'ya
'yanki ? wani' irin murmushi' ammi tayi me dauke da tarin ma'anoni
kana tamike ta bar rahima zaune a agurin
baki bude da madaukaki
Yar mamaki!!!!


Fatash........

Maman hamra rufe bakin
taji nace fatash to se a
page na gaba,😂😂😂
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GsLlgKf7MsD3M4Hoo7U65P


💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 5```



Buga kofar dakin take iya karfinta,cikin kuka take
fadin"fatash son ina hadaka,da allah kabude
kofar nan kasaurareni,
meyasa kake mun haka fatash?nifa mahaifiyarka
ce" tafada cikin zamewa ajikin kofar tana kuma rushewa da wani kakkar fan kuka,
""Shiko wanda takeyi danshi baima san tanaiba,

Fasto david shigowarsa kenan daga gurin bautar su, yaci karo da kukan matar tasa abigail, girgiza kansa yayi kana yanufi bangaren dansa fatash,dan ya tabbatar acan yake jiyo ihun abigail,hasashen sa kuwa ya tabbata, dan yana zuwa yatarar da ita
abakin kofar se birgima take, tamkar wata karamar yarinya, tsaida idanunsa yayi akanta yana mai kiyasta irin, tashin hankalin da take ciki" jin kamar motsin mutum akanta, yasa tayi wata iriyar zabura, dan anata tunani tayi zatan fatash ne ya tausaya mata yafito daga dakinsa
sai dai kuma taga akasin haka cikin sauri, ta wada jikin mijinta tana mai cigaba da kukanta,mai
sosa zuciya, ahankali yasa hannu ya yi mata kyakykyawan masauki akirjinsa, yana mai ci gaba da dan bubbuga bayanta, cikin taushin murya yace"ya'isa haka kiyi shiru !' ko so kike ki kara tunzurashi? dasauri tasa hannu ta goge hawayen kan fus karta,

Kana cikin karaya da da al'amarin dannata, tace'"
david pls katemaka mun,
karo'kar mun son yatemaka yabude yafito
ina san magana dashi, yaufa kwana biyar kenan
tun randa ya dawo ban gansa ba!' ta fada tana dan dukan kirjin david ,
cikin wani irin rudadden kuka me karya garkuwar jiki, cikin lallashi david yace" mata haba Abigail
na gaya miki ki rage wannan damuwar da kuka,kinsan dai in har baki nutsuba dannaki bazai taba saurarenki ba
dan kinfi kowa sanin halin abinki, to meyasa kikeso ki ruda kanki da kanki? cikin yadda da maganar sa, tace hakane
david, to amma kasan abinda fatash yayi dole ne nakasa control din kaina, na shiga tashin hankali sosai yadda baka
tunani!' david ya' gyada kanshi tare da cewa" muje ki nutsu tukun kafin
na rakoki mu hadu mu lallabashi ko zamu samu
ya canja ra'ayi!'cikin gamsuwa da shawarar mijin nata ta bi bashi suka nufi bangaren su".


......Bauchi.......


Anan bauchi kuwa fatima
ce zaune gefan fafi tana dama musu fura,tana dan jan fafin da hira shi kuma lokaci- lokaci yake amsawa saboda nisan da yake a tunani, can dai fatima ta aje furar tana dan tuttura dan karamin bakinta tare da cewa wai
fafi tunanin me kake? ka barni ni daya inata magana ? yanzun da nice da yazu ka faramun fada,ta fada tana mai goge hawayen da suka gangaro mata kan kunci,cikin dawowa hayyaci fafi yace" batula ba tunani nake ba, ya.fada.da mur mushi a kan fuskarsa, dan yasan fatima bata son yana ce' mata batula, aikuwa tunzuro dan tattausan lip dnta tayi, cikin yanayin shagawabarta ta tsantsan yarinta tace" allah kuwa fafi ba sunana batula ba ,fafi ya danyi dariyar karfin hali, kana yace" a' a fa bintuna
shima batula sunan kine
kuma ai yana da dadi, meye abin rashin so cikin
sa? tunzura bakin ta kumayi tace" fafi nidai banaso, yace to shikenan
na daina fada, tafisu tafi sauran 'ya'ya, ya fada yana mai fadada murmushinsa, yace" maza miko mana furar musha kar yunwa ta karasamu,da sauri ta janyo kwanan furar ta bude musu suka farasha.


