Showing 129001 words to 132000 words out of 184937 words
wahalar kamo hannun ta ba, Bintu jinta tayi kawai asaman cinyar sa,zabura tayi zata tashi,ya riƙeta cikin haɗa fuska yace"malama saurara ba abinda zanyi miki cizona kawai zan rama!'zaro manyan idanunta tayi bakinta na rawa tace"to ai ban cijeka ba!' amma aikin cinye min baki!'ya faɗa yana mai tsare ta da manyan idanun sa masu maiƙo tamkar an ɗiga musu man gyaɗa,ɓoye fuskar ta tayi a ƙirjinsa tana jin tamkar ƙasa ta buɗe ta shige ciki,ci gaba yayi da cin abincin sa,sai da ya gama kana yace"kinci abinci?girgiza masa kai tayi,tashi yayi da ita ajikin sa kana ya maida ita inda ya tashi ya zaunar yace"maza kici yanzun nan ki sameni a ɗaki muyi magana!'yasan idan ya zauna bazata iya sakewa ba shiyasa yayi mata haka,cikin sauri tace"bazan iya cin komai ba idan har banyi abinda zuciyata ke Umar tata ba a yau!'zuba mata ido yayi na sakanni kana yace"nace kici abinci ko!'ganin yadda ya tsatstsare ta da mahukuntan idanun sa yasa ta shiga tura tuwon da ya saka mata batare da tana gane ɗanɗanon sa abakinta ba,bai matsaba sai da yaga cewa tabbas ta ƙoshi kana ya janyo hannun ta suka koma ɗakinsa, brosh yaje yayi kana ita ma yasa ta tashiga tayi,yana sane da yadda yaga duk ta ruɗe bata yin komai cikin nutsuwa sai duban lokaci take yi,zama yayi abakin gadon yace"itama ta zauna,a ɗarare ta zauna,kafin yace komai ta miƙa masa wayarta tare da danno masa recording ɗin Muryar Nafisa wadda ta fito tar- tar tana bawa Bintu labarin tsiyar da ta shuka,bai tanka ba kuma bai motsa ba sai idanun sa da suke kan wayar Bintu tamkar wanda yake ganin Nafisa azahiri.
"Recording ɗin yana zuwa ƙarshe Abdallah ya kashe wayar tare da miƙewa tsaye goya hannayen sa yayi yana ɗan zaga filin ɗakin,a fili yace"hakan yana nufin ke nan su Fafi suna waje ɗaya da Abbana,mutum ɗaya ne duk ya sace su?idan hakane meye hurumin su acikin wannan al,amarin?munji manufar Nafisa sai kuma manufar baƙin azzzlumin!'sanadin juya bayan da yayi ne yasa baiji fitar Bintu ba sai rufe ƙofar ta,cikin zafin nama yabi bayanta wanda tana gab da fita daga falon ne ya cimma ta,cikin zafin naman da bai san yana dashi ba ya kamota, cikin wani irin yanayin damuwa yace"Bint Ina zakije?me kike Shirin aikatawa ba tare da kin sanar dani ba?cikin wani irin azababban fushi da ƙwarin gwiwar da take ji,tace"t wan can ɗakin zani kuma a yau zan fiddo abinda aka ɓoye acikin sa ko akeyi aciki,tun tuni mafarki na ya nuna min cewa wan nan ranar itace ranar da zan baiyana abinda ke cikin ɗakin nan,kuma Allah ya bani ikon ganowa wan nan ɗakin shine zai kawo mana ƙarshen wannan mugun mutumin,Yahh Abdallah dan Allah kabarni naje inaji ajiki na cewa a kwai Babban Al'amarin dake ƙunshe cikin ɗakin nan!'kallon agogo tayi cikin tashin hankali tace"lokacin zai wuce,sha biyu ta kusa ƙara sawa bayan kuma shine lokacin da jikina da zuciya ta suke bani cewa Allah zai bani nasara,a mafarkina angaya min cewa da zarar biyu tayi banyi abinda ya dace ba komai zai iya faruwa saboda a wannan lokaci ne mai dakin yake fitowa dan aikata mugun nufin sa!'tana kawowa nan a maganar ta ta fita da wani irin sauri, Abdallah bashi da zaɓin da ya wuce yabi ta tunda taƙi sauraren sa ma balle yasamu abin cewa,addu a ce dai bata yankewa daga bakin sa da zuciyar sa.
