Showing 174001 words to 177000 words out of 184937 words
sannan ya kula da abinda Taufiƙan takeyi,ruwa ne take tsiyayawa Ya Abdallah a glace cup,tana ƙoƙarin miƙa masa,da sauri BINTU ta rike cup ɗin, ɗagowa tayi dan ganin waye sai tayi ido huɗu da fararen idanun Bintu da kyakykyawar fuskarta da take wani irin glowing na tsananin gyaran da take sha, murmushi tayiwa Taufiƙa da ta daskare a gurin, tana cewa ayya Anty Taufiƙa saukar yaushe ashe kin dawo?ta faɗa tana mai shanye ruwan,yayin da idanunta suke san kallon idanun ogan nata amma sam hakan ya gagara,sai ɗan tura bakinta da tayi,wanda batayi aune ba, taji Abdallah ya sunkuceta cikin sauri sai waje,wani irin kuka Taufiƙa ta shiga yi mai tsanani da ban tausayi,ita kuwa Bintu magiya ta shiga yi masa ya sauke ta kar su haɗu da wani,ba dan hujjarta ya sauketa ba,sai dan baya son kwakwazonta ya janyo hankalin Hajiya Babba,kama hannun ta yayi suka fara tafiya wanda a da taso yi masa gardama saboda tsoran fadan Hajiya Babba,sai kuma taji baza ta iya ba,
Cikin nasara da fatan Abdallah basu tarar da inno a falonta ba,hakane ya ƙara bashi ƙwarin gwiwar jan Bintu har can cikin ƙuryar ɗakunsa,suna shiga ya juyo da ita gareshi yana fuskantar ta,sunkuyar da kanta tayi tana wasa da yatsun hannunta,a hankali ya matso daga da ita,kana ya ɗago fuskarta,ita kuma tayi saurin rintse idanunta,zubawa eye lashes ɗin ta ido yayi,yana kissima abubuwa masu yawa can kasan zuciyarsa,a jikinta taji irin kallon da yake mata,dan haka ta shiga ɗan ware idanun nata dan ganin abinda yake kallo a jikinta,idanunta ne suka shige cikin nasa,yayin da ita kuma gaba daya ta diririce,cikin sanyin murya da tura baki tace"zan tafi kar Hajiya Babba ta nemeni!'haɗe fuskar ta yayi da tashi kana ya fara magana cikin shu'umar Muryar sa,me saka lakar mutum narkewa,yace"Bint""me kuke nufi dani ne ke da kakanninki?cikin rashin fahimta tace"kamar ya?cikin tura kanshi cikin wuyanta yace"da suka ƙwace minke ke kuma kika biyesu saboda baki damu dani ba,ya kuma tura kanshi a wuyanta yana shaƙar ƙamshin ta da yake neman zauta tunaninsa,yana faɗin Ummm Bint na gaji haka bazan iya ba,bazan iya nisa dake ba,bazan iya raba makwanci dake ba,bazan iya nisan tar numfashinki ba,Ina son halinki,inason kyawunki,inason nasabarki,Bint Ina son wannan ƙamshin naki,komi naki abinso ne,ya ƙara sa faɗa yana sauke mata numfashin sa,wanda yake hadewa da ƙamshin jikinsu yana bada wani irin yanayi mai wuyar fassarawa, maganganun Abdallah sun rikitar da tunaninta sun kuma jefa ta cikin tunanika iri iri,ji tayi ya ɗago kanta cikin wani irin sanyin jiki,ya sumbaci saman lip ɗin ta,kana yace"my Bint,kije Amma ki sani zaki bar mijinki da kewarki da muwar rashinki zata iya jefani wani hali!'daga haka ya saketa ya faɗa toilet,binsa tayi da ido,tana jin wani irin abu na mata yawo a tsakar kanta,cikin mutuwar jiki ta fita daga ɗakin,tana ƙissima yawan damuwar ta akan damuwar Abdallah,
Dady Habib fa yana cikin kin tsaka mai wuya,duk inda ya motsa sai yaji kukan jarirai,babu hali bacci ya ɗan fizge shi sai yayi mafarki da wasu daga cikin ƴan mata da samarin da ya salwantar da rayuwarsu,ko ina yayi babu daɗi,ji yake inama yana da halin ta riyo rayuwar sa da yayi domin ya goge duk wasu kura kurai da ya aikata,idan ka ganshi baza kace wannan hamshaƙin mai kudin bane mai ji da dukiya,su kansu masu tsaran shi sun fara tausayawa halin da yake ciki,dan ganin tun kan aje ko ina Allah ya fara kama shi da irin abubuwan da ya shuka.