Rayuwar fafi da diyarsa Fatima, rayuwace me cike da ban tausayi, rayuwa ce ta kunci da talauci, kasancewar shi fafi ba cikaken lafiya gareshi ba, fatima kuma yarinyace,mace abar tattali da killacewa, shiyasa fafi duk ciwon dayake damunsa haka zai daure ya fita yaje ya samo dan abin da zasuci,
fafi ba sana'a yake ba sai dai dan ayyuka wanda basufi karfin girman sa ba, ahaka rayuwa take gungura musu cikin karfin gwiwa da taimakon ubangiji,

Yayin da kuma ata wani bangaren, fafi yake fuskantar wani 'kalubale me tsananin sarkakiya,
wanda shine dalilin dayasa yake kaffa-kaffa da rabin ranshi fatima,baya san tasan komai, kuma bayasan ta gane ko mai, ayanzu saboda acewar sa fatima tayi 'ka'kanta da shiga wannan babban al'amari aduk sanda ya tuna wata rana yana'iya barin bintu sai yaji tamkar zai shid'e dan tsananin tashin hankali, sai dai idan yatuna da allah da kuma irin addu'oin dayakewa diyar tasa sai yaji salama aransa, dan hakika fatima tana cikin jarrabawar rayuwa,wanda sam ita bata san da haka ba, yana koka mata'aduk sanda yatuna sarkakiyar da take cikin rayuwarta,sai dai yayi yakinin cewa Allah zai kawo mai taimakon ta, dan warware bakin kullin dake cikin rayuwar ta,
yayi yakinin Allah zai kawoshi, tabbas mafarkinsa zai zama gaskiya,dolene ya bar rayuwarta kodan tseratar darayuwarta, bayasan shi
dakansa yazamo silar karawa rayuwarta kacaccalewa,adai-dai lokacin dayazo nan atunaninsa, yasa hannu yashare hawayen dasuke ta damben saukowa saman fuskarsa, tare da cewa" fatima banasan kisan koni waye dole nayi nisa da rayuwarki!'ya fada abaiyane tare da kara sakin wani kakkarfan kuka wanda ya kasa boyeshi.




.....Abuja.....

estate
Cike da nutsuwa hjy zainab (inno) ta dubi, aunty nafisa tace" yanzu nafisa kina ganin wannan halin da kika tsiri yi agidannan shine dai- dai awajenki!'ko kinaso kice mun rashin haihuwarki ne yajawo miki shiga wannan damuwar?to bari kiji na gaya miki gara tun wuri ki maida hankailinki jikinki, idan kuwa ba haka ba allura zata tono garma!' takarasa maganarta cikin nutsuwa da yanayin kamala, ta yadda idan ba kana gab da ita ba baza kataba cewa ga abinda take fadawa matar dan kishiyarta kuma 'yar aminiyarta hjy ladidi ba,

Aunty nafisa taja wata doguwar numfashi me cike da fargabar bullowar wani gagarumin tashin hankali da kuma kwantacciyar damuwar da take kokarin tasowa ,tace" inno bazaki taba ganewa ba, ni kadai nasan yawan tarin damuwar da nake ciki da kuma tsananin fargaba, inno na rasa gane manufar mutanen gidan nan' idan ka dasawa wannan ayar tambaya daga baya sai kafara kokwanto, idan zargina yasauka daga kan wannan sai yafada kan wancan inno al'amarin gidan nan akwai rikitarwa da saka mutum cikin rudani, baka taba gane me amana bare me gaskiya, baza kataba gane mugu ba, bare makiyi!' tana dire maganarta inno ta dauka dacewa" kamar yadda kikeyi, ki boye fuskarki haka suma sukeyi harma sun zartaki a'iya taku, yadda bakisan zuciyarsu ba, suma basu san taki ba , yadda bakisan shirinsu ba, kema basu san nakiba, koni kaina da ke zaune gabanki matsayin surukarki ban san me kike shiryawa azuciyarki da rayuwarki ba!' tarufe zancanta tare da zubawa nafisar ido danjin abinda zatace" cikin kidima da bayyah nan nan tsoro!' tace'" ni kuma inno ? toni me zan kullah ? inno nima baki yarda dani ba?
inno tayi wani dan murmushi !' kana tace" yo nafisa ai duk wanda ya kwana yatashi cikin gidan nan ba abin yarda bane, ko da bakone ya shigo ya fita saina dora masa ayar tambaya, bare kuma ke surukar gidan nan!' cikin tsananin mamaki aunty nafisa tace" to inno meyasa ? kuma saboda me? meyasa kowa yake zargin kowa aginnnan ?
kuma suwaye ? inno tayi murmushi tare da cewa" nafisa nima bansani ba, bansan kuma suwaye ba, ban san a'ina bane ,da yaushe ne, duk ban saniba, shiyasa nace' miki ke kanki abar zargice agidan nan,'yayan gidan ma ba abin yarda mane bare kuma ke nafisa,kawai dai Ina baki shawara karki bari ta bare dake, shawarace kawai!'zukudi aunty nafisa tayi cike da matukar al'ajabin lamarin!' na cikin wannan estate wannan shi ake cewa" kowa tasa tafishshe shi".



