Showing 165001 words to 168000 words out of 184937 words
tasan ba wai ruwan yake buƙata ba,tace"maza jeki kaiwa mijinki yana cikin falonsa!'ai kafin ta kai ga rufe bakinta tuni ta tsinci Bintu abakin kofar falon Abdallah,riƙe baki tayi cike da dariyar yarintar Bintun.
Kamar an jehota haka ya ganta a gabansa kasan cewar tun shigarsa bai zaunaba,zuba mata idanunsa masu saukar mata gajiya yayi,haka nan ta dinga jin wani irin sanyi har cikin kashinta sunkuyar da kanta tayi tana jin wasu ƙwallan da bata san daga ina suke ba,ɗan ware idan sa ya kuma yi akanta,kana a hankali ya riƙota kamar wanda yake tsoran kar yaji mata ciwo,ɗagowa tayi ta shiga yi masa wani irin kallo daya fara sashi kokuwa da numfashinsa, cikin wani irin salo da shauƙi ya haɗe ta jikin sa,tare da ɗora fuskarshi saman kanta,zame ɗan kwalin kanta yayi ya shiga shinshina gashinta kamar wanda ya samu turare,Bintu cikin wata irin kasala ta kuma lafkewa cikin faffaɗan ƙirjinsa,can kasan maƙoshi ta tsinkayi Muryar sa yana cewa my Bint,sai kuma me kike bukata? Ummm faɗa min!"ya faɗa cikin cusa kanshi a wuyanta yana goga fuskarsa da ɗan gemun sa akan uyan nata, cikin wata iriyar kasala da yake saukar mata ta shiga goga fuskar ta a kan ƙirjin sa tare da cewa"Ni kam ka gama min komai bani da wata sauran damuwa,ka cika min burina ka dawo min da farin ciki na, wannan ma kaɗai ya isheni!'ɗan murmushin gefan baki yayi tare da cewa a'a faɗa min dai ina sauraren ki da akwai wani farin cikin da kike bukata!'girgiza kanta ta shiga yi jikin ta yana kuma mutuwa da salon da ogan nata yake mata,kamar daga sama taji bakin shi cikin nata wata doguwar sumba yayi mata tare da cewa hmm Bint ki duba mana bakya bukatar wan Nan?a ruɗe ta kuma girgiza masa kanta,ya kuma sumbatar idanunta yana cewa da wannan ma,ya sumbaci goshinta da wannan ma,daga nan ya zarce da yiwa bakinta wata irin tsotsa tamkar wanda ya samu sweet.....
Mu haɗu a falon Alhaji Baba zama na biyu
Fatima y Adam✍🏽
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page 59 ```
"Kiran da yaji a wayar sa dake soke gaban rigar sa ita ta fara dawo dashi hankalin sa,amma duk da haka bai saki Bintu ba,a hankali ya zare bakin shi daga nata,tare da zuba mata ido,hannu tasa ta rufe fuskarta saboda kunya,leƙa fuskar ya shigayi tare da cewa duk bakya buƙatar waɗan nan eye Bint?janye jikin ta tashiga yi a ƙoƙarin ta nasan guduwa,domin ita sam bata gane inda maganarsa ta dosa ba,riƙeta yayi ganin zata gudu yace"baki bani amsa ba,ko sai anjima zaki gaya min?da sauri ta daga kanta kamar zatayi kuka, murmushi yayi tare da sumbatar dogon hancinta,kana ya saketa,sai da taje bakin ƙofa kana ta ɗan dakata tare da juyowa tace"kayi sauri ka fito kazo falon Alhaji Baba saboda ina buƙatar ganin farincikin Ammi da Oga Abdallah!'tana gama faɗa tayi waje da gudu fuskarta dauke da murmushi,zubawa kofar idanu yayi hannuwan sa zube cikin aljihun shi,ɗan shafa cikinsa yayi dan shi sai yanzu ne ma yake jin yunwar gashi kuma su kaɗai ake bukata a falon Alhaji Baba,kafin ya samo mafita sai ga Bintu ta dawo hannun ta ɗauke da plat wanda yake shaƙe da jelof ɗin shinkafa da uban kifi wanda kusan rabin abincin kifine,sai ƙamshi take gwanin da ɗi da burgewa,har tazo gaban shi ta janyo dan Centre ɗin tsakiyar falon ta ajiye yana kallonta,sai da ta ɗago taga kallon da yake mata,sai kuma ta tura baki tare da cewa wai miye ne haka da kallo?bai bata amsa ba sai zama da yayi yana maida duban shi kan abincin,cikin kasalar da ganin ta ke saukar masa yace"abun burgewa mata tana son mijinta yaci abinci kamar kinsan yunwa nakeji!'kamo hannun ta yayi ya zaunar da ita kan cinyar sa tare da cewa ke kinci abincin ne?girgiza kanta tayi,bai ce komai ba ya shiga miƙa mata abincin bayan ya ɗebo a spoon,Bata son yawan yi masa gardama hakan yasa ta buɗe bakinta ya shiga bata abincin,sai da ya tabbatar ta koshi kana shima yaci,yana gamawa ya ɗaga ta yana cewa muje Bint kar muga dakarun Alhaji Baba akanmu!' dariya tayi kana ta zagaya hannun ta ta saƙalo hannun shi,a haka suka fita dan zuwa falon Alhaji Baba.