A yanzu dai Alhaji Baba ya samu nutsuwa,hankalinsa ya kwanta, duk inda ya juya ƴan uwanshi da ƴaƴan shi da jikoki ne suke walwala,babu wani abu dake damunshi sai ɗan damuwar Habibu,shi yasa yake tunanin kiran Abdallah dan afito dashi haka,a ganin Alhaji Baba ai idan aka barshi da hukuncin Allah ma ya isa,su Alhaji Nasir kuwa tuni ya yanke ma amalar a minta a tsakanin su,sai dai mutumci,har kar kasuwanci da duk wani abu da ya shafe su ya yanke,ta kanas Alhji Salisu mijin Nana ƙarama yazo ya gurfanar agaban Alhaji Baba ya roƙe shi gafara,tare da neman masa gafarar Nana ƙaramar,dan tunda suka koma gida take borin sai ya saketa tunda baya san mahaifinta shi da mahaifinsa,kuma dama ba dan Allah ya aureta ba,dan haka sai ya saketa, Alhaji Baba a take ya kira wayar Nana ƙarama ya bata baki tare da nasiha mai ratsa jiki,babu yadda zatayi dole haka tayi hakuri ta ɗan gana ta zauna a gidan mijinta,
Tun ranar da suka rabu basu kuma haduwa ba,dan kuwa sosai ake shirin bikin ƴaƴan gata dan harda su Farida da Hauwa'u sai Taufiƙa da Siddiqa har da Rahima,kowa ka kalla shirin bikin yake,gyara kuwa tamkar za a canja musu halitta,dan fatar su har wani jaja da sheƙi takeyi,duk wannan abun da akeyi BINTU da Abdallah basa cikin haiyacinsu,bukace suke da ganin juna, amma Abdallah tsabar miskilanci ya haɗa yayi fushi da kowa ya ma bar gidan gaba ɗaya ya koma wajen Dady jafar, BINTU kuwa sai tsabar damuwar da take ciki sai ana acikin yi musu gyaran jiki sai dai kawai kaga hawaye na tsiyayowa daga idanunta,kamar yauma da suke cikin tafkeken dakin da aka zuba masa kayan gyara nau'ika iri iri,Rahima ta dubeta yayin da taga tana faman goge hawaye da bayan hannunta,ƙunshe dariyar ta tayi kana tace"Ya dai yarinyar Ya Abdallahn ta,me yafaru haka?tura baki tayi tana hararar Rahima saboda taga dariyar da take yi mata,Rahima ta ƙyalƙyale da dariya tana cewa,gaskiya Batula salon nan naku na burgeni,wai amma idan an cewa mutum ya faɗa tafkin soyayya sai yace ba haka ba,hasalima shi bai san soyayya ba!'ta ƙare maganar da sheƙewa da wata muguwar dariyar tura haushi,shigowar Ammi ce ta tsayar da ita tana rufe baki da hannun ta,Ammi tace"ke Rahima bana son sakarci,wan Nan dariyar ta lafiya da meye? da sauri BINTU ta koma jikin Ammi tana ci gaba da tsiyayar hawaye, cikin san fashewa da kukan da ya tokare mata maƙogaro,tace"Ammi da take,tun ɗazu take tsokana ta!'Ammi ta kuma jefawa Rahima harara,kana ta dawo da duban ta kan Bintu cikin lallashi tace"rabu da ita mamana,jeki zauna a ƙara sa miki,idan angama kizo zan baki abun daɗi banda su oo!'tura baki Rahima tayi kana tace"da ɗin abun dai yanzu nima ina da tudun dafawa!'gwalo Bintu tayi mata,daga nan Ammi ta fita ta barsu ana ci gaba da gyara su.