A cikin wannan daren kuma tuni ƴan aiken Abdallah sun cika aiki sun sanƙamo masa Abigirl wadda take ta ihun neman dauki,duk da cewa Muryarta bata fita saboda manne bakinta da sukayi da salatif,tun tana iyawa har ƙarfin ta ya ƙare ta haƙura, kasan cewar basu taho da wuri bane yasa suka kai har wannan lokaci na shabiyu da min tuna na daren ranar,samuyal ne ya dubi Safwan cikin gurɓatacciyar Hausar sa yace"Safwan baka lura da moto ɗin dake binmu tun fitowar mu daga cikin gari ba?ya faɗa yana mai leƙa bayan sa,Safwan dake gaba kusa da drever shima saita madubi yayi dan san gasgata maganar samuyal ɗin,sani dake tuƙi yace"tabbas maganar samuyal haka take ashe bani kaɗai na luraba, kawai nayi shuru ne saboda nayi tunanin ko hanya ce ta haɗamu!'Samuyar yace"nima daga farko abinda nayi tunani ke nan amma yanzu na fara zargin wani abu saboda da hanya ce ta haɗa mu to tabbas zasu iya wuce mu ko kuma mu muyi musu nisa!'shuru su kayi gaba ɗayan su kowa da abinda yake rayawa a zuciyar sa,sai daga can Safwan yace"ko Oga Abdallah zamu kira mu sanar dashi?sani yayi saurin cewa a'a ba haka za ayi ba bai kamata mu katse masa baccin sa ba,dabara zamuyi yadda zamu gane idan ma mu ɗin suke bi tunda kunga yanzu bamu tabbatar ba!'Samuwar yace"good i dea,hakan ne yasa suka ɗauke hanya suka canja daga hanyar da suke kai dama sun zo dai dai titin da zasu hau su shigo Abuja.
Yanzu kam sun tabbatar da abinda suke zargi dan kuwa motar su ta kuma biyowa tare da ƙara gudu daga dukkanin alamu dai yanzu so suke su cimmasu, Safwan yace"sani ƙara gudu so suke su tare mu da alama dai wan nan abar dake tare damu suke son karɓa!' yana nufin Abigirl wai,cikin wani irin gudu motar ta ci gaba da biyo su wanda ga dukkanin alamu ma kamar so suke su bige motar su Safwan ɗin,ganin haka yasa hankalin Samuyal ya tashi,cewa yake kashemu suke sonyi!' sani yace ku kwantar da hankalin ku insha Allah muna tare da Allah kuma zai fidda mu ƙarshen sune yazo, ga dukkanin alamu Abigirl ta san sirrin su shi yasa suke son kasheta ganin bazasu sameta bane yasa zasu kashemu baki ɗaya!'
A can ɓangaren su Bintu kuwa lokacin da Abdallah ya biyota har tayi masa nisa hakan ne yasa ya haɗa da gudu ya cimmata, ESTATE ɗin yayi shuru bakajin motsin komai saina iskar damunar da take kaɗawa A hankali,atare suka shiga wajen da taimakon addu'a A bakunan su,har suka je bakin ƙofar basu daina ambaton Allah ba,cikin ƙarfin gwiwa Bintu tasa hannu akan ƙofar tana ɗan turawa,cikin raɗa Abdallah yace"Bint ya zamuyi mu buɗe ƙofar nan duba ko wajen ɗan mukulli babu!'Yahh Abdallah angaya min yadda zamuyi ƙofar ta buɗu,ta tsafi ce ƙofar dan haka karya tasirin ta addu'a!'ta faɗa tana ƙara ɗora ɗaya hannun nata akan ƙofar,matsowa yayi shima tare da yin yadda tayi rufe idanun ta tayi shima sai yayi hakan, addu'oi suka fara karantawa a fili,cikin ƙudurar Allah saiga ƙofar na yin ƙasa tamkar wadda ake janye ta ta cikin ƙasa,bin ta sukayi da ido har ta nutse cikin ƙasan gurin,kallon juna sukayi alamu yayi mata da su shiga, cikin tsananta addu'a da miƙa lamura ga Ubangijin talikai suka afka ɗakin wanda yake dun ɗum da duhu baka iya ganin ko tafin hannun ka,da sauri Abdallah ya riƙo Bintu bakin su ya kasa daina ambaton Allah.