Kamar yadda akayi a farko haka yanzu ma kowa ya hallara har da ƙari,saboda yanzu da akwai Alhjin Nafisa da kuma Hajiyar ta Ladidi,kowa ya nutsu,shigowar Abdallah da Bintu kawai ake jira,yayin da Hajjah take cikin wani irin hali duban farko zaka san cewa a kwai tsoro da tarin fargaba a tare da ita, Anty Nafisa ma tun da ta ga zuwan baban ta da kuma Hajiyar ta cikinta ya kuma durar ruwa,cike take da tashin hankalin abinda zai biyo bayan abinda ta shuka,
Hannun su rike dana juna sukayi sallama,wanda su sun manta a yanayin da suke,sai da Bintu taga kallon da Inno take watsa mata kana ta ankara,da sauri ta zare hannun ta daga nasa,can wajen Ummin ta ta nufa ta zauna tare da kwantar da kanta a kafadar ta,shi kuwa Abdallah daga nan gefan Dady Mansur da Dady jafar ya zauna,Alhaji Baba ne ya bawa Abdallah umarni da ya buɗe taro da addu'a,bayan sun shafa addu'ar ne Alhaji Baba ya dubi Abdallah tare da cewa,har yanzu kai muke bi Abdallah meye abu na gaba da zaka gabatar mana dashi?wayar Safwan ya kira yace"ku shigo dashi!'baiyi minti ɗaya da kashe wayar ba,akayi sallama a ƙofar falon tare da sako kai alokaci ɗaya.
Kaf mutanen falon sai gasu a tsaye,daga mai murza idanu sai mai zaro su dan san da ɗa tabbatar da abinda idan nasu yake gani,A hankali Alhaji Baba ya shiga takowa har zuwa inda Dady Abubakar yake tsaye cikin kyakkyawar shiga ta kamala kai baka ce shine wanda yayi tsawon shekaru ba tare da yasan inda kansa yake ba,kama hannun sa yayi cikin nasa jikin sa har rawa yake gwanin tausayi, zuba masa idanu yayi sai ga hawaye shar suna tsartuwa daga idanun Alhaji Baba jarumin namiji,sai ga Hajiya Babba ma tazo saboda ta kasa daurewa tsayawa daga nesa ga Ni take kamar zata iya yin saken da zata kuma rasa ɗan nata,ita kanta Hajiya zulaihat alkunya tayi amma idanun ta tamkar zasu faɗo ƙasa saboda kallon Abubakar kuka take yi mai tsanani wanda yake tafe da wani irin kewa da shauƙi,duk ƴan uwansa dake zaune a falon babu wanda yake son ko ƙifta idanun sa yayi dan kar ya buɗe yaga babu Dady Abubakar,Abba Umar ne yazo da sauri tare da cewa, Alhaji Baba yayane fa ko baku gane shiba?bai sauraren su ba ya tafi ya rungume ɗan uwan sa tare da sanbatun farin cikin sake kasancewar sa acikin su, cikin ƙanƙanun lokaci falon ya dau sautin kukan mutane,Hajiya Babba kuwa kama su tayi gaba ɗaya shida Umar ɗin ta rungume ta kasa cewa komai sai wani irin murmushi wanda yake haɗowa da wasu zafafan hawaye,shafa kawunan su takeyi kamar baza ta sakesu ba,A hankali Alhaji Baba ya zaresu daga jikin ta shima yayi musu kamar yadda tayi,duk kan su sun rasa bakin magana sai zubar hawaye ,cikin nutsuwa yajasu suka koma inda yake a zaune daga nan yabawa sauran ƴan uwan sa damar raɓar Abubakar ɗin dan nuna farin cikinsu na dawowar sa,cur cur haka zaka ga duk wanda suka rungumi juna ya koma yana hawaye kai abun dai gwanin tausayi,rarrafawa