Tunda taji kira daga falon Alhaji Baba taji duk bata da nutsuwa,da sassarfa ta ƙarasa falon,inda ta tarar da Abbanta da Dady Abubakar da Dady Mansur sai inno,ga kuma uban gayya Oga Abdallah a hakimce tamkar wani sarki fuskar nan a cakuɗe,sai da ta zauna sannan ta kula da Taufiƙa da ke durƙushe gaban Alhaji Baba tana ta sheshsheƙar kuka,a san yaye tace"Alhaji Baba gani!'ɗan gyara zaman shi yayi tare da gyaran murya kana yace"yauwa Alhamdulillah, Taufiƙa ga shi nan na kira duk wanda yake da ruwa da tsaki akan al'amarin aurenki dan haka ki maimaita abinda kika faɗa min kafin shigowar su!'sunkuyar da kanta kasa tayi tana fatan dacewa Allah yasa kar Bintu ta kunya tata, Allah yasa kar ta ƙarya tata, cikin kwantar da murya tace"dama naje na samu Bintu munyi magana ta fahimta nida ita,tace"ta amince na auri Ya Abdallah zamu zauna lafiya amma bazata iya zuwa ta faɗa ba,sai dai Ni nazo na sanar da kai idan yaso in aka kirata aka tambayeta zata amsa cewa ta amince!'ta ƙarasa faɗa tana mai yiwa Bintu wani irin kallo na neman ɗauki da taimako,har da hada hannayen ta biyu bata tare da kowa ya luraba,sai Bintun da takewa Taufiƙan kallon mamaki da tambayar yaushe mukayi haka dake?maganar Alhaji Baba ce ta dawo da hankalinsu kansa,yace"to kinji ke Bintu shin wannan magana gaskiyane?kuma kin amince da auren Yara uwar ki da mijinki?wani irin duka ƙirjin Bintu yake,ga kuma tashin kallon da take jinsa a jikin ta na Abdallah,wanda sai kayi da gaske zaka san cewa kallon nata yakeyi,Dady Mansur ne yace"ke muke sauraro faɗima!'sam bata san lokacin da ta shiga gyada kanta ba,idanunta kuwa sunyi jawur,ƙiris suke jira su zubar da zafafan hawayen da suke cikin su,bata gama dawowa hayyacinta ba taji Abbanta yana cewa to tunda ta amince Alhamdulillah!'shi dai Dady Abubakar kallon Bintu kawai yake cike da san ta ɗago su haɗa ido, Alhaji Baba yace"Abdallah tashi ka dauki matarka ku tafi gida na baku sati ɗaya,wanda shine ranar da za a ɗaura auren ku kaida Taufiƙa,idan yaso sai a zarce da bikin gaba ɗaya!'Dady Mansur yace"hakan yayi Allah yayi muku albarka,amma Alhaji Baba wane gida zasuje nayi zatan suma a nan cikin ESTATE zasu zauna?Alhaji Baba yace"a nan zasu zauna amma sai angama gyaran sashen nasu dan haka suje ta ɗan anyi bikin sa tare gaba ɗaya!'a hankali Abdallah ya miƙe ya ɗan rissina yayiwa Alhaji Baba rada kana ya fita,inno tace"idan tayi tsami Maji!'Dady Abubakar yace"tashi maza ƴar albarka kibi mijinki!'tashi tayi jiki a sanyaye tabi bayan Abdallah, Taufiƙa kuwa kamar zata taka kanshege da farin ciki itama ta fita burinta ya kusa cika zata auri rabin ranta,su kuma suka cigaba da tattauna abinda yake sirrinsu ne.