Sosai fa mutanen ke son tura motar su Samuyal cikin rami,amma hakan ya gagara dan dukkan su addu'oi ne ɗauke abakin su, idan kacire Samuyal da ba Musulmi ba,shi kam amatuƙar ruɗe yake dan baya son mutuwa ko kaɗan,ji yayi kawai bakin sa ya kama innalihin da su Safwan suke ta ambata cikin ɗan ɗaga sauti yake ƙara nanata ta akan harshen sa,tun yana faɗa ba daidai ba har ya dawo yana faɗa dai dai,sai ya zamana duk addu'oin da suka kama marasa tsauri shima yana iya kamawa kamar allahumma ajirni filmusi bati wakalifni khairan minha, da la ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalumin,lahaula da A uzu bikalimatullahittammati min sharril ma kalaƙa,cikin ƙudura ta ubangi da kiyaye bayin sa da suka tsaya gareshi suka nemi taimakon sa,a maimakon mutanen su sami na sarar jefa su Safwan sai kawai burki ya ƙwace wa drevern waccan motar kafin ƙiftawar ido sun afka dogon ramin da suke san jefa su Samuyal,ji kake bam motar ta tashi da wuta.
Wata irin doguwar ajiyar zuciya suka sauke tare da faɗin Alhamdulillah!' a fili sai shima Samuyal ya kuma faɗa, sai lokacin suka samu nutsuwar tunawa da abinda Samuyal yayi, shi kuwa Samuyal tuni ya tafi duniyar tunanin ƙarfin mulki irin na Ubangijin sammai da ƙassai,ganin abun yake tamkar sihiri wato waɗan nan addu'oin da sukayi sune suka tseratar dasu daga hannun waɗan nan mugayen,suma dai su Safwan basu ce masa komai ba amma suna fata da buri wan nan abin da ya faru yanzu ya zama izina da kuma sanadin da Samuyal zai gane gaskiya,ita kuwa Abigirl saboda abin da suka shaƙa mata bata san duk wan nan abin ya faru ba,
Wayyo Yahh Abdallah duhu babu haske ya zamuyi yanzu ta ina zamuga makunnin fitila?Bint ki nutsu Mana Ina ƙwarin gwiwar taki ya tafi?bakiga Allah yabamu nasarar shigowa ɗakin ba?kuma kina gani saboda Allah yana tare damu bamu sami wata matsala ba,kuma kin san abinda yake faruwa dake duk lokacin da kika zo wajen amma a wannan lokaci dake nasarar tana garemu babu abinda ya faru, kuma zamu fita lafiya insha Allah!'jikin sa ya shiga lalubawa,cikin ikon Allah kuwa sai gashi ya zaro karamar wayar Bintu,cikin farin ciki yace"Alhamdulillah,tare da kunna toch ɗin wayar.
Kamar an min tsine shi haka ya farka, cikin matuƙar tashin hankali da kiɗima ya lalubo wayar sa, wajen kira ya shiga ya lalubo nombar dayake son kira,yadda ya saurara yake jiran aɗauki wayar haka yake sauraren bugun zuciyar sa,har wayar tayi ta katse ba'a ɗauka ba,kira yasake yi nan ma dai abu ɗaya ne No respond,zirga zirga ya shiga yi cikin ɗakin yana cigaba da kiran wayar,can bayan wasu ƴan mintuna sai aka ɗaga wayar,ba tare da ya saurara yaji mai magana ba ya hau surfa ruwan ashar da masifa,dan wulaƙan ci kunaji ina kiranku amma kunyi biris dani,shin kun ɗauko Abigirl ɗin kun kasheta? yallaɓai ba masu wayar bane ga yanzu aka tsinci wayar abakin ramin hanyar da ta tsaga ta shigo Abuja da Kano,ansami masu motar da motar sun faɗa ramin nan sunƙune gaba ɗayansu babu wanda ya tsira!'cikin rawar baki yace"motar ɗaya ce ko biyu?me maganar yace"a'a mota ɗaya ce"kashe wayar yayi tare da wulla ta gefe,ya shiga yarfa hannuwa,shike