yayi har gaban inno matar da ta so shi ta nuna masa kauna tamkar ita ta haifeshi,ɗora kanshi yayi bisa ƙafafunta,hannun ta tadora a kansa tana mai cigaba da zubar hawaye,A hankali tace"Abubakarina Allah ya nufi ganawar mu,yau ƙudura ta hadu da irada,ƙudurar Allah ce take ta wanzuwa acikin wannan zuri'a tamu,dama inaji ajikina zuwan Bintu da Abdallah cikin ESTATE ɗin nan haskene da warwarewar duk kanin matsalolin mu,na daɗe inajiran wannan rana mai ɗumbin tarihi a garemu, Allah ya karemu ya kuma shiga tsakanin nagari da mugu!'ɗagowa yayi cikin san kwantar musu da hankali,yace"inno ku daina kuka godiya ya kamata muyiwa Allah da ya nufemu da sake haɗuwa!'A hankali Bintu ta tashi taje har gaban Ammi ta kama hannun ta ta miƙar da ita,kowa sai ya maida kallonshi kanta,bata tsaya da Ammi ba sai a gaban Dady Abubakar,hannun shi ta kama ta haɗa dana Ammi idanun ta cike taf da hawaye tace"duba nan Dady kar kamanta da macen da ta ɗauki tsawon shekaru idanun ta na tsiyayar da hawayen rashin ka da na gudan jininta,Ammi kenan macen da tashaƙi ɓacin ran da ya kusa illata rayuwarta, duk saboda kai,Ammi ki kawar da fulako ki tarbi Dadyn mu,saboda abinda ke zuciyar ki ya wanku,abinda ya tsaya a ƙahon zuciyarki ya faɗa!'kuma takawa tayi taje ta kamo hannun Abdallah, tana zuwa ta haɗa dana Ammi da Dady Abubakar cikin hawayen tausayin su,tace"ya Abdallah inaso kayi farin ciki kamar yadda kasani, kaji irin abinda naji lokacin da ka haɗani da Ummina da Abbana,kaima yau gaka ga Dady ga kuma Ammi,ta ɗan kalli Ammi da ta zuba mata ido tana san fahimtar inda zancan BINTU ya dosa tace"Ammi ga nan Ya Abdallah shine ɗanki da suka ɓace lokaci ɗaya da Dady,wata irin zabura Ammi tayi sai kuma ta koma tare da riƙe hannun Abdallah kamar zata ɓallashi, Allahu Akbar tabbas naji ajikina kullum fatana kenan abinda nake tunani akan ka ya zama gaskiya, Alhamdulillah,yau haske ya baiyana duhu ya yaye,yau ranar farin ciki ce a cikin wannan ahlin,ta faɗa cikin zubar da wasu zafafan hawaye wanda zamu iya kiran su dana farinciki,
Dady Habib kuwa tamkar zararre haka ya koma yana zaune amma duba ɗaya zakayi masa kasan cewa baya hayyacin sa,cewa yake yi nayi sake nayi sake yau gashi ƘUDURAR ALLAH ta baiyana,Dady Mansur dake hankalce da shi da Dady jafar sune kawai suka fahimci halin da yake ciki ga kuma maganganun da yakeyi,wanda basu ji abinda yake cewa ba,amma dai tabbas alamu sun nuna Dady Habib yana cikin wani yanayi na tsaka mai wuya,kowa a cikin falon nan farinciki yake, amma banda waɗan da suka shuka suke jiran girbewa,idan ka duba zuciyoyin su tamkar ƙabari haka suke,su kuwa su Alhaji Hashir sun shige cikin masu taya ɗan uwan su murna da samun ɗan sa da jikokin sa,tunda su sun samu salamar yafiyar wanda suka yiwa kuma nasu ƙullin makircin bai kai na su Dady Habib ba, wannan dalilin ne yasa suka samu nutsuwar zuciya.