__________________


Wata hatsabiyar dariya shugaba azikwi ya buahe da'ita!' san nan cikin katuwar muryarsa, yace" nanuu kai kadai ne zaka shiga dakin nan dan cika ragowar bukatar dodo jack, bayan kai bama bukatar kowa yashiga, san nan Abu na biyu dolene mu nemo yarinyar nan domin itace ragowar cikar burin mu, rasata yana dai- dai da rushe rayuwarmu da farin cikin mu,haka kuma idan ba mubi 'ka'idoji ba shima kawota rayuwar mu, babban tashin hankali ne da rasa rayuka,dan haka bayan aiki da tsafi dole muyi aiki da tunani da lura da kuma tuggu!' yana rufe bakinsa wanda aka kira da nanuu yace" shugaba ina da yakini akan baza musaba umarni da san zuciyarmu ba, ita kuma yarinyar muna nan muna bibiyarta,datemakon jack bazamu kusre ba!'

To fa waiya abin yakene? duk inda kuke zatansa ya wuce ku dan kucigaba da bina asannu.


Comments........
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GsLlgKf7MsD3M4Hoo7U65P


💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 6 ```



'Dakine guda acikin estate din ta can wani bangare na musamman wanda ba kowane yakebi ta hanyarba, babu wanda yasan meye' acikin dakin da kuma mamallakan dakin,sai dai kuma wani abun mamaki babu wanda aka taba gani ya bude dakin ko kuma yabi ta hanyar,da dakin yake,
dayawa-yawan zuciyoyi nakai komo da taraddadi akan dakin, haka kuma zuciya da gan- garjiki suna son kai kansu inda wannan dakin yake, amma kash,hakan ya kasa samuwa daga dukkanin bangarorin dake son sanin abunda aka 'kunshe acikin dakin da kuma amfanin zamansa anan, kai harma da mamallakan dakin.
Adai-dai kuma wannan lokacin ne dije me aikin hjy madina matar mansur, tafito da wani kullin abu ahannunta sai yan dube-debe take kai kana ganin yanayinta zaka hango rashin gaskiya aidanunta,cikin sanda ta nufi can baya inda wannan dakin yake, alhj mansur da tun fitowarta ya hangota a lokacin da yake fitowa daga bangaren alhj baba(alhj balarabe)cikin sauri da azama ya mara mata baya dan ganin abinda take kokarinyi,abinka da namiji kakkarfa nan da nan ya taddata,cikin wata iriyar gugitacciyar tsawa,yace"ke dijeeee karki sake ki kara wani taku daga nan inda kike!'dije cikin tashin hankali da rawar jiki ta tsaya tare da juyawa dan ganin wanda yake neman fasa mata 'ya'yan hanji da wannan' razananniyar tsawar ,ganin uban dakinta tsaye yana aika mata da wani' shakurarren kallo me cike da gargadi da barazana,yasa ta kara kidimewa,da sauri ta karaso inda yake tsaye tana mai cewa"yallabai agafarceni wlh sani akayi bada niyar kaina nazo gurin nan ba, cikin tsareta da ido alhj mansur yace" dije.wani irin gan-gancine yakaiki ga zuwa gurin nan? kinsan kuwa komu bama iya zuwa hanyar nan amma ke kike kokarin saida ranki akan kudi!' wayasaka ki wannan aikin? kuma mezakiyi anan din?san nan meye wannan ahannunki? yayinda dady babba(alhj mansur) yakewa dije wadan nan tambayoyi ita tuni ta dade da antayawa' zuzzurfan tunani na yaya zatayi ta tseratar da rayuwarsu ita da yarta,tabbas idan bata kai wannan ajiyar inda akasata takaiba tana cikin tsaka me wuya,sannan kuma shima kaiwar wani tashin hankalinne wanda shima ya hada da rayuwarta, san