nan yanzu Abigirl tayi nasarar kubuta daga gareni yanzu wannan shegen yaron sai ya samu nasarar ganin bayana?tabbas na kaɗe idan har ya samu kan Abigirl yanzu me ya kamata nayi ke nan?ya tambayi kansa,cikin sauri yace"ya kamata naga shugaba domin yasamomin mafita,na rasa yadda zanyi da Abigirl ita ba musulma ba amma sai taurin rai ko me yasa na kasa kashe ta ta hanyar tsafi?ya kuma tambayar kansa kamar wani zararre,wani abu naga yayi tare da faɗin wasu ƙalasimai irin na waɗan da suka riga suka bata suka bar turbar gaskiya,cikin ƙanƙanin lokaci saiga shugaba azukyi ya bayyana agaban sa,durƙusawa yayi cikin magiya da tashin hankali yace"shugaba ka taimakamin duk wata dabara ta fara ƙwace min shegun mutanen nan sun tsira daga tarkon da na ɗana musu,yanzu kuma na rasa fafita, ka taimakamin na sace Abigirl daga hannun yaron nan!'shugaba Ezukyi yace"nanu ka sauka daga kan hanya ne shiyasa al'amuran suke ta zuwan maka a haka,amma bari na gwada na gani!'wani siddabaru yayi saiga su Safwan acikin mota suna gab da shigowa cikin gari,hannun sa ya miƙa dan ɗauko Abigirl daga cikin motar amma kafin ƙigtawar ido ya dawo da hannun da wani irin sauri yana yarfa shi ga dukkanin alamu wani abu ne ya samu hannun,cikin zafin da yakeji ajikin hannun yace"nanu a kwai matsala fa dan kuwa bazan iya taɓa Abigirl ba,kana ganin yadda suke ta addu'a ga kuma karatu da suka saka gaskiya bazan iya ba,sai dai mu canja wata hanyar!'nanu yace"to tunda hakane shugaba mu rufe mata baki mana,kaga idan sunje babu bakin da zata iya faɗar ko mai a kai na!'shugaba Ezukyi yace bari mu gwada wannan,saida yayi siddabarun sa na tsawon minti ɗaya kana ya dubi nanu da ya zuba masa ido yace"munyi nasarar wan nan, amma dai kasan duk sihirin da kayi yana zaune ne karkashin ikon wannan ɗakin dan haka ka daɗa kiyayewa!'ɓat ya ɓace ba tare da Allah ya bashi ikon gano matsalar da nanu yake ciki ba, ta shiga ɗakin nan da su Abdallah su kayi,sai alokacin hankalin nanu ya kwanta yasan kafin su Abdallah su ankara zai kashe Abigirl shi ke nan bakin sa ALAIKUM,
Zuba masa ido Sarah tayi cikin tausayin mijin nata,kana ta ɗan numfasa tace"dan Allah yaya Habibu ka tashi daga kan sallayar nan kazo mu kwanta haka tun ɗazu fa kake abu ɗaya ai rai ma yana buƙatar hutu ga cofee ɗin na kawo maka,kazo ka ɗan sha ko zaka samu nutsuwa!'wani irin kallo yayi mata, kana yace"Sarah me kike faɗa hakane dama ana gajiya da ibada?to idan ma ana gajiya Ni dai bazan gaji da roƙon Allah da kai masa kukana ba,kuma kike batun nutsuwa ai tunda na ɗora goshina aƙasan gurin nan na miƙa lamurana gurin Allah to nutsuwa ta gama samuwa a gareni,dan haka kar ki kuma hana Ni yin ibadata,tunda ke bazaki yi ba!'ya faɗa cikin nuna ɓacin ransa da abinda tayi ɗin,cikin kwantar da murya tace"kayi haƙuri ba manufata ke nan ba ya za ai na hana ka ganawa da ubangiji amma kayi haƙuri insha Allah bazan sake ba!'ɗan murmushi yayi tare da cewa yauwa ko kefa kawai ki tayani da addu'a Allah ya kawo mana ƙarshen matsalolin mu!'tace" insha Allah yaya Habib!'daga nan suka koma suka kwanta kowa da abinda yake saƙawa azuciyar sa.