A hankali Abdallah ya rungume mahaifiyar sa ya haɗa da Dady,Rahima da ta ƙaraso itama ta rungume ɗan uwanta,ɗago idanunshi yayi ya ɗorasu kan rigimammiyar fuskarta kamar yadda yake faɗa,nuni yayi mata da ta share hawayen fuskarta, murmushi ne ya suɓucewa Ummi da sauran waɗan da suka kula da abinda Abdallah yayiwa Bintu,ita kuwa Bintu umarnin mijinta tabi tasa hannu ta goge hawayen da suka ɓata kyakykyawar fuskar ta,zama yayi ya zaunar da Ammi da Dady Abubakar,kana ya koma mazaunin sa,fuskar sa ɗauke da wani ɗan maƙalallan murmushi,shuru falon ya kuma ɗauka yayin da zuciyar Dady Habib ta cigaba da bugawa da sauri da sauri, zufa kuwa tamkar wanda ake sheƙa masa ruwan zafi.
Abdallah ya buɗe baki zaiyi magana kenan, sai Dady Habib ya riga shi cikin yanayin fita daga haiyaci da tashin hankali na birnin kunya, yace"me zakace? me kuma yayi saura?kai dai wan nan yaro bakaji da kyauba,na tabbata dama zaka zama annoba arayuwata shi yasa tun farko naso wan can shegiyar ta kashe min kai,amma sai ta munafunceni saboda wata manufa tata,to gashi nan dai itama bata tsira daga tarkonka ba, wallahi bazan ɓoye muku ba na tsaneka kai da mahaifinka da wannan tsinanniyar yarinyar me kwana ido biyu,duk kece kika jawo komai!'ya faɗa yana nuna Bintu da kamar zai je ya rufeta da duka,a tsorace kowa yake kallon Dady Habib,Alhaji Baba kuwa bakinsa buɗe da tsananin mamaki yake duban ɗan nasa,haka jama ar da basu san komai akan abinda ke faruwa ba, Abdallah kuwa waya ya yiwa Safwan tare da bashi umarnin a shigo da Abigirl,ci gaba yayi da kallon Dady Habib da ya kasa zama sai muzurai yakeyi yana kuma faɗar maganganun da tun ba a fahimta har mutane suka soma fuskantar inda tashin hankalin nasa ya dosa.
Safwan ne yayi sallama ya shigo tare da Abigirl wadda tayi firi firi da ita kana ganin ta kasan cewa alhaki na biye da ita,tsakiyar falon Alhaji Baba ya zaunar da ita,kana ya juya ya koma inda ya a fito,kowa sai hankalin sa ya dawo kan Abigirl ita kuma hankalinta yana kan Dady Habib da ya zuba mata ido kamar wanda yake son aikamata da wani saƙo na gargaɗi,kawar da kanta tayi ta maida kan Abdallah da ya farayi mata magana cikin nutsuwar sa ta ko da yaushe,yace"kamar yadda na gaya miki ranar ne bana so kiyi min gaddama ko kuskure acikin abinda nake son sani daga gareki,nasan kin san abinda zai iya biyowa baya akan rashin bani haɗin kai da zakiyi,dan haka inaso ki faɗi komai da komai da kika sani akan yadda kika sameni, da yadda kika raine Ni da kuma manufarki akaina!'daga haka yayi shuru tare da maida kallon sa can ɓangaren da Bintu take,yayin da kuma ɗaukacin mutanen dake falon suka maida hankalinsu kan Abigirl, wadda ta zubawa Dady Habib ido,shi kuma yana maida mata da kallon gargaɗi, harma ya manta abin da yagama faɗa yanzu cikin fita hayyaci,kawar da kanta tayi daga gareshi tare da share hawayen da suke ta rige rigen sauka kan fuskarta,Dady jafar ne yace"ke muke sauraro!'duban shi tayi cikin saddaƙarwa tace"zan faɗa,zan faɗi duk wani abu da nasani,amma dan Allah karkuyi min komai,kubarni na koma garin mu bazan kuma waiwayar garin nan ba, ko da me maƙwaftaka dashine!'Dady jafar yace"idan har kika faɗi gaskiya kuma waɗan da kika aikatawa laifi suka yafe miki,to babu abun da za ayi miki,dan haka muna sauraranki!'