nan fadin wanda ya aikota shima yana dai-dai da rasa rayuwar danta, to yanzu meye mafita agareta?kai suwaye anan gurin? ta ji wata murya daga bayansu ayayin da me maganar take nufosu saida ya karaso san nan ta fahimci waye alhj habib ne wanda ake masa lakabi da Abba 1,cikin nutsuwa ya dubi dady babba wanda yake ta faman muzurai yana wani hade rai,yace dashi yaya meke faruwane anan?cikin hargagi dady babba yace"kawai kaje babu ruwanka bana san saka ido da munafurci,Abba ane yayi murmushi cikin sanyiwa dan uwan nasa biyayya yace"yaya kayi hakuri ba Ina nufin wani Abu bane mara kyau amma kayi hakuri,dije kuwa hamdala tayi ganin ta samu hanyar kubuta daga wadan nan razannun tambayoyi daga uban gidanta,cikin sanda ta fece daga gurin ba tare da sun ankaraba.
cikin fada-fada da yanayinsa na rashin hakuri yace"ai dama habibu dole ka bani hakuri tunda kasan baka kyauta mun,duk abinda zanyi idanka yana kaina ka daukeni tamkar wani mara gaskiya Ina amatsayin yayanka kuma babba acikin gidan nan idan ka dauke yaya nana da sakina da hafsa kaf gidan nan nine babba amma bani da damar da zan aiwatar da abu ya zauna acikin gidan nan, saika kai karata gurin alhj baba, to Ina mai tabbatar maka billahillazi idan baka fita harkata ba zaka ga abinda zai faru, babu ruwana da ciki dayan da muka fito dan wani lokacin rufin asirin da dan uba zaiyi maka dan ciki dayan bazai yi maka shi ba!' yana zuwa nan not azancen sa ya kada babbar rigarsa ya juya afusace ya bar Abba ane tsaye da tsananin mamaki da takaicin halin dan uwan nasa.

Cike da razana da bayyanannen tsoro take duban nafisar, san nan cikin dan daga sauti tace'" nafisa kina da hankali kuwa? kinsan abinda kike shirin aikata mana kuwa!'sai kuma ta dan sassauta, cikin kwantar da murya tace" haba nafisatu yaya kike son bata rawarki da tsalle kinsan kuwa babban tashin hankalin da zamu dauwama aciki in dai ki kai saken da wannan' sirrin ya tonu,to bari in fada miki abinda har yanzu baki sani ba, alhj balarabe estate ta wuce duk inda kike tunani, ta wuce zatan me zato, a'iya tuggu da makirci, kowa yana' iya takunsa baza ki taba gane abinda ke cikin zuciyoyinsu ba,dan haka ki sake sabuwar damara indai har abinda kike fada gaskiyane!'ahankali nafisa ta dago kanta dake sunkwiye, idanunta sun kumbura sunyi ja tamkar garwashin wuta,tace'" mama na kasa!' damuwata tayi girman da bazata iya boyuwaba, Ina cikin mummunan tashin hankali aduk sanda naga dare yayi gari zai waye, damuwata 'karuwa take duk sanda na tuna lokaci yana zuwa da zan iya rasa umar,tsorona karuwa yake' aduk sanda na tuna, bansan wane rana bane wane lokacine, da wane yanayine wan can rudadden al'marin zaizo me cike da sarkakiyar da warware shi sai wanda ya kullah shi,mama ayanzu inajin garamun mutuwata da zuwan wan nan rana bazan iya kallon idanun umar ba, dana sani mama da na hakura da saukar KUDURAR ALLAH da ban kasance ahalin da nake ciki ayanzu ba!' ta karasa maganar da sakin wani rikitaccen kuka me bayyana abinda yake can cikin kasan zuciya,ita kanta mama kukan take yi wanda yake cike da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login