Tunda suka shiga motar take kuka har suka fara tafiya,shi kuwa Abdallah babu abinda yace"mata,saima wakar ɗawisu da yasaka ya shiga bi a hankali cikin sassanyar Muryar sa,mai daɗin sauraro,inda yake cewa,zana sanar miki amsar tambaya a cikin zuci babu kowa sai ke ɗaya,ɗif tayi da kukan da takeyi sai Muryar sa dake ratsa duk ilahirin sassan jiki da jinin ta,lumshe idanunta tayi kamar mai bacci tana ci gaba da sauraro tare da mamakin yadda akayi ya Abdallah ya iya waka haka,
[11/15, 5:17 PM] F Y ADAM: 💕
*KUDURAR ALLAH* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page 62 ```
[11/15, 5:19 PM] F Y ADAM: 💫💥💫💥💫💥💫💥💫💥💫
*_ALBISHIRINKU MATAN AFRICA DA KEWAYE , SHAHARARRAR KUMA KASAITACCIYAR MAI SAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI MAMAN YUSUF YAR SOKOTO TANA YI MAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE CIKIN FADIN NIGERIA DA NIGER KARKU MANTA MACE MAI KYARA KANTA BATA BORANCI_* 💃💃💃💃💃💃💃 07069711327
_Akwai zafafan kayan Mata masu kyau da arha cikin sauki da rahusa Kuma duk inda kike zamu aika maki kayanki cikin aminci da yardar Allah ba cuta ba cutarwa don a Dade anayi sai gaskiya uwargida da amarya ku garzayo Kar abaku labari_
Munada kalolin Kaya kamar haka💥💫💥💫💥💫👇🏻👇🏻
Maganin sanyi sahihi Mai fatattakar sanyi cikin kankanin lokaci na maza Dana Mata
Maganin gyaran nono domin dawo da martaban nononki hadin gargajiya da bashida illah ajiki
Maganin hips Mai tado da hips cikin kankanin lokaci
Maganin kiba Wanda zaisa ki ciko dai dai misali kiyi kyau kema ki shigo cikin jerin Mata masu aji
Maganin rage kiba da tumbi Wanda zaisa ki sace ki koma Yar dai dai abin alfaharin kowane namiji,
Akwai kalolin gumbuna masu kyau da saukar da ni'ima
Maganin matsi masu ciko da gaba da matseki Kamar Yar budurwa uwa uba zasu Baki dandano Mai gamasar da maigida
Kalolin garrika masu bawa mace niima da jimawa ajiki
Kalolin tsumi Sha yanzu magani yanzu dasa Mai gida ihun Dadi
Zumar mallaka
Zumar goron Tula
Zumar ridi
Zumar Mai rubutu
Hadin mallaka
Turaren mallaka
Shu'umar humra
Turaren AL'AJABI
Matan gaske
Ak 49
Sirrin tafin k'afa
Turaren fuska
Hatsabibin turare
Kwallin mallaka
Zoben mallaka
Jigidar maida tsohuwa yarinya
Maltinar Mata
Karya gado
Yajin Mata (yajin Mai ciko da mace)
Yajin maza (domin Karin k'arfi)
Muna dahuwar Kaya kamar haka💫💥💫💥👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
Dahuwar zabo (mallaka)
Kazar Yar gata
Yan shila
Ciccibi
Dambu
Zuciya
Yan ciki
Kwai ukku
Tsoka Tara
Kifi
Da sauransu
Akwai sirrika sosai da muke hadawa ga wacce kishiya ta addabeta ko wadda take fama da butsarin namiji ko mafadacin namiji ko namiji Mai yawon dare ko Wanda yake bin Mata insha Allah duk zaku samesu Kuma da yardar Allah za'asamu biyan bukata
Muna bada magani ga yarinyar da tsautsayi ya fad'a Mata ta rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar da namiji Kuma insha Allah zaadace da yardar Allah
Abubuwan da yawa gsky Wanda in nace Zan lissafasu sai nakwashi tsawon lokaci maiso tabini PC don ganin kalolin kayan da muke dasu ,
Karku manta mace Mai gyara kanta Bata boranci taku ce maman yusuf Yar mutan sokoto 07069711327
.