Wani irin rawa jikin Bintu ya shiga yi cikin kiɗima da tashin hankali tace"Oga Yahh Abdallah kana ganin abinda nake gani? innalillahi'wa'inna ialaihi raji'un!'shine abinda Abdallah ya shiga furtawa cikin nasa tashin hankalin,ɗakine wanda aka tara kayan tsafi dana siddabaru kala kala ko mai kagani da ɗigon ja ajikin sa,sassan jikin mutane kuwa yafi hamsin wasu an tsaface su a haka wasu kuma sun mutu sai gangar jikin ce ke aiki, idanuwan Bintu ne suka shiga ƙoƙarin rufewa saboda tsabar tashin hankali,da sauri Abdallah ya tarota yana goge mata fuska tare da cewa Bint ki tashi karki suma da akwai matsala zaman mu bazai yiwu agurin nan ba ki faɗa abinda ya kamata muyi yanzu,kamar wanda ya watsa mata ruwa haka tayi saurin buɗe idanunta saboda tunawa da tayi da wata ƙofa acikin ɗakin wadda aka bata tabbacin sai ta buɗe ta,saidai duk iya hangen ta bata ga wata ƙofa ba,cikin tashin hankali tace"Yah Abdallah mu duba a kwai wata ƙofa da matar tace"mu duba kuma Ni bangan ta ba anan!'cikin sauri yaja hannunta tare da cewa muduba sosai!'tace"sakeni na duba wani ɓangaren kaima kaduba wani wajen!'bint mu duba tare kawai bazan yadda ki keɓe ke kaɗai acikin wannan lokacin ba!'da sauri suka shiga tutture ƙwalangwal ɗin da suka yiwa ɗakin ƙawanya tare da cire duk wani abu da suka ci karo dashi ajikin bangon ɗakin,ɓanna sukeyi fa bata wasa ba,gaba ɗaya sun har gitsa ɗakin baka jin sautin komai saina karar zubewar abubuwa da fashewar su,kafin wani ɗan lokaci ɗakin ya turnuƙe da wani irin hayaƙi me shiga tsakiyar kai harda wani yaji me ƙarni da saka amai,cikin fitar da numfashi da ƙyar Abdallah yace"Bint zo mu fita kar dakin ya ƙone damu ko ki samu matsala da wannan hayaƙin!'itama numfashin take fitar wa daƙyar tare dacewa bazan bar ɗakin nan ba sai na ɗauko abinda aka ɓoye a ciki!'me akaɓoye aciki bayan kina ganin abubuwan da suke ciki!'Ya Abdallah bazaka gane ba kawai karabu dani sai na ɗauko shi koda bazan same shi a raye ba!'waye ne haka?bata bashi amsa ba saboda ganin wani waje daga can kusurwar ɗakin anyi shedar zanen ƙofa amma babu ƙofar,gurin ta tunkara gadan gadan tare da saka hannunta a tunanin ta bangone saboda babu wata alama da zata nuna maka ba bango ne gaba ɗaya ba,ashe ƙoface akayi mata kalar fentin san nan kuma ashafe take babu tudu, kamar yadda bangon yake haka take sak sai wannan shatin da Bintu ta gani, cikin sauri suka kalli juna da Abdallah,kana kuma atare sukayi Bismillah suka tura ƙofar saiga ƙofa ta buɗe.
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page 49 ```
Kamar an tsunkule shi haka ya tashi afirgice,zoban sa da yake ta faman wuta ya kalla abin baƙaramin ɗaure masa kai yayi ba,saboda tunda yake da zoban baitaba nuna masa wan nan alamar ba,da sauri ya tashi tsaye Saboda tunawar da yayi duk sanda zoben yayi wuta shike nuna masa cewar da akwai matsala,siddabarun sa yayi dan ya ɓullacikin ɗakin ba tare da yayi tafiya ba kamar yadda ya saba a duk sanda yaso,sai dai ga mamakin sa abin yaƙi yiwuwa hakan ne ya kuma tabbatar masa cewa da akwai babbar matsala,cikin sauri ya fita daga ɗakin nasa ya wuce falon sa ya fita duk cikin tashin hankali da fargaba,duk takun da zaiyi bugun zuciyar sa ƙaruwa yake.
Ihu Bintu ta saka tare da kanƙame Abdallah cikin wata irin kiɗima da rawar jiki,riƙeta yayi ajikin sa tare da zubawa daskarerren mutumin ido, lulluɓe yake cikin wani abu kamar yana, babu abinda ke motsi ajikin sa sai ƙirjin sa dake nuna alamun bugun zuciya,ƙirjin Abdallah shima babu abin da yakeyi sai bugu dan har yanzu bai fuskan ci waye a cikin wannan dabai bayin ba amma dai tabbas ganin mutumin ya tsunkar mai da zuciya,Bintu ce tayi saurin dawowa cikin hankalinta lokacin da kunnuwan ta suka fara jiyo mata alamun taku ta can wajen dakin saboda tagar da ke kusa da ita wadda take agarƙame, jijjiga Abdallah ta shiga yi cikin tashin hankali tace"wayyo Yahh Abdallah lokaci yayi yana nan tahowa mu ɗauke shi mu gudu!'yace"Bint sai dai mu mu nemi gurin tsira tunda kinga bashi kadai bane,kuma idan mun ɗauke shi bamu san inda zamu kaishi ba!'cikin tashin hankali da kukan da ya kufce mata tace"Yah Abdallah saboda shi nazo saboda na fita dashi nazo idan ban fita dashi daga gurin nan ba to babu amfanin da