SHEKARA TALATIN da suka gabata,
Sunana Abigirl Adebayo ina zaune acikin garin Abuja nida mijina pastor David,tun da mukayi aure bamu taɓa haihuwa ba,tun bamu damu ba har muka fara nuna damuwar mu afili, mutane suka fara fuskantar halin da muke ciki,wala agida ko choch kullum addu'oin mu shine Allah ya bamu haihuwa,sai dai abin yaci tura shuru kamar ba roƙo muke ba,har ta kai da cewa na fara bin manyan bokaye da matsafa,amma duk abin da nakeyi mijina David bai sani ba,dan Ni nafishi damuwa da rashin haihuwar mu,mahaifiya ta ita ta kuma ƙara iza mun wutar san haihuwa saboda huɗu bar da tayi min wanda a da sam ba tunanina kenan ba,tayi min nuni da yadda David yake da arziki,ta nuna mini cewa idan ban haihuba,bazan taɓa samun abinda nakeso daga David ba,tace"min ai yanzu dan ban aihu bane yasa baya sakimin kuɗaɗe masu yawa,amma duk randa na samu baby to zanyi arziƙi ta sanadin baby,huɗubar ta tayi tasiri gareni,hakan ne yasa na kuma tashi tsaye gurin neman aihuwa ba dare ba rana,a kuma cikin lokacin ne komai ya faru,a ranar da bazan manta da ita ba,naje gurin bokana yake sanar dani Lallai sai na samo ƙaramin yaro na raine shi tsawon shekara talatin sa an nan zan samu abinda nakeso wannan shine laƙanin da bokana ya bani,kuma shine dalilin da yasa na taho ina tunanin hanyar da zanbi dan samun yaro karami.
Ina cikin wannan tunanin sai kawai na tsinkayi kukan yaro tamkar al mara,kasancewar daji ne sai na fara tunanin ko dai aljanu ne suke san zautani Saboda sun san laƙanin da boka ya bani,sharewa nayi na cigaba da tafiya,amma sai naji kukan yaron yaƙi tsagaitawa kamar dai anayi masa wani abu ne,dan haka sai kawai nabi kukan da sawayena,banji tsoro ba saboda na saba shiga irin dajikan nan saboda neman biyan buƙata ta,daga ɗan nesa na tsaya dalilin hangen wani mutumi da nayi da jajayen kaya na riga da wando da kuma yaro a hannun sa yana shirin yanka shi,abin ya bani mamaki har kuma lokacin ban daina tunanin ko jinnu bane,amma dake sam bani da tsoro sai kawai na tunkari gurin da niyar idan ma jinnu ne ai Ni ina da buƙatar su cikin rayuwata,ina zuwa nasa hannu na tare hannun mutumin dake shirin yanka ƙaramin yaron da bai wuce shekara uku ba,ɗagowa yayi a fusace,ganina sai kawai ya kasa magana ya tsaya yana kallona da mamakin abinda ya kawoni cikin wannan dajin,zaiyi magana ke nan na tari numfashin sa da cewa,kaiko mutum ne ko aljan? sai naga ya tuntsure da dariya tare da cewa ke kiji min da shegiyar mata,ai Ni zan tambayeki bake ZAKI TAMBAYENI ba,ko da yake ai idan aljana ce ke to tabbas zanji ajikina domin duk da cewa Ni ba aljan bane,amma ina gane su,saboda tsananin tarayyata dasu!'nace,to meyasa zaka kashe yaron nan?kai tsaye ya bani amsa da cewa saboda zai zama masifa arayuwata zaman shi tare da mu acikin ESTATE zai iya rusa duk wani burina!'sai nace masa'mai zai hana ka bani shi domin cika wani buri nawa!'girgiza kai yayi tare da cewa Ni kashe shi nake son yi,lallai sai ya mutu!'da na ga alamun dai ba zai bani shi haka nan ba kawai sai na bashi labarina da abinda yasa nake son ya bani shi ɗin,amma da na fahimci cikin gaggawa yake son mutuwar yaron, sai kawai na juya maganar mai makon nace shekara talatin da boka ya bani, sai nace shekara biyu,na kuma bashi tabbacin da nayi shekara biyu da shi zan kasheshi,a nan dai mukayi yarjejeniya,bai kuma ɓoyemin daga inda yaron yake ba har sunan kakansa sai daya sanar dani amma duk a matsayin gargadi ne,dan ya tabbatar min da cewa duk ranar da nayi kuskure cikin alƙawarin mu sai ya kasheni har lahira,da wannan batun muka rabu,da sauri na juya na koma gurin boka na na nuna masa yaron da na samu,yana ganin Abdallah sai kuwa ya zabura tare da cewa zaki iya rainin sa amma duk ranar da na bari ya karbi Musulunci shikenan duk abinda nayi ya tashi a banza, kuma shima sihirin da zaiyi min na tsawon shekara talatin ɗin