Don Allah wadda Bata shirya ba tabari sai ta shirya sannan tayimun magana🙌🏼🙌🏼🙌🏼🙌🏼🙌🏼ngd
07069711327
Pg 62
A haka suka ƙara so wani hadaɗɗen gida mai hawa biyu,yana yin fakin ta fito tana bin gidan da kallo,tsabar yadda gidan ya burgeta yasa bata san sanda ta fara washe fararen haƙoran ta ba,juyowa tayi tana son yi masa magana amma ganin yadda ya haɗe fuska yasa tayi shiru tare da dawowa hankalinta,takawa ya farayi tabi bayanshi abinda ya faru ɗazu yana dawo mata,nan da nan saiga hawaye sun cika idanunta,bata samu damar ƙarewa ran tsetstsan falon kallo ba saboda yanayin da take ciki,hayewa sama yayi ya barta nan tsaye tana fama da hawaye,take wasu tunanika suka fara tsere a zuciyarta,yanzu haka ma haɗa baki sukayi da Taufiƙa shi yasa baice komaiba,kuma gashi yanzu yana ta haɗe mata rai,zama tayi tare da zuba tagumi,zuciyarta cike da tsoran zama da Abdallah,tunda tasan dama can ba wai sone ya haɗa su ba,wata ƙil yana ganin yanzu amfaninta ya ƙare ne shi yasa zai auri matar da yake ganin ta dace dashi,kuka ta fashe dashi mai tsanani tanajin wani irin tafasar zuciya,da zafin ƙaunar da ta riga ta gasgata cewa tanayiwa Oga Abdallah,wanda a da sam bata tsammaci haka ba,kuma idan za a rutsata da wuƙa bazatace ga yadda so yake ba,amma yanzu ta hakikancewa zuciyarta cewa dole ta yadda da zazzafar soyayyar da ta kamata,yanzu ke nan ta zama mai son maso wani kamar yadda takewa Taufiƙa kallo? yanzu reshe ya juye da mujiya kenan?zamewa ƙasan tattausan carpet ɗin dake malale tsakar falon tayi tana cigaba da kukan tausayawa kanta,ji take gaba ɗaya duniyar tayi mata zafi tausayin kanta kuwa sai ratsata yake yi,
Sai da yayi wanka ya fito,kana ya lura fa har yanzu Bintu bata biyoshi ba,ɗan tsaki yayi yana mai jin haushin yadda zuciyarshi ke azabtuwa akan yarinyar da sam bata damu dashiba,shi yana can yana fama da azabar zuciya da rashin sukuni akan ta,ashe ita kuma tana nan tana neman yadda zatayi ta cuso masa wannan baƙar kunamar cikin rayuwarsa, cikin jin haushin abun ya fita,can ya hangota ta maƙure guri ɗaya kamar maijin sanyi,sai kuma yaji wani iri a ransa,sam baya da wani kwarin gwiwa ko karsashi akan ganin Bintu cikin damuwa,hakan na sa yaji duk ya tsani kansa,ko a tarihi bai tambajin makamanciyar ƙaunar sa da Bintu ba,wani irin sone ya shige shi wanda lokaci daya yayi masa mummunan kamu,lumshe idanunsa yayi yana tuna lokacin da ya fara sauraren waƙoƙin soyayya duk saboda Bintu da kuma binciken da yasha akan gane launinso,da yadda yasha fama da bince kafin ya yadda da soyayyar da tayi masa kamun kazar kuku,
