Showing 42001 words to 45000 words out of 184937 words

Chapter 15 - KUDURAR ALLAH COMPLETE BY FATIMA Y ADAM

21 Jul 2024

16910

gyaɗa da na ƙosai har ta rigashi fita daga kiching ɗin, binta yayi da kallo cike da mamakin tsoro irin nata.


Kuka takeyi sosai wanda yake cike da san garta da kuma san ƙarawa miya gishiri,faɗawa falon nasu tayi tana mai ƙara zuzuta lamarin da shegen kukanta,Hajiya Saratu da ta fito daga kiching hannunta ɗauke da ruwan jarka,tayi turus tana kallon borin da Farida keyi cikin tsakiyar falon, cikin ɗaga murya tace"ke lafiyar ki kuwa? kamar wadda aka yiwa mutuwa!' Farida ta miƙe zaune,cikin rikici irin na auta,tace" momy wallahi garamin mutuwa da irin cin mutun cin da akayi min yau, ki duba ki gani marin ƴar aiki ne da marin ƙaton namiji A kan wannan kyakkyawar fuskar tawa!' A hankali Hajiya Saratu ta samu guri ta zauna tana bin Farida da wani irin kallon tuhuma,kawar da kanta tayi tana zunɓura baki dan tasan momin ta ba goyan bayan ta zatayi ba,aikuwa cikin ɓata fuska Hajiya Saratu tace"me kikayi mata dan nasan ruwa baya tsami banza, tabbas akwai abinda kikayi mata keda su Siddiqa, dan na tabbatar yarinyar nan baza ta mareki da gangan ba!' Dady ne ya shigo bakin sa ɗauke da sallama, cike da kulawa yake duban Farida, kana yace" auta meke faruwa ne? da sauri ta isa gurinsa ta raɓa jikinsa,tace" Dady marar maka Ni Akayi,kuma nazo na faɗa wa momi ta rufeni da faɗa,ba tare da ta saurareni ba!'Alhaji Habib,ya maida dubansa kan H Saratu,yace" haba Saratu me yasa kike hakane idan baki rarrashe ta ba waye zai rarrasheta? gaskiya bana son haka!'Hajiya Saratu tayi murmushin takaici kana tace" Ni banyi mata faɗa dan wani abuba sai dan nasan bata da gaskiya,kuma kaima kasan halin ƴarka sai dai so ya rufe maka idanu,zama yayi tare da Farida kana yace" ai ban ce miki bata da laifi ba amma ai kya saurareta kiji ba'asi tunda ita aka mara!' juyawa yayi yana duban Farida yace" auta gayamin me yafaru aka mareki?nan kuwa Farida ta karkace ta shiga faɗar ƙarya da gaskiya,tana gamawa momy Sarah ta dubeta tace" yanzu ke bakiji kunyar ƙaryar da kika zauna kina sheƙa mana ba?tura baki tayi tace"nikam gaskiya na faɗa!'to munji nasu laifin ke kuma ina naki yake?shiru tayi batare da ta kula momin tata ba, Dadin Farida yace" gaskiya basu kyauta ba da suka mareki harsu biyu dan mugunta,amma kiyi haƙuri kar ki kuma shiga har karsu babu ruwan ki dasu kinji auta!' ta shi tayi ta nufi hanyar ɗakinta sai kuma ta dakata tare da juyowa fuskarta Babu alamun wasa sai tsantsan burin ɗaukar fansa tace Dady bana yafiya kuma bazan yafe musu ba har sai ranar da na ɗauki fansa na gansu suna kuka fiye da kukan da suka sani!wucewa tayi ɗakinta tayi cikin sassarfa,wani mugun kallo momi Sarah ta shiga wullawa mijin nata kallon kaga irinta ko,miƙewa tayi tabarsa nan zaune yana murmushi wanda Ni kaina ban san manufar murmushin nasaba.

A ɓangaren su Taufiƙa ma kusan hakane ya kasance,sai dai su saɓanin Farida ne ita tasamu rarrashi da ga gurin Babanta,yayin dasu kuma har kusan marinsu saida inno tayi, ta ƙare musu tatas ta ɗora musu da cewa nariga nasan halin Bintu tun kafin zuwan ku babu wanda ya taɓa kuka da ita ko ya kawomin laifin ta yarinyace sam mara shiga sabgar mutane tana da nutsuwa da hankali,kuma nasan tunda har Abdallah ya shiga lamarin lallai baƙaramin rashin mutunci kukayiwa Bintu ba, dan haka abinda yasa tayi muku yayi dai dai naji daɗi,kuma bazan hanaku ci gaba da rashin mutuncin kuba zan kyaleku dan ina da mai gyara muku zama sangar tattun banza sangar tattun wofi,kutashi ku fitamin A ɗaki!'tashi sukayi suka fita suna mai cin alwashi A kan ci gaba da ƙuntatawa rayuwar Bintu baiwar Allah.


A hankali take tafiya dan zuwa sashen Hajiya Babba,domin kai mata Masar da tayi mata alƙawarin zatayi mata saboda tana matuƙar son masa,tazo dai dai mahaɗar da zata sada ta da kori dan da zai kaita falon Hajiya Babba,sai kawai ganin mutum tayi A gabanta tamkar an jehoshi,da sauri ta ja da baya tana shirin sheƙawa da gudu,cikin hanzari Sayyid yasha gabanta yana cewa ke dalla matsoraciya mutum ne kuma ɗan uwan ki musulmi!'ɗan dakatawa tayi tana maida numfashi,kana cikin ladabi ta gaidasa,amsawa yayi yana Binta da wani shu'umin kallo,yayin da kwaɗayayyun idanunsa suke bin ko'ina najikin ta da kallo,hakan da taji ajikin tane yasa tayi ƙoƙarin zagaye shi dan wucewa, sai dai me wani irin figa taji yayi mata har yana ƙoƙarin mannata da jikinsa,A matuƙar fusace ta angijeshi tare da nuna sa da yatsa tace"kai wane ne A cikin halittu da har zakayi ƙoƙarin yin shishshigi ga halittar da tafi karfika halittar da ba ayita domin kaba kuma wadda take haramtacciya agareka? cikin cire tsoro da shirinta na fara yaƙi ga dukkanin wanda yake shirin zame mata annabo a rayuwa, taci gaba da cewa to A kul kuma A hir ɗin ka karka kuma yin wannan gangancin idan ba haka ba kuwa, hmmm,ta karkaɗa yatsan ta tare da ratsashi ta wuce ta barshi sake da baki da hanci,bashi ne ya motsa ba har sai da yaga shigarta falon Hajiya Babba kana ya jinjina kansa tare da cewa shike nan Bintu kike kowa kin jefo kanki komar Sayyid Mansur Balarabe muje zuwa muga idan zaki ci riba...


Bayan ta kaiwa Hajiya Babba Masar sai ta biyo ta can bayan ɓangaren Alhaji Mansur, inda tanan zata miƙa ya maida ita ɓangaren wannan ɗakin tana kusan ƙarasowa ta shiga ƴan dube dube ko da da wanda yake binta duk da zuciyarta cike take da matsanancin tsoro amma tariga tasa aranta sai taje wajen nan yau dan ta daɗe tana neman wannan damar saboda tasan dole sai ta cire tsoro ta kuma fara ƙoƙarin tun karar haɗarin dake gabanta,jin wayarta na zumm zumm yasa ta dakatawa daga tafiyar da takeyi,ɗagawa tayi tare da yin sallama,ta can ɓangaren Hajiya ladidi tace"Bintu ya akayi meye labarin da kika samu daga wajen Dide?cikin ƙara duba bayan ta da gefen ta Bintu tace"Hajiya ki kwantar da hankalin ki na riga na gama samun kan Dije zata dinga sanar dani duk wani abu dake shiga da fita ta ɓangaren ta,kawai dai yanzu abinda nake buƙata daga gareki shine inaso ki dinga sanar dani duk wani abu dayake tafiya wanda kike da masaniya A kansa acikin gidan nan, saboda ta hakane zan dinga binciko miki abubuwa masu mahimmanci wanda zasu kasance miki matakin nasara A kan burinki!'wata irin dariyar farin ciki Hajiya ladidi ta saki kana tace"gaskiya yarinyar nan kin burgeni ashe haka zakiyi min rana amma naso yiwa kaina sakiyar da babu ruwa,karki damu wannan ai Abune mai sauƙi ai duk ƙaruwar muce!'cikin sauri,Bintu tace"au ai nasan Anty Nafisa zataji daɗin wannan lokaci,tunda dama daga mu sai ita mukasan mai muke shiryawa A cikin gidan nan!'Hajiya ladidi tace ke fice nan ai ita kanta Nafisa bata san manufar mu ba kawai dai muna amfani da ita ne,kamar yadda ita ma take da tata manufar batare da tasan mu mun sani ba,itace dai bata san komai kanmu ba!'cikin nuna halin ko inkula Bintu tace"to ai Hajiya Ni bandamu da duk abinda kuke ciki ba Ni kawai A yanzu burina nasamu kuɗin da zan gina rayuwata,to amma kuma Hajiya wani hanzari ba gudu ba kina ganin ba sai nasan waƴanda kuke tare dasu ba saboda gudun samun matsala ta ɓangarena? Hajiya ladidi ta saki murmushin ƙeta A ganinta ta riga ta gama dulmiyar da Bintu ta gama shiga hannunta dan haka ita yanzu lokacin baccinta ne yazo,tace" Bintu babu ruwan ki da wannan Ni kaina A yanzu bana ce miki ga wanda nake haɗa hannu dashi ba sai dai natabbatar shi ɗin ahlin ALHAJI BALARABE ne kuma bandamu da nasani ba burina kawai shine A gabana!'Bintu cikin gaiyato ƙarfin hali da san kawar da halin da tashiga na ruɗani tace" tom shikenan Hajiya baki da wata matsala da Ni komai zai tafi yadda kikeso!' Hajiya ladidi tace"amma Bintu ina so maganar Nafisa ya kasance tsakanin mune baza taji wannan magana ba mu cigaba da tafiya a yadda muke!'Bintu tace" haba Hajiya ko bakiyi min gargaɗi ba bazan taɓa gayawa Aunty Nafisa komai ba,Ni na gaya miki abinda nake buƙata dan haka babu ruwana da abinda kuke shiryawa ko kukesan cinmawa,idan hakane kuwa kinga babu ruwana da tsakaninku aiki na kawai zanyi na kauce,saura na zubawa ƘUDURAR ALLAH idanu!'Hajiya ladidi tace"yauwa Bintu na gode da fahimtar ki gareni sai mun sake waya!' to shikenan sai anjima!'duk wannan wayar da Bintu takeyi tana yine cikin ta ka tsantsan da ankarewa.

da sauri ta bar gurin ta ma fasa zuwa gurin saboda yanzu tana buƙatar dogon tunani da kuma shawarar Dije,tana shiga ɗakinta tasaka mukulli ta rufe zama tayi tsakiyar ɗakin tana maida numfashin tashin hankali, kanta yayi matuƙar daurewa da wannan lamarin wato ita kanta ƴar da uwa munafuntar juna sukeyi lallai wannan al marin babbane, to yanzu yaza ayi na gano wanda suke haɗe da Hajiya?can kuma ta zabura gami da cizan yatsa A fili tace" tabbas Hajiya ladidi kin gama kashe kanki tunda kika yadda naji sirrin junanku ke da ƴarki,kuma da kanki zaki lalibo mugun da yake saki aiki!'sai kuma ta ƙyalƙyale da dariya tana mamakin kanta,tare da mamakin Hajiya ladidi, dama sakarar mata ce bata da wani wayo? tana zaune jikarta tayi mata wayo ta bugi cikinta gaskiya abin nan yayi mata daɗi,abin yakowo citta......


More comment.....

More typing......
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



Wannan page din nakine sister khadi ke da rufy AA COMMENT ɗinku yana bada citta.

Fans ɗin ƙudurar Allah ina godiya da addu'ar ku gareni Allah ya ƙara mana zumunci da so da kauna,love U kwando kwando



```Page 21 ```




Yau gaba ɗaya jikin Bintu A san yaye yake kasan cewar tun safe mutanen nata suka haɗa dabar hira A falon inno, wani abin takaicin ma har da mazan suka gayyato,kuma ba komai ne yasa sukayi hakan ba sai dan kawai yau sun shiryawa Bintu buhu buhun rashin mutunci, saboda tun sassafe suka ga fitar do don nasu,yau kwana biyu da faruwar wancan abun, dan haka yau dama suka samu.


Bayan ta gama jigilar kaiwa da kawowa tayi musu girkin dasuka buƙata, sai da ta jera musu komai na buƙata A gabansu kana ta wuce dan ƙoƙarin ta na barin falon,Sayyid ne yace"ke dawo nan uban waye zai savin ɗinmu? Farida ta yatsina fuska kana tace"Ni kije kisake min sakwara dan bazan ci wannan abincin ba!ita kuma Siddiqa tace" Ni kuma kiyi min danbun shinkafa! Bintu cike da takaici take duban su ta kasa cewa komai saboda mamakin ɗabi'ar su Hauwa'u ce tace"dalla Malama kije kiyi musu abinda suka buƙata kin tsaya mana akai yawa tsohuwar maiya!' juyawa tayi har ta fara ta fiya sai kuma ta ɗan da kata tare da juyowa jin Siddiqa na cewa banzar yarinya dama ai wan can uban shishshigi shine kwarin gwiwarta, ranar har da wani zagewa tana sheƙa mana mari to yau zakici ubanki idan kina dashi!'A hankali ta buɗe bakin ta tana son cire tsoronsu dake dan kare A ranta dan Allah ya gani Bintu tana tsoron taɓa lafiyar jikinta dan tasan zasu iya naɗa mata na jaki, amma badan haka ba sam batajin zata iya raga musu ta ɓangaren ragargaza musu magana ko wace iri ce, cikin san jawo ƙarfin gwiwa tace" to shikenan bazanyi girkin ba tunda aibaku kuka ɗaukeni aiki ba kuma ba asaminku A cikin albashi na ba balle kudinga wahalar dani kamar baiwarku,ta faɗa A yayin da take shirin bawa ƙafarta iska,dan tasan tsaf zasu naɗa mata duka,kamar ta sani kuwa Farida mai jiran ƙiris ita ta miƙe tayi wani irin tsalle ta sha gaban Bintu,da sauri Bintu ta matsa baya cikin yanayin ta na nuna firgici ,Nabil yace"ke Farida meye haka ne? Hauwa'u tace"idan bataya mu dukanta zakayi ba kayi shuru da bakinka inno bata nan tana ɓangaren Alhaji Baba Dan haka zaneta zamuyi la ada waje!' Sayyid yace" malam ka rabu dasu su zane bakin tsiwar duk da mugun sanda nake mata hakan ba zai hana nayi mata rashin mutunci ba!'Bintu tace"Ni dan Allah ku rabu dani babu ruwana daku,kuma ai gaskiya na faɗa ba aikinku nazoyi ba da haka sai ku rabu dani!kan ta rufe bakinta Siddiqa tasa hannunta ta doke bakinta,aiko Bintu taji zafi tuni idanun ta suka kawo ruwa wata zuciyar tace"da ita karki sake ki bari suga hawayenki daga nan zasu ƙara rainaki, dan haka sai tayi ƙoƙarin shanye hawayenta,A hankali ta shammace su ta angije Farida ta hankaɗata tayi ƙasa bata tsaya wata wata ba ta arta ɗakinta tasaka key, Farida ta lailayo wani uban ashar ta dan ƙara mata, Sayyid yace" kuzo kuji wani abu wannan duk ba mafita bace!' gaba ɗayan su suka zo suka haɗa kai yayi musu ƙusƙus, Siddiqa ta yi wata shewa tare da cewa lallai yarinya kin ɗauko ruwan dafa kanki kin shiga uku a gidan nan!'dariya suka saka gaba ɗayansu suka shiga ɗibar garar girkin Bintu maisa kunnen oga Abdallah motsi.


Taufiƙa ce ta samu Bintu A kiching tana yiwa Abdallah abincin dare sai dai bata jima da ɗorawa ba saboda tsoron kar ta fito su haɗu su casata, Taufiƙa tace" Bintu me kike dafawane haka? batare da ta bata amsaba ta zuba mata ido cike da mamakin yadda tayi mata magana cikin kwantar da murya, murmushi Taufiƙa tayi tace"ko yau kin kurmance ne? girgiza kai Bintu tayi kana tace" yau tuwon semo nakeyi masa da miyar ɗanyan kubewa sai farfesun kifin ruwa!' Taufiƙa ta riƙe baki cikin mamaki tace" wai shi kam dan Allah Bintu meyasa yakeson irin wadannan abincin? Bintu tayi dariyar ta me kyau har kumatunta na loɓawa kana tace"wallahi Ni ma bansani ba kawai dai kowa kinsan da abinda ya fi burgeshi A rayuwarsa to shi dai yana san abincin mu na gargajiya!' Taufiƙa tace" kuma hakane fa maganarki!' yanzu dai ki kawo nayi masa girkin nan yau inaso yaji irin baiwa ta nima saboda nan gaba!' ɗan jim Bintu tayi cike da tunanin ta bata ko kar ta bata,Taufiƙa tace" Bintu bazaki bani ba?kinga dolene na koyi duk irin abibcin da yake so saboda gaba yadda nake mafarkin zama matarshi kinga hakan shine dai dai ko?Bintu cike da mamaki take bin bakin Taufiƙa da kallo kai wannan irin wawanci haka, sai yanzu ta gane manufar ta na yadda ta can ja mata lokaci ɗaya ashe ita da manufarta wato ashe ita ma ta faɗa komar soyayyar Oga Abdallah,tab amma lallai sun gamu da wahala in dai Oga Abdallah ne, Bintu tace to shikenan muyi tare!' Taufiƙa tace" Ni dai ki tsaya kawai ki tayani da hira har na gama sai ki ɗiba kikai masa!' Bintu tace Tom shikenan,amma fa ranta cike yake da tsoro kawai dai ta bayarne saboda kar ta jangwalo wa kanta wata rigimar bayan ta ɗazu da tasan ba ƙyaleta su Farida sukayi ba,

Sunayi suna hira har Taufiƙa ta gama komai aka zuzzuba cikin kuloli, daga nan ta koma ɗaki sai da tayi sallar isha'i kana ta fito ta ɗibi kayan abincin ta nufi falonsa,bayan ta jera komai kamar yadda ta saba ta fito tashiga wajen inno suka fara taɓa hira.


Sai da ya gama komai na aldarshi da yasa ba na yau da kullum kana ya nufi dining ya zauna ya fara savin ɗin kansa. lomar farko da yayi kasa haɗiye wa yayi sai da ya nufi sink ya zubda kana ya kuskure bakinsa ya koma ɗakinsa ya shiga yayi brosh,zama yayi cikin kujerarsa ya haɗa hannayen sa biyu ya rufe fuskarsa, yunwa yakeji sosai danshi bai cika san zama da yunwa ba, tun daya saba bawa cikinsa haƙƙinsa, wayar sa ya ɗauka ya dannawa inno kira,bayan sun gaisa yace" inno yarinyar nan tazo!'daga haka ya maida wayar ya ajiye,inno suna tare da Bintu har lokacin,duban Bintun tayi dan tasan ita yake nufi sanin cewar babu wanda yake shiga ɓangaren sa idan ba itaba,tace" tashi kije saraki na kira wataƙil wani abun yake buƙata!' dum,haka ƙirjin Bintu ya buga cike da fargaba ta tashi ta tafi tana fatan Allah yasa ba ganewa yayi ba ita tayi girkin ba.


A hankali tayi sallama tare da ƙara sawa gabansa ta duƙa,kana tace" Barka da dawowa wani mugun kallo ya fara watsa mata kafin yace" wa kika bawa yayi abincin can? yana maiyi mata nuni da kan dining table,kallon gun tayi kana cikin tsoron abinda zai biyo baya tace" Ni nayi!' ɗan wara idonsa yayi akanta gami da cewa ko? gyaɗa kanta ta kumayi a tsammanin ta ya yadda, miƙewa yayi yace" zo nan!'tashi tayi tabi bayansa har zuwa dining ɗin, sai da ya zauna kana yayi mata nuni da itama ta zauna,A ɗarare ta ɗosana ta zauna gaba ɗaya idanunta sun fiffoto waje saboda tsananin tsoro,nuna mata wanda ya faraci yayi yace" oya maza kicinye su duka,zaro idon ta kumayi da sauri ya kawar da nasa,cikin ransa yace" yanzu zata fara firgita mutane da waɗan nan shanyayyun idanun,fuska ta kwaɓe tana shirin sakan mai san gar tattun hawayen ta,yayi saurin ɗora hannun sa kan laɓɓansa yayi mata alamun tayi mai shiru,haka nan ta haɗiye kukanta ta sanya hannu ta gutsiri tuwan tare da kaiwa bakinta,kasa haɗiyewa tayi tafara ƙoƙarin furzo shi,zaro mata manyan idanunsa yayi wanda suke da wani irin maganaɗisu acikinsu, ga wani maiƙo- maiƙo dake cikinsu tamkar manƙuli aka ɗiga musu,tuni ta kuma rikicewa dama ga yanayin da take shiga a duk lokacin da ta kasance tana shaƙar numfashi akusa dashi,sai ya kuma haɗe mata ya dinga bata wani irin yanayi mai wuyar fassarawa har wani sanyi sanyi take ji A can cikin ƙashushuwa da ɓargon ta,ƙasa tayi da kanta tana haɗiye tuwan daƙyar,haka ta dinga cusa tuwan cikinta tana kuma zabgawa Taufiƙa Allah ya isa saboda ita tajawo mata wannan tashin hankalin,bata taɓa zatan bata iya abinci ba ita A tata wautar tayi zatan kowa ya iya abinci mai daɗi shiyasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login