A jikinta tajishi, taji irin kallon da yake mata na tsantsar so da tausayi,ɗago kanta tayi a sukwane dan tabbatar da shi ɗinne,kallonshi take idanunta na tsiyayar hawaye,tanajin zuciyarta na bugawa,tare da kuma jin wani rauni na shigarta,ji tayi bazata iya ba,sam bazata iya dakon soyayyar shi ita kaɗai ba,ita macece mai rauni bazata iya jumurin barin zuciyarta cikin halin neman ɗauki ba,tun farko shine me taimaka mata a duk kan abun da ya shafi rayuwarta,dan haka yanzun ma shi zai taimakawa zuciyarta,da wani irin gudu mai haɗe da sassarfa ta isa gareshi,wanda shi kuma take yayi gaggawar yi mata masauƙi acikin faffaɗan ƙirjinshi,a hankali ya shiga sunsuna gashin kanta,yayin da ita kuma take murza fuskarta a ƙirjinshi,cikin wata iriyar murya wadda kana ji kasan tana neman ɗauki ne a cikin soyayya,tace"wayyo,wayyo bazan iya ba,ya Abdallah na gaza zuciyata baƙuwa ce akan wan nan yanayi,ban san komaiba sai asanadinka,ban fahimci komai ba sai a kwanakin na,ban gane manufar bugawar zuciyata akanka ba sai a kwanakin nan,ban gane ma anar damuwar da zuciyata tayi akan ka ba sai a kwanakin nan,ke nan na daɗe ina shan wahalar da na kasa gane kota mece ce,na daɗe ina azabtuwa akan abinda bani da masaniya akan sa,sai yanzu na gane ya Abdallah dan Allah kar ka juyan baya,ka dauka cewa har yanzu Ni marainiya ce,ka dauka cewa har yanzu bani da gata kai kaɗaine gatana mai share hawayen fuskata majinginata,kuma farin cikina!'ɗaga ta yayi ba tare da yace mata komaiba,bai dureta a ko ina ba sai katafaren ɗakin da yake dim ɗim da duhu,sauke ta yayi tare da kunna wutar ɗakin,zaro idanu tayi tana bin kwalliyar da aka ƙawata dakin da ita,wasu jajayen fulawowine a ka yi kwalliya dasu a kowace kusurwar ɗakin,shi kanshi gadon abun kallone,zaunar da ita yayi a gefan gadon kana ya fita,jim kaɗan ya dawo hannun sa ɗauke da wani plat wanda aka wrapin ɗinsa, ajiyewa yayi a kusa da ita kana yayi mata alama da ta sauko,saukowa tayi jikinta a sanyaye har yanzu zuciyarta bata daina bugu ba,ganin bata samu amsa daga ya Abdallah ba,fuskarshi take kalla tamkar zatayi kuka lokacin da taga ya buɗe plat ɗin,wasu irin kaji ne masu maiƙo da kyan kallo kana gani kasan gashin ma na musamman ne,har lokacin bai yi mata magana ba,sai tura mata da ya shiga yi a bakinta,tayi ƙoƙarin kawar da kanta aniyarta na ƙinci amma sai ta hadu da hukuncin kaifafan idanun sa,wanda dole tasa ta buɗe baki ta shiga karba,duk da cewa ba ƙaramin daɗi gashin yayi mata ba amma hakan bai hana ta ci gaba da tsiyayar hawaye ba,yana kallonta bai ce mata komai ba,har sai da yaga tana yin kamar zatayi amai kana ya ƙyaleta,daga nan ya kuma yi mata umarnin bebaye akan taje tayi alwala,haka ta kuma tashi taje tayi wanka ta ɗauro alwala,a kan sallaya ta sameshi,dan haka ta bishi sukayi salla daga nan suka fara nafilfilu wanda har saida ƙafafun Bintu suka fara hajiya,bayan sun idar ya daɗe yana addu'oi,itama ya kama kanta yayi mata addu'a,idanunta ne sukafara lumshewa alamun bacci,ji tayi kawai ya zare hijabin dake jikinta,ɗaukar ta yayi cak ya nufi gadon da yasha shimfidar alfarma da ita,kwantar da ita yayi kana ya janyo igiyar ƙwan dakin ya kashe,sai dakin ya bada wata kala mai kyau,jinshi tayi ya kwanto jikinta tare da yi